Showing 3001 words to 6000 words out of 23135 words

Chapter 2 - GIDAN MAGAJIYA by oum yasmeen Book 1.txt

06 Nov 2024

4333

wallahi yau yan sandan wambai zan kirawo su kwashe ku in kunje can kwayi bayani




Shikkenan da haka ma in kikai kin hutar da kowa cewar saudat me idon cin naira




To yar bantan uba shegiya da fuska yawa ruɓaɓɓiyar gwanda duk anbi an kwashe fata da man bleaching cewar kahu bulama




da sauri magajiya tace






"Kahu saudat zuby rabi uwani...tun muna mu haka daku ku fito min da kuɗina....,


da sauri uwani ta sallame salla daman tayarwar ta kenan tana cikin sujjada taji ta ambaci sunanta a sukwane ta fito tace




"Magajiya kinga na zauna miki a katarar ki wa'yanda kike tare dasu sune ɓarayi bani ba me zanyi da kuɗin kii....,




yarfa hannu rabi tayi ta murguɗa baki yace






"Waya sani abu a duhu ai ita sata ba mannata ake agoshi ba ba kama ce da ita ba wallahi wata kila mu da ake ganin cewa mu gamu gamu nan ne sai agaba haka bane.....,




kafin ya ƙarasa UWANI ta sauke mai botikin karfe aka ihu ya zabga da sauri zuby tayo kan'sa uwani tana haki tace






"Shege ɗan katan uwa ni zaka faɗawa sheganta ka to har aran gama munyi da yan boko haram balle kai karan ƙada miya....,




da sauri magajiya ta shiga ɗurkusasshen ɗakin'ta ta ɗauko mayafi zanin jikinta na suyar waina ta cire ta hullar da mukulli hannunta tace






"Wallahi duk wani tantirancin ku kunsan na fiko yanzun nan zan tawo da su sajan bala kunsan sauran...,


tana kaiwa nan ta fice kulle gidan tayi tana sauri matasan da suke zaman majalisa a kofar gidan wani daga cikin su yace




"Allah ya rabamu da haifar ya'yan kuka...,




har tayi gaba sai taga in bata mayar mai ba baza ta iya bacci ba tsayawa tayi tana yi musu kallon sama da ƙasa tace




"Ku jirayi dawowata dan har ku wannan tashin hankali bazai kyale ba dole a fito min da kuɗina wallahi tana kaiwa nan tayi gaba




da sauri kowa ya shiga kwashe yana sa yanasa domin sunsan halin Magajiya ba mutuncine da itaba bata kunya bata shayi akan kuɗin sai ta kulle mutum wajan kamar anyi shara kowa ya tashi na cikin gida kuwa suna nan suna tashin hankali......


batayi wata tafiya ba ta isa policetesion
mayafinta da tasa a kafaɗa ya dawo hannunta ɗaure shi tayi a kugu ta shiga washe baki sukai wani ɗaga cikin su yace




"a'a yau manyan ƙasa gatan kanana...,




Kofur musa d.p.o yana ciki...?,




eh yana ciki amma yace kar kowa ya shiga wani kallon tara saura kwata tayi mai wani tsoho da yake zaune yace




"Jami'in doka kace min yayi tafiya....,




da sauri magajiya ta kalli tsohon tace




"Baba maganar wanan la'anannam Allahu'ta'ala zaka yarda da ita tab kana ruwa....,


Sajan bala ne ya fito daga cikin cell yace




"Sweetheart yau kece agurin namu....,




ajiyar zuciya ta sauke tace




"Sajan bala ina cikin matsala mutane nane suka ɗaukar min kuɗi wallahi...,




aikuwa yau sai sun san sun taɓo matar ɗan sanda kai da sauri ya juya sarawa ogannasa yayi washe baki yayi ganin magajiya yace






"A'a yar barno me ta kawo ki nan kar dai wannan yaran ki ne aka kama masu yawan dare ya nuna wasu ƙananan yara rayuwar su abar tausayi kina mace kina harkar ta zubar wa'iyazullahi... Allah ka shirya mana zuri'a...,




Allahumma amin




sai lokacin ta lura da su tace




"a'a kuɗi wayan can yan iskan suka daukar min...,




yanzu dai kawo wani abun da zamu zuba a mota mutafi kamusu




Innalillahi yanzu oga nura ni zaku yiwa abin da kukewa wa'yanda basu waye ba tab lallai shiyasa nace ku kaini gurin d.p.o kuma billahillazi inga mutum acikin gida sai na karta mai rashin mutunci mabayyani wallahi






kai sajan bala kofur musa ko bita ku kamo mana kowaye zasu yi bayani ne




Saramai suka kai suka ce to




Baiwar Allah dan Allah kisa baki ɗana aka kama ya saci garin kwaki wallahi yunwa ce da matsi na rayuwa yasa yayi haka kuma na maƙocina ne




tausayi ya bawa Magaji tace




"Kar ka damu baba sajan bala na nawa ya ɗauka...?,




na dari biyar sai kuɗin beli dubu biyu




kallon bangon policetasion ɗin tayi tace


"naga ansa beli free ne....,




sosa kai yayi yace






"Kawo abin da zaki kawo kiyi gaba mu sake shi....,




Dubu biyu ta bashi ta ɗauki dubu biyu ta bawa baba godiya ya shiga yi mata yana sa mata albarka fita tayi su sajan suna binta abaya can gurin me awara ta hango dinana nunawa su sajan shi suke ji yayi an cabki wandon sa cikin bala'i ya ɗaugo yace






"Wanne dan durin uwar.....kafin ya ƙarasa sukai ido huɗu da sajan bala....,



Haɗa rai yayi yace


"to me nayi mai nayi maka ba dpo yayi mini tsakani dakai ba....,




dungure mai kai yayi yace




"Uwarka kai min shige mu tafi...,




tirjewa ya fara yi da be lura da magajiya ba sai yanzu yace




"Magajiya dake za'a haɗa baki aci zarafi na....?,


Dinana kuɗina dubu sittin aka ɗauke min suwa ye ke tare dani in baku ba..,




Gaskiya ne yanzu na fahimta sai yau na gane maganar hausawa da suke cewa zuciya bata da ƙashi inban da haka in taɓa gani nayi sata banni da ɗan taɓe taɓen mata anan nafi kauri amma saboda ido wa ka raina shine ina gaban buɗurwata kika sa aka tuzarta ni....






Da hallacan muje tafiya suke suna ta faɗa sa mukulli tayi ta buɗe gidan hanka ɗashi su kofur sukai kahu yana zaune yana jan jarbi tashi yayi ya saki salati ganin wayan nan annobar yace




"Falmata amma dai wayan can yan Allah ya shirya za'a kama ban dani ko...,




shigowa tayi tace






"a fito min da kuɗina hankalin kowa ya kwanta in kuka ƙi wallahi sai kwanan cell gobe sai gidan gyaran hali....,




Rabi da take zaune dafe da fashashshan ƙai tace






"Innalillahi magajiya ki rufan asiri yanzu ina zan sa kai na wallahi fata ta bata son cizon sauro kinsan dai ance ciwon ya'mace na ya'mace ne su tafi da dinana da bulama yake kowa yauwa kun manta ba a tawo da manjagara ba ina kyautata zaton shi ya ɗaukar miki...,




To ɗan shegiya wa yace maka ina tsoron su gani billahillazi na kama ka sai na cire maka raini dake tsakanina dakai...,




zaro ido rabi tayi ɗaurin ƙanta ta cire tana fifita dashi.....✍️



gidan magajiya yasha babban da labarin da nake kawo muku kudai ku kasan ce da alkalamin


*Oum yasmeen matar mijinta*








GIDAN MAGAJIYA




Wannan littafi kirkirarre ne banyi da nufin tozarta wani ko wata ba duk wanda yaga yayi dai-dai da rayuwar'sa to ya ɗauka arashi ne......




Ku fitar mana da littafi ku karanta kuna nushaɗi kusan cewa Ubangiji zai barku wallahi hakkin mune Ubangiji bazai taɓa barin kuba muna amsar kuɗi ne saboda mu rage raɗaɗin typing hannun mutum duk ya ƙage ke ki karanta a kwanciyar hankali wata shari'ar sai a lahira🗣️




https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k




Kuyi following ɗin channel ɗina domin na kusa dena posting a ko ina sai a channel






Episode 5








Shege wanda Ubangiji ya la'anta billahillazi zamu haɗo a way


Ku dakata kuɗina nake muku magana kun mai dani mahaukaciya tagumin da uwani tayi ta cire tace






"Yanzu falmata bazaki bi wannan abin a hankali ba ayi bincike....,




Banza tayi mata kamar ance kalli can inda ta zauna tana al'wala sai ga kullin kuɗi da sauri ta ɗauka farke baƙar ledar tayi kirga kuɗin ta fara kuɗin ta cas ba abin da yayi ciwon kai...hamdala tayi ta soke a kugu tace




"yan iskan karya....,




Wallahi Allah ancu ce ni haka kurum kin ɗora mana sharrin sata gaskiya magajiya ki canza hali tun kafin Ubangiji yayi ƙuliƙulin kubura dake wallahi


Cewar rabi....




takaici ne ya kama xuby ta ɗauki mayafin'ta ta tasa a ƙafaɗa tace






"To su kofur sai ayi gaba nan gurin baku da rabo....,




harara ya gallamata yace




"to yar hau ke wallahi kike yaye ni tun kafin insaki a bayan kanta....,




Ka dade baka sakani ba tana kaiwa wannan ta fita shigiya da kafa yawa katafila kina wani rausaya kamar matatciyar bishiya da take shirin waɗowa


Rabi ya faɗa yana wani murguɗa baki dinana da takaici ya ishe shi yace






"Magajiya wallahi zan san zaman da zanyi dake.....,




Ka dena zuwa gidan nan daman me kake tsinana mata


taɓarya ya ɗauko ya biyi rabi da ita da gudu ta fita sallamar su kofur tayi suka fita akan dokin kofa ta zauna ta zuba tagumi ta shiga tunanin rayuwa jin maganar Sama'ila tayi yace






"yaya yunwa nake ji....,




da sauri ta ɗago tace




"Sama'ila ɗauki kuɗi a kan katifa ta ka siyo mana taliya ka biya gurin masu siyar da pieces ɗin kaji ka siyo cinya da kirji na dubu biyu.....sai ka siyo mana kayan miya...ka kaiwa uwani ta girka mana,






kahu da yake zaune yace






"Falmata kice yau me yar gaɓa za muci a gidan nan....,






kallon kahu tayi wanda take wa kallon kamar mahaifiyar'ta wani zubin halin sa ke ja masa tace






"Eh....,




gyara kwanciya yayi yace






"To Allah yayi albarka ya bayyana fatima....,




jindaɗin addu'ar sa tayi tace




"Amin.....,


Sama'ila ne yace




"Yaya yaushe za mu koma damaturu....,




kama haɓa tayi tace


"Ka rufa mana asiri so kake muje ayi dabgen mu....ai ko a mafarki bana fatan Allah ya maidani Maiduguri ai mun ga tashin hankali.....,




Shiga ɗaki yayi ya ɗauko ya fita Radio kahu bulama ya ware har maƙota anaji kwanciya yayi a katifa Yana jin labarin duniya kamar haka




Ayau ne shugaban rukunin Company AK SARDAUNA CONSTRUCTION sannan director general ma Hukumar DASS bayyana cewa insha Allahu sun kusa gama titin da zai kai ka har zuwa katsina tun daga nan kano kuma ya bawa wa'yanda ta sanadiyar haka suke samun tsaiƙun tafiya yayiwa wakilin mu ƙarin bayani




Waccan gwamnati ta bami aiki ba tare da tabiya mu bu shiyasa na dakatar da aikin amma wannan sabuwar gwamnati ta taka rawar gani gurin biyan yan kwangila hakkinsu


Inda yana gama wannan jawabi ne jirginsa ya ɗaga zuwa babban birnin Chaina


Ga zantawar da mukai da al'umma mene ra'ayin ku game da titin da shugaban ƙasa ya ɗauko tun daga kano har i zuwa hanyar da zata sadaka da Katsina nazeer lawan gare Ka


Sunana nazeer lawan nine me kawo rahotanni ga hirar da mukai da wasu matasa


A gaskiya mu ba wannan muke buƙata ba a inganta harkar lafiya da tsaro dan an gyara mana titi mutane ba kwanciyar hankalin da za suje su amfana da titin kullum ana bin mu ana kashe mu






Wakilin rahotanni yace




"Kar ka manta direbobi sun sha bin hanyar nan suna haɗari saboda rashin kyahun hanyar....,




ba rashin kyan hanyar bane yake sa haɗari ka bincika kaji yan fashin dare ne suka assasa haɗarin


Kai me zaka iya cewa game da ci gaban da aka samu tsawon shekaru takwas ana aikin titin nan aka tsaya sai yanzu me girma shugaban ƙasa ya fitar da kuɗi domin a ci gaba da aikin nan




hakan ya da yayi abu ne me kyau Allah ya ƙara mai nisan kwana ya bashi ikon sauke nauyin mu


To godiya muke nazeer lawan


a wanni ɓangaran kuma ministan ilimi A'isha AK sardauna ta halarci taron shugabannin makarantun kama daga kan primary secondary college university insha'Allah zata jajirce ganin harkar ilimi ta gyaru a ƙasar nan inda ta faɗi jimullar yaran da basa zuwa wa makaranta.....




a fusace magajiya taje ta kashe radiyo bacci ne ya fara ɗaukan bulama firgigit ya farka yace






"magajiya lafiya.....?kika kashe min Radio...,




Kahu sai yau she zaka kagane ka dena sauraron wannan ƙanzan kuregen ne




tasho zaune yayi yace






"Falmata labarin duniyar ne kanzan kurege lallai kinji hausa....,




komawa tayi ta zauna tace






"Kahu ka faɗamin abu ɗaya a aka faɗa da ka amfana dashi mu talakawa ba wannan ne a gaban mu ba a inganta mana tsaro rayukan mutane nawa a kullum suke salwanta....? muna tsaka da bacci aka kore mu aka yanka wasu daga cikin mu yara ƙanana suka zama marayu...mata nawa aka kama aka yi musu fyeɗe sannan aka yi musu kisan hulakanci....yara da yawa sun na ƙasa so muke akawo mana ƙarshen wannan zaluncin ba wannan shirman banzan ba a kawata titi su haukan titin adin gayi musu jiniya turawa su zo.....


zuga suna aiki a kasar su su hau kan gada su shiga su ɓulla yawa wasu kurege kahu dan amfanin kansu suke gyara titi badan amfanin mu ba wallahi kahu ace zan shiga siyasa kuma a zaɓe Ni sai *NAKAWO KARSHEN WANNAN ZALUNCIN......*




Allahu akbar ba shakka malama falmata ai kamata yayi ki tara mutanan ki ki musu faɗa kafin kizo kan shuwagabani...,




ɗaki ta shiga hawaye na bin kuncinta karewa ɗakin kallo tayi duk irin daular da take ciki tana ji tana gani ta baro'ta tabar abu mafi muhimmanci a rayuwar'ta jin maganar mahaifinta tayi ta dawota sabuwa fil tana amsa kuwa a kunnanta




Bazan shiga ƙungiyar ku ba saidai in Ku kasheni bazan zaɓi farin ciki na ba in sulhuntar da rayukan musulmai ba....karya kuke wannan abin da kuke ba jahadi bane cin zarafin Musulmi ne......✍️


*Yan aljanna a dinga yi min sharing Allah ya bawa kowa abin da yake nema duniya da lahira*




GIDAN MAGAJIYA


oum_yasmeen


✧⁠☆typing....


✷⁠✷✷✷✷⁠✷⁠✷⁠✷


EPISODE:.6


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k




Kanta ta dafe dayake tsananin mata ciwo zama tayi salamar Sama'ila ce ta dawo da ita duniyar da muke tashi tayi ta ɗauro alwala salla ta haɗa azahar da la'asar ko tsayawa addu'a bata yi ta fito




Lokacin uwani ta gama shan wahalar hura huta ta ɗora tattasai sauke tukunyar tayi ta zuba ruwan wanka ta tsaya agurin tana girgiza kafar ta jin motsin sauke tukunya a sukwane uwani ta fito daga bayi tace




"Wanne shegen ne ke buɗamin tukunya....?,




shiru tayi ganin magajiya girgiza kai tayi ta koma alwala ta ɗauro shiga ɗaki tayi


sauke ruwa magajiya tayi ta zuba a botiki mai da tukunyar da ta sauke tayi
Sannan ta juya ruwan a botiki


shiga daki tayi ta ɗauko kwandon wankan ta ta shi ga bayan gida




✧✧✧


******CHAINA SHANGHAI PUDONG


miƙe ƙafafuwan'sa yayi akan Centre table sosai yake jin daɗin karanta jarida wayar sa ce tayi ringing gaban sane ya waɗi ganin wacce take kiran shahada yayi ya ɗaga kiran cikin ladabi yace




"Assalamu alaiki Barka da war haka hajiya....,


Bata tsaya amsa gaisuwar'sa ba balle sallamar'sa ta zarce da cewa


Asif ya kukai da kai wata fa ba ƙoƙarin cika banji ko ɓatan wata wannan juyar tayi ba




lumshashun idanuwasan ya buɗe ya maida su yawa na masu jin bacci yace




"Ki hakuri hajiya komai nufi ne na Allah..,


ai kafin ya ida zancen'sa tace




"Wallahi wata na cika sai kai aure....dan mu dangin mu irin haihuwa ne damab tun farko kafiyar ka ban ga abin so a silindar gas ba ba kyan fasali amma ka nuna kafiya dangin turawa ai su tun yaro na ciki suke kashe mai kwaikwayon haihuwa....kaf cikin ahalin mu kowa na haihuwa ban da kai ƙannan na baya wanda akai musu aure bayan auran ka daga me ya'ya biyar sai me huɗu....dole inga jikan babban ɗana....,


cije lips ɗin'sa yayi besan wacce tsana hajiyar sa tayi wa aysha ba duk da wani zubin da laifin aysha ƙasa yayi da muryarsa yace




"hakan ma baza ta faru ba insha Allah zaki ji kyakkyawan sakamako....,


Allah yasa ta kashe wayar ba tare da taji me zai ce ba


jikin'sa a sanyaye ya ajiye wayar ɗaga kansa sama yayi kallo ɗaya zakai mai kasan buzune ga hutu da ya ratsa fatar'sa har ɗaukan ido ji yayi karanta jaridar ya ishe shi tashi yayi dogune ga jikinsa duk a murɗe laptop ɗinsa ya janyo ya zauna duba saƙone ya shiga yi


wani sako ya gani Niheela M.S banza yayi da saƙon ya ci gaba da duba masu mahimmanci wani saƙon ne ya sake shigowa dafe kansa yayi dake tsakanin


ciwo buɗewa yayi kurawa rubutun ido yayi yana karantawa


_assalamu alaika amincin Allah ya tabbata a gare ka ya wanda zuciya'ta take so ina fatan a yau in sami a bin da na dade ina jira a ko wanne lokaci ina tsammanin ganin saƙon ka duk da nasan kana tarun aiyuka_


*daga masoyiyar ka ta har abada NIHEELA M.S*




takaici ne ya kama shi waya ya ɗauka cikin ba da umarni yace




"Zan turo maka wani email kai min bincike a kansa....,


Okay sir kashe wayar yayi ɗaya wayar'sa ce tayi ringing ɗauka yayi ganin my love CE ɗauka yayi ya kara a kunne batare da yayi magana ba tace




"Honey nayi kiwar ka....,




Shafa lallausar sumarsa yayi yace




"hmmm yanzu in nace ki biyoni cewa zaki aikin ki.....,


gaban tane ya waɗi karfa yace ta biyo shi bazata iya tafiya wata ƙasar ba ba aikin'ta ne ya akai'ta ba tace




"Ak aikin al'umma ne duk randa nayi ritaya zan buɗe Foundation ne in nemi guri in zauna in kula da kai sannan in Allah yayi min nuɗifin'sa sai kaga na haifa mana baby's masu kama da daddy su....,






ajiyar zuciya ya sauke ya gyara zama yace




"Aysha lokacin karfina ya kare a lokacin buƙatar sanyin idanuwa nake wa yanda zan kalla naji dad'i.....,




iska ta furzar me huci ta gyara zaman'ta tace




"A kullum ƙara zamar min wani fure kake wanda yake yaɗo baza ka taɓa jin ƙasa ba kai mazajene a cikin maza me isa wani zubin kake da saurin karaya....?,




rufe laptop ɗinsa yayi yace






"Aysha bakya tsoro rashin kulawar dakike bani a masu farauta ta su sami nasara....?,




Dariya tayi ta juya sitiyarin motar ta tace




"Zuciyar ASIF ba ko wacce mace face matar'sa na baka duk wata yarda....,




Murmushi yayi har ana iya gano jerarrun haƙoransa yawa sankara saboda haske da ɗaukar ido yace




"yanzu ina aiki in ajima muyi yawa....,




Okay nima ina kan hanyar zuwa gida wallahi na gaji gobe na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login