Showing 18001 words to 21000 words out of 41234 words

Chapter 7 - RABON KWADO BOOK 1 COMPLETE .txt

Unknown   

18 Jan 2025

4666

4months kenan da kawo ni gidannan amma ko quda ban taba gani ba kamar banida dangi,gashi rayuwar gidan bata sauya ba kullum jiya i yau,dan ma bana ganinshi sosai dan sai tashi ta kawoshi yake shigowa bangaren.


Wannan shine asalin labari na.
Ku biyo ni dan jin yadda zata kaya har zuwa qarshen lbrn.


Taku har kullum KHAERATY Er mutan ungogoπŸ’‹πŸ’‹
[07-23, 20:40] Sistoh: πŸ’™πŸ’™RABON KWADO...πŸ’™πŸ’™








Er mutan ungogoπŸ’‹πŸ’–πŸ’‹πŸ’–πŸ’‹








πŸ…Ώ71-πŸ…Ώ75




Ban tashi dawowa daga tunanin ba sai 12:39pm.


Ba shiri nayi Addu'a na kwanta,ina fatan Allah ya bani ikon tashi da wuri dan sallamar yarana.


A hankali nake bude idanuwa na wadanda suka sauka akan qaton agogon dake mannne a bangon daki.


Da sauri na duro daga gadon dan idan ba idanuna bane 6:31am na gani agogon ya nuna.


Alwala nayo cikin hanxari kafin na gabatar da sallah.Yau ko krtn qur'anin dana saba banyi ba haka na miqe ina tunanin ta ina zan fara.


Indomie zan dafa duk wanda yaga bazai ci ba ya batta dan na fara gajiya da wannan tsirfar,ko haka suke yi da ya fatima tananan?ko kuma nice da aka mayar baiwa ake min wannan iskancin.


Cikin muntuna da basu haura 20 ba na kammala indomie sannan na soya kwai.


Kwan na qara fasawa Dan yin alalar kwai(awarar kwai)ko kuma kwai cikin kwai naji wasu na kiransa.


Qullawa nayi a farar leda bayan nasa kayan dandano dana qamshi.


Nan ma ban dau lkc ba na kammala na fito.Amma da yake ban farka da wuri ba dana duba agogo 7:27.


A hanzarce nayi musu wanka tare da saka musu uniform,yau ko shafa musu powder din dana saba banyi ba.


Wajen oga shahid naje inda saida na dakeshi sannan ya maida hankali ya shirya na taso qeyarshi gaba.


Yana zaune a daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon yayi crossing din legs yana girgizasu a hankali,ga dukkan alamu mulki da rashin mutunci yake ji dashi.


Kamar ko yaushe wucewa nayi dan Zuba musu breakfast ba tare dana gaidashi ba,dan tun ranar dana gaisheshi yaqi amsawa ban qara gigin gaidashi ba.


Gsky ni baxanci indomie ba"naji shahid ya fada.


Kada Allah yasa kaci,ai kana da hannu zaka iya shiga kitchen ka dafa abinda ranka yake so"na fada a qufule dan yaron ya fara kaini bango.


Jin abinda shahid din yace yasa suma duk suka daina cin abinci,shidai yana zaune baice mana komai ba saima wayarsa da yake latsawa.


Malamai idan bazaku ci ba zan tashi dan ina da abinyi"nace cikin fada dan zuciyata kamar ta fito.


Haba ai abin ya isa hk kullum nice cikin aiki sannan uba yayi min yara su yimin?wlh ina raga musu ne sbd maraicinsu,kuma abinda nasan bazan yiwa yaran dana haifa ba wlh bazan iyayi musu ba,Amma da sbd halin ubansu ne wlh ko kallo basu isheni ba.


A barni da ciwon rabuwa da masoyina mana,a bari naji da kadaici da kewar su ammi dake damuna mana,A barni da baqin ciki da takaicin dake raina na banzatar dani da kowa nawa yayi,a bari naji da aiyuka da dawainiyar da nake kullum mana.
Amma bayan wadannan sai anxo ana min wani fi'ili?
Kawai na sakawa zcytah hqr ne,amma har a gayamin seniority nida nayi bording scul.


Tashi kawai nayi na nufi daki dan idan na cigaba da zama a wajen takaicin zai min yawa.


Bansan lkcn da suka tafi ba nadai kwanciya nayi ina hawayen takaici.


Tunda na shiga dakin ban kuma fitowa ba,dan ko girkin da nakeyi kafin su dawo banyi ba.ni kaina yunwa ce take nuqurqusata tunda ko breakfast banyi ba,wanka kawai nayi dama ina fashin sallah.


Tashi nayi na taimakawa kaina na bude friege na dauki fresh milk na kwankwada sannan na fara dawowa dai dai.


Harabar gidan na fito wanda tunda nazo gidan leqe ma saida dalili.
To nagaji da wannan rayuwar takura kan,fitowa zan ringayi ina shaqar ni'imar ubangiji.


Zagaya gidan nayi tayi harda inda ban taba zuwa ba yau saida naje.Tsarin gidan ya burgeni amma da ace nida ya sadiq za muyi rayuwa a ciki da abin yafi qayatarwa.


Iskar yammar data fara kadawa yasa na qara shagaltuwa dan sosai yanayin yayi min dadi.


Duk wata damuwa saita ragu a zcytah,dan na dade banji irin wannan nishadin ba.


Allah sarki nusaiba,itama tanason iskar yamma,dan ita har ware hannuwa take kiga tanata sakin murmushi.


Zama kawai nake naita mata dariya.
Takance min"Khadija bazaki gane abinda nakeji game da yanayin nan ba,ina imaging abubuwa da dama wadanda bazasu lissafu ba.Amma kuma kinsan masoya sunfi more irin wannan yanayin musamman ma idan suna tare"


Allah sarki sis itama ta manta dani,koda yake kowama bayan su ya zee yake,nidai Allah ya kawo ranar da zan fita a gidan nan naga gari.


Sai wajen magriba sannan na farga da lkcn dana bata a wajen,aikuwa na samu gurin dibe kewa na raya a zcytah.


Iman na fara karo da ita tana rusa kuka.


Babynah menene kk kuka"nace ina tsugunnawa a gabanta.


Ba tpy kikayi kika barmu ba"tace tana shassheqar kuka


Srry kinji iman dina?bazan kuma tpy na barku ba ina tare daku kinji?"nace ina share mata hawaye.


Daukanta nayina saba a kafada dan basa min wahalar dauka,har shahida idan ta rayomin har goyata nake.


Ya fatima taita yimin fada wai nice nake qara sangarta yaran nan shiyasa suke tabara son ransu.
Nidai dariya kawai nake nace"ba dai a shiga tsakanin uwa da yaya ehe"


Sai kiyi tayi ai,ni dai idan mutum ya fara ciwon qirji sannu da dura madara ne kawai nawa"


Allah ka jiqan baiwarnan taka amin.




ina su ya shahidan suke?"na tmby iman.


Tana daki wai abinci xata ci"


Wanka nayi musu kafin suma na basu fresh milk din suka sha dan har lkcn ban huce ba bare na dora abinci.


Ni yunwa nakeji"shahid dake tsaye a bakin qofa ya fada.


Ko kallon inda yake banyi ba,tunda baisan sunana ba kuma bazai iya shigowa ba.


A qasan carpet din dakin muka baje ina koya musu karatun qur'ani kafin daga bisani suka dauko jakunkunan su sukai bitar abinda aka koya musu.


Saida daddynsu ya dawo sannan muka gama,suka tafi wajenshi ni kuma na hau gyaran wadrob.


Aunty wai daddynmu yace kixo"iman tace tana darewa baya na.


Wash baby,lukutar nan dake zaki ringa dare min baya saikin karya ni"
Dariya mukasa dukanmu.


Saida na dade kamar bazaje ba kafin na tashi muka tafi kiran.


Zama nayi ina dora iman akan cinya ta.


Da hikima duk ya kori yaran kafin ya juyo kaina.


"Wato harkin samu damar da zaki ringa yiwa yarana tsawa a gabanah koh?Da kinsan bazaki iya jure duk wata dawainiya tasuba kika ce zaki aure ni"


Saurin dagowa nayi na kalleshi,wato nice ma nace zan aure shi?ko a tunaninsa da son raina akai auren?.




To inaso ki sani idan har bazaki iya jurewa ba kiyi musu duk abinda suke so to wlh yanxu muka saka qafar wando dake.Sannan ki fadan dalilin da kika hana shahid abinci,dama ba tun yau ba na fahimci banbancin da kike nunawa akansu,to wlh baki isa ki raba min kan 'ya'ya ba dan duk daya suke ba bambamci."


Sannan akwai purnishment da kika saka yaranah sukai late a scul,purnishment din kuma shine Zaki girka traditional food kala uku da kuma juice suma kala uku,zaki iya tashi ki bani guri"


Kayi hqr,amma gsky bazan iya wannan girkin ba,dan duk lkcn da nayi sai nayi jinyar kaina.Kuma bada sani na sukai late ba nima makara nayi a bacci"na fada dan wlh bazanyi girkin nan ba wanda nayi dai a baya allah ya bani lada.




Ni kike fadawa bazaki iya abinda na sakaki ba koh?"ya fada yana kallona.


Shiru nayi amma duk abinda za'ayi na riga na fada bazanyi ba dan ba yar aiki aka kawo masa ba.


Banyi zato ba na ganshi a gaba na,zcytah kawai bugawa take amma idan ka ganni a zahira zakai tunanin irin jarumar nan ce.


Dan kinga bana shiga harkarki shine raini zai shiga tsakanin mu?ina daga miki qafa sbd darajar fatima wlh"


Nima ai sbd itan nake daga maka qafa"nace tare da kama hanyar daki da gudu.


Inajinsa yace "mara kunyar qarya kawai"


nidai nace oho dai.😜
[07-23, 20:47] Sistoh: πŸ’™πŸ’™RABON KWADO...πŸ’™πŸ’™






Er mutan ungogoπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹










πŸ…Ώ76-πŸ…Ώ80




Washegari ta kama asabar,muna falo a zaune ina tsefewa shahida kai,domin duka gashin namu yayi datti musammanma ni,domin su nayi musu kalba sati biyu da suka wuce.


Duk rashin son kitsona amma yanxu duk gashin ya isheni,a gida kuwa kar kuso kuga yadda Ammi takeyi dani akan kitso amma yanxu nema nake ido rufe ayimin ko kalbar ce.


Baby a ina akeyi muku kitso?"na tmby shahida ina cigaba dayi mata tsifar.


Da momy tana nan daddy ne yake kaimu salon ayi mana,idan kuma bayanan driver ne yake kaimu"


Kuma Aunty kinsan matar ta iya sosai idan muka dawo ma har daddy yana cewa munyi kyau"




To naji fadi ba'a tmbyki ba,idan daddynku ya dawo kice ya kaiku ayi muku kinga har gashinku ya fara lalacewa,ko kunasu ku zama kwakwidoπŸ˜‡?"


Aa nidai banaso"Iman tace.


Muna gama mgnr yana shigowa,inda sukaje sukayi hugging dinsa.


Ko zama baiyi ba akun ta fara sharhi.


Daddy,wai Aunty tace ka kaimu ayi mana kitso kar muzama kwakwido"


Dafe kaina kawai nayi dan ta kwafsa min,sbd me zata ce nace?


To kuje ku shirya akaiku kaima shahid kana buqatar aski sai kazo kaima muje"yace yana zama.


Da gudu suka nufi daki sunata murna.


Dafatan kin gama girkin dana saka ki"naji ya fada.


Ni sam na manta da wani girki wlh,koda ina sanen ma bayi zanyi ba,sbd niba yar aiki bace😏.


Ganin banyi mgn ba yasa ya nufi dinning area domin duba wa.
Koda baiga komai ba baiyi mgn ba yaran suka fito suka bar gidan.


Allah sarki,dama ni ina za'aje dani?Ai ya fatima itace matar so shiyasa ake zuwa da ita.


Wanke gashina naje nayi nazo nayi masa kalba duk da ba wani kamuwa tayi ba amma naji sakayau.


Yau ma a lambu na wuni saida magriba ta kawo kai sannan na koma kuma har lkcn basu dawo ba.
Wasa wasa har nayi sallar magriba ga gidan ya fara duhu sbd yau hasken bai kawo ba,amma da anayin magriba haske yake gauraye gidan bansani ba solar ce ko inji oho.


Fitila na shiga dubawa wanda tsahon zama na a gidan ban taba nemanta ba.
Haka nasha duba har na gaji dan daqar nake ganin hanyar danake takawa.
Abun takaici ga wannan calculartor din taqi kawowa tunda ban taba saka ta a caji ba.


A hankali tsoro ya fara kamani dan ga duhu gashi banaji motsin kowa.
Haka na cigaba da zama a duhun har issha ina tsammanin dawowarsu amma shiru.


Ban qara tsorata ba sai da na fara jiyo kukan mage ta window wanda a rayuwata bana qaunar mage.


Tun ina daurawa ina addu'a har dai naga kamar kukan qaruwa yake na fashe da kuka tare da darewa gado na lullebe a bargo.


Jin kukan bana mage daya bane yasa na firgice na fara qwalla qara ko zan samu agaji amma inaa.


Tun ina toshe kunnena da hannu har na gaji na saddaqar mutuwa zanyi domin jin kukan nake kamar a kusa dani.


Haka na bata tsahon dare ina kuka wanda yasa muryata dashewa sbd ihun dana sha.


Sai wajen asuba na daina jin kukan magen,kamar hadin baki sai ga haske ya bayyana.


Kuka na na cigaba dayi wanda baka iya jiyo kukan sbd dashewar murya.


A daren dai banyi bacci ba,koda asuba daqar na tashi nayi sallah sbd wani zazzafan zazzabi da nakeji.


Daqar na samu bacci ya daukeni wanda daka kalleni kasan bana dadi nakeyi ba.


Sai 12pm na farka kuma har lkcn akwai zazzabin a tare dani amma dai ba kamar na dazu ba.


Lallabawa nayi na samu nayi wanka tare da yin brush kafin nazo na zira wata doguwar riga.


Fita nayi kitchen dan samarwa kaina abinda zanci.


Fried indomie nayi na dawo falon ina cusawa dan ba wani dadin abincin nakeji ba.


Da sallama ya turo qofar dake sadashi da bangarensa ya qaraso.
A ciki ciki na amsa ba tare dana kalli inda yake ba.


Ban kula ba kawai na ganshi kusa dani ya zauna.


"Sannu fa Mai tsoron mage"yace da murmushi a fuskarsa.


Da mamakina kalkeshi.Dama shine ya shirya min wannan muguntar?koda yake bai kamata nayi mamaki ba domin dama can mugu ne.




Kamar yadda bakya yafiya haka nima ba nayi,kuma na tanadi hanyoyin ladabtarwa kala kala domin sbd keπŸ‘‰,Amma duk ranar da kika shirya yafiya nima a shirye nake da ajiye makamai na.Bawai ina buqatar hakan bane domin bani da matsala ta wannan fannin,kuma ko gobe kk qara wani lefin ko na baki purnishment ki qiyi wlh ba daga qafa"


Bai jira abinda zan fada ba ya koma inda ya fito duk da ni dinma ba abin fadar gare ba.


Kuka na kuma dasawa wanda tasa jikina qara zafi sosai,daqar na rarrafa na koma daki na lullube da bargo dan wani sanyi nake ji.




Saida nakai tsahon kwana biyu kafin zazzabin ya sakeni kuma har zuwa lkc ban kuma saka kowa a idona ba.


To dama wa zan gani?waye ya damu dani bare yazo ya duba ni?
Da ace da ne nayi wannan zazzabin nasan gata sai na rasa inda zan saka kaina.


Sannu,sannu auta,yanxu ina yake miki ciwo?me kikeso a dafa miki?me kike son ci a siyo miki?


Ire iren wadannan tmbyoyi haka nake shansu,amma yanxu ko sannu ban samu ba.


Hk na ringa dauriya ina qarfafa jiki na ,dan gaba daya gidan yayi datti,hk na shiga gyarawa dan qarfafa jikina.


Da yamma ina zaune ina game mai miciji a calculator ta dan ba shiri na zirata a caji dan naga ranar ta.
Tun ban iya ba har nazo na fara iyawa dan koba komai ta ringa debemin kewa da rage kuka da tunani.


Da gudu suka shigo suka rungume ni suna dariya kowa yana cewa"na riga"


Nidai a sakeni kar a qarasani"nace murmushi dauke a fuskata.


Aunty wai Grandy tace tana gaidake"iman tace.


Ina amsawa"


Aunty kinga yau bamuje scul ba munacan gidan grandy...kuma"


Kefa matsalarki kenan shahida,idan bakyanan mutum yaita kewa,amma kina dawowa ki ishi mutum da mgn"Nace ina kwanciya.


Sum sum tabar wajen da alama fishi tayi.


Dole naje nayi rarrashi kafin ta hqr muka dawo nml.


Da dare kamar yadda suka saba da daddynsu ya dawo suka tafi wajensa,ganin na fara tunane tunane yace na tashi na nufi kitchen dan rage aikin da zanyi gobe Da safe.


Haka ya zanto kullum idan suka tafi nakan shiga na rage aiki,idan abin doya zanyi da safe saina feraye tun dare sannan na dafa tea na zuma a flask.hakan da nakeyi yana taimaka min sosai wajen gama shiryasu da wuri dan hk yanxu baya samun damar dazai min mugunta.


A haka har azumi ya shigo inda na duqufa kai kukana ga mahallicina akan sauyin rayuwat dana samu,da kuma nemawa ya sadiq dani kaina sauqi a cikin zcyiyinmu.


Cikin ikon Allah abubuwa suka fara raguwa a zcytah,inda na maida hankali wajen kula da yaranah da kuma koya musu karatu.
Yanxu tare muke shiga kitchen da shahida dan yanxu tana 9years ne,sosao take taimakamin kuma take gane abubuwa sbd kasancewarta mai tmby komai ta gani saita magantu.


To alhmdllh yanzu shima shahid yana shigowa cikinmu ayi krtn dan shima ina saka shi cikin addu'atah








Kuyi hqr da wannan bansamu lkc bane amma next zanyi mai yawa insha Allah.NgdπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
[07-23, 20:47] Sistoh: πŸ’™πŸ’™RABON KWADO...πŸ’™πŸ’™








Er mutan ungogoπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹








πŸ…Ώ81-πŸ…Ώ85




Cikin ikon Allah yau idan mun kai azumi 27.


Dama rayuwar haka take kana naka allah na nasa,sai dai muyi fatan cikawa da imani.




Muna zaune a falon bayan shan ruwa,iman tana danna min qafafuwa na sbd gajiyar da nayi na haka kayan shan ruwa,domin duk cikinmu iman ce kawai batayi.


Sosai nake jan yaran a jiki ina koya musu abubuwa wadanda nasan zasu amfane su,hakan yasa muka zama abokai dasu dan har shahid yanxu shiri mukeyi dashi.




Ta qofar waje ya shigo da alama yanxu ma ya shigo a gidan.


Kamar ko yaushe suka tashi suka rungume shi suna masa welcome.


Tashi nayi na nufi daki dan irin haka idan ya dawo daki nake tpy na barshi da yaransa.




Har bacci ya fara daukata najiyo muryar shahid.




Aunty khadija ki tashi kiga kayan sallarmu da daddy ya siyo mana"


Dan dole na miqe dan yadda suke jijjigani kowa yanaso na tashi naga nasa kayan.


Masha Allah kawai nake maimaitawa dan kayan sunyi kyau sosai,dan ba sai an fada maka ba kasan an kashe kudi masu yawa wajen siyansu.


Kowa kala 4 ne kayan sai takalma kala 2.




Gsk daddyn nan yanaji daku"na fada ina qara daga kayan dan sun tafi dani.




Aunty ai yace ba suke nan ba,gobe za'a karbo sauran a wajen dinki"shahida tace.


To kun dai ce kun gode koh"


Aunty wai ke ina naki kayan sallar?"iman ta jefon tmby.


Nawa suna nan da safe zan nuna muku"nace ina yaqe.




Aunty kema daddy ne ya siya miki?"ta qara tmby.




Aa ammina ce ta siya min"nace ina miqewa dan adana kayan domin nasan idan na zauna qara tmbyta zatayi ba kamar shahida.




**-**-**-**-***-**




Da safe muna zaune a falo ina yanke musu farce ya shigo yana wani ciccin mgn.




Ummina ku shirya na kaiku kitso kar yamma lkc ya qure"yace yana kallon shahida don sunan umminsa gareta.


Daddy ni fa?"shahid yace.


Kaima ka shirya zan kaika aski"yace yana zama.


Da suka dawo cikin hikima ya korasu wajen mota kafin ya juyo kaina.


Ina shirin miqewa najiyo murtarsa.


Anjima za'a kawo kaya,dan gobe friends dina zasu zo kuma za'a kaiwa ummi da gidan Abbi abinci"yace yana ciccijewa kamar wanda aka yiwa dole.






Kamar yadda ya fada bai dade da fita ba aka kayo kayan.


Kaji ne da kayan miya sai sauran abubuwan amfani.


Ba bata lkc na fara aiki dan naga aikin mai yawa ne.


Sosai na rage aikin dan sinasir nake sonyi goben da miyar kajiπŸ˜‹sai wasu kajin dana ware dan soyawa.


Sai wajen 11pm suka dawo dan har na fara cire ran dawowarsu.


Ai kuwa sunsha jan lalle wanda yayi maroon sbd kamu,sai twisting da akayi musu shima ba'a cewa komai.
Shahid kuwa aski da gyaran fuska yasha.


Nan fa akaita bani labarin abubuwa,nidai gado na haye dan ganin basu da shirin kwanciya dan kowa ya dauko kayansa da suka shigo dasu suna gwadawa.


Leshi ne mai kyau da tsada,sai wata dakakkiyar shadda da akayi musu iri daya dukansu.


Da wuri na shiga kitchen washe gari,dan saqon na shiryasu da wuri zasuje idi tuni ya riskeni.


Saida na gama suyar kajin na dora miya bayan na hada qullin sinasir din sannan naje dan shiryasu.


Zama nayi na tsara musu kwalliya tare da musu daurin dan kwali da yake wai yace shaddar zasu saka.


Ras yaran suka fito dan idan ka gansu kamar ka sace su ka gudu.


Fitowarmu tayi dai dai da fitowarsa,inda shima yake sanye da shadda irin tasu sai zuba qamshi yake kamar wani angoπŸ˜„




Ganin sun manta dani sunata kwasar selfie dinsu tasa naja jiki na koma kitchen dan cigaba da aiki na.


Allah sarki ni,kowa yana tafiya idi ni ina kitchen ina aiki,nima da a gidane da yanxu mun tafi nida abbi koda nusaiba.


Gashi ace sallah guda bani da kayan sallah?duk da ba rasa sababbin kaya nayi ba amma ai kayan sallah daban yake.


Ace sallah guda ba kitso bare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login