Showing 1 words to 3000 words out of 23135 words

Chapter 1 - GIDAN MAGAJIYA by oum yasmeen Book 1.txt

06 Nov 2024

4334

GIDAN MAGAJIYA


Perfectly pen's


Episode 1


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


Unguwar kofar mata dake kwaryar birnin kano


Hadarine ya haɗo ta gabas gari yayi wani irin duhu ga iska na kaɗawa amma duk da hadarin nan magajiya ita da maƙarrabanta ko a jikin su wai an tsikari kakkausa suyar wainarta take gefenta dinana ne zaune yayi zaman dirshan a ƙasa sai aikin rubutu yakai




ture kaga tsiyarta ta gyara ta juya wainar'ta ta dubi dinana tace




"Dinana wai lafiya tun da ka shigo gidan nan kake ta aikin rubutu wannan ai takardar kampo ce me za kai da ita......?,




dariya ya sheƙe da ita ya ɗaga paper nan wacce take cike tab da rubutun chaina yace






"Uwar shagalallu wannan wasiƙa nake wa mara yar gidan honourable jiya ta yomin wasika cike tab da turanci kin ganta nan ya ciro takarda a aljihunsa ya ci gaba da cewa


shine nake bata amsa da chainanci tun da nasan kaf gidan nan in bake ba ba me iya fassaramin wannan turancin ke ma wallahi wannan turancin yayi miki tsauri......,




gabaki ɗayan su suka sa dariya ban magaji da ta haɗa rai sai ban kawa dinana harara take tace




"Dinana fitar min daga gida tun da abin naka rashin mutunci ne ina laifin ka tsaya iya kanka sai ka haɗo har da ni....,




abin juya waina ya dauka ya kwashe mata ganin tana shirin konewa yace






"to yar hau kina masifa wainar tana kokarin konewa.....,


fakar idonta yayi ya gutsire gefe kasa kasa yace






yar masara ina tare da ke kullum hayaki ba faɗeni ko rabin fafe ba zaki iya ban ba to bara inci ta haram


Ahayyye rasss wani ɗan daudo ya shigo yana wata iriyar rausaya da sauri kahu bulama ya fito da hannu ya nuna mai hanna yace






"Maza koma inda ka fito wallahi ba zan yarda da wannan iskancin a gidan nan ba.....,




rataya jakarsa yayi ya kama haɓa yayi wani fari da idanuwansa yace






"Kahu wa yake wallahi ina bakin ka gurin magaji nake zuwa ba gun Ka ba cin arziki ya kawo ni ato.....,




da sauri ya yo kansa matsawa yayi yace




"auzubillahi me zan gani shi yasa masifo sukai mana yawa ina mace kana ƙoƙarin taɓani innalillahi magajiya....,




sororo kahu bulama yayi magajiya ce ta taso gyara zanin da ta ɗora akan doguwar rigar ta tayi sai taunar chingum take ƙwai ta saki ya bada wani sauti ƙasss ƙas tusssh tace






"ki rabi ba ruwan ki wannan fa kahuna ne kai kahu ba ruwan ka da rabi ciniki tazo tai min a unguwar nan ba akwai masu sai da waina ba amma ta tsallake ko ina ta zo guna gaskiya kahu ka dinga jan girman ka.... kullum sai kai faɗa da wa'yanda suke zuwa guna....,




Zani rabi ya bankaɗe yace




ato faɗa mai kullum yana mana kallon hadarin kaji gurin wasu yan mata dake kan tabarma suna hura taba suna caca ya zauna yana taunar chingum




babbar rigar'sa ya gyara yace




"to nace ba ....dan Allah zan sami wannan wainar sai ki ci gaba lissafi duk ranar da muka koma Maiduguri lokacin da komai ya lafa sai in biya ki..akwai huluna na dana saka mantawa nayi ban dauko suba lokacin da muka tawo gudun hijira garin nan zan in siyar in baki bashin ki.....,






da sauri ta kallesa tace






"Kahu...,


Na'am magajiyar ya'yan Allah ya shirya




Kahu.......kahu




hularsa ya gyara yawa an kifa lotsassiyar tasa yace






"Magajiyar karuwai ina jinki....,




cikin hausarta mara fita tace






"wallahi kahu ai kafin ta ƙarasa yace




"Haba yar gidan faɗimatu dan Allah temaka min.....,






kai dai wallahi malam Allah ya shirye ka me zanyi da abin da ya fito daga hannun yan daudo da karuwai da yan sane wata mata ta fito tana masifa






jin dan shin huka tayi a huyanta jiyowa zata yi taji waya sa mata huku ji tayi ance






Kina jiyowa sai na burburma miki huƙa a hanci ta huce ta maƙoshin ki magajiyar kike faɗawa haka yana wani cije baki alamar rikakkan ɗan daban




Wata uwar buɗa magajiya ta saki tace




Manjagara sauke huƙarnan wallahi nasan in har ina tare da ku bani da sauran damuwa maza sauke'ta kallonta yayi yace






"Magajiya da kin barni da yar hau wallahi in ci kutumar....ubanta la'ada waje yasin.....,




Manjagara nace ka sauke ta nace




sauke'ta yayi tace






"Innna gobe ma in halinki ne ki ƙara tana faɗar haka ta koma ta zauna


Kahu bulama da yake tsaye a ransa kuwa wani irin takaici ne ya kama shi daman magajiya ce ta ɓata ba yar uwar'sa ba da ya huta da wannan tashin hankali da magajiya ke sa shi kullum ba shi da nutsuwa yan iska fal a gidan wannan gidan shine gida na goma sha biyu da suka kama dan ma ita ke biyan kuɗi ko wanne gida kuɗin su baya ƙarewa ake tashin su duk saboda magajiya




Wata me kama da kilaki ce ta shigo ta saki uwar buɗa tace






"Kaga magajiyar ya'yan haram an buga dake an barki maƙiyan ki fadawan ki kin ci dubu sai ce to wallahi ke zamani ce dole a tafi dake.....,






kai ta dinga rausayawa dinana yayi karab yace






gama kirarin ki sai kin biya za kice waiiina ato bama bada bashi






mayafin'ta da ta aza a kafaɗa tace






"To me matatciyar zuciya ka zauna a katarar mace sai dai taci ta rage maka....,




Dariya ya saki yace




"Ai arziki wani yayi yaga in zai ci riba sai de ya kare a hisba...cin bashin ki yayi yawa...,




wani kallo take mai tace






"uhmm wato rashin mutuncin ka har ya kai haka ka dube ni nayi maka kama da wacce zan ci bashi never wallahi.....,






tashi yayi yace






"to tsohuwar kilaki waya faɗa miki yanzu ana yayin irin ku ki bari masi jini a jika suyi irin su saudat me idon nera....,




tashi saudat tayi tana wata rausaya ta juya kugu ta liƙi ta shiga yiwa dinana tace






"Yanzu duniyar bala ja'u mu take yayi wallahi ba wata tsohuwa ba....,






Ai kafin ka ce me fada ya kaure an shiga bawa hamta iska botiki rabi ya ɗauka yana rawa yana cewa






Kutaso babban ku taso kai ku tasu ba me raba ku a zamanin nan na yanzu




Cikin kunar rai magajiya tace.....✍️






Kuyi following ɗina dan samin ci gaba kullum zan dinga yi muku update






GIDAN MAGAJIYA




EPISODE 2


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


Na shiga uku so kuke wannan gidan ma a kore ni to wallahi ba zan lamincin wannan iskancin ba kai Rabiu ga hanya nan ka koma inda ka fito......ke sauda zo ki fita.....,






Rabi'u gatsal ya kike neme ki sani jinsin rijalu gaskiya ba ki min adalci ba






Kahu bulama da yake gefe yayi garaf yace






"ai wallahi ina gab da kai ka hisba daman irin ku suke kamawa....,






Ayyiriiiyi ya saki buɗa ya baga cinya yace


"yanzu in ka ɗabe mu ya zaku ku maza ai wallahi namiji sai da nisa'u....,




sakar baki kahu bulama yayi yace






"Ina neman tsari da wannan bak'ar ƙaddarar.....ni da auran jinsin na....,






harda kafa yayi ya gyara ɗaurin kansa yace




"to mene aci wannan abu na headquarter kana da babba ina da socket....,






RABI'U magajiya ta faɗa da karfi tace






"Wallahi nagaji da iskancin da kuke min...,




yarfa hannuwa yayi yace




"Allah ya baki hakuri nayi nan ya nemi guri ya zauna sauda ma neman guri tayi ta zauna.....,






ganin sun dena fadan ta koma ta zauna ido hudu tayi da dinana ya zage sai ci mata waina yake karkata ɗauri tayi tace




"wallahi ka gama ci ka biya ni kuɗina ko ficika baza suyi ciwo ba ta koma ta zauna zare ido ya fara domin ko kobo bashi da ita




dariya hindu ta daki tace




"Alhamdullahi mu da akewa kallon hadarin kaza za mu iya ci da kan mu....,




Nawa ne kuɗin wainar da ya ci miki




Cewar sauda




ba tare da magajiya ta dube'ta ba tace




"₦500...,




zaro kuɗin tayi tace


"Dinana nawaje na zo ka amsa....,




Au kai zuwa zakai ka amsa ko da yake zuciya ta mutu.... Hindu ta fadi haka tana shekewa da dariya




Be ce mata ƙala ba ya shige ya amsa to yar bala'i ga shinan kin so ki kunya'ta ni ina tare da ke ana ce min me yiwa mace aiki




fisga magajiya tayi ta tura mai ragowar ta ci gaba da yin wainar ta






***********ASOKORO
Villa Toscana Restaurant Plot 73, Usuma Street, Off Gana Street






Tissue ta yaga ta goge gefe da gefen baƙin ta tace






"zee kin tabbata A.k yana zowa gun nan...,




ɗagowa tayi ta janyo glasses ɗin ta ajiye wayar'ta tayi akan table ɗin da tace




"ni da na ganshi ido da ido....kinsan dai fuskar'sa ba boyayyi bace musamman wanda yake social media....,






ajiyar zuciya ta sauke tace




"Allah isa yau yazo yau ita ce damata ta ƙarshe gobe zan bar abuja na koma Sokoto...,




wasu samarine su biyu suka shigo cikin restaurant ɗin sanye da riga blue da wando baƙi ajikin rigar an rubuta


*A.K SARDAUNA CONTRACTION COMPANY* da sauri wannan matashiyar ta tashi sanye take da fitted gown ta ɗan yafa shantili a kafaɗar ta sai taunar cingum take kafin ta isa gere su tuni sun shiga wani guri cikin sauri ta dubi zee tace






"Zee wayan nan daga gani ma'aikatan sane ko za mu sami wani information akan'sa.....muje gun su....,




girgiza kai zee tayi ta riƙo hannunta tace




"Wallahi nabeelah kar ki gigin zuwa gunsu kin san wane kuwa A.K Sardauna....? a yanzu shine shugaban DASS fa ni wallahi bansan me isa kike neman saba kar ki jajamin gidan da nazo cin arziki su koreni.....,




kallon'ta tayi tace




"Ke wallahi kin fiye tsoro wata kila ma kiga yana da sauƙin kai....,






dariya zee ta saki tace




"Haba kawata mutum kamar'sa kiyi tunanin zaki same shi cikin sauki canza wannan tunanin.....,




takardar bill ɗin abin da suka ci aka ajiye musu saurin zaro ido nabeela tayi tace




"Zee wannan ɗan abin da muka ci 12k....,




da sauri ta ɗauki jaddawalin suna nayan abin da suka ci farin gani tayi Grilled Chicken with Roasted Vegetable₦12,000 tace






"Wallahi haka yake ni dake 24k....,




Gumi ne ya shiga tsassafo mata ta ko ina 20k ne a jakarta kuɗin da take saka ran da so zata tafi gida zee CE tayi ƙarfin halin cewa




Bara in kira excellency dan gwamna ko zai biya mana dan ni wallahi bani da ko ficika




jikin'ta yayi sanyi ta ja kujera ta zauna fake live ba tayi ba wayar'ta ce tayi ƙara dakyar take iya ɗaga hannun ta ɗauki wayar video da tasa a tiktok ne mutane suna ta yi mata liking......




Cikin contact ɗinta ta shiga neman number dan gwamna cikin sa'a ta sami number bugu ɗaya ya ɗauka kashe muryata tayi tace




"Hello baby.....wallahi nayi missing ɗin ka...,




da sauri ya diro daga kan matatciyar katifar sa yace




"Allah ko baby...,


Wallahi baby kana ina.....,




dan jim yayi sannan yace


"Wallahi ina guarding...wallahi na fito shan iska...,




Okay dan Allah ko zaka zo Villa Toscana Restaurant ne




zaro ido yayi me zai kawo shi gurin masu fada aji yana Kaduna me zai kawo shi abuja besan kowa ba amma sai ya mazai yace






"Okay am dazu daddy na yayi min Magana zan raka shi wani guri wallahi da nazo kinsan tun da na haɗu dake a tiktok wallahi naji kin min....,




okay na gode ta faɗa a sanyaye ta kashe wayar ta duban nabeela tayi tace




"Nabeela ba abin yi fa garan da na haɗu da shi jiya a tiktok yace min shi ɗan Abuja ne a maitama yake ki nemo wata mafitar....,




suna haka sai ga wa'yannan samari sun fito hannunsu riƙe da ledojin an rubuta sunan restaurant ɗin da sauri samir ya tsaya yace


Manage bara na koma ciki naman ta fadeela sectary tayi min sautin ice-cream da bara ce ta faɗowa nabeelah ta tashi tace.....✍️




*Oum yasmeen*




_Ayi hakuri yau ba yawa_




GIDAN MAGAJIYA


EPISODE 3




https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k




Masu tambayar complete na Wannan littafin ban gama ba typing nake...




da sauri zee ta riƙo ta ƙasa ƙasa tace




"Nabeela me kike shirin yi...?,


hannunta ta bige tace




"Kina da wata mafitar ne ni Wallahi 20k CE a jikin account ɗina kuma da ita zan koma gida...,




ta gumi zee tayi tace




"Nabeela wata kilama wasu sun som fuskokin mu kina ganin wannan ba zubewar mutunci bane kamar mu celebrity muna neman temako....ki yi tunani...,


kai nabeela ta shiga girgiza mata tace




"Zee bamu da wata mafita sama da wannan kina ganin wayan nan jajayan fatar sun san hakuri....ko sun san babu...?,




kai zee ta dafa da yake sara mata tace




"Allah ya fitar damu...,




banza tayi mata mayafinta ta gyara cikin sa'a kuwa sai ga su sun dawo tace




"Assalamu alaikum...,


AYMAN da yake danna waya ya amsa fuskar nan ba walwala domin ya tsani mata marasa kamun kai daga ganin'su basai an faɗa maka ba su waye su cije lips ɗin ta na ƙasa tayi cikin takaicin halin da Ak ya sata aciki tace




"Dan Allah bayin Allah temako nake nema....,




da sauri ya ɗago ya kare mata kallo a nan gurin ake neman temako tab Allah me iko haka ya raya a zuciyar sa yace




"Allah isa zan iya...,




Kaga mu ba yannan garin bane mun manta jakar mu a tesxi kuma ita ce jakar kuɗin mu sai da muka gaba cin abinci muka ga babu gashi ba muriƙe number din me tesxi ɗin ba


Okay na nawa ne....?,




Hamdala tayi tace




"24k....,




juya wa yayi ba tare da yayi magana ba gani tayi yana nunowa baturan dan ƙasar Italian su ATM card ɗinsa ya bayar aka cira kuɗi




da sauri ta bishi za tayi mai godiya suka shiga mota suka tayar tsaki taja ta koma tace




"Sai ki taso mu tafi dan baƙara ba....,






dariya zee ta saki tace


"haba Nabeela Sokoto gobe ma mu dawo wallahi sun iya girki ke kinji kuwa kazar nan....ji nayi kunne na kamar ya cire....,






dariya ta saki ta rataya jakarta tace


"Da sun kira mana security da kinyi bayani a bayan kanta wallahi...,




itama dariya tayi ta rataya jakarta daman ba ta fito da mayafi ba suka fito titi zee tace






"Nabeelah sokoto yanxu ina muka nufa....,




dan jim tayi da sannan tace




"Nima wallahi ban sani ba ....,


kenan kin hakura da neman sa....




da sauri ta kalli zee tace




"Zee gida zan koma wallahi nagaji kuma sai kuma na dawo....yanzu muje gidan da kike zaune gobe sai in tafi...,




da sauri ta dafe kirji tace






"Yar sokoto rufan asiri aɗosane nake a gidan nan wallahi daman zaman dole nake in ina cikin gidan zan sami me dan shi yayi zaton gidan ubana ne ya biyoni ya aure ni.....,






dafa kafaɗar zee nabeela tace




"Hmmm uhmmm Allah ya temaka....,


amin inhar zuciyar ki kika faɗa




dukan wasa takai mata ta goce tana dariya


tsarar me napep sukai suka shiga inda batare da sunyi ciniki ba otal ɗin da ta sauka ya akai ta ya ajiye ta 2k ta zaro ta bawa zee ta bashi sukai sallama inda ya ƙara gaba da zee har Kofar gida ya kaita sauka tayi ta zaro kuɗin da nabeela ta bata tabashi cire p-cap dinsa yayi yana mata wani kallon up and down yace




"Wannan me kike bani....,




da sauri ta kalli kuɗi tace




"Kuɗi mana....,




Fitowa yayi yace






"Tun daga villa na ɗauko ku ina ta yawo da ku ban dauki kowa ba dan haka kuɗin ku 5k....,




Kai daga kata malam in Rashin mutunci kake ji dashi wallahi ka sami dai-dai dakai kai wanne irin ɓarawo ne tafiyar nawa mukai da har zaka ce miki haka....,






Wallahi in baki shiru ba zan zube miki kwando kwandon rashin mutunci ke ni rayuwar agige nayi a karkashin gada


wani kallon tara saura kwata tayi mai tace






"Au Allah....Dan tasha...to na fika ta shanci wallahi ko kallona kayi kasan ruwa ba sa'an kwado bane...,




kee wacce irin dabba ce ai be karasa ba ta zabga mai mari wayar hannunta ya war'ta ya shige mota ga unguwar shiru ba kowa balle ta nemi ɗauki gumi ne ya shiga yanko mata wannan wanne irin ibtila'i ne wayar nihila ce ta ɗauka bata sani ba kasa zaune tayi ta ƙasa tsaye yau ta tabbata inhar niheela ta gane ita ta ɗaukar mata waya sai tayi kwanan ƙauye ba tare da burin'ta ya cika ba




___________magajiya


Karfe uku ta tashi daga suyar waina gyara gurin ta fara tana yan wake waken'ta rabi tana zaune suna buga ca'ca inna gamawa tayi ta ajiye tsintsiyar ta saki miƙa tace




"yar faki faki ba yawa sai lada bara inzo inyi salla....,


kahu bulama da yake zaune yana jiran tsammani yace


"yanzu magajiya sai yanzu zaki sallahi uku da rabi har ta gota....,




har ta shiga bayi ta fito tace




"kahu gwani ina da niyar yin salla Allah ya gani yan ciniki ne sukai min yawa ban samu damar yi ba wayan can fa kaga suna da niyar yi adinga kyatatawa ɗan adam zato dan Allah....,




tana kaiwa wannan ta shiga bayi ahayye rass shishshigi ba farin jini cewar rabi




saudat me idon cin naira ai gwara wanda yake faɗakar da mutane akan subi Ubangiji da wanda yake saba mai yana namiji yana mai da kan sa mace wallahi ina nan zan kira yan hisba su kwashe duk wani me baɗala agidan nan kowama ya huta




Chass anayi muna jin dadi wai kin san me saudat....,




kwai ta saki yace Tush tace


"a'a rabi..sai kin faɗa...,


rabi jiya ganin ido naga wani tsohon najado yana bara zuciya ta mutu da sauri magajiya ta fito bata ƙarasa wanke fuskartar taba tace






"Alkur'an bazan yarda ba cini kin wainar tawa kuka ɗauke ni zaku tozar ta ina manjagara ina dinana yau za ayi bura'uba wallahi ina jin na wai wai yau ni saku yashe...,




innalilahi rabi ya fada zaninsa na kokarin suɓucewa ido huɗu sukai da kahu yace






"haba malam har wani karkata kai kake zaka kalli tsiraicina adin ga yin na Allah wallahi wannan bayi bane wallahi...✍️


Ina masu so atallata musu ajojinsu to kofa a buɗe take domin karin bayani ku neme ni ta wannan number


09061890481




GIDAN MAGAJIYA




nafa kusan daina posting ako wanne group kuyi following ɗina domin samun karanta gidan Magajiya complete ina masu so atalla musu hajojinsu to kofa a buɗe take


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


Episode 4




Billahir'lazee huwarramanu kabi a hankali kat in maka ɗaukan amarya




Ihuuuu kai kar ka ganni ni macece ina da rauni to wallahi kabi a hankali




Ya ishe ku haka ni zaku mayar mahaukaciya ina maganar kudina kusan dubu sittin kuna min maganar banza to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login