Showing 21001 words to 24000 words out of 32417 words

Chapter 8 - Farautar Farin Ciki Hausa Novels Document Na Maryam Isma'il Jorderh.txt

tare da share kwalla tace"Maryam kin haifo mani bala'i,amma ina so ki sani ajalinki kika haifa ba dai ni ba,wallahi ba'ayi dan da zai kashe ni ba,ni Zafar ke kika barauniya,kuma zai wulakanta ni"wani kukan ta kuma saki taci gaba da cewa"ki kira mani Aminu yau sai ya zaba ni ko Zafar a gidan nan,kuma yazo ya fitar mun da karuwar daya kawo a gaban idona ya dauketa ya haura sama".




"Hajiya dan Allah kiyi hakuri,wallahi bansan yayi haka ba,dan Allah kibar kuka,yanzun nan zan maki maganinsa,dan Allah kaka ki share hawayenki"Ammi ta fada.


A hassale kaka tace"to uban waye yace kuka nake❓,bakin ciki ne yamun yawa da bansan ruwa ya fara fita a idona ba,wallahi wallahi nan da sati mai zuwa sai an daurawa yaron can aure,zamu gani ni da shi waye a gaba,idan bazaiyi aure ba sai dai yabar gidan nan,dan bazai janyo mana abun kunya ba,Duk laifi ai naki ne,ko tarbiya ta gagare ki❓wallahi kin ban kunya Maryam"bata jira cewar Ammi ba ta fice daga dakin tana kwalawa Ramadan kira.


Da sauri Ammi ta mike ta nufi hanyar dakin Zafar ,tana zuwa ta soma buga kofar tana fadin"Muhammad ka bude kofar nan yanzu".




Jin muryar Ammi yasa ya yunkura,saurin rikosa Nihal tayi tana gada masa kai cikin muryar kuka take fadin"Kaka zata kashe ni idan ka bude,ni sai ka mayar da ni gida".


Shafa kanta yayi tare da cewa"babu abunda zai sameki".Cire hannunsa tayi daga rikon data masa yazo ya bude kofar.


Carab Ammi tayi da kunnansa tare da murdawa tace"kai kullun burinka ka janyo mun fitina kaji dadi ko Muhammad"


"ahhhh,ashhh Ammi kunnena zai cire,ki daina biyewa rikitacciyar tsohuwar can wallahi".




*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*
*Dan Allah duk wanda ya karanta ya taya ni da addu'a ina da bukata a wurin Allah,fatana Allah ya cika mana burukan mu gaba daya*




Jorderh✍🏻
[3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇


```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```






*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


79




"Kakance kake kira da haka❓neman maganarka yayi yawa ko Muhammad"cewar Ammi ta kare maganar tana duban in da Nihla take duk ta takure alamar a tsorace take.Sakin kunnan nasa tayi tare da sakin kayataccen murmushi lokaci daya ta furta" 'yata".


Jujuyawa Nihla tayi ta hango ko ba kowa a tare da Ammi,ganin ba kowanne yasa ta kara so da sauri tare da tafiya zata duka a gabanta.Saurin riko kafadunta tayi tare da rungumeta a jikinta tana sakin ajiyar zuciya kafin ta zaunar da ita a chair suka koma suna fuskantar juna.Sunkuyar da kai Nihla tayi tare da cewa"Ammi ina ina wuni"


"lafiya qlau alhmdllh,ya hakuri da rayuwa❓"Ammi ta bata ansa.


"Alhmdllh"shi ne abunda ta samu damar furtawa kawai.


"ki saki jikinki Nihal ,ko kin manta a nan din gida kika dawo❓,ki daina tsoron Hajiya nasan duk abun nan da take yi ba zata iya cutar da ke ba.Hajiya tana da kirki sosai misalinta kamar kwakwa ne,a waje tana da matukar tauri da wuyar fahimta amma a ciki tana da tsananin taushi da tausayi sosai".Ammi ta fad'a.




Kwanto da Kai Zafar yayi akan kafadun Ammi tare da cewa"ke dai dan tana sirikarki shi yasa ko yaushe kike a bayanta".


Wani irin dundu da aka saukewa Zafar a baya yasa shi saurin dagowa yana so yaga wanne isashen ne,wa idon sa zai gane masa in ba Hajiya kaka ba❓.Fuskarta a matukar daure babu alamun annuri a tattare da ita.


"nayi maki wani abunne da zaki mun dukan nan❓"Zafar ya tambaya.


Ko kadan Kaka batayi ta kansa ba illa kallonta data mayar ga Nihla tare da cewa"ke maza ki bace mun da gani,ki kama gabanki wannan ya zama takunki na karshe a cikin gidan nan".


Da sauri Nihla ta mike tana niyar antayawa da gudu,ko ina a jikinta banda tsananin kyarma babu abunda yake yi,rike hannunta Zafar ya yi ya juyo yana kallon Hajiya kaka tare da cewa"shiyasa na kawota dakina,kuma bangarena ba naki ba,ban kuma san lokacin da kika fara kirgawa yan gida mutanan da kike so su shigo ba".




Nu na shi tayi da yatsa tana cewa"ba da kai nake ba,ka bari nayi magana da wacce zatayi ta kanta a gidan nan".


Saurin mikewa Ammi tayi tana fadin"Hajiya dan Allah kiyi hakuri,kai kuma Muhammad kada na sake jin bakinka a wurin nan".


Sallamar Daddy ce ta katse masu maganar su,da sauri Nihla ta janye hannunta daga rikon da Zafar ya yi mata ta karasa gaban Daddy da sauri,wani irin kauna bege da kuma tsananin tausayin kanta ya taso mata ganin Daddy ya kuma tunzura ta tana ganin kamar zata ga Abba a bayansa,wasu zafafan hawaye ne suka kawo a idanuwanta.Tsaye ta tsaya cak ta kasa motsa tare da zuba idanuwanta akan fuskar Daddy.


Murmushi ya sakar mata tare da bude hannuwansa yace"shikenan tunda ba Abba Umar bane kin rasa damar zuwa ga mahaifinki❓ ba za ki sake jin dumin Mahaifi ba❓ "


Wani irin kuka ne ya kubce mata da matukar sauri ta fada jikin Daddy tana shashekar kuka.bubbuga bayanta Daddy ya shiga yi tare da fara lallashinta.


Kamar wata statue haka Hajiya kaka ta daskare,ido suka hada da Zafar ya yi mata kwalo,saurin kawar da kai tayi tare da fadin"Al-ameen".


Ansa kiran Daddy ya yi tare da karasowa gabanta.Cike da isa da gadara tace"ina so yarinyar nan ta bar gidan nan.Bana kuma fatan sake ganin kafarta a gidan nan,ina kuma umurtarka da cewa nan da sati daya ka daura auren Zafar da Aisha".


"to" shi ne abunda Daddy ya fada sannan yaci gaba da cewa"bawai naki ta taki bane Hajiya,sai dai yau gani a gabanki a matsin Umar ina rokonki da kuma baki hakuri,Umar yana gabar mutuwarsa amma ke yake ambata da kuma tabbatar mun da cewa shi bai aikata abunda kike zarginsa da shi ba,yana kuma umurtata da in nema masa yafiyarki,in kuma rike masa Maryama amana,Maryama marainiya ce Hajiya bata da kowa kuma kinsan ita din dawainiyar Zafar ce tun daga ranar data diro duniya,haka zalika Mahaifinta ya kuma damka masa amanarta ,kuma Zafar bai gajiya ba ya ansa ya kuma yi alkawarin riketa kamar yarda yawa mahaifiyarta,shin Hajiya zaki so jininki jikanki mafi soyuwa a kama shi da laifin cin amana❓da kuma kasa rike alkawarin daya dauka❓ wannan karan amanar daya kuma dauka tana da matukar girma fiye da wacce kika sani"


Hannu ta daga masa alamar ya isa kafin tace"idan bashi ya yi ba wa ya yi❓ shi kuma jikan nawa a haka zai kare da rikon amanar mai lalura❓duk wani abunda ya tara sai ya kare a kanta❓"


Murmushi kawai Daddy ya yi kafin yace"Ummana idan lokaci ya yi zaki sani,dan Allah ki yafewa Umar ki kuma bari Zafar ya sauke nauyin daya dauka akan Maryama,ka da ki hukuntata da laifin da aka aikata tun tana zanin goyo".


Kasa furta komai Hajiya kaka tayi ta raba ta gefan Daddy ta wuce da sauri shi da Ammi suka bi bayanta.


Saurin mikewa Nihla tayi bakinta na rawa take fadin"Yaya zan tafi gida,dan Allah kada ka hanani".Kafin Zafar ya yi wata magana tuni ta runtuma a guje .Murmushi kawai yabi bayanta da shi,sosai murmushin ya haskaka fuskarsa ya yi matukar yi masa kyau ya kuma fito da ainahin zallar kyawu na fuskarsa.


Ko kadan Nihla bata tsaya ba sai da ta shigo cikin tsakiyar parlon su,a nan ta tsaya tana mayar da numfashi.A hankali ta soma bude idanuwanta ta kuma bude su tar akan fuskaf Irfan dake fuskantar ta amma idanuwansa a kasa ya kasa kallonta.


"lafiya kuwa❓waya biyo ki Nihla❓Aunty ta fada.


Kafin Nihla ta bada ansa Miemie dake shigowa tace"babu wanda ya biyota tsabar farin ciki ne kawai"


Sosai Aunty ta sake fuska tare da fadin"to Alhmdllh,Nihla ki kawo wa bakona ruwa,su lami basa nan".


Gyada kai Nihla tayi alamar to ta juya tare da nufar hanyar kitchen tana kokarin mayar da hawayen da suke kokarin zubo mata,ruwa da kuma lemu da cup ta daura a plate ta dauko ta dawo parlon a saman table na tsakiyar dakin ta ajiye tare da juyawa zata wuce dakinta,yayin da zuciyarta ke dukan ukku ukku a yanzu kam bata da iko ko karfin zuciyar tsayar da ruwan dake kwaranyowa daga cikin idanuwanta zuwa akan fuskarta.Tsaki Miemie taja tare da fadin "amma dai Irfan kaji kunya wallahi".


Murmushi kayace a fuskarsa yace"anya dai Miemie yau kinyi gaskiya kuwa❓miye abun jin kunya a tattare da soyayya❓lamarine na zuciya ka kuma mikata a in da ya dace in da kuma kasan zaka samu kwanciyar hankali da tsantsar kulawa".


Saurin juyowa Nihla tayi tana kare masa kallo,tana kuma jin maganganunsa kamar saukar aradu a kanta,cike da karfin hali ta tako zuwa gabansa,da sauri ya dauke kansa tare da juyawa idonsa daga kallonta."sau daya dai Irfan ka kalle ni ka kuma fuskance ni,wanne irin mutun ne kai❓ haka shi ne tukuicin soyayya❓ kana tunanin yin hakan da kayi zai haifar maka da nasara ne a rayuwarka❓ barina da kayi bai taba mun ciwo ba Irfan,amma ka rasa wacce xaka so sai Matar mahaifina❓"


"Nihla wannan ba tarbiyar dana baki ba ne,ki tsare manya kina masu tambayoyin da kika ga dama,kamar yarda ya fada lamarine na zuciya kuma ita take da hukunci akan wanda zata so ko kuma wanda zata ki,shin laifi ne dan Irfan ya nuna ni yake so❓ ta ina hakan ya zama kuntatawa❓ Irfan ina so yau ka bayyana zabinka a cikin mu biyun,Shin ni ce ko kuwa Nihla❓ina ga hakan shi xai kawo karshen duk wannan".


"ka daga kanka Irfan ka kalli cikin idanuwan Nihla ka gaya mata baka santa "Miemie ta fada.


Kallonsa ya mayar ga Miemie tare da cewa"Haba Miemie nasan kinsan furta kalmar kiyayya bata da dadi ko a wurin makiyinka balle kuma ni da Nihla take so,bazan iya kallon idonta ba dan hakan ya haramta a gare ni"kallonsa ya mayar ga Aunty fuska cike da fara'a yace"Auntyna a soyayyah bana ganin kowa sama da ke,kece cikon rayuwa da farin cikin Irfan,rasa shi tamkar wata illace ce ko tawaya a rayuwata,ke ce zabina kuma mafarkina a ko yaushe".


Wani irin kuka ne ya kubcewa Nihla tayi part dinta da gudu cike da tsananin tashin hankali da rashin sanin madafa.


Fuska cike da hawaye Miemie ta kallesu tare da cewa"shi fa sharri kare ne duk in da ka aikasa zai dawo maka,da yardar ubangiji yarda Nihla tayi kuka dukanku sai kun koka,yarda kuka tozarta rayuwarta sai taku ta tozarta,yarda kuka ci amana sai amanar Allah ta ci ku,ko Nihla ta fada ko karta fada Allah yana kallonku kuma zai mata sakayya".Kuka ne yaci karfinta ta masa ci gaba da magana ta juya zata wuce taci karo da Kamal dake tsaye ya daure hannuwansa a kirji yana kallonta.Karasowa yayi tare da jan hannun yana nuna mata alamar tabar kuka.....




*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*


Jorderh✍🏻
[3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇


```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```






*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


80


Rike hannun Kamal tayi da karfi cikin nata,hawaye kuma na zarya akan fuskarta.Janta yayi zuwa dakin Nihla yana kuma lallashinta,tsaye tayi gaban bed din da Nihla ta fada tana kuka kamar ranta zai fita.Rungume juna sukayi da kyar Kamal ya samu ya shawo kansu tare da basu baki,rike kafadun Nihla Miemie tayi suna fuskantar juna cikin sanyin murya ta fara magana"Nihla meye a tattare da Aunty da har baki iya daukar fansa a kanta❓kina zaune kina kallo garin ta Farauto farin cikinta ke tana salwantar da naki Farin cikin❓ me ake da mata irin wannan".




Murmushi mai tsananin kyau Nihla ta saki har jerin fararen hakoranta suka bayyana,hannu tasa tare da share sauran hawayen daya rage akan fuskarta "Auntyna duniyata ce,Auntyna matsayin uwa take a gare ni,Auntyna taci kashina taci fitsarina duk da hakan ya kasance a fuska biyu ne,Auntyna tana da daraja a idona,tafi gaban wulakanci a gabana,ko ba komai zan kirata uwa wacce ta tsaya mun a lokacin farin ciki da akasinsa,ta jajirce a kaina kuma duk yarda take da fuska biyu hakan besa ta bani gurbatacciyar tarbiya ba,ta kula da ni tamkar yar data haifa a cikinta.Lokacin da Yayana Zafar ya yi tafiya itace mace data tsayawa maraicina ta kula dani ,haka zalika lokacin dana rasa mahaifi na kalleta a matsayin family tawa daya tak data rage mun a duniya wanda take da alaka da mahaifina,shin ki gaya mun duk wannan alkhairan data mun be isa na kauda kai akan abunda ta nuna tana so ba❓ba amfanin idan an cuce ka ka rama da cuta ilimun mu bazai mana amfani ba kenan,ina kuka ne badan abunda Aunty tamun ba ,a'a ina kuka ne ta dalilin wai Irfan ne zai maye gurbin da Mahaifina ya bari,ina kuma kuka ne akan na zama sakara dana mika yardata ga wanda besan darajata ba"Shiru Nihla tayi tana mayar da numfashi.


Girgiza kai Miemie tayi tare da janye jikinta daga rikon da Nihla tayi mata tare da cewa"ya ishe ni haka,na gaji dajin wannan maganganun naki da basa da hanyar kamawa balle dadin rikewa,yardarki da yawa shiya bawa waccan matar lasisin cutar da ke,ki gane mana Maryam karki kuma zama wata sakara akan wasu hujjojinki da bazan taba ansa ba,Nafisa ba zata taba zama uwa a gareki ba,garama kisan abunda kikeyi"jan mayafinta tayi tana niyar barin dakin,saurin rike gefen mayafin Nihla ,a fusace Miemie ta juyo tana zabgawa Nihla harara.Murmushi Nihla tayi tare da cewa"yau kuma zakiyi fushi da Aminiyar taki ne❓idan kika yi fushi da ni baki yi tunanin zafin dazai kuma shigata ba❓".


Can't control her tear's of happiness da matukar farin ciki tayo baya tare da rungumar Nihla a jikinta tare da cewa"Allah ya barmun ke,ya kuma kawo maki karshen duk matsalolinki" .Da ameen Kamal ya ansa tare da fadin"tunda an manta da ni a nan tsaye sai azo mu tafi ni na tuna da kaina".Bye bye Miemie tayiwa Nihla tabi bayan kamal suka tafi.


Sai lokacin wani radadi da rashin kwarin gwaiwa ya dirsar mata,kamar wata gunki haka ta daskare a wurin kwakwalwarta na tunasar da ita kalaman Irfan da suka kasance kara a zuba mata garwashi a kunnuwanta "shi ne wanda na fara so!a rayuwata irin son da bana hadasa da komai,irin son da zuciyata zata iya fashewa idan naga wani na rabarsa,son da wani irin zazzabi ke rufe ni idan har ban gansa ba! irin son da yake rufe ido wanda bana ganin kowa sai shi,irin son da a kansa na daina bacci sai dai naita juye-juye,akan sonsa na daina koshi wanda hakan ya haifar mun duk dadin abinci bana iya kaisa bakina balle harna iya gane dandanonsa! ,yanzu duk wannan son besa Irfan ya ji tausayina ba ya kuma tallabi maraicina😭❓ ta kare maganar wasu siraran hawaye na gangarowa akan fuskarta.A hankali ta zame hular dake rufe da yalwataccen gashin kanta,ta yi kokarin yiwa kanta masauki akan pillown dake bayanta ta kuma lulawa duniyar tunani.




Hannusa zube cikin aljihunsa yake taku tamkar kasa zata tsage saboda yacce take ansa takun nasa cike da izza,mulki da isa! hannunsa daya ya zaro daga aljihu tare da b'alle bottum din wuyansa na rigar suit din dake jikinsa.Bakinsa dauke da siririyar sallama ya saka kansa cikin parlon Hajiya kaka.Tsaye ya yi tare da dago kyawawan golding eye's ball's dinsa ya sauke su akan Hajiya kaka dake zaune tare da wata matashiyar budurwa.


Baki Hajiya kaka ta washe fuska dauke da yalwatacciyar fara'a ta mike tare da cewa"Aysha yau ga Zafar a gabanki,kuma mijinki nan da kwana shidda insha Allah".Budurwar da aka kira da Aysha ta dago kanta a hankali tana sauke idanuwanta akan Zafar Ma sha Allah shi ne abunda ta fada tana kuma kara fadada fara'arta dan wannan shi ne ganin Zafar na biyu da tayi kuma tun ganin farko ya tafi da dukkan tunaninta da wata farin cikin rayuwarta,tun daga ranar take jin babu wanda ya cancanta da ita sai shi"kura masa ido tayi ta kuma kasa janyewa,lokacin daya tayi saurin runtse idonta da matukar karfi sakama kon idanuwan Zafar da suka shiga cikin nata,wani irin suck taji wanda yasa ta kasa ci gaba da kallonsa tayi sakama kon kwarjin daya yi mata.


Karasa shigowa yayi tare da zama akan chair dake fuskantar Kaka cikin natsuwa ya furta"Ga ni!".


Lumshe idanuwa Aisha tayi yayin da so da tsantsar kauna suka soma daukar mata daddadar muryarsa tana mata yawo a kai.


"wannan itace Aysha matar dana zaba maka Zafar,ka ganta dan ita ta riga ta ganka kuma ka fara shirin biki "Kaka ta fada.


Shiru Zafar yayi tare da dago kai ya kalli Kaka yace"ki bamu waje to".


Alhmdllh shine abunda Hajiya kaka ta fada tana kuma cewa"nasan ai dole kaso zabina ,kaine jika mafi soyuwa a gare ni kasan bazan maka zabi marar kyau ba,ku zanta da kyau,Allah yayi maka albarka".Ta kare maganar tana wucewa bedroom dinta.


Murmushi kawai Zafar ya saki,wanda hakan ne yasa Aysha shagala da kallonsa dan ba karamin kyau yayi mata ba.Yana juyowa da kallonsa tayi saurin yin kasa da kai zuciyarta na bugawa.


"a wannan zamanin ban tunanin akwai wadda za'awa zabin miji ko mata haka kawai ya amince,shin ke sanina kika yi ne da kika amince da zabin kaka ta❓ Aysha ba abunda kika rasa bare nace bana sonki,ko a ina babu wanda zai kushe halittarki,sai dai ina mai matukar baki hakuri ,bana da ra'ayin yin wani aure a yanzu".


Saurin dagowa tayi tare da dubansa cikin sarkewar murya tace"ni naga kayi mun,kuma zan iya jiranka ko yaushe ne"Cewar Aysha.


Hannu yasa tare da shafa tulin sumar kansa kafin ya bata ansa da cewa"ki gane bana da ra'ayin son mace biyu danni ina da wacce nake so kuma na riga na zama mallakinta i'm sorry"ya kare maganar tare da mikewa ya yi hanyar fita.


Da kallo tabi bayansa dashi ,sai da ya kurewa ganinta sannan wasu hawaye masu dumi suka samu basarar gangarowa akan fuskarta....


*Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe*




Jorderh✍🏻
[3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇


```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```






*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


81




Da kallo Aysha tabi bayan Zafar harya bacewa ganinta,dukar da kai tayi tare dasa hannu ta soma share zafafan hawayen da suka gama wanke mata fuska,sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da dagowa tana kallon Hajiya kaka dake tsaye gabanta ta kureta da ido.


"me yake faruwa❓,ina Zafar din❓,Aysha kina jina fa"cewar Kaka,"Kaka ya tafi"Aysha ta bata ansa tare da mikewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login