Showing 30001 words to 32417 words out of 32417 words

Chapter 11 - Farautar Farin Ciki Hausa Novels Document Na Maryam Isma'il Jorderh.txt

Irfan da iya karfinta,a guje ta mike zata yi waje ,Daddy ne ya yi saurin tare kofar da take niyar fita,ko ina a jikinta kyarma ya ke bakinta rawa take ta kasa furta komai face nuna hanya da take yi.A haka Zafar ya shigo dakin yana karewa Daddy da Nihla kallo.




*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*




Jorderh✍🏻
[3/3, 21:53] Maryam Jordan: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*FARAUTAR FARIN CIKI*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇


```By``` ```Maryam``` ```ismail``` ````Majidadi```






*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*MARUBUCIYAR*


*SANADIN GATA*
*YAUDARA KO BUTULCI*
*DALILIN SO*
*SO DAYA*
*ASALINA*
*ADDININA*
*SHI NE AJALINA*
*RUHIN FANSA 1&3*
*HANAN* paid book
*ABU BILAL* Paid book
*TABON 'DA NAMIJI*
*FARAUTAR FARIN CIKI* ✍🏻🤸🏻‍♀️


END END END




Ido cike da hawaye Nihla ke kallon Zafar kamar idanuwanta zasu fado,kai ya gyada mata da karfi ta fada kirjinsa tana fashewa da kuka tare da cewa"Yaya dan Allah ina so na gan shi,ina so nayi magana da Yaya Irfan".Kuka ne yaci karfinta bubbuga bayanta yake yi tare da alamar lallashi.Kamota Daddy ya yi tare da zaunar da ita,kallonta ya yi "Nihla kiyi hakuri babu wanda yasan da hakan,shiyasa Abbanki ya bawa Zafar aurenki yana kuma ganin babu wanda zai iya kula da ke sama yarda Zafar zai iya kula da ke,kiyi hakuri ki yi biyayya akan kaddarar data sameki."Daddy ya kare maganar yana kallonta.




Kasa tayi da kanta shiru tayi hawaye na zuba a fuskarta cikin karfin hali tace"Daddy i'm not complaining,Allah yasa haka shine alkhairi a rayuwata,ni hakw tawa kaddarar tazo amma Daddy dan Allah ka ce masa ya barni nayi magana da Yaya Irfan ko sau daya ne".


Cike da tausayinta Daddy yace"Maryama ki daina wannan kukan zakiyi magana da Irfan insha Allah,bana so ciwanki ya kuma tashi saboda wannan wahalan da ki ke yi,har gida Irfan zai zo ya sameki nayi maki alkawari".




Kasa da kai Zafar ya yi kafin ya kalli Ramadan da shigowarsa kenan yace"ka dauki kuje da Nihla dakin Ammi,zamuyi magana ne".


Da kallo kawai Nihla ke binsa rashin gane wacce magana za'ayi yasa ta mike tana yin gaba Ramadan na bin bayanta.


Daddy,Ammi,Kaka kowa hankalinsa ya mayar ga maganar da Zafar keyi.


Sake da baki haka Daddy ke bin Zafar da kallo gaba daya he's spechless wani irin rudu da tashin hankali ne suka tarar masa gaba daya,cikin son tabbatarawa da kansa abunda yaji yace"kana nufin Kamal ya bawa Nafisa gubar da Alhaji Umar yaci❓".


"kwarai kuwa Daddy,mutuwar Abba ba hakanan tazo kai tsaye ba,hakan ya faru ne ta dalilin kashe sa da akayi,ina da rahoto na asibiti,sannan kuma Abba da kansa ya fada mun muguntar da Aunty ta ke shirin yi akan dukiyar Nihla,ya gane hakan ne bayan wata rana daya dawo daukar wasu files a nan ya sameta tana waya da Kamal sai ya wayance kamar beji komai ba wannan dalilin ne yasa ya daura aurena da Nihla"kallonsa ya mayar ga Hajiya kaka yace"kinata zargin Abba akan satar hakudan kudade ga takardu ki duba Kamal da Nafisa sune wanda suka saci kudin a office din Abba,wanda dukanku kusan yarda Kamal yake amintacce a wurin Abba".


innalillahi wa'inna ilaihir raju'un shi ne abunda Kaka ke maimaita ta kuma fashe da kuka hannu ta daura a kai cikin muryar kuka tace"yau naga abunda ya ishe ni,ni da kaina na auro wa 'Dana bala'in daya tarwatsa mun kan zuri'a Allah bazai bar Nafisa ba,ga Umar harya mutu banje na ganshi na roki gafarar shi ba,innalillahi wa'ina ilaihir raju'un."kuka rurus haka Kaka ta saka kamar zata shide.


Riketa Ammi ta yi duk da ita ma bata da bakin magana kuka kawai take yi,Daddy kam hularsa ya cire yana yin fita da ita,tuni zufa ta gama rufe shi ta ko ina,bai taba tunanin rashin Imanin Nafisa ya kai haka ba duk da dama yasan rashin kirkinta da kuma irin satar da takeyiwa Abba.


Kamar wacce aka ingizo haka Miemie ta shigo dakin,fuskarta caba caba da hawaye kamar wata zautacciya haka yake binsu da kallo ya yin da hawaye ya kasa tsayawa a idanuwanta.Wani irin zaro ido Zafar ya yi cikin dakewa yace"ke me ki ke yi a nan❓."


Cikin muryar kuka take magana"shin Yaya bai kamata na san halin da Kamal ke ciki ba ne❓,Kamal shine rayuwata shine farin cikina kowa cikin ku yasan haka,na rayi da son shi na bude idona da son shi dan mi yasa zaku zabi boyemun hakan❓."


Kasa karasa magana ta yi tuni kyarma ta kwace mata juyawa tayi tabar dakin tana gudu ,kamar wacce aka jefa haka ta harde steps tayi kasa kafin ta karasa kasa taji ta fada jikin mutun ,duk da idanuwanta na rufe hancinta da bugawar zuciyarta basu yi kasa a gwaiwa ba wajen sanar mata da zabin zuciyarta ne wa to kamal,a hankali ta soma bude idanuwanta da suka soma sauya launi,da duk iya karfinta daya rage mata tasa wurin ture Kamal ta mike da sauri,a tsawace take fadin" meya kawo ka wurina❓ko akwai wani daya rage zaka cutar a nan❓ni ko iyayena❓yayyena ko kuwa Nihla❓,nayi dana sanin saninka a rayuwata kamal,na kasa yarda ni ce naso makashi ,mayaudari,maciyi amana,innalillahi wa'inna ilaihir raju'un"karar kukan Miemie yasa kowa fitowa,dib haka jin Nihla ya dauke na wani lokaci janye dogon riganta dake jan kasa tayi tare da soma safkowa daga stairs a guje ko ganin kirki bata yi,sai da ta iso tsakiyar parlon ta tsaya tana haki kamar wata zautacciya haka take bin Miemie da kallo tana bakinta na rawa take fadin"Mie..Mie Kamal da A...aunty suka kashe ...Ab...Abba❓".


"Kwarai da gaske,Kamal shi ne wanda ya bada gubar da aka ciyar da Abba naji hakan da kunnena,nayi danasanin rayuwata Nihla,a kullun rayuwarki nake tausayi ban sa ni ba ashe tawa ma abun tausayi ce,wanda na bawa yarda da duk soyayyata shi ne wanda ya zama sanadiyar tarwatsewar ahalina"Miemie ke fada cikin kuka.


"ya isa,ya isa haka"Kamal ya fada da karfi,cikin daga murya da tsananin fushi yaci gaba da cewa"nayi hakan ne duk dan saboda ke ne,nayi hakan ne dan na baki rayuwa mai kyau,bani da kowa sai ke soyayyarki itace ta mayar da ni mutun,idan da ban biyewa Nafisa ba taya zan sameki ❓bayan tana ikirarin idan na juya mata baya zata saka a koreni aiki,Aysha ta ina zan ganki har ki soni❓,na rokeki duk abunda zaki mun kimun amma karka gujeni dan Allah"ya kare maganar nasa tare da hada hannuwa wuri daya,for the first time da hawaye ya fara gangarowa akan fuskar Kamal.


Ragab haka suka ji karar faduwa Nihla ta fadi akan gwaiwowinta tana jujuya kai da sakin wani irin kuka mai kara,da sasasarfa Zafar ya yo kasa shima ya tsugunna akan kafarsa,janyo Nihla ya yi yana lallashinta,a jikinsa ta fada tana wani irin kuka mai cin rai da tsananin kuna,ji takeyi zuciyarta ta yi mata nauyi kamar zata fasa kirjinta ta fito,lallai wani kukan da hawaye salama ne,a wannan lokacin ne ta nemi ruwan hawaye ta rasa lallai ashe bayan duk kuncin da tayi a baya salama ne akan na yau da take jin kanta dama mutuwa tayi ta huta,lallai Aunty da kamal sun kasance wani jigo na turata ga kusantar bakin cikinta da kewarta.'Dago idonta tayi tana kallon Aunty dake shigowa parlon da iya karfin tana fadin"ina Nihlan da Irfan suke❓lallai tunda yaci amanata yau tashi tazo karshe".


Janye jiki Nihla tayi daga jikin Zafar ta mike,saurin riketa ya yi yana girgixa mata kai,alama ta yi masa daya saketa,cikin takun karfin hali ta isa gaban Aunty,kallan kallo sukeyi kafin Aunty tace"saboda ke,saboda ke yau na gagara cika burin da nake dauke da shi na tsawan shekaru,kinsa Irfan ya guje ni ya kuma yaudare ni,abunda wani bai taba yimun ba,naso har na gama abunda nake na tafi na barki ba tare dana taba lafiyar jikinki ba amma kinki bani damar hakan,kada ki zarge ni a duk abunda xai faru da ke Nihla,komai laifinki ne".




Cikin muryar kuka Nihla tace"yanzu duk abunda kika aikatamun yafi ace raina kika dauka da ki rabani d mahaifina,shin kinsan menene shi a gareni? shine duniyata,alfaharina da duk wani abu da zanyi takama dashi,na miki kallon Uwa ban taba jin daidai da rana tsaya zan iya saba maki ba duk da Irfan da kika dauke a wajena ,ashe kedin me fuska biyu ce,kedin rayuwata kike nema kin kuma ci nasarar rabani da duk wani farin cikina,sai dai ina mai farin cikin sanar da ke cewa babu wani da zai kaiki kotu ko wani wuri kara,hakkin ran salihin bawa kadai ya isa ya hanaki jin dadin duniya,Allah kadai xai iya maki sakayya akan abunda kika aikata,duk wata kotun duniya tayi kadan wajen daukar fansan ran mahaifina,dukiya kike so❓dukiya ta saka ki yin duk wannan❓ki dauki komai kije dashi ,da nasan wannan ne burinki wlh raina da duk wata dukiyar dake garemu fansa ce ga ran mahaifina"kuka ne mai tsananin karfi ya kwacewa Nihla,bata ankara ba taji an fizgeta da karfi gefe,feee haka garin maganin ya soma bin iska wanda ke hannun Aunty da taso zubawa Nihla.Kamar statue haka Aunty ta tsaya tana kallon Irfan daya zanje Nihla,kwararo ido tayi kamar mayya sabon kamu kafin ta fasa kara da karfi tace"ka kuwa san abunda kayi mun Irfan❓Malan ya gaya mani ma damar wannan maganin behau jikin Nihla ba to tabbas ni zan haukace ba ita ba"


Kowa kallon Aunty yake yana jinjina rashin imani irin nata,"bakin halinki da mugun abunki kab kanki zai kare badai kan jikata ba,baka mai bakar aniya wacce bata san abun arziki ba,tsintacciyar mage Allah wadaran halinki Nafisa ,Allah shi zai mana sakayya akan abunda kika aikata mana".Kuka kaka ta fashe da shi,jin shewar Aunty yasa tayi wuki-wuki da idi tana kallon Aunty dake kururuwa tuni ta cire Dan kwalinta ta baje guntun gashinta ya gama mikewa tsai-tsaye kartar jikinta takeyi da akaifan dake hannunta,ihu take tana fadin duk wani abu data aikata.Da sauri Zafar yaso ya janye Irfan da Nihla wanda aunty ke niyar kaiwa hari.Saurin ja da baya tayi tana rufe ido dan wani irin tsoro da kwarjinin Zafar ya kuma dirar mata a guje tayi hanyar waje tana sambatu da jiwa kanta ciwo.


A tsawace Miemie tace"kaima kabar gidan nan bana bukatar ko a lahira na kuma ganin wannan mumunar fuskar taka Kamal,na tsaneka na tsaneka".


"baxan iya rayuwa babu ke ba Miemie,idan kika rabu da ni hakan shine karshen rayuwata,amma ina so ki sani ina matukar sonki"kamal ya kare maganar yana yin hanyar waje da sauri.Fadaww jikin Ammi Miemie tayi tana kuka kamar ranta zai fita.


Daddy ne ya dauko tsadaddiyar zoben azurfa da kuma zoben zinari ya saka su a yatsun hannun Nihla tare da cewa"wannan shi ne sadakinki da ni a matsayina na wakilinki na karba a hannun Abban Zafar da kuma shi,ina fatan ba zaki bamu kunya ba ,duk da labarin ya sauya kala Nihla kiyi hakuri ki karbi Zafar a matsayin zabin da Allah ya yi maki".


Hawaye kasa tsayawa sukayi a fuskar Nihla,kai kawai take gyadawa Abba amma ta kasa furta komai.


A rude Ramadan ya shigo gidan yana fadin "innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Mota ta kade Kamal ko kamanninsa ma baka ganewa wani mumunnn hadari ya faru da shi,kuma a take a wurin ko shurawa beyi ba".Saurin Jan Miemie Ammi tayi ta wuce sama da ita.




5years later.


Fitowarta daga mota kenan sanye take da fararen kaya na nurses sosai kayan suka mata kyau,tayi kiba a bunta murmushi shinfide akan kyakyawar fuskarta.A hankali take taku harta iso kofar da zata sadata da cikin gidan.Da gudu Karami yaro Dan kimanin shekara ukku ya rugo ya rungumeta yana fadin "oyoyo Mummy".Tuni fara'a ta kuma yalwata akan fuskarta ta duka tare da daga yaron sama tace"Faruk sarkim rigima,oyoyo Abbana"Nihla ta fada.Rungumeta yaron ya yi wanda kallo daya zaka masa ka gane tsantsar kamarsa da Zafar kamar ya yi kaki ya ajiye.Da shi a kafadunta ta karasa ciki parlon yana ta zuba mata surutu.Da gudu Famal da Faman yaran Mieme da Irfan suka rugo tare da rungumarta suka rike mata kafafu suna ihun murna.Jin ihun murnar yara yasa Zafar dake zaune yana aiki a laptop ya tureta ya fito da sauri yana fadin"Miemie kina aikin me❓idan kuma suka sakamun mata ciwo fa❓"da sauri ya karaso ya karfi Faruk tare da janye Faman da Famal yana cewa"ku bar Mummy ta huta yanzu ta dawo aiki fa".


Miemie dake zaune tana wa Little Nihla wasa tace"haba Yaya oyoyon ma,to idan ka hana kowa riketa ai baka hana ta dauko takwararta ba,maza karbeta kafin Abban su Famal ya shigo mu wuce".


Dariya Nihla ta sanya tace"kwarai kuwa Abba Irfan ai yamun takwara dole na dauke kayata,ana yayeta ma ko mutun be so dole ya bani takwarata".


Juyar da kai Miemie tayi tare da cewa"kanki ake ji,ni da tun yanzu zaki dauketa ma aida kin faranta mun".


Dariya Aunty Aisha ta saka dake xaune(Aysha yanzu ita ta auri Ramadan dam sam Kaka taki bari ta kubucewa Family dinta),tace"ku kullun dakun zauna musun ku kenan,ni a hada mun duka yara na fiku bukata,kunga Affan(Al-ameen shine yaci sunan Daddy) sai yama yini ban gansa ba daga wannan ya figa sai wannan ya figa".


Tsuke fuska Hajiya Kaka tayi wacce shigowarta kenan parlon ga alamun kara tsufa duk ya bayyana a jikinta tana cewa"Allah kadai zai saka mun Aisha anshi yaron ki tunda baki bani da zuciya daya,daga yauma na gama tabq yaron uban kowa".Ta kare maganar tana ajiye mata Affan akan cinyarta Dan kimanin shekara 1.


Murmushi Nihla ta yi ta daura hannuwanta akan kafadar Kaka tace"rabu da su Hajiya kakata,ga Faruk nan ba baki baki daya ".


"Yimun shiru ko zan dauki kowa banda gadon rashin kunya,wancan yaro tsab ba abunda ya baro na labcecen ubansa,in daukesa Zafar yazo ya kare mani rashin daraja da rashin arziki ba ruwana ni kinga tafiyata".kaka ta fada.


Murmushi Zafar yayi yace"eh ban badawa dai".Harara Daddy ya jefa masa yace"ya isheka haka Zafar,duk yaron da Kaka take so dole ta dauka".Cikin tabbatarwa Ammi tace"kwarai kuwa".


Irfan da Ramadan da shigowarsu kenan Irfan yace"ta dauki kowa banda little Nihla".Sake da baki Ramadan yace"kaima ta baka ansa daidai da kai yanzu ai"duk parlon suka saka dariya cike da tsananin farin ciki da jin dadi.Kallo daya zaka masu kasan cewa lallai farin ciki ,natsuwa da kwanciyar hankali sun gama ratsa ahalin duk da kalubalen rayuwa iri-iri da suka fuskanta amma yanxu ya zama tarihi babu abunda suke fama dashi sama da tarin farin ciki da kaunar juna,bakin ciki ya kau......




Alhmdllh


*kyakyawar gaisuwata ga Maman noor,Hassan Atk,Muhammad kareeem Mk,Sdeen,ina maku fatan alkhairi aduk in da kuke,hakika nayi farin ciki ta yarda kuka bada gudumawa akan yadamub littafin nan har inda banyi tunani ba,na gode sosai Allah yabar zaman tare*




*ina rokon Allah ya albarkaci abunda na rubuta na daidai a littafin nan,wanda yake akasin haka ina rokonsa ya yafe mana,ya kuma bamu ikon yin amfani da darasin dake cikin littafin*




*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*




Jorderh✍🏻

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login