Showing 6001 words to 9000 words out of 32417 words
Chapter 3 - Farautar Farin Ciki Hausa Novels Document Na Maryam Isma'il Jorderh.txt
Aunty tana tambayan Abba ya jikin Nihlan,kafe Zafar tayi da mayun idanuwanta wani irin mumunan kallo ya jefa mata wanda yasa hantar cikinta juyawa ta kuma ɗauke fuska da sauri, Zafar kam gaban Abba ya tako tare da duƙawa gabansa yace"Alhmdllh Abbana yanzu tana cikin koshin lafiya tana ɗakin hutu".
Hannu Abba ya ɗaga yana godewa Allah daya bashi lafiyar ƴarsa kafin ya ɗaura da godewa Zafar.murmushi yaɗan saki tare da cewa"Abbana ka daina godemun yiwa kaine itama ae kamar ɗaya take da Miemie a wurina".
"DR mun gode ƙwarai,Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci ya kuma ƙara ɗaukaka".
Wata irin juyowa Zafar yayi yana taune lips ɗinsa kamar zai huda iska mai zafi ya fesar kafin ya tashi yabar wajen.da wani irin mayataccen kallo Aunty tabi Zafar tare da haɗiye yawu muƙuttt kamar a yau ta fara ganinsa kullun idan zata gansa da irin kallon da take binsa dashi kenan.
Miƙewa Abba yayi tare da cewa"Hajiya Nafisa muje mu ganta".
Firgigit Aunty ta dawo daga duniyar tunanin data lula tana kallon Abba tare da sakin murmushi kafin tabi bayanshi suka shiga ɗakin da Nihla take,drugs Abba ya gani duka an siya kallon nurse ɗin dake ɗakin yayi yace"Muhammad bai gajiya shine ya siya maganin ko?"
Fuskarta ɗauke da fara'a tace "eh ƴallabai".
Sosai Abba ke jinjina karamci da tausayi irin na Zafar wanda daya biye mahaifinsa da yanzu baya tare dasu balle har ya zama Garguwa ga cutar da Allah ya ɗaurawa Nihla.
Ganin Nihla nata baccinta hankali kwance yasa Abba cewa zaije ya dawo amma nazai jima ba,sai da Aunty tayi masa rakiya har ƙofar ɗakin kafin ta dawo ta zauna tana saƙawa da kwancewa a rai.
Wayanta ta ɗauko tare da dannawa number Irfan kira,zaune yake a gefan katifarsa yana ɗaure igiyoyin takalminsa da yake sakawa yaji wayarsa na ruri,hannu yasa tare da ɗaukowa,tsurawa number ido yayi ganin besanta ba tana kuma niyar tsinkewa yasa ya ɗauka tare da faɗin "hello"
Wani irin lumshe idanuwa Aunty tayi tana jin muryar Irfan na ratsa duka wani lungu da saƙo na sassan jikinta cikin salo da jan hankali ta langwaɓar da murya tace"barka dai farin cikina! haba ya kake son wahalar da zuciyar da tunaninka ya riga ya gama hudata Irfan? haƙiƙa bana da wani sukuni ko farin ciki idan har ka kasance da yiman rowar kanka ko muryarka,ina fatan ka gama tunani dayin zaɓi mai amfami akan tayin dana maka Irfan ina matuƙar sonka kuma na maka alƙawarin yi maka komai sa sadaukar da komai akan soyayyarka,kaine namiji na farko dana fara so ,ina fatan bazaka taɓa bani kunya ba".
Tunda Aunty ta fara magana Irfan ya rasa wacce duniya yake shin sama yake ko ƙasa?,duk yanda yake ji sai dai hakan bazaisa ya cutar da kansa ba ko ya kori alkhairin daya doso shi cikin ƙaramin lakaci.
Murmushi ya saki yana jin wani sanyi har cikin ransa cike da ɗauki da daɗɗan murya yace"ki ɗauka a ranki cewa IRFAN nakine Auntyna kece mai sarrafa farin cikinsa da duk wani akalar rayuwarsa,Irfan bazai taɓa kaiwa ko ina ba in har babu ke Masoyiyata ,waye zai zaɓi wahala da soyayyah akan kuɗi da tsaleliyar Hajiya irinki,ke kyajyawace danni idan ina kallonki ina maki kallon ƴar shekara 18 ne dan zan iya cewa kin fisu komai ma Hajiyata".
Wani irin daɗi farin ciki,natsuwa suka dirarwa Aunty lokaci ɗaya baki na rawa tace"na gode farin cikina,nayi maka alƙawarin sauyawar rayuwanka tun daga yau"
*ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE*
JORDERH CE✍🏻
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*wannan page din sadaukarwa ne ga farautar farin ciki fans,ina jin dadin comments dinku dan haka ga kyautar page kuyu yacce kuke so dashi*
Page 26~30
Sauke wayan AUNTY tayi tana jin farin ciki na ratsa duka sassan jikinta,ji takeyi kamar duk duniya tafi kowa gata da samun dace,wani irin murmushi ta saki tana cewa"yesss sora kuma plan b yanzu ne lokacina yayi".Jin tarin NIHLA yasa tayi saurin juyowa tana fadin"Alhmdllh sannu Nihla ya kikejin jikin naki?".
A hankali ta soma bude lumsassun idanuwanta wanda suka mata nauyi,kallonta takai ga Aunty kafin tayi kokarin sakin murmushi mai kama da kuka cikin nishewan murya tace"ruwa".
Karasowa tayi tare da taimaka mata ta tashi,sannan ta zuba mata ruwa a glass cup ta dauka tare da kaiwa bakinta,biamillah tayi ta daura hannunta akan na Aunty ta soma shan ruwan tasha da yawa kafin ta janye bakinta daga cup din tana mayar da numfashi.sannu cewar Aunty.kai kawai ta gyaɗa mata kafin tace"AUNTY Irfan".
Wani kallo mai wuyar fassaruwa Aunty ta jefa mata kafin tace "meye ya faru da IRFAN din kuma?".
ƙasa NIHLA tayi da kai ta kasa cewa komai ta fara wasa da ring ɗin dake sanye a zara~daran fararen yatsunta.dafata AUNTY tayi kafin tace"Maryam kin ɗaukeni kamar mahaifiyarki,munyi zaman lafiya da Amminki hakan yasa tana haiguwarki ta bani ke a matsayin amana,baki buɗe ido kika ga wata ba matsayin uwa sama dani kuma Allah yasan nayi kokarin riƙeƙi amana Maryam,ki ɗaga ido ki gaya mun damuwanki tun jiya nake lura dake baki da sukuni".
Hawayen da suka soma zubo mata a fuska tasa hannu ta share cikin dishewan murya tace"A..a...Aunty sh..shi..shine inata kiransa wayan bata..ta..ta shiga".
Murmushi Aunty ta saki tace"na farko dai da zan bawa ƴata shawara ta ɗauka yau dana gaya mata ta kwantar da hankalinta ta daina tashin ciwanta akan IRFAN,duk abunda yake naka ne zaizo gareka duk daɗewa,Maryam bana so ki riƙa raunata kanki akan soyayyar da bata kamace ki ba,kisa ranki a inuwa ki kwantar da hankalin ki in Allah yaso komai zaiyi daidai ,ki daima tashin hankalinki".
Gyaɗa kai kawai NIHLA tayi dan ita kadai tasan me takeji a ƙahon zuciyarta,kamata Aunty tayi ta kaita toilet ta hada mata ruwan wanka bayan ta gama ta taimaka mata ta shirya kafin ta tsareta tayi breakfast ta kuma bata drugs,tuni taji daɗin jikinta sai dai rashin ƙarfin jiki.
Jib dib dib haka zuciyoyinsu ke bugawa a duk lokacin da suka zo kusa da juna,tsayawa yayi jikin ƙofar tare da runtse ido da ƙarfi kafin yayi ƙarfin halin tura ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.Aunty ce ta ansa sallaman da ido ya bita yana kuma yin kicin-kicin da fuska ya rasa me yasa yakejin tsanar matar nan duk lokacin dazai ganta sai yaji kamar ya haɗiye zuciya saboda tsabar takaici da ƙunci.ɗaure fuska yayi kamar an masa sanarwar mutuwa ya ƙarasa shigowa kai tsaye gaban gadon Nihla ya isa cikin murya da sai ka saurara sosai zakaji me yake fada yace"akwai in da yake maki ciwo ne?".
Ɗago dara-daran idanuwanta tayi ta kalleshi suna haɗa ido tayi saurin yin ƙasa da kanta tayi narai narai da fuska kamar zata fasa ihu.wani irin haushi da takaici suka saka ZAFAR a gaba hannu yasa ya bige mata ɗan ƙaramin bakinta da take turowa ya kuma ɗaga hannun da niyar kama kunnenta.
Kuka ta saki tayi saurin kaucewa tana faɗin"ni ba abunda yake mani ciwo".
Harara ya watsa mata tare da sakin siritin tsaki yayi waje abunsa .bayanshi tabi da harara tana guni ƙasa ƙasa.sarai yana jinta amma beko juyo ba ya fice abunsa.
Kai tsaye gida

Kai tsaye gida ya wuce,Kabir ne yake jan motar har suka karasa gida bece komai ba a motan yanata dannar labtop din shi,a parking lot ya ajiye motar sannan suka fita a tsaye ya samu Idi mai gadi yana masa sannu da xuwa,fuskar shi kadaran kadahan ya basa hannu cike da girmamawa yana fadin "BABA IDI barka da ƙoƙari".
"barka dai magajin Alhaji,,,,sannu da wowa".
Ansawa yayi tare da juyawa yana kallon jerin motocin da aka ajiye ,kafin ma yayi magama Idi yace"yanzu ba dadewa Dan uwanka yaje ya dauko ALHAJI basu daɗe da shigowa ba".
Jinjina kai yayi tare da cewa"bara na shiga ciki"a fito lafiya suka masa kafin ya wuce cikin gidan.
murmushinsa mai kyan gani ya saki lokacin da idanuwansa suka sauka a kan wani farin kyakyawan Dattijo dake zaune cikin shiga ta alfarma gefansa Ammi ce sai a ƙasa Ramadan da Miemie kowa fuskaraa cike da fara'a.cikin takunsa mai ɗaukar hankali ya ƙarasa gaban Daddy tare da ajiye gwaiwowinsa a ƙasa tafukan hannayenaa ya ɗaura akan cinyar Daddy murya a disashe yace"ko dai nayiwa Daddyna laifi ne,da zai shigo gari ba tare da sani na ba?kuma be nema naje ɗaukosa ba"
Janyo hannunsa Daddy yayi ya miƙar dashi ya kuma zaunar dashi a kusa dashi,,hamnunsa ya ɗaura akan kafaɗar Zafar fuska cike da fara'a yace"bana tunanin Zafar zaimun laifin dahar zan kasa saka shi ɗakko ni,naga kana da ayyuka da yawa ne shiyasa nasa Ɗan uwanka ya ɗauko ni".
Gaɗa kai Zafar yayi alamar gamsuwa kafin yace"ina fatan ka dawo cikin aminci kuma lafiya qlau?"
"lafiya Alhmdllh,ku tashi muje mu gaishe da Hajiya dama jiranka nakeyi ka dawo".
Kicin kicin da fuska Zafar yayi tare da danne jajayen lips ɗinsa kamar zai huda amma ya kasa faɗin komai.
Miƙewa Ammi tayi tace"to sai kun dawo bara na shirya dining kafin ku dawo".
Miƙewa Miemie tayi tana sharara dariya ganin Ramadan yana ta cin magani shima.
Wani banzan kallo ya mata yace"hala na zama taaran wasan ki?".
Buɗe baki tayi da niyar fara surutun nata,"kada ku dame mu a nan"sukaji Zafar ya faɗa kafin kace me duka kowa ya adana maganar da yake niyar yi suka yi gaba.
Tsaki yaja kafin ya miƙe sukabi bayan su Miemie zuwa parr ɗin Hajiya kaka.
Sallama ɗauke a bakinsu suka shiga ,zaune yake akan capet tayi ɗaiɗaya ga apple a hannunta tana ci yayin da ƙafarta ke miƙe akan tum tum sai cika take tana batsewa.kallon su ta soma yi ɗaya bayan ɗaya sai da kowa ya gama zama sannan ta saki fuska tace"a'a Aminu sannu da shigowa,ya hanya?yanxu nake cewa na shigo sai ka rigani kuma sannu da zuwa".
Kan Daddy a ƙasa yace"yauwa Hajiya,barka da gida ".
Ramadan da Miemie ne suka haɗa baki wajen gaiaheta fuska a sake ta ansa tace"ke uwar kilbibi me kila dawo yimun a gida?".
Dariya miemie ta saka tace"da kika samu nazo ko?ina nan zaki zo nemana"
Sai a lokacin Zafar yace"barka da hutawa".
Kamar jira take ta ɗago tana zabga masa harara cike da masifa tace"da ban wuni ba da zaka ganni sarkin mararsa kunya?tun ranar daka gama ɗebemun albarka ka kara shigowa ka gaishe ni ne?to bari kaji dama na tsaya ubanka ya dawo ne sai in ji ta ina ya samoka da har zanaa doka kabi ka take,shege labcecen banza".
Wani irin takaici ya turniƙe Zafar yace"dama gudun wannan faɗan naki yasa bana shigowa ɗin,zancen gaskiya kuma a zamanin nan ba'ayin haka ,ido kika fini ne da zaki min zaɓin mata?".
Hararan da Daddy ya zabga masa ne yasa ya miƙe da sauri yana ficewa daga part ɗin,KAKA na ƙwala masa kira amma ko juyowa beyi ba bare tasa ran zai ansa mata.
"Aminu kana gani,akan idonka Ɗanka ke wulakantani amma ka saka ido kana kallo to ina so kaje ka gaya masa har gidan nan sai nasa ka koreshi dan be isa ya gaya mun maganar banza ba".
ƙasa Daddy yayi da kai yace"Hajiya dan ALLAH kiyu haƙuri insha Allah zan masa magana hakan bazai kuma faruwa ba abunda kike so kuma shi za'ayi".
Tsaki taja tana faɗin "yadai fi maku wallahi"ta ƙare maganar tana cin apple ɗin dake hannunta.sallama suka mata kafin suka taho.
Zafar kam yana shigowa parlo yaci karo da glass jug na ruwa ƙafa yasa ya halbasa ya tarwatse akan tayil lafin yabi ta ciki ya wuce yana huci.
Ammi dake tsaye hammunta riƙe da kula ta bisa da kallo ita kam ta rasa wacce irin zuciya Zafar ke gareshi kuma ina ya gadota ita lamarinsa ma har tsoro yake bata,girgiza kai tayi tace"Allah ya shirya,Lantana kizo ki gyara parlon nan"ta ƙare maganar tana ci gaba da harkokinta.
Tsaye take da waya a kunne shiru tayi alamar tana jin abunda ake faɗa kafin tace"komai ya daidaita Kamal yanzu shiri na gaba kawai ya kamata,banga dalilin sake ɗagawa ba kuma ina so nan da kwana huɗu komai ya tafi mun yacce nake so".
Dariya sosai Kamal yayi kafin yace"da kyau giwar mata cika burinki yana burgeni zuwa gobe zan shigo sai ayi komai yarda ya kamata amma ina so ki kula da kyau".
"baka da matsala da wannan"abunda Aunty ta fada kenan tare da kashe waya.
a ranar aka sallami Nihla daga asibiti danta warke dama haka ciwan mai sikila yake kamar bugun aljannu.
*ALLAH KA GAFARTAWA IYAYENMU KAYI MANA KYAKYAWAN ƘARSHE*
*Gobe bazanyi typing ba dan zanyi tafi*
JORDERH✍🏻
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Page 31~35
Da matukar karfi Zafar ya fizgi kofar dakinsa ya shiga ,jujuya kai ya soma yana jin kamar zuciyarsa zata fasa kirjinsa ta fito dan takaici,hannuwansa duka biyu yasa yana cukuikuya sumarsa,fadawa yayi akan chair yana fesar da numfashi,jiki a sanyaye Ammi ta gama jera abincin ta fito ta haura sama dan duba Zafar.
Bakinta dauke da sallama ta shiga dakin,tsaye tayi tana kare masa kallo yacce ya hada kansa da gwaiwa daga gani kasan kwata-kwata bashi cikin hayyacinsa karasowa tayi tare da zama gefansa cikin sanyayyar murya tace"Muh'd?
A hankali ya dago rinannun idanuwansa wanda suka soma sauya kala ya zubawa Ammi su ,hannuwansa duka biyu ta runtse cikin nasa tana furta"innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Allahumma ajirni fi musibati wa'akilibni khairan min ha".
Kamar mai koyon magana ya soma maimaita duk wata addu'a da Ammi ke karantawa cikin kankanin lokaci yaji zuciyarsa ta masa sanyi kwantar da kansa yayi akan kafadar Ammi yana sauke ajiyar zuciya.
Murmushi tayi cikin san jan hankalinsa tace"kada ka sake fushinka ya rinjayi tunaninka muh'd,ko wanne irin hali ka kasance a ciki karka manta da neman dauki daga mahaliccinmu nasan ka sani kuma ka iya amma wannan zafin zuciyar naka ya daina rudarka kaji".
Ido ya zubawa Ammi kafin ya dauke tare da furta"insha Allah Ammi zanyi kokarin yin haka".
Hannu ta daura a tulin sumar kansa tace"Allah yayi maka albarka muh'd,Allah ya zama gatanka ya kyautata mun rayuwarku kai da y'an uwanka".
Wani kyakywan murmushi ya subuce masa tare da furta"ameen ameen Mamana".
Janyeshi tayi daga jikinta ta mike tare da kama hannunsa tace"muje kaci abinci".
Bai iya mata musu ba haka yabi bayanta har suka safko,a dining suka iske su Abba suna zaune Miemie harta zuba masu abinci suna niyar fara ci.
Karasowa sukayi Ammi tace"Affuwan Daddy bansan kun shigo ba".
Murmushi yayi yana kai spoon cike da shinkafa a bakinsa yace"don't u worry,ae kara a lallaso sarkin zuciya ,kafin ya gama fushin yazo kuma yayi biyayya akan zabin kakar tasa".
Wani irin kwalalo dara-daran idanuwa Zafar yayi