Showing 6001 words to 9000 words out of 25328 words

Chapter 3 - MIJIN KWAILA Book Complete .txt

duka dai d'ayane,to inason magana dakai ga mahaifiyarka can cikin gida don haka kashigo ayita a gabanka ta 'kare."
Gaban isha'q yabuga da 'karfi,idanunshi tuni sun canja launi daga farare zuwa green tsigar jikinshi tabada yarrrr,aranshi yana addu'ar kada Allah yasaka yasake rasa zahra akaro na biyu bayan tadawo gareshi.
Kai yama rantse komai rintsi bazaifa rabu da sanyin idaniyarshi ba,aidukkan mai imanin dayasan tarayyarshi da zahra abaya bazaiga laifinshi don lokaci guda ya mayincema little zahra ba.
Abune mafi tsanani agareshi yakice soyayyar da'aka dasa tun zamanin 'kuruciya yanason zahra yana 'kaunarta yanamata *so d'aya tak*son daya rantse babu mi'ki ko algussu acikinshi.
Jikinshi babu 'karfi yabi bayan abba wanda tuni yakai zaure,
Inbayanga addu'ar samun nasara babu abinda isha'q yakeyi acikin zuciyarshi.
Da sallama ya kunna kai cikin gidan,lokacin yayi dai-dai da fitowar zahra daga band'aki,
Idanunta suka sar'ke dana juna lokaci guda duk rashin kunya da fitsarar zahra taji isha'q yamata wani kwarjini wanda ita atata haukar jitayi ya burgeta don zahra akwaita dason y'an gayu,uwa uba tanadason kwalliya duk da cewarta ita ba'kace amma saitafi su anty hafsa zama y'ar gaye.
Tasauke idanunta cikin na isha'q wanda yamace atsaye yana kallon baiwar gashin dake kan zahra,yatunano tashi zahran batada irin wannan gashin,
Ya runtse idanuwa,yana tasbihi ga Allah wanda ya'kagi kamanni tsakanin zahra dakuma little zahra.
Itama dr.ru'kayya mamakin irin gashin zahra takeyi,lokaci guda taji yarinyar tazaunan daram acikin zuciyarta tabbas soyayyar datake yima marigayiya zahra ce zata koma akan wannan zahran,
Kai itama tana ganin kobada aureba yakamata zahra tazama wani 'bangare daga jikinta,she luv xahra moree.
Isha'q yatako kamar wanda kwai ya fashemawa aciki yazauna kusa da mahaifiyarshi yana gaida umma wadda takafe kyakyawan saurayin da idanu tana dad'a tasbihi ga Allah daya tsara halitta mai tattare da baiwar natsuwa irinta isha'q.
Zahra kam bata saurare suba taja jakarta da hijab tajefa d'aki,
Tadawo kitchen tana neman abincinta hankalinta kwance dukkuwa da sarai tagane isha'q,shine mayen kallonta d'innan idanunshi basamata kyan kallo,saitaji gabanta yana fad'uwa idan tana kallonshi.
Dr, ru'kayya ta kalleta a tausashe tace"zonan d'iyata zahra,
Kamar baki,saiga zahra tataka sif-sif zataje inda dr.rukayya take,
Idanunta suka sar'ke dana isha'q akaro na biyu,
Ta murgud'a mashi baki had'i da jefa mashi harara.
Yasakar mata murmushi,
Abinda ya 'kufulata yasaka tacije baki had'i da girgiza kai.
Saida taje kamar zata wuceshi taje wajen doctor ru'kayya tasaka 'kafarta ta take hannun isha'q wanda yadafa 'kasa dashi.
Yajanye hannun da sauri,yana yarfawa.
Ta kwashe da dariya lokacin data ra'ba jikinta dana dr.ru'kayya tace"yaro kaci gaba da kallona kamanta ranar dana 'kala maka sheri sojoji suka kamaka ko.?"
Tafad'a tana cije le'be da fiddo sexy eyes dinta waje.
Isha'q ya girgiza mata kai alamar kada ta fad'a,
Amma saicewa tayi"tomiye kuma naga kanata girgiza kai,hhhh katuna marin da wannan mai 'katon cikin yayi maka ne.?"
Abba ya daka mata tsawa yace "rufe mana baki,waya tambayeki."
Umma ai kunya bata barta zama wajenba,saita tsiri fura wutar dole.
Dr. Ru'kayya tayi tsam tanason tunano ranar da isha'q yadawo yacemata bashida lafiya dataga fuskarshi da kumburi ta tambayeshi yace mata yafad'ine wajen training.
Ta girgiza kai kawai.
Abba yafara magana"to masha allah isha'q kaine ka aiko mahaifiyarka akan kanason inbaka auren zahra."?
Isha'q ya gyad'a kai kanshi yana 'kasa yana wasa da yatsun hannunshi.
Abba yasaki murmushi nasu na manya yace"to isha'q bazan 'boyemaka ba,bakuma don kunada arzi'ki yasaka zan fad'i ra'ayina akanka ba,wlh kallo d'aya namaka naji nasamu natsuwa dakai.sannan akwai alamar kwarjini da wata baiwa da Allah yamaka wadda dukkan mahalukin daya mallaki hankalin kanshi ya kalleka zaigane kai kamilin mutim ne,"
"Hakane"?
Yajuya yana tambayar umma,wadda ta tsugunna bakin adarkin kitchen,
Umma tace"hakane malam".
Dr. Ru'kayya sai murmushi take anyaba mata d'an lelenta.
Abba yad'orabdafad'in"kaikuwa wacce 'jarabta ce takaika za'kulo zahra amatsayin matar dakakeson aure,nafarko zahra dai yarinya ce 'karama nabiyu zahra bawani kwayon da zaya rud'i mutum gareta ba,illa tulin sumar kai wadda harmun gaji da askewa mun barta taji da abarta.sannan bazan 'boyemaku gaskiya ba,zahra batada kunya ka ganta nan,"
Ya nunata da yatsanshi,
Takuwa zumbure baki tana 'kunkuni.
Dr. Rukayya tace"a'ah zahra d'iyata meyasa kike hakane,abban kikema gunaguni."
Zahra tace"nifa badashi nake ba,"
Umma ta 'amshe to anan ciki waye tsarar wasanki dawa kike"
Ta nuna isha'q da yatsa,tana sake turo baki"bashine yaketa kallonaba,kuma wai har yana runtse idonshi d'aya,(kashe ido)
Kunya kamar ta kashe isha'q haka yaji.
Dr.ru'kayya maka mashi mafecin dake hannunta tayi dacewa"tashi maza kabar nan,mara ta idanu kawai."
Yakoyi 'kememe abinshi baiko motsaba.
Abba yad'ora dafad'in"to agaskiyar zance nikam bantashi yima zahra aureba,donkuwa dukkanin yayunta babu wacce na aurar batare da ta samu sakamakon takardar n.c.e ba,don haka idan nace zanyima zahra aure awannan lokacin na zalunceta nakuma shiga hakkinta duk da bawai musuluncine ya hana aurar da yarinya tana shekaru sha biyu ba,hasalima shekara tara musulunci ya yarda ka aurar da yarinyarka,amma yanzu zamani ya canja akwai cutuka da dama da ada bamudasu sai yanzu,sannan zahra bawai wayone ya iaheta ba,bayaga rashin ha'kurinta tanada mugun surutu dakuma su'butar baki.
Amma nayi maka al'kawarin muddin zahra ta girma tace tana sonka zan aura maka ita,wannan shine kawai maganata."
Dr. Rukayya ta kalli isha'q wanda idanunshi suka kad'a sulayi jajur,
Tace "tokaji da kunnuwanka abinda abba yace,saikayi hakurin zahra ta girma kusan shelaru goma nan gaba 'kila."
Hawayen dayake 'kokarin ri'kewa tuni sun 'balle,babu kunya ya ri'ke kafafun abba yana ro'konshi"abba don girman Allah kada ka nisantani da zahra abba,ka tausayamun soyayyata da zahra *had'in Allah*ne,bana nufin cutar da rayuwarta har abada pls abba."
Duk da taurin zuciyar abba saida yaji tausayin isha'q amma kuma donme ze tauye rayuwar zahra.
Umma jitayi bazata iya kallon hawayen isha'q ba,saita shige d'aki abinta.dama ita nata biyayya duk abinda abba yatsara awajenta yagama tsaruwa.
Dr.ru'kayya ta kalli isha'q daya kasa dena fitar da hawaye tace"kajiramu awaje inazuwa."
Yatashi ya fita,yana sake waigen zahra wadda dukkan jikinta yayi sanyi 'kalau tana kallon isha'q badai tagane akan me suke tattaunawa ba.
Dr. Rukayya tasake rusunama abba tace"nagode da kyautar dakayima d'ana amma na ro'keka daka taimaki rayuwarshi,don Allah kada kayi fancakali da lafiyar damuke tarairaya tashi,natabbata isha'q zai rike zahra amana,
Wlh namaka rantsuwa babu wani abu na ga me da auratayya dazai shiga tsakanin isha'q da zahra harsai takai munzalin hakan,
Sannan karatu konan da inane zan tsayama zahra tayishi,inada yarinya bazata shige tsarar zahranba atare zan renesu don dukansu y'ay'a nane."
Ta tsagaita tanason jin amsar da abba zai bata.
Nima natafi break
September 26, 2016 at 10:43pm · Public
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀


BY MAMAN MEENAT




EDITED BY AISHA ABDULLAHI (UMMUN FAROUQ)




Chapter 8.




Tad'anyi jim tanason jin amsar da abba zai Bataan .


Abba yasake gyaran murya gami da tofar da wayu gefe,yana sakace ha'kori da asuwaki yace"nifa hajiya kindai gaza fahimtata ne,amma tayaya zan baku auren yarinya haka kawai nifa bansanku ba,nadai ganku ne kawai gaskiya abune mai wahalar gaske hakan."


Dr. Ru'kayya taja numfashi"malam mu bawasu 'boyayyu bane a garinnan,mijina sunanshi alhaji saifullahi mai rid'i yana sana'ar kai rid'i turkey yanada shagon gold anan abubakar gumi."


Abba ya kafeta da idanuwa kafin yasaki dariya dace"Allahu akbar azzawa jallah gwanin hikima,dama ku iyalan alh saifullahine,mutuminane kai mutum na gari.bazan ta'ba manta alkairinshi gareni ba."


Yanuna umma data le'ko daga d'aki tana murmushi yace"gata kinganta nan haihuwarta ta farko kamar bazatayi ba,banida sisi a aljihuna banida kadarar sayarwa aka tsawwala mana kudin yimata tiyata dubu tamanin nad'aga gidan danake ciki zan sayar bawan Allah yaganni a asibiti ina kuka yake tambayar meya faru,na sanar mashi wlh hajiya atake ya shiga ofis din likita yarubuta mashi kudin a takaddar banki,yace ayi gaugawar ceto rayuwar saudatu.kuma yace nabishi ofis dinshi,bayan yabani takarda ta address naje shine yabani dubu d'ari nafara sarin bulawus ina kaiwa kasuwa da wannan sana'ar Allah ya d'aukakeni gashi ina cikin rufin asiri har yanzu."


Dr. Ru'kayya tasaki
lallausan murmushi tasan mijinta yafi dahaka kaf halinshi isha'q ya d'auko.


Abba yadinga mamaki itama umma saida tasake yima Dr Rukayya godiya,
Abba ya 'kwalama zahra kira yace maza kice 'bakonnan na waje yazo yanzu yashigo ciki.


Tafita kai bako d'an kwali tahangoshi yajingina bayanshi a mota yayi lamo Allah kadai yasan abinda yake tunawa.


Ta dage iyakar 'karfinta tace"kai mai motar nan,kai mayen kallon mutane kazo ana kira."


Isha'q yaji gabanshi yasake bugawa yace "ina zuwa,tajuya zata shige gida,
Yace"jirani mana."
Tawaigo tana 'kare mashi kallo saikuma tabuga zani da murgud'a d'uwawu"sumbuqa sagwaigwai takashin mage da barima hada sarqa a gabanta",
Isha'q yadafe kai "oh Allah zahra kam anya tanada cikakkiyar lafiya kuwa?"
Ita komai nata sai tasaka wauta da shirme.
Ya ta'be baki dacewa "aini nace naji nagani."
Yashigo da sallama yasamu waje ya zauna,
Abba yasaki murmushi dacewa"taso kadawo kusa dani d'ana isha'q. "
Isha'q yakoma jikin abba yana du'kar dakai.


Abba yace"isha'q kadaiga wacece zahra,amma ahakan kace kaji kuma ka gani ko.?"
Isha'q yace "hakane abba agaba duka wannan zata dena aikowa da tashi 'kuruciyar."
Abba ya gyad'a kai yace"kuzama sheda ni malam adamu jafar nabama isha'q saifullahi auren d'iyata zahra ko bayan babu raina."
Wata zabura isha'q yayi dacewar "Allah abba gaskene kabani zahra,bakuma mafarkin dana saba yi bane.?"
Abba yace"ba mafarki kakeyiba isha'q idan mahaifinka yadawo daga tafiyar dayayi za'a tsaida lokacin biki,kafinnan zakaji sharad'ina daga bakin mahaifiyarka."
Dr. Ru'kayya baki har kunne take zuba godiya gasu abba da umma.
Takamo zahra wacce takoma gefe tana y'ar 'kwado tace"zo d'iyata zahra kina sona,zaki zauna wajena?".
Zahra tayi jimm kafin tace"indai kinsan gidanku akwai bene tozan zauna indinga shan dad'in bene."
Dr. Ru'kayya tasaki dariya dacewa "kema d'akinko akan bene yake ma."
Zahra dad'i yac tace"indai da gaske kike tokice kwarakwatsi",
Umma tace "au zaki fara shirmen naki kenan,"
Dr. Ru'kayya dari take sosai dacewar "zahra koban rantseba bazan maki 'karya ai."
Tazuge jakarta tafiddo rafar y'an hamsin-hamsin tami'kama zahra"karbi kisaya sweet kinji d'iyata zahra,aibanzata 'karama bace dana siyo maki ice-cream."
Zahra ta kalli kud'in gami da zaro idanu tace"nidai banaso,ki'aje kud'inki bene kawai nakeso kihau dani,indingayin sululu."
Mamaki yacika dr.ru'kayya aranta tana riyawa ashe duk wautar zahra tanada tarbiyya?
Lallai zasuji dad'in zama da'ita lokacin da 'kuruciya ta barta.
Babu yanda batayi da zahraba,amma 'kememe ta'ki karbar kud'in dole ta mayar a jaka.
Tanamasu umma godiya dacewar zata aikoma zahra da sweet tunda ta'ki karbar kudin.
Har zaure umma tarakata itakuwa tari'ke hannun zahra tace taje taraka mota.
Sunfito bakin lungun isha'q yana bud'e mota,idanun zahra yasauka akan jabiru wanda jiya ya 'kalamata sheri wai taje kwad'ai gidansu ummilolo,
Bata tsaya tabi takan dr.ru'kayya ba,tafincike taruga da gudu tayi wajen jabiru wanda ya d'auko ni'kan gari akai.
Tana zuwa ta hankad'ashi garin ya zube a kwata,sannan ta cukumi rigar jabiru tafara 'kuli-'kulin kubura dashi Dr.ru'kayya tana daga nesa ta hango yara harsun fara zagayesu suna wa'kar"bamu rabawa sai dai mu'kara zigawa bugi cikin."
Subhanallah cewar dr.rukayya wadda tuni tanufi inda zahra take dambacewa,
Dasauri tarike hannu zahra wadda take yayyafa ruwan bala'i,
Jin anri'ke hannunta yasaka batare data waigo ba tace "wlh kowaye yasakeni inba hakaba najuyo saina yima mutum wanka da ruwan kwatar nan,
Dr. Ru'kayya tace"oh oh zahra haka kike ashe.
Zahra tawaigo suka had'a idanu da Dr Rukayya,
Tace"shinefa jiya wai yace naje gidansu ummilolo naci garin kwaki,alhalin karya yakeyi ni aigidanmu anmafi cin dad'i abbanmu kullum da dare yanama siyomana kifi itakuma umma saitayi wanka taje can d'akin abban mu har....."
Dr. Ru'kayya tace "ya'isa zahra nasan kunacin dad'i ai,amma kiyi hakuri bakiga kin sakashi kukaba."?
Tace"aima wlh danban shillirashi nayi mashi fad'an y'an chanis ba,dasaikinga nafasa mashi baki.
Rannan ma damukayi fad'a da hinde saida nakusa 'kwa'kulo mata kunne,itakuma irin fad'an sharuhkan nayi mata."
Dr. Ru'kayya ta jinjina kai tana kallon isha'q wanda yayi tsuru,baiso mummy tagane halin zahra yanzu ba.
Yasanta dasakama ranta damuwa dayawa,
Tajuya ga zahra dake cema yaron"yaro zan kamaka,zamuje lungun bata kashi saina gurje maka baki da kashin kaji ha'koranka sun zube,banza latas karas kabeji masu kwana abakin titi d'an kabewa mai..."enough pls."
Dr. Ru'kayya tafad'a ranta a'bace"kewai waccce irin yarinyace,ahaka kikeson inje dake gidan bene kina dakarmun d'iyan ma'kota.tonikam ba'a haka dani,idan bazaki sake haliba lallai zan 'bata dake sam banason masifa kin ganni nan."
Zahra tayi tsit,sannan tace"nadena ai."
Dr. Ru'kayya tayi murmushi dacewa "gud girl"
Tashafi gashin kanta,
Tayima yara y'an kallo tsawa kowa ya kama gabanshi.
Itama mota tashige tana d'agama zahra hannu,lokacin gaf da magrib.
Motarsu na 'bacewa zahra ta hango su ummilolo da sauran 'kawayenta,taje suka kashe "tace yara albishirinku?"
Duka suka kasa kunne dacewa"goro fari 'kal"
Tarage murya sosai"amanatun amana wa'azabatun azaba,idan kuka tona taciku,kun yarda?"
Duk sukayi tsuru,
Tace "inbaku yardaba shikenan."
Sukace "munyarda zahra,"
Zahra ta tafa hannaye dacewa"yara kuka gayama wani saina dirji baki ehe."
"amanatun lauratun 'kwan kiyashi,yara ankusa yimun aure.
Duk suka zaro idanu waje suna kallonta sun sandai 'karya ba halin zahra bace,don sam tsage gaskiya take komai d'acinta.
Ummilolo tayi karfin halin cewa"mai 'karya"
Zahra ta'amsa da "d'an wuta abishi da duka har wuta lantarkin babalo da an kyasta sai wuta."
Duk suka ce"yeeeee dagaskene.
Nanfa aka zauna ana labarin aure,ummilolo tace "tab ashe zahra ke zaki dinga dafa abinci kiyita ci dayawa cikinko yayi 'kullumeme saimuga zahra ta haihu."
Sauran yara suka kwashe da dariya,
Zahra ido ya raina fata tace"ai sai in'ki cin abincin,inyita shan ruwa kawai."
Uwande tad'an fisu wayewa tace"kai wlh ance bacin abinci kesa mutum ya haihu ba."
Duk suka zaro idanu sukace "to menene"?
Tace inkun yarda amana,
Sukace sun yarda.
Tace"wlh yara idan kuka yarda namiji ya ri'ke maku hannu ya luliya tafin hannunku saikuga ciki yafito 'katoto,"
Zahra data gama tsorata tace"lalalala aikuwa Allah yasoni ban wasa da maza."
Daga nan aka rufe cafta,akace atafi satar kifi,wajen y'an kifi.
Haka kuwa akayi xahrace gaba sungama tsara plane na yanda zasu saci kifi,
Suna zuwa saitin wani mai kifi yakasa a faranti yana tsaye gaban kifinshi,
Zahra nazuwa wajen saitin kifin ta yanke jiki tafad'a akan farantin kifi,
Sauran yaran duk sukayi fuskar tausayi"wayyo zahra sannu,"
Mai kifi ma fad'i yake subhanallahi sannu yarinya.
Zahra ta bala riga akan kifi ta dumbuji uku,
Sannan tari'ke ciki"wayyo cikina ummilolo zoki tadani.
Ummilolo itace mai hijabi,dan haka tana zuwa zahra ta 'kunsa mata kifin a hannu,
Tasaka ariga,
Suka mi'ke suna kakka'be jiki zahra na d'angyashi.
Kamar ance maikifi ya kalli kashin kifinshi yaga anyimashi rani,
Yabisu aguje yana 'kwala masu kira,
Sukuwa 'kafa menaci ban bakiba,
Tuni sun sata.
Maikifi saida yayi Allah ya'isa saboda balagaggun kifayen suka d'auke,gashi ranar ba ciniki.
Awani lungu suka ma'kale zahra ta'amshe kifin ta finfincinar masu,tana la'kume sauran.
Uwande ta kalli d'an nata,taga na ummilolo yaninka nata biyu,tace"gaskiya anyi son kai,na ummilolo dayawa namu kad'an".
Zahra takaima bakin duka tana harararta"sannu mara gode Allah,da kud'in babanku aka saya kifinne,"?
Uwande tayi gum tana mamular kifin da aka bata kai da bindi.
Nan sukayi gaba,
Dai-dai kwalbatin y'an ganda suka hango wata budurwa da saurayi ana tafe ana rangaji suna gogar kafad'un juna,
Ummilolo ce tafara gani ta lakaci zahra,duk suka ware idanuwa suna mamaki.
Zahra tace"aje ajanye gyalen tsinanniya,"
Nanfa kowa tacire takalmi suka ma'kala a jijiyar hannayensu,suka d'age zani sama.
Saida budurwanan tazo saitin majalisar masu ganda,zahra tayi wuf ta fizge gyalen dake kafad'ar budurwar,
Suka auna aguje,budurwar tarasa yazatayi,ta waiga dacewa"honey dallah kabisu ka'amso man gyalena,kaga kayan jikin rabin 'kirjina duk awaje yake."
Saurayin yace"tabd'i,sarai nagane yarannan masu gudu kamar barewa,nida rannan gaban idanuwana suka janyema wata budurwa zani,yaseen da rarrafe tashige gida,camon ki kare wajen kawai mutafi asfa gayu d'innan kingane ai "
Ran budurwar ya 'baci kawai saita tsugunna ta fashe da kuka,
Me mutane zasuyi banda dariya da ihu...
*Nima nadara,nabi bayan zahra balbali zahra bala'i ta'ba d'aya kaga goma*


KUNA TARE DA MAMAN MEENAT, INSHA ALLAH
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀


BY MAMAN MEENAT


EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN FAROUQ, HYDR)


Muna miqa saqon ta' axiyan Hamma umar Allah ya jiqan shi yayi mishi rahma yasa mutuwa ta xama hutu a garesh, muma in tamu taxo Allah kasa muyi mutuwar shahada)








Chapter9.




Daga wajen tonon fad'a su zahra basic zame ko'inaba sai gida,saboda lokacin tuni angama sallar magirb,
Da sand'a tale'ka cikin gidan tace "inshigo'"
Umma dake ninke kayan da abba yacire dazu ta harareta dacewar "dawwama anan,har mahadi ya bayya,"
zahra taahigo kanta tsaye,tad'auki buta tafara alwalar magrib umma bata tankataba.
****************
Hadadd'en saurayin dake sanye cikin 'kananun kayan riga shirt dakuma wandon jeans kirar kamfanin Gucci,akwai kwatsetsen takalmin kafarshi mai shegiyar tsada gordon rush,
Face dinshi manne da space na Prada,watch na hannunshi dolce jikinshi manne da mayen turaren American crew.
Sumar kannan nashi ka rantse na macene saboda gyara da kula kai infarct isha'q 'karshene akan tafin hannayenshi kawai yakan kashen kud'i masu yawa,ha'koranshi kuwa akoda yaushe suna walwali da daukar idanu saboda time daya ware musamman domin su yakan je wajen wankin hakora lokaci zuwa lokaci.
Hatta da tafin kafar isha'q baya barinta face ya tsaftaceta da mayukan dake tsaftace 'kafa dasakata taushi.
Yanda yake wana steering kadai abin kallone,duk inda ya gifta mutane kan bishi da idanu musamman motar dayake tu'kawa new modern ce kirar mazda mx-miat abin saiya bada wani styles na daban.
Adai-dai kofar gidan sadiq ya matsa horn mai. gadin yale'ko dakai lokaci guda ya wangale get din yanama isha'q barka da zuwa,
Yafaka mota inda aka tanada don hakan,lokaci guda yazaro wallet d'in dake manne abayan aljihun jeans dinshi,yafiddo 2thousand yamikawa mai gadin,baijira sauraren godiyar damai gadin keyiba yayi gaba abinshi yana wana keys na motarshi.
Dai dai shiga harabar gidan yahad'u da hindu matar sadi'q da tsohon cikinta tana ganinshi tasaki murmushi"yau makuwa kayine isha'q yau agidan,"
Yasaki simple smile nashi kafin yace"yakike ya jiki kuma."
Tayi gaba tashige falo tana fad'in"banacin mi'ke,"
Bayanta yabi ya nitse cikin manyan kujerun dasuka zagaye falon yadauki remote yana canja channel daga Bollywood zuwa dstv yana searching 'kwallo,
Hindu tuni tacika gabanshi da kayan sanyi tasani yafi shan hollandia ko malt sune best drinks nashi.
Ya fincine hancin malt na gongoni yana zubawa a glass cup yana tambayar"ina mutumina ne."?
"yana jinka yanzu zaka ganshi yafito wankane yana shiryawa."
Isha'q yad'an dara,dacewa kice nazo asa'a dama tad'i zai rakani."
Idanu hindu ta fiddo waje"to gaskiya bari yafita ba,haka kawai wata budurwar ta kwaceman shi."
Tafad'a tana turo baki da alamar fushi.
Isha'q dariya sosai yakeyi yanacewa"aigara kishirya don mutumina hudu zaiyi,"
Maganar sadiq ta katseshi"a'a banganeba,wato kai ka'ki aure shine zakazo ka 'killen dannawa auren ko,"
Yafad'a yana dariya lokaci guda yana zaunawa kan hannun kujerar da isha'q yake kai.
Yami'kama isha'q hannu suka tafa duk suna dariya
Isha'q yace albishir fa nazo inyi maka,
Duk suka bishi da idanu sunason jin abinda zai fada masu,
Yasake kora maltina yana kallon sadiq wanda ya tsareshi da idanu,
"anbani zahra abokina,daga yau nakoma angon zahra "
Wata zabura hindu tayi"nice to hear isha'q seriously pls dagaske kasamu zahra?"
Isha'q ya saki dariya lokacin da sadiq yakai mashi duka yana fad'in abokina bakada mutunci wlh,wato saida ka rikita masu yarinya da salon wankanka ko?"
Amma duka sati biyu da had'uwa ace har anbaka saikace kaza,koda yake nasanka gwanin iya sarrafa soyayya but natayaka murna sosai abokina aikawai daga wannan wankan muwuce inga amaryar nan."
Hinduma fad'i take "nayi murna isha'q kaga nasamu 'kawa,"
Isha'q ya sauke numfashi.
Headache wlh typin din bayamun dad'i kuyi hakuri pls,
Tun d'azu nakeson typing amma kaina yana matsamun dafatan zaku gafarceni.


Kuna tare da maman meenat, Aisha T.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login