Showing 27001 words to 30000 words out of 32417 words
Chapter 10 - Farautar Farin Ciki Hausa Novels Document Na Maryam Isma'il Jorderh.txt
da Kaka fada ya kare kuma".
Dungure masa kai tayi tace"da'allah labcecen banza ni ba ni wuri na wuc....."kasa karasa maganan tayi jin Muryar Nihla na kiran "Yaya...ya...ya"idanuwanta a rufe gq hawaye na gangarowa da ga cikinsu,saurin mikewa Zafar ya yi ya karasa kusa da bed din ya rike hannuwanta yana cewa"Nihla,ga Yayanki a kusa da ke,me kike so❓"kamar wacce ta yi mumunan mafarki firgigit haka ta mike ta rungume Zafar da iya karfinta kamar za'a kwace mata shi a hankali sautin kukanta ke tashi yana zagaye ko wacce kusurwa da lungu na dakin,ta yananayin kukan nata kadai ya isa ka gane kuka ne mai cike da tarin kunci,takaici da kuma tsananin kewa.
Runtse ido kaka ta yi tana kuma jin wani irin yanayi yana shigarta,lokaci daya jikinta ya dauka tsam kamar wacce aka soka da allura,hanyar waje ta yi hakan yasa Ramadan da Ammi suka bi bayanta don mayar da ita gida.
Miemie kam a guje ta iso wurin gadon ta hada Zafar da Nihla ta rungume tare da fashewa da kuka.
Jin muryar Miemie na yawo a kanta yasa ta dago idanuwanta da suka gama rinewa tare da yi mata nauyi ta zuba su a cikin na Miemie"ki..ki daina..Ku..kuka"ta fada.
Murmushi ne ya subucewa Miemie taja Dogon hancin Nihla tana cewa"kukan farin ciki nake in law".
Zumburar baki Nihla ta yi tare da murgudawa Miemie baki ta juyar da kai,ba Miemie ba hatta Zafar sai da ya murmusa sosai hakan ya yi mata kyau duk da tana cikim jinya.
Karasowa jikin bed din Daddy ya yi yace"y'ata❓sannu kinji,ina yake maki ciwo❓".
Jin muryar Daddy yasa ta tashi da sauri tace"Daddy".
Da na'am ya ansa mata yana kara matsowa kusa da ita.
Ganin Daddy a kusa da ita yasa take ganin kamar Abbanta ne a kusa da ita tace"Abba,kaina kafana ,hannu Abba da ko ina ciwo yake mun".
"Allah ya baki lafiya,sannu insha Allah zai daina kinji,kiyi hakuri haka Allah ya kaddara maki,sannu"Daddy ya fada.
Dr Aminu ne ya shigo bayan sun gaisa da Daddy ne yace"Dr muje a iba jinin".
Kai Zafar ya gyada tare da gyarawa Nihla kwanciyarta kamar jira take ta lumshe ido sai bacci.
Daddy ne yace"jinin za'a kuma saka mata❓"
Da eh Zafar ya ansa "kamar ko yaushe jinin nata ya kone ne ,tana bukatar kari".
"Allah ya baka lada Zafar,Allah shine kawai xai biyaka akan kokarin rike amanar da ka ke yi,Allah ya dafa maku ya kuma biya maku bukatunku na alkhairi".
Da ameen ameen suka ansa sannan Daddy ya tasa keyar Miemie gaba suka wuce gida,dan yasan idan tana nan ba zata taba bari Nihla ta huta ba.
A harabar gidan su Daddy suka iske Kamal yana jiran Miemie a mutunce Kamal ya gaishe da Daddy sannan suka zauna shi da Miemie kallonta ya yi tare da cewa"yan matana wannan fara'a haka❓duk ta mecece❓ke da kika dawo daga asibiti nasa xan ganki fal fa damuwa shiyasa nazo rarrashi tunda tabin ranmu ba lafiya".
Kallonta ta maido gareshi tace"ya akai kasan muna asibiti❓".
"Aunty ce ta gayamun Nihla ba lafiya"ya bata ansa.
Wani irin hade fuska Miemie tayi tare da jan dogon tsaki tace"matsiyaciya kenan,wallahi hakki baxai taba barin Nafisa ta zauna lafiya ba da ita da duk wani mai goyon bayanta cikin tarwatsewar rayuwar yar uwata,sai dai kuma wani hanin ga Allah baiwa ne,cin amanar da zaluncin da tayi hakan be hana Allah zabawa Nihla zabi na gari ba".
"My luv yau kuma Auntyn tawa ake xagi a gabana"Kamal ya fada.
"fin zagima My luv,komai zan iya yi a kanta,tunda bata da tausayi bata da kuma mai fada mata ta ji,a kullun ina takaici da bakin cikin kasancewarta wani bangare a cikin rayuwarka,da ina da yarda zanyi to tabbas zan kankare hakan na raba duk wani alaka a tsakaninku tunda kaima bana da tabbas din ba taudararka zata yi ba,kai nifa ko menene nawa na gane yana da alaka da wannan butulalliyar matar da tayi silar tarwatsewar ahalina wallahi wallahi bazanyi jinkiri wurin rabuwa da shi ba,any way na manta ban fada maka cewar a yanzu Nihla matar Yaya Zafar bace".
Dam dam haka zuciyar kamal ta bada sauti,tuni gumi ya gama rifeshi ga wani irin sanyi dake ratsa jikinsa yace"My luv me nake ji hakan yana fitowa daga bakinki❓wanne irin aure kuma tsakanin Zafar da Nihla❓a yaushe aka yi shi❓kina nufin ko nine nake da alaka da Aunty zaki iya rabuwa da ni❓"kamal ya jerowa Miemie da wadan nan tambayoyin a lokaci daya ya kuma tsareta da idanuwansa da tuni suka gama fita a hayyacinsu,kunnuwansa suka kara tsayi da budewa suna neman ansa kota halin yaya.
Murmushi Miemie tayi tare da cewa"aure da kasan anayi mana,to shine a tsakanin su,da Allah ya rabata da Irfan sai ya bata Namiji adali wanda yasan ciwanta wato Yaya Zafar.Kuma da kake hada kanka da ita dan Allah kama daina,kai ba maciyi amana bane,ba kuma zaka taba kasancewa irinta ba karma ka batamun rai".
Jiki kam na Kamal tuni ya gama sanyi da daskarewa kwakwaran motsima da kyar yake iya aikata shi lallai allura zata tono garma kenan! akwai daukar dala ba gammo kenan sai dai ko da a wasa bazai iya daukar rashin Miemie a tare da shi ba,dan itace rayuwarsa kuma bugun numfashinsa rayuwarsa ma fansa ce ga tata.
Tafa hannu Miemie tayi akan fuskar Kamal tace "ya ya dai❓".
"babu komai,kije gida zan kiraki"be jira ansarta ba ya tashi yabar gidan,a guje yaja motarsa kamar wanda zai tashi sama .Da kallo Miemie ta bishi kafin ta wuce cikin gida tana jin yau jin kanta take kamar wata sarauniya.
Ko daidaita parking Kamal beyi ba ya fito yabar motar a kofar gida da key a jiki ya shiga gidan su Nihla garin sauri har hadawa yake da gudu gudu.Tsakiyar parlon ya yi wa kansa masauki.
A tsorace Aunty da Irfan suka tashi tare da hada baki wurin tambayar ko lafiya.Ruwan sanyi Kamal ya dauka tare da shararawa kansa daga tsaye kafin yace"lallai akwai tashin hankali da matukar damuwa,ina mai bakin cikin sanar da ke cewa Zafar ya Auri Nihla".
Dib haka jin Irfan ya dauke kamar wani gaula haka ya soma bin Kamal da kallo a matukar tsawace yace"karya kake,hakan bazai taba yiwuwa ba,wannan wacce irin zance ne marar kan gado,yarinyar dake asibiti kwance❓".
Ragab haka Aunty ta fada akan kujera tana cewa"Kamal anya ba wani abu kasha ba❓".
"tunda kike da ni kin taba ganin nasha wani abun maye❓maganar gaskiya nake gaya maki Zafar ya auri Nihla".
Wata irin dariya Aunty ya saki tare da mikewa a hassale tace"lallai dole Zafar zai mutu ko da lokacin mutuwarsa beyiba,tabbas idan hakan ta kasance aikin da nayi tsawon shekaru zai iya ruguza shi a yan kwanaki,tabbas shi zai mutu kai idan ya kama har Nihlan ma ta mutu,dole ka kashe su Kamal".
Wani irin zabura Irfan ya yi kamar wanda ciwan hauka ya taba yace"nevee babu jaddawalin kisa a tsarin nan,kina nufin zaki iya kashe Nihla❓".
"Ko kadan banso hakan ba,amma ya zanyi tunda kaddara ta tunzura ni❓"Aunty ta fada.
Kamar wani sakarai haka Kamal kebin Aunty da kallo,tsab kalaman Miemie ke masa yawo da ansa kuwwa a kai,glass cup din hannunsa ya yi wurgi dashi tare da sakin wata kara yace"....
*Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderh✍🏻
[3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*MARUBUCIYAR*
*SANADIN GATA*
*YAUDARA KO BUTULCI*
*DALILIN SO*
*SO DAYA*
*ASALINA*
*ADDININA*
*SHI NE AJALINA*
*RUHIN FANSA 1&3*
*HANAN* paid book
*ABU BILAL* Paid book
*FARAUTAR FARIN CIKI* ✍🏻🤸🏻♀️
84
"kina tunanin zan iya sadaukar da soyayyata dan biyan bukatanki ne❓,meyasa zan kashe Yayan wacce nake so❓ni da ke da kowa kuma munsan yarda take son shi❓sam hakan bazai taba yiwuwa ba Nafisa kidai canza abunyi".Kamal ya fada.
"kamal me yake damunka ne❓har yaushe zaka zabi soyayya akan rayuwarka❓tunda ka riga ka shiga lamarin ya zamar maka dole kamun biyayya kamun kuma abunda nake so ,idan kuma har kayi wasa a kan hakan har ita Miemien da kake takama da ita ina mai tabbatar maka ba zata tsira ba".
Tas tas haka kike jin Kamal ya dauke Aunty da tagwayen maruka har biyu,da sauri Irfan ya shiga tsakiyarsu tare da cewa"dan Allah ku daina wannan fadan,ta hakan ku gaya mun ta ina zaku samu mafita❓rabuwar kai bazai taba kawo masalaha ba".
"ka mare ni❓wallahi ina mai tabbatar maka sai kayi dana sanin marin nan da kayi,tabbas marin nan shine silar rabuwarka d wannan yarinyar da aka haifa a tafin hannuna amma ka wulakanta ni saboda ita"Aunty ta fada.
Hade fuska Kamal ya yi tare da cewa"muddun sunan Miemie bai fita a bakinki ba to ina mai tabbatar maki ke zaki fara yin dana sa ni a rayuwarki,wanda nasan sai kinyi din ma,ki sa ni duk wani iya shege da iskanci da kike nema gidan shi ki ka zo,bazanyi jinkiri ko daukar lokaci ba wurin yin maganinki ki tuna wannan"be jira cewarsu ba ya yi gaba abunsa.
Daura hannu a ka Aunty ta yi tare da koma sharab akan chair ta fada tana fadin"innalillahi tabbas rabuwa da Kamal kamar wani tonan asiri ne na rayuwata".
"kin aikata wa ni abun ne da baki so kowa ya sa ni❓"Irfan ya tambaya tare da zuba mata idanuwansa wanda tuni sun gama canza kala dauriya ce kawai yake yi.
"a'um dama ba ga dukiyar dana kwasa ba nan na baka,shi ne nake gudun tonuwar hakan".Aunty ta fada a daburburce.
Gyada kai kawai Irfan ya yi kafin ya fita daga parlon.Tafiya yake amma kamar wanda bashi da lakka ,kwata-kwata be ga ne gabas bare yamma ko kadan be san wacce duniya yake ba,kamar wani zautacce haka yake tafiya,hannunsa ya daura a kan kumatunsa tuni yaji damshin hawaye ,gyada kai kawi ya yi yana tunanin iya tsawon shekarun daya dauka beyi kuka ba,lallai dara taci gida,yau wani aikin ya juye da farin cikin rayuwarsa,tabbas ya dauki tsawon lokaci ya na farautar farin cikinsa amma yau rana daya kab komai ya rushe duk danadin da ya yi akan hakan amma ya tashi a tutar ba bu,lallai Al-amarin Allah sai kallo,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un sune kalaman dake fitowa daga bakinsa,hakan ya yi daidai da faduwa akan gwaiwowinsa da ya yi ya fashe da wa ni irin matsanan cin kuka mai matukar cin rai da kunci.
A hankali take taka kafarta tana bin bayan Zafar tsab ta warke ras sai dai rashin kwarin jiki a haka har suka shiga mota suka bar harabar asibitin dan kishin gidawa ta yi tare da lumshe idonta,tsayawar da motar ta yi yasa ta dago lumsassun dara-daran idanuwanta ta zuba su a cikin in da suke,wani irin zabura ta yi ta mike sosai a motar tana rau rau da ido kamar zata fasa ihu cikin rawan murya tace"Ya..ya..yaya meyasa ka..ka..kawo ni nan❓ka mayar da..da ni gida".
Ko kallonta be yi ba yace"nan ne gidanku da ga yanzu dan haka ki fito bana son shirme".
Kara rudewa ta yi jin ya ambaci nan ne gidan su,a tsorace ta saka kafarta da sauri ta fito ta kama rigarshi daga baya ta rike kamar wanda ya yi mata sata,kyafta ido kawai take daka ganta kamar an tsoma kaza a ruwan zafi.
"ki sa ke ni mana".Saurin girgiza kai ta yi ta kara boyewa a bayansa tace"Dan Allah ka mayar da ni gida,wurin Aunty zan je".
Kamar wanda aka safkarwa da mutuwa haka ya hade fuska yace"idan kika karw kira mun wannan sunan a gidan nan sai na sassaba maki,oya wuce muje".
Make kafada ta yi a dole ya yi gaba ta bisa baya tana rike da shi har cikin parlon.Kuuuuu haka cikinta ya bada sauti kamar zata saki zawo a wurin jin muryar Hajiya Kaka a parlon afkawa ta yi bayan Zafar ta rungumesa da karfi tuni kyarma ta kace mata ko kadan ta kasa lekowa ta kalli parlon,cak Zafar ya tsaya jin an cukuikuye shi,dariya Ammi ta yi tace"a'a Malan Muhammad a karaso mana".
Shafa kai ya yi kafin yace"taya zan karaso bayan ta mun daurin goro?"
Nokews suka yi kowa a dariya,kamar daga sama haka Muryar kaka ta karade parlon tana fadin"Maryama zo nan kinji".
Raba ido Nihla ta fara yi,janye jikinsa Zafar ya yi kafin ya juyo yaja hannunta,suna tafiya a hankali tana tsaitsayawa a baya,gaban Kaka Zafar ya tura Nihla,kamar wacce tawa sarki karya haka ta dukar da kai tare da kama jikinta jira take a ce ar ta saka gudu.
Kallon yarda take yi ne yasa Miemie da Ramadan sakin dariya ,hararar da Zafar ya jefa masu ne yasa sukayi shiru ba shiri.
Kamar da ga sama ba zato ba tsammata sai dai aka ga Nihla a jikin Kaka ta rungumeta,fuskarta fal farin ciki ga hawaye na bin gefan idonta.
Sosai kowa ya cika da mamakin hakan,dan ko da wasa babu wanda ya taba kawo wa ransa hakan zata faru ko Kaka zata karbi Nihla ta sauki haka .
Basu gama karewa da Mamaki ba sai da kaka ta dago Nihla ta tarbi fuskarta da hannu bibbiyu ta fara magana"ban taba tunanin kara sake dawowarki a gidan nan ba,sai gashi da kika tashi dawo wa ba kin dawo a matsayin jika ba kawai kin dawo harda matsayin da nake da buri a kanshi,lallai kina da sa'a daya kasance kin kama zuciyar jika mafi soyuwa a gare ni,duk wani farin cikin mu yana tattare da nashi,barka da zuwa Maryama Zafar Al-ameen sirikar gidan nan ta farko".
Dib haka jin Nihla ya dauke ko kadan tama kasa fahimtar menene kalmar sirika ke nufi❓kamar wata doluwa haka take bin Hajiya Kaka da kallo,ganin yananyin da take yasa Ammi zuwa ta kamata tare da cewa"muje kiyi wanka ki huta kinsan yanzu kika dawo da ga asibiti".Bin Ammi kawai take duk abunda take tana daga mata kai ne kawai amma sam bata ko fahimta kwatakwata ta kasa gane tareyen da Hajiya kaka tayi mata,a haka ta samu tayi wanka tea kawai tasha kasa kara saka wani abun a bakinta ta yi gaba daya zuciyarta a cushe take bata gane ma duniyar da take,kamar daga sama a jikin window din da take ta hango Irfan na shigowa cikin gidan taku yake yi irin na cikkakun maza,ganin yana doso kasan window d take yasa ta dukar da kanta dan taga shin wai da gaske nan yake tahowa❓lallai kam Zafar ta ga ni tsaye ya zuba hannuwansa cikin aljihun wandonsa a hankali yake taunar lips dinsa tare da tsotsa kamar zai huda.Baya tayi zata fadi sai tayi saurin dafa bangon da take ji,ganin sunyi musaba yasa ta saurara dan jin abunda suke fada.
"kamar ko yaushe Zafar da nake gaya maka bana da niyar futar da Nihla,Nihla ita ce rayuwata,itace farin cikina,zan iya sadaukar da rayuwata dominta,amma yau naji wani batu wai Nihla ta kasance mata a gareka,tabbas bazance nayi bakin ciki ba sai dai zance nayi farin ciki da hakan dan tabbas nasan Nihla zata samu kula,zata samu kuma wanda zai iya sadaukar da komai nasa a kanta wanan shine burina tun asali ko ni idan zan gagara kula da nihla zanyi fata allah ya turo mata da jagora wanda zan jibanci maraicinta alhmdllh addu'ata kuma ta ansu".
Hannu Zafar ya daga tare da tsayar da Irfan yace"duk menene na wannan maganganun❓kana son farin cikinta kuma ka zabi cutar da ita❓kaine jigon bakin ciki da kuncin rayuwar Nihla a yanzu bata da matsalan daya wuce kai Irfan ya kamata ka gane haka,dama dan ka gaya mun wannan maganganun akan Matata yasa kazo nan❓,to thank u find a way just leave".
Wasu hawayen bakin ciki ne suka zubowa Irfan yace"komai zaka gaya mun bazan taba jin haushi ko kunci a kai ba,nasan duk kallon da kowa kemun kenan,amma ina so na fada maka har gobe har jibi ba za'a tabayin namijin da zaiwa Nihla soyayyar da nake mata ba,sai dai na yarda Allah bai halicce mu dan mu kasance tare ba,ni ban zabi na kuntatawa Nihla ba sai dai rayuwa ce ta zo da haka,nayi hakan ne na sadaukar da soyayyata dan na ceto Nihla daga tarkon da take niyar fadawa na kishiyar uwa,na sadaukar da farin cikinmu ne dan na samawa Nihla rayuwa mai kyau a gaba,nayi duk wannan ne dan gujewa rudin zuciyar Nafisa da take kokarin mallakar dukiyar Nihla kota halin yaya,na anshi soyayyar Nafisa ne badan ina sonta ba sai dai amfanin masoyiyata wanda nasan da naki hakan tabbas wani labari ake yi ba wannan ba"jikka ce Irfan ya mikawa Zafar yaci gaba da cewa"ka ansa wannan duk wani dukiyar Nihla ne da Nafisa ta bani akan na adana mu yudu da shi,ni kuma bazan iya cin hakkin wani bawa a duniyar nan ba,tabbas hakan ya yi mun amfani ko da zan kasance cikin bakin ciki amma nasan Nihla zata rayu cikin farin ciki,and shawara daya ka yi kokari ko ta halin Ya ya ka kubutar da Miemie daga soyayya da Kamal"yana gama fadan haka ya juya zai tafi,hannunsa Zafar ya rike tare da cewa"kana nufin kayi duk wannan ne dan kubutar da nihla❓"
Murmushi kawai Irfan ya yi tare da gyada kai yace"ni zan wuce".
"hakika baki da duk wani abu da zan malllaka maka yayi kankanta wajen gode maka ,kai namijin kirki ne,wanda irinku ko wacce mace zata bukata ta samu,tabbas kowa ya kalleka da mumunar fuska sai dai hakan bai gushe ba face sai da alkhairanka suka bayyana gare mu,kayi hakuri da nesanta ka da farin cikinka da na yi,Abba ya daura aurena da Nihla ne a ranar da zai bar duniya badan haka ba babu abunda zai hanani sadaukar maka da soyayyata dana raina na jima ina jinta tun kallon farko dana dauki Nihla a ranar da aka haifeta,na rayu ne akan soyayyarta kuma soyayyarta ita ke bani kwarin gwaiwa da jarumta da kara son kasancewa tare da ita".
"Wannan bazai taba zama da matsala ba Dr,tabbas na cika da farin ciki da kai ka auri Nihla nasan ko bayan raina kai Garkuwanta ne"Irfan ya fada fuskarsa cike da fara'a Juyawar da zaiyi idanuwansa suka sarke a cikin na Aunty wacce take tsaye bayan Irfan ta kuma gama jin duk wani batu da suka tattauna,wani irin kuka ne ya kubce mata ta yi waje a guje .Share guntun hawayen da suka zubo masa ya yi kafin ya yiwa Zafar sallama ya fice faga gidan shima.
Kamar watq statue haka take sulalewa zuwa kasa,ko kadan bata iya banbance tanayin da take ciki,wani irin kuka mai cin rai ta saki tare da kwala kiran sunan