Showing 21001 words to 23135 words out of 23135 words
son da yake miki sai ya dena ....,
Hidaya ya zanyi da su kina gani a gaban ki nayi wayar nan amma me yace min duk abin da kika kwatantamin nayi
ai wallahi tun farko ke kika bari yasan cewa kuɗin'sa kike so haba ga shinan ya sakar miki kuɗi amma ba farin ciki ko gaba zai iya yi miki gori kudin'sa kika gani kika manne masa
Hidaya nasan nayi kuskure ya zanyi da wannan result nifa ke da matsala bashi ba ko wanne lokaci ya gani zai iya karo aure saboda haihuwa yake so
ai shi yasaka nace miki za mu nemo mafita dole ki canza ki dinga yi mai biyayya fiye da da sannan dole mu bi malam mai su rufe mai baki duk wanda zai mai maganar haihuwa yaji ya tsane sa
nagode sosai kawata
Washe gari kano
da asuba kahu ya fito daga Masallaci bayan an idar da salla abin mamaki wasu mutane ya gani a cikin mota wasu kuma na dan zazzagawa rayawa yayi wata kila wani taron ya shige gida samin magajiya yayi a zaune ta idar da salla sai uwani da take tsakar gida tana wanki yace
"yau kuma da huri haka....,
Eh wallahi alanguburo ai gwara inyi da huri ya bushe da huri garin nan na damuna ko wanne lokaci ana iya yin ruwa
hakane wallahi kinyi da bara magajiya yau da huri haka
murmushi tayi tace
"kahu wallahi yau da huri na kwanta...,
ai gwara ki dinga haka ita sallah asuba kariya gareta
hakane kahu shiga ciki yayi haka kurum taji gaban'ta na waɗuwa amma sai ta ci gaba da addu'a gari ne yayi haske waje kuwa tuni ma'aikata suka zagaye gidan da bindigogi duk fuskarsu a rufe da baƙin yanki ga baƙin glass mutane suke liƙe ta sama domin ba damar zuwa ma'aikata ne guda hudu suka tiso keyar su dinana rabi sai kuka haka dinana har da majiya shiga cikin gidan sukai fitowar malam daga bayi kenan a guje ya koma yana cewa innalilahi yau na shiga uku ɗaya daga cikin su ne yace
"Baba fito ba abin da za muyi maka...,
jikin kahu yana rawa ya fito sauran kaɗan ya saki gudawa ɗayan yace
"Ina magajiya....,
"Gani me za a siya da sassafen nan Ku ishi mutane...ta fada tana fito daga daki turuss tayi ta zaro ido kirjin'ta na yin sama yana ƙasa kallon dinana wani daga cikin su yayi yace
"Wannan ita ce....?,
aa yallaɓe sunana falmata lawan maina wallahi kai dinana ni zaka gogawa kashin kaji wallahi ban taba aikata wani laifi ba bata ƙarasa ba taji dayan ya saita ta da bindiga yace
"kina kara wata magana sai na fasa kanki ina wayar da kika sata....,
da sauri ta miƙo mai daman tana hannun'ta ankwa wata mace a cikin su ta shigo ta sa mata kuka take sosai takalli kahu tace
"Kahu....✍️
labari ya zo tsakiya na kusan dena posting a ko ina ku hanzarta following ɗina
*GIDAN MAGAJIYA*
Oum yasmeen
*End of book 1 mu haɗu a book 2 shima free ne kar wanda yace ku bada kudi ya baku document har yanzu ban fitar da document ɗin'sa ba typing nake*
EPISODE 19-20
Kina kara wata magana jikin ki zai fa gaya miki tsit tayi tana kuka kahu na sharar hawaye ba baƙin magana wa'yannan Mala'ikun duniya na gabansa ɗayan ne yace
"Baba wannan wayar da ka gani kidnapping ɗin matar director Janal Asif kabir sardauna akai to wayar nan ta tace mun ƙama sauran Sim ɗin a hannun wa'yannan....,
Wallahi Allah siya tayi bata san abin da akai ba ita ce katan mu ita ke ciyar da mu
ko sauraran sa basu tsaya yi ba sai kokarin fita da suke da su
uwani kuwa tana kuryar ɗaka jikin ta na zikiri Allah Allah take subar gidan tusa ƙiyar'su akai kahu har waje ya fita ko wannan su mota daban a ka sa shi kuma prevent car a guje suka fice daga lahin su ka hau kan titi kuka sosai magajiya ke yi ta haɗa kai da gwiwa tun da take a rayuwar'ta bata taɓa ganin tuzarci irin wannan ba roƙo take Allah ya ɗau ranta ta huta tasan yau mutanan unguwa suna nan suna murna wannan abu ya sameta
miƙar hanyar Abuja sukai dan ko a bangaran'su na nan ba a ajiye su ba kai tsaye can za a huce da su ganin suna ta waya ta gane bama anan aza a ajiye su ba shikkenan mutuwar'ta tazo domin ta san tun da abin na manya ne fasa kansu kawai za ai ba za a tsaya bincike ba
karfe biyu suka isa abuja babban headquarter su fito wa sukai ita ma ta zuro kakafuwanta da ko talmi babu balle mayafi sai yar hular da take kanta ba sosai ta rufe tulin sumar kanta ba duguwar riga ce a jikin'ta buba abin mamaki bata ga su dinana ba kai Allah ya tsinewa kaska wani ɗaki aka shiga da ita duhu diɗim sai wani table a tsakiya sai kujera biyu kallon ta wannan jami'ar tayi tace
"ga gu nan zauna....,
zama tayi yayin da wahaye ba bin fuskarta fita tayi kai tsaye office ɗin director ta nufa da yake yace musu in sun dawo su kirashi bata tarar da wani cinkoso ba ta kalli sakatariyar sa tace
"zan iya ganin oga...?,
kallon sama da kasa tayi mata ta ci gaba da danna laptop ɗin'ta tace
"you can't see him because you are not in the appointment with him today he has a lot of work...,
cikin ɗaga murya tace
"She told us that when we came back from the operation, one of us came and told him that he wanted to meet them first....,
da sauri ta tashi tace
"You are raising your voice about the work of the men you took with you, but you are going to come and tell him.....,
dai-dai fitowar sa daga office ɗin'sa domin har maganar da wowarsu ta zo mai be tsaya kallon su ba ya huce su ta kaici ne ya ishi surayya tace
"burin ki ya cika sai ki huce ki ban guri....,
kallon inda take bata yi ba ta huce ta tare da jan karamin tsaki ta fita yana fita duk yawan ma'aikatan gurin sara mai su ja shiga yi kowa ya tsaya da aiki fuskarnan ba ɗigon annuri ya daga masu hannu domin ransa a ɓace yake da zuwan wannan rahoto mace mace har da mace me yiwa wani tarbiya ita ta saka kanta a cikin wannan hali koman daran da ɗewa zata zama uwa shiga yayi ya zauna har lokacin bata san ya shigo ba tana kuka ta kifa kan ta akan table hannayanta har yanzu na cikin ankwa lurar da tayi tana motsi tana ƙara dame hannun'ta dan haka ta tsayar da shi gu daya gyaran murya yayi hadi da buga table ɗin ɗago kan ta tayi idon'ta yayi ja tsoro ya bata tuni zuciyar'ta ta shiga harbawa zama ya gyara a ajiye wani abu akusa da shi yace
"ya sunan ki....,
buɗa baki tayi zata yi magana kuka ya ƙara kwace mata cikin tsawa yace
"Tambayar ki nayi da baki tanadi zuwan nan ranar nan ba mayanan ki ƙadai zasu fitar da ke daga gun nan inhar muka ƙara bincike muka ga baki da sa hannu a cikin wannan laifin amma in har sunan kiya fito nan gurin shine kabarin ki....,
jikin'ta ne yawa kakkarwa ta kasa koda motsi dan karin kumallon safe da tayi shi ta shiga amarwa iya tsorata ta tsorata daga nin wannan mutumin a gaban'ta saboda tsoro ta kasa tantance wane a agaban'ta harda yatsun'sa yayi ya ƙara cewa
"Tambayar ki nake ko sai nayi miki abin da zaki magana ba zaki faɗa mana ta dadi ba.....?,
kukan ta ne ya ƙara tsanan'ta tashi yayi ya fita cikin ɓacin rai ya kira wo wani shugowa yayi yace
"ga ta nan in har ba tayi magana ba ku mata duk kan wani horo har sai tayi magana masu cin amanar ƙasa kina mace kin banzatar da darajar da Allah yayi miki duk abin da za kiyi baza mu taɓa sassauta miki ba ko tausaya miki kone masu kona gidajan mutane kuna cin zarafin'su...,
muryar'ta a dashe tace
"ba sai kun min komai zan faɗa muku abin da na sani...,
fita yayi ba tare da ya tsa jin maganar'ta ba inda sabo ya saba da wannan rainin hankalin mutanan nan wasu ma sun gwammace a kashe su da su faɗi ubangidan su amma in suka sa musu na'ura dole suyi magana abin da basu shirya fitowar'sa ba dole su faɗa wani guri ya shiga inda rabi yake zaune zama yayi yace
"Ya sunan ka....,
kusan dai yadda yake magana haka yayi mai yace
"Rabi'u hamisu....,
tsawa ya daka mai yace
"daidaita muryar ka ko inci ubanka ba sunan ka rabi ba....to wallahi za ka dawo dai-dai ne..,
gaban rabi ne ya waɗi yace
"Eh amma wanda mahaifina ya saka min Rabiu.... saboda ta kaita dogon zance ake ce min rabi....,
wato kai da dan iska ko
shiru yayi jikinsa na rawa ko a mafarki be taɓa tunanin zai ga wannan tashin hankali ba
katsai masa tunanin yayi yace
"Wane uban gidan ku da yake saku wannan kidnapping...,
Narantsai da Allah ban san kowa me yin wannan harkar ba layi na siya agun kaska dina dinana bamu san cewa ga abin da akai da layin ba wallahi wannan ne kaɗai abin da na sani amma ban san wani masu kidnapping ba
haɗa rai ya ƙara yi yace
"taya akai wayar ta zo hannun ku in mun yadda cewa siya SIM kukai....?,
wallahi magajiya ce ta siya a hannun kaska duk tare muka siya yana zuwa gidan ta siyan abinci
tashi yayi ya zuba hannun a aljihu yace
"wato ba zaku faɗan gaskiya ba sai jinkin ku yayi tsami....,
rantsuwa ya fara yi amma ina har ya fita shiga dakin kusa da shi yayi inda dinana ke zaune zama yayi yace
"Wace ce Nuratu...?,
wallahi Allah ban santa ba ban taɓa ganin'ta ba
Cikin kakkausar murya yace
"tanan kuka bullo za ka faɗa gaskiya a cikin ku wace nuratu ko sai na fasa maka kai ya fito da yar ƙaramar bindiga yana saita kansa da ita fitsari dinana ya saki hakuran'sa har gwaruwa suke da juna saboda tsabar tashin hankali yace
"Wallahi Allah ban santa ba....,
cire bindigar yayi yace
"wacce aka kawo ku da ita ita wace ce....?mene alakar ku da ita....?,
magajiya sunan'ta
tsawa ya buga mai yace
"wato ka biyo tanan hanyar ne dan kar mu gane magajiya sunan gaskiya ne ...?,
sunan'ta falmata lawan maina yar garin Maiduguri ce sanadin haduwar mu ina zuwa gidan su siyan wainar'ta amma itama wallahi siyan wayar ta yi a hannun wanda muka siyi layin kaska..
wane kaska
a jalwala yake dan gaban mu ƙadan yana saida wayoyi da layi ka yayi mana talla layin unlimited credits card haka yace mana muka siya dubu biyu sannan yace muyiwa magajiya tallan wayar dan akaf cikin mu ita ce me sana'a kuma zata iya siya mukai mata talla ta siya yace zai kawo mata receipt jiya ya kawo min gidan mu yace tafiya ta kama shi na sashi a aljihun wannan kayan da niyar da safe in bata
kai ASIF ya jinjina ya kama hannunsa cire ankwar yayi yace
"fito min da receipt ɗin....?,
hannunsa yana rawa ya shiga laliban aljihun'sa cire wa yayi Asif ya amsa dubawa yayi washe garin anyi kidnapping ɗin su nazeer aka siyar da wayar kai ya jinjina ga sunan ta nan ma duk yadda akai me sai da wayar nan yana ɗaya daga cikin wa'yanda sukai kidnapping ɗin su nazeer wata kila ma yan uwansa basu san ya dauki wayar ba tashi yayi ya fita wani waje ya shiga kamar lap da sauri suka dena abin da suke kowa yayi mamakin ganin Ogan nasu saramai sukai ya miƙawa wani ma'aikaci yace
"kai min binciken wannan lambobin yanzu sannan ka dubu biometric hannun wa da hannu wa yaje sannan sai ka tura da sakon ma'aikatar kula da bvn wannan shatin hannu ya taɓa yin register da su....,
da sauri ya amsa yace
"to fita yayayi ya koma dakin da magajiya ke ciki iya wahala ta wahala domin shocking aka saka mata ko ɗaga kanta bata iya yi cikin ɓaci rai wata ma'aikaciya tace
"taƙi magana cewa dai take wallahi bani bani bace siya nayi....,
ku sata a dark room bata wahala bane ina tunanin sauran bakin su ɗaya amma su sunyi bayani ko wanne kareta yake suma ku kai su wani daki ku ajiye yana fadar haka ya fita dagata tayi ta daka mata tsawa dakyar take iya tafiya jikin'ta duk amai wani baƙin daki aka saka ta dakyar mutum zai iya tashi tsaye suka rufe kwanciya tayi idanuwanta na zubar da hawaye....✍️
*Allah ya raba mu da sharrin banji ban gani ba ya kare mu da taka sahun ɓarawo*
Alhamdullahi ayau na kawo karshen book 1 sai mu haɗu da ku a book two