Showing 18001 words to 21000 words out of 32417 words
Chapter 7 - Farautar Farin Ciki Hausa Novels Document Na Maryam Isma'il Jorderh.txt
fuskar su,daukar yankan apple Mummy tayi wanda Zafar ne ya saka mata Mummy ,yake kiran Mamansa Ammi ,Umar kuma Abba ,Al-ameen kuma Daddy,ta kai bakinsa ,bude baki yayi tare da ansa ya kuma mayar da kansa akan kirjinta ya kwanta,a lokacin yana dan kimanin shekara biyar.Gyara zama Ammi tayi tare da sakin nishi tana tallabar katon cikin dake gabanta haihuwa yau ko gobe.Fuska daure Hajiya Kaka ta shigo dakin ta zauna a chair tare da yin daya kan daya.Saurin safkowa kasa Mummy tayi tana kara rungume Zafar a jikinta bakinta na rawa fuska cike da tsoro tace"Hajiya ina wuni".Banza Hajiya Kaka tayi mata ta juya tana ansa gaisuwar sauran yaran dake gaisheta a parlon.Mikewa Zafar yayi tsaye tare da jan hannun Mummy yace"tashi,tashi muje daki,kar Allah yasa ta ansa gaisuwan dama ke kike gaisheta".Kafin ,Zafar ya rufe baki Hajiya Kaka ta tangare masa keya,a fusace ya juyo fuska murtuke yace"kar dai kimun ihu a kai".Saurin janyosa Mummy tayi tare da cewa"Muhammad zamu bata kanawa manya rashin kunya".
"har kina da bakin fadin hakan?ae duk abunda Zafar zaiyi laifinki ne ke kika bashi tarbiya kuma sunan da yake ansawa naki ne,dole zaiyi abunda yake so".
"ki daina wa Mummyna fada,babu ruwanta ni ne nake so na gaya maki haka saboda kina takura mata"Zafar ya bada ansa.
A fusace Hajiya kaka tace"zanyi maganin ku kai da uwar rikon tana,Umar ina so kayi aure,Umarni ne na baka ba shawara ba,ina so naga jikanka kafin na rasu,idan kuma bani da iko da kai zaka tabbatar mun ba nono kasha ba sai ka bijirewa Umarni na".
Kasa Abba yayi da kai tare da cewa"Hajiya duk yarda kike so haka za'ayi,insha Allah zaki sameni da bin umarninki a ko wanne lokaci".
"Allah yayi maku albarka "ta fada tare da ficewa yabar parlon.
Wasu zafafan Hawaye masu dumi suka zubo a fuskar Mummy,da sauri Zafar ya tallabi fuskarta tare da cewa"kibar kuka Mummyna ,ki daina biye mata,ita fada kawai tasa gaba,idan na girma zan zana soja in halbe maki ita,Insha Allah kuma zaki haifo mana baby mai kyau kamar ki".Murmushi ne ya subucewa Mummy ta rungume Zafar.Ana cikin wannan yanayin ne Ammi kuma ta sake sanbalo yaronta kyakyawa ranar suna yaro yaci suna Ramadan,duk da tsananin kulawar da Zafar ke nuna masa da tsananin so amma sam bai yarda ya dau lokaci a bangaren Ammi.Watan Ramadan ukku Hajiya kaka ta samowa Abba matar aure,yarinya mai tashe da kyau da halayyah mabanbanta mai suna Nafisa,tayin farko Nafisa ta amince da auren Abba duk da ba wani son sa take ba dukiyarsa kwai take kwadayi,a lokacin Nafisa tana yar shekara 23.Auren Nafisa shi ne dalilin rushewer wannan Familyn ta kasance itace wacce take rike da kaddarar gidan,ita ce asalin kawo bakin ciki da rarrabuwar kan ko wanne a gidan su,tayi amfani da damar zama mata a gidan ta hanyar cika burukanta da dama,sati biyu da haihuwar Ramadan Aunty ta shigo gidan a matsayin matar Abba.
A fuska Nafisa mata ce mai tsakanin kirki,son kowa da kuma kyautatawa duk wani dake gidan.Zafar ne ya taso da tsananin kiyayyarsa duk soyayyarsa da abu data taba shi to ya gama amfanarsa ko menene,ko parlo yake zaune tana fitowa zai tatara kayansa yabar mata parlon.Duk wata y'ar tsamarsa da Kaka ya janyeta ya dawo da ita akan Nafisa wanda su Mummy ke kira da Aunty.Nafisa ta kasance tauratuwa kuma masoyiya ga Hajiya Kaka ta kwacewa kowa fada,komai lamuran Hajiya kaka a wurinta suke,da komai daya shafi gidan. Wannan kenan.
Zagaye daki take yi,maganganu da yawa suna mata yawo a kai.Kwatakwata ta rasa sukuni babu abunda take buri da so daya wuce mallakar dukiyar Familyn gaba daya da kuma babban burinta na raba Mummy da Abba.Kamar wani gunki haka ya iso ta gefanta tare da rabawa zai wuce.Saurin juyowa tayi tare da daga hannu tana kokarin janyo hanun Zafar.Da matukar karfi ya bige hannunta kafin ya karasa a hannunsa,dara-daran idanuwansa ya kuma zazzarosu waje tuni sun sauya kala da kawo k'yalli k'yalli alamun ruwa ya fara taruwa a cikin su,hannu ya daga tare da nuna ta da yatsa tare da cewa"karki kuskura,har abada duk ranar da kika yi gigin taba ni nayi maki alkawari da wanda raina yake a hannunsa a ranar sai na cire maki wannan kazamin hannun naki".Hannu yasa tare da damkar sumar kansa ,da sauri ya karasa ya dauki qur'an din da yazo dauka ya dauka ya wuce Mummy da Ammi dake tsaye cike da tsananin al-ajabi sun daskare da ganin yaro karami yana irin wannan halayyar.Zafar kam ko kallonsu beyi ba yabar parlon yayin da zuciyarsa ke cike da tsananin kiyayyar Aunty tana kuma bugawa da matukar karfi..
*Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderhβπ»
[3/3, 21:52] Maryam Jordan: ππππππ
*FARAUTAR FARIN CIKI*
ππππππ
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
77
Mummy ce ta katse shirun da duban Aunty tare da cewa "dan Allah kiyi hakuri,kinsan lamarin yara ba kamar Zafar mai wuyar sha'ani zan masa fada insha Allah bazai kuma ba".
"wallahi Mummy babu komai,kada ki damu kanki waye besan yara ba?komai ya riga ya wuce".Aunty ta bata ansa tana wuce wa ciki.
Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tare da cewa"lallai yaron nan so yake nayi maganinsa ,kiji daukar magana yanzu idan Kaka taji wannan maganar fa?".
Dafa kafadunta Mummy tayi tare da cewa"insha Allah ba zata ji ba,bari naje na same sa"batajira cewar Ammi ba ta bi bayan Zafar kai tsaye dakinsa ta nufa,zaune yake akan prayer mat ga al-qur'ani a gabansa yana muraji'a,shigowa ta yi ciki ta zauna a gabansa,sai da yakai ayar da yake yi karshe kafin ya dago ya kalli Mummy .Ba laifi fuska a sake yace "Mummy wani abun na damun ki ne? ."
Kuma daure fuska tayi kafin tace"ai dole abu ya dame ni Son,yanzu kai ya dace ace matar Abbanka ka ke wa magana haka?".
Saurin ja da baya Zafar yayi dan da nan annurin fuskarsa ya guje, taune lips dinsa ya yi kamar zai huda ya kasa cewa komai."Zafar magana na ke maka fa".
Kallon Mummy yayi tare da cewa"to Mummy ban san me zance ba ae,dan Allah ki daina shiga tsaka ni na da waccan matar na roke ki".
Sake da baki haka ta bisa da kallo,rasa me zata cw ma tayi hakan yasa ta mike tabar dakin.Shikam nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana kuma jin tsantsar tsanar Aunty a ransa.
2yrs later
Abubuwa da dama sun faru masu dadi da mararsa dadi,dama rayuwa haka ta gada.
Ammi ce zaune a gado ,kowa na gidan yana parlon a lokacin Zafar yana shekara 16 Ramadan na dan shekara 11 ,ko wanne ka gani cikinsu fuskarsa dauke take da yalwataccen murmushi marar yankewa,cike da fara' Daddy ya mikawa Mummu babyn dake hannunsa tare da cewa"Allah ya raya mana Nana Aisha."
Wani irin murmushi ne ya subucewa Abba yana kallon Daddy cikin hanzari ya karba babyn daga hannun Mummy yana cewa "masha Allah yau Hajiya ta dawo,ina godiya da wannan karamcin insha Allah daga yau zamuna kiranta Miemie ,kuma na mallaka mata kamfanina na gidan Ashana dake nan garin kano".
Wani irin yunkurowa Aunty tayi da karfi har tana niyar fadowa daga kujera tace"haba Alhaji daga haihuwar yarinyar?".
Wata uwar harara Zafar ya afka mata cike da masifa yace"an kasa da ke ne? kiyi kokari ki haiho Aminiyarki Jamila sai ita a bata ta hassada sai ta kare".
Dakuwa Ammi ta masa tare da cewa"ungo nan Muhammad,sai dai ta haifo Maryam badai Uwar mu ba".
Dariya Ramadan ya saka tare da cewa"wallahi Yaya duk ranar da Hajiya kaka ta ji kana cewa a haifota wallahi ka shiga rububi".
Harara Abba ya masu yana cewa"ku kama kanku a wurin nan,bama son shakiyan ci".
Gyara zama Mummy tayi tare da tallabar k'aton tsohon cikin dake gabanta haihuwa yau ko gobe tace"mu dai a bamu babyn mu yunwa take ji".
Da sauri Ramadan yace"Mummy wannan babyta ce Ammina ta siyo mun".
Mugun kallon da Zafar ya jefa masa yasa yayi shiru da sauri,tsaki yaja tare da dafa cikin Mummy yace"na raye gori,insha Allah nima Mummyna mace zata haifa mun mai kama da ita,in kuma saka mata sunan Mummy".
Kowa fuskarsa fal fara'a ,kama Mummy Zafar yayi ya tusata gaba da rigima dole sai da suka tafi part din su.
Bayan sunan Miemie da kwana biyu Mummy ta tashi da nakuda,cikin sauri aka tafi da ita asibiti,tafiyar ta karshe,barin gidan nata da ahalinta da rai na karshe,hakika mutuwa dole ce kuma ance sabo ake wa kuka ba mutuwa ba...Tun daga mutuwar Mummy komai na rayuwar Zafar ya gama canzawa dandanan yake kasancewa cikin tsakananin fushi da kunci,ko kadan be son hayaniya magana ma gaggararsa take yi,a ko yaushe yana rike ne da Nihal,saukin sa daya gama zana jarabarwar gaba da secondry ne kullun yana gida,ko daidai da second baya barin Nihal wani irin tsantsar so da kulawa mai cakude da tsantsar tausayi.A bangaren Nihal ma hake ne,tunda ta fara wayau bata yarda kowa ya bata ta daga Abba sai Zafar.Lokacin da Zafar zai tafi makaranta ba karamin daga aka sha ba dan da kyar aka samu ya tafi dan kafewa yayi ya jingine makarantar wai shi ba zeje ba,sai da Abba ya dage kafin aka samu ya koma makaranta...A lokacin ne kuma fir Aunty ta dauke Nihla daga hannun Ammi ta lullubeta da soyayyar karya ,tun Nihla na kukan Zafar harta hakura ta saba da zama da Aunty.A wannan lokacin ne kuma Aunty ta shammaci kowa da soyayyarta ta karya,ta kwashi dukiya mai tsananin kauri da yawa wanda ita kanta bata san iyakarta ba ta hanyar Abokin ta'addancinta data hadu dashi wato Kamal shine yabi mata duk wata hanya ya bata kwarin gwaiwar da nema mata wanda suka iba kudin ta hanyar office din Abba,wanda sosai companyn nasu ya raunana har masu hannun jari a ciki duka suka janye.Wannan dalilin ya kawo babban sabani ga ahalin guda biyu da rikici yaki cinyewa Hajiya kaka ta kira Abba a matsayin mayaudati maciyi amana ta kuma yanke duk wata alaka dake tsakanin su dashi,sai a lokacin Aunty ta samu sukuni ganin ta samu galabar rarraba ahalin.Ba karamin wuya Abba yasha ba kafin Allah ya tado masa da dukiyarsa ta hanyar wasu da yake bi kudade sukaita maido masa nan Allah yasawa kudin albarka suka bunkasa ya tsaya da kansa tsayuwar da ko shi kansa besan iya abunda ya tara ba.
Lokacin da Zafar ya dawo,yayi bakin ciki itace rana ta farko daya fadi akan kafafunsa hawaye masu tsananin zafi suka zubo masa,jujuya kai yakeyi cikin tsananin bacin rai ya dago idanuwan sa da suka gama sauya kala ya kalli Hajiya kaka tare da cewa"Dan da kika raina a hannun ki,shin ke kin yarda zai iya aikata haka? a duk gidan nan akwai mai riko da gaskiyarsa da kuma amanarsa?,Ammi kema kin yarda? Daddy kaima?" a rikice yake gaba daya.Cikin tsananin tashin hankali yace"to idan kin raba shi da saura ni bazaki taba yanke alakata dashi ba kada ki manta Amanata tana hannunsa,kuma duk kiransa da nake muna waya da ita bai taba shaida mun cewar bakwa tare ba".
"kayi mun shiru Zafar,babu abunda ke damunka daya wuce yarinta,duka shekaranka nawa,to ina so ka sani baka ba wannan amanar".Hajiya Kaka ta fada.
Buga kansa yayi da karfi tare da cewa"a hannun dana karba bata raye bare na mayar mata da nauyin dana dauka,ina so na gaya maki babu kuma yarda za'ayi na janye jikina daga cika alkawarin dana dauka duk runtsi kuwa".Yana fadin haka ya fice daga gidan da sauri.Kiran Abba yayi kafin ya samu ya gane bayan gidan su suka koma,a lokacin Nihla na da shekara hudu ,ko da ya shiga gidan ba karamin tashin hankali ya shiga ba ganin Nihla ba lafiya anata fama a kuma lokacin ne Abba ke sanar masa Nihla sikila ce,Zafar yayi tashin hankali kunci damuwa akan ciwan Nihla,hakan ne yasa ya sauya ra'ayinsa daga zama Soja ya juya mafarkin sa zuwa karantar Likitanci dan ya kula da amanar.
Ci gaban labari.
*Allah ka gafartawa iyayen mu kayi mana kyakyawan karshe*
Jorderhβπ»
[3/3, 21:53] Maryam Jordan: ππππππ
*FARAUTAR FARIN CIKI*
ππππππ
```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```
*ππ°AINUWA πΌRITER'SβπΌ*
*π¦SSOCIATIONπ€π»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
78
A hankali ta soma bude idanuwanta da suka mata nauyi alamun baccin bai gama isarta ba,sam baya mata dadi yasa ta farka,akan tuskar Zafar idanuwanta suka sauka wanda ya kureta da ido fuskarsa a sake,kokarin tashi yake yasa ya karaso gabanta tare da taimaka mata ta tashi zaune,ji yayi jikinta zafi sosai alamun zazzabi na neman rufeta yasa yace"ki daina wannan koke koken,kinga zaki janyowa kanki ciwo".
Rau rau tayi da ido tare da fadin"Yaya Irfan ne".
Hannu yasa tare da dalle mata baki yace"kada na sake ji kin ambata mun sunan nan,in ba haka ba ranki zai baci"
Kasa tayi da kanta ta soma wasa da yatsun hannunta ganin duk ta takura kiris take jira ta saka kuka yasa yace"kiyi hakuri kinji Mamana,bana son damuwar nan taki ne,ko dan lafiyarki ya kamata a ce kiyi hakuri,Mamana kika rasa Mahaifiya kika rasa Mahaifi sai saurayi ne zaki kasa hakura da shi? saurayin ma irin Irfan ?"
"Yaya ba barina da yayi yake mun ciwo ba,amma sai ace ya rasa wacce zai so sai Auntyna,wacce nake dauka a matsayin mahaifiyat..."bata karasa magana ba Zafar ya daura yatsan shi akan bakinta tare da cewa"ba ta haife ki ba,ba kuma zata taba zama mahaifiyarki ba"tashi yayi ya hado mata drugs dinta ya bata ta sha,Hijab ya bata ta saka yace"tashi muje".
Bata musa ba ta mike tare da saka platshoe dake gabanta ta bi bayansa,babu kowa a parlon haka suka fice,yana gaba tana binsa har suka zagaya bayan gidan su.Saurin cin burki tayi ko kwakwaran motsi ta kasa.Dama yasan za'ayi haka kallonta yayi fuska a daure tare da cewa"wuce muje mana".
Girgixa masa kai tayi,tana kokarin yin baya,hannunsa yasa tare da riko nata ya soma tafiya cikin muryar tsoro take fadin"dan Allah ka barni bazan shiga ba,ni gida zan koma".Wata uwar harara daya aika mata da ita yasa ta yi saurin hadiye sauran maganar cikin hade fuska yace"Billah na kuma jin bakinki sai na mammare ki".
Gate din gidan ya tura tare da shiga,lumshe idanuwanta tayi,hawayen dake makale suka sauko akan fuskarta,abubuwa da yawa suke dawo mata a kai,ta zo gidan yafi a kirga lokacin yarintar ta amma Hajiya kaka na korata,hakan yasa tun tana naci harta hakura ta saba da rashin zama a gidan,ganin ya nufi main entarance na gidan yasa ta danji sanyi sanyi,kanta a kasa take binsa.Dam dam dam haka kirjinta ya bada sauti lokacin data dago idanuwanta ta ganta a tsakiyar parlon gidan ga Hajiya Kaka hakince a kan kujera tana aika mata da sakon nin harara.a take kyarma ta kwace mata tana niyar rantamawa da gudu.Murza hannunta Zafar yayi tare da kuma rikesa a nasa hannun.A hankali ya soma taku zuwa benen da zai sada shi da part din sa.
"Zafar!" shi ne abunda Hajiya kaka ta fada cikin tsananin bacin rai,kai tsaye gabansa ta dawo ta tsaya tare da nuna Nihal da hannu tace"menene jinin Umar yake yi a gidan nan?".
"tazo gaishe da yan uwanta ne ta kuma ga Amminta wacce take matsayin uwa a gareta"Zafar ya bata ansa.
"karya kake ! wacce alaka ce a tsakaninta da yan gidan nanβ,balle harda raina ina cikin gidan nan ka shigo mun da ita a gida"Kaka ta fada a hassale.
Murmushi yayi tare da cewa"Hajiya kaka,alaka da yawa mana,to tazo gaishe da Kakarta ne"ya fada tare da turo nata Nihal a gabanta.
Da matukar karfi Nihal ta juyo tare da afkawa a kirjin Zafar ta rungumesa da karfi ko ina a jikinta kyarma yake ,tuni hawaye sun fara zarya a kan kuma tunta,wani irin tsoron Hajiya Kaka ya taso mata lokaci daya.
Saurin kawar da kai Hajiya kaka tayi tare da cewa"ka ce mun kuma rashin tarbiyar har ya kai a gabana kake rungume mace?,kaji kunya yarinyar da aka haifa akan idonka? ka fitar da ita daga gidan nan yanzu kafin nayi abunda raina yake raya mun".
kallonta Zafar yayi tare da cewa"shiyasa zan kaita part dina ba naki ba nace,tsabar gulma ce ta kawo ki nan din ai".
Wani uban rankwashi ta kai masa a kai,ashh ya fada tare da rike mata hannu yace"wallahi kika kara dukana nasan mi zan maki,naga in da aka taba hana Mata shiga dakin Mijinta"yana fadin haka ya suri Nihal da gudu ya wuce ta gefan kaka.
Tamkar saukar aradu haka Kaka taji maganar Zafar na ansa kuwwa a cikin kunnuwanta,tuni kyarma na niyar kwace mata ,bata tsaya sauya shawara ba ta rufawa Zafar baya,sai da yaga tazo dab da kofar tasa ya mata gwalo tare da dannawa kofar key yana murmushi da tunanin fitinar daya taro a gidan nan yau.
A kan chair ya ajiye Nihal tare da cewa"matsoraciya ni sake ni,sai kace wacce na sato".
A hankali ta soma dago kanta daga jikin shi zubawa fuskarsa ido tayi ,uwar harara ya watsa mata da sauri tayi kasa da kai tana turo baki,tureta yayi daga jikin sa ya gyara zama tare da jawo table din gabansa ya fara dube-dube a laptop.Hannuwansa biyu yasa tare da toshe kunnuwansa yace"wallahi Hajiya Jamila idan zaki kwana nan bazan bude maki kofar nan ba,in yaso ki karya ki shigo".
Kuka Hajiya kaka ta fashe da shi tare da cewa"walllahi haihuwarka annoba ce Zafar,shege debabban albarka,wallahi ba zaka samun hawan jini ba sai dai ka kashe uwarka Maryam,labcecen banza,dana sani tun a ciki nasa an zubar da cikinka,kuma wallahi baka isa ba ka fiddo wannan yarinyar ka mayar da ita gidan ubanta,jinina yafi karfin jinin barayi".
"kibar cika mun kunne,ke kika koya masa satar tunda ke kika raine sa ae,kuma ke kika gayyato barauniyar a gidan,wallahi ki fita harkata a gidan nan kafin na maki rashin mutunci".
Hannu kaka ta daura a kai tayi dakin Ammi da gudu tana rurin ihu,a tsakiyar parlon Ammi ta fadi tana kuka wiwi kamar wacce ake fitarwa rai.
Dariya sosai Ramadan ya saki suka tafa tare da Miemie kafin yace"maganin ki kenan,tsab zai mana maganinki tunda shi kadai ke iya maki"
Dariya kamar zai kashe Miemie kafin tace"amma dai kasan duk yau bamu ba kwanciyar hankali ".
Da gudu Ammi ta fito daga bedroom har tana tuntube gaban kaka ta fadi tana salati "Mama lafiya β"shi ne abunda ta ke fada.
Gefan zani kaka tasha