Showing 18001 words to 21000 words out of 23314 words
Chapter 7 - KANO TO JIDDA BOOK COMPLETE DOCUMENT by Zahra Muhammad Mahmud--.txt
airport din sannan tafara neman hanyar tashar mota,
tashar yan kura aka kaita anan tasamu mota me zuwa madobi,daga madobi tahau ta yako, da aka sauketa a yako mashin biyu ta ɗauka ta ɗora kayanta,suka nufi laminkwai.
Gidansu nanan yadda tabarshi sema ƙara lalacewa da yayi.
A ƙofar gidan aka sauketa,tashige da kayanta.
da sallamarta ta shiga gidan,lokacin baffanta na zaune yana wanke kwanukan da ya dawo tallan abinci.
Da wani uban gudu yataso har yana faɗuwa yazo ya rungume suhaima,kuka yake wanda itama take tafara kukan.
lantana dake ɗaki jin kukansu ne yafito da ita.
wata uwar tsawa ta dakawa baffa wanda ba shiri yasaki suhaima ya nufi gurin lantana ya rusuna.
Se alokacin lantana taga suhaima duk da girma dakyau data ƙarayi hakan be hanata ganetaba.
wata uwar shewa tasaki sannan tace.
"Ragowar larabawa har sun gama yayinki sun aunoki gidane?"
shuru suhaima tayi tana kallonta.
"Hhhhh aƴ ita dama bariki alelen gero ce inka iya yayi kyau inbaka iyaba ta kwaɓema,tode ke da duka alamu takin batayi kyauba"
Suhaima bata kulataba illah ma ɗibar kayanta da tayi tanufi ɗakinta nada,ɗakin yana nan yadda yake sede ya tsage akowanne lokaci ze iya faɗuwa.
sharewa tayi sannan ta jere kayanta agefe ɗaya.
Ranar lantana wuni tayi tana bin makwabta tana faɗa musu ay suhaima ta dawo daga karuwanci,kan wani lokaci gaba ɗaya kowa yaɗauka.
koda ta gama abinci bata bata ba daga ita har mahaifinta.
fita suhaima tayi ta siyo kayan abinci da sauran kuɗinta,tabiya gidan su hanne ƙawarta ta samo tukunya tazo ta haɗa murhu ta ɗora abincin.
hartagama lantana se habaici take mata,itade nata ido,mahaifinta ta zubawa itama ta zuba.
sukaci sannan kowa yanufi makwancinshi.
se tsakar dare mahaifinta ya sato jiki yazo ɗakin suhaima sukasha hira anan yanemi gafararta harda kukanshi,yafemishi tayi,itama tana kuka,amman bata bashi labarin tayi aureba bare tabashi labarin abinda yadawo da ita.
washe gari tun asuba baffa yatafi ɗebo ruwa seda gari yay haske sannan yadawo,saboda yanzu kura lantana tasiya mecin jarka goma da ita yake zuwa daurawan yaɗebo ruwan.
Suhaima tausayin mahaifintane yasa tazo ta dunga juye ruwan, koda zeyi wanke wanke ita ta amsa tayi.
dako taga yaɗauki farantin kayan abinci ze tafi tallah da sauri tazo ta tareshi anan lantana tafito tafara ruwan balai.
"ke harni zaki nunawa bariki to wlh baki isabs,dole kibarshi yaje yanemomin kuɗi inko bazashiba to wlh sede ke kitafi ki yi tallan dan wlh ba zaman banza a gidana"
suhaima amsar farantin tayi tafice baffa yabita da Allah yamata albarka.
bayan fitar suhaima wanki lantana ta jidowa baffa ta sashi agaba akan se ya wanke.
ɗakin suhaima tashiga ta jide kayanta,sede Allah be bata ikon taɓamata handbag ɗinta ba,zuwa tayi tasiyar agarin yako ta amso kuɗaɗenta,sannan taja kunnen baffa akan inyasake yace itace ze gamu da ita.
baffa har kuka yayi,dan tausayin halin da suhaima zata shiga inta dawo ta tarar ba kayanta.
Suhaima ko tunda tafito yara suke binta suna mata waka,waiga karuw ga karuwa.
har suna jamata hijabi,daga karshede seda ta ruga da gudu sannan suka kyaleta.
koda ta dawo gidan ganin ba kayanta bata tambayaba dan tasan sun halaka kenan,kukanta kawai taci tashare hawayenta.
Rayuwa tayiwa suhaima tsanani,itace wanki shara wanke wanke,dan bazata jure ganin mahaifinta nayiba.
Tallah ko dama tuni tacigaba dayi,gashi kayanta kala ɗayane,abun gwanin ban tausayi,
awannan lokacinne cikinta yafara fitowa,duk da cewa dama watansa biyar ta iso nigeria to amman be fitoba se awannan lokacin,nanfa mutanen gari sukace dawa Allah ya haɗamu.
inde zata fita se sun jefeta,haka take haƙuri,koda mahaifinta yatambayeta waya mata ciki,kawai cemishi tayi acan nasamoshi.
lantana abun nema yasamu,wahalar duniya ganawa suhaima take sabida tahana mahaifinta ya wahala.
cikin suhaima ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe amman hakan be hana lantana cigaba da azabtar da ita ba.
Yau suhaima tun cikin dare marar ta ke ciwo amman haka ta daure da asuba tayi ta ɗauki kura tanufi ɗebo ruwa.
da kyar ta debo ruwan,ciwon ya tsananta da zuciyarta kawai take turo kurar harta iso garinsu.
daidai gidan su hanne ƙawarta tagaza ci gaba da tafiyar,da rarrafe tashiga gidan tana kuka.
tunkan maman hanne ta ƙaraso gurinta faya tafashe,da sauri ta ɗagata suka ƙarasa ɗaki.
nanfa suhaima sunan Allah kawai take kira tana faɗin.
"Allah kadubi maraicina karabani da cikinnan lafiya,Allah kada ka ɗoramin wahalar dakasan anan bani da gata senaka"
maman hanne har kuka tayi sabida tausayinta.
nande maman hanne ta dunga bata duk wani sassake datasan yana rage wahala,ayko cikin hukuncin Allah ɗanta namiji yafara kunno kai,da taimakon maman hanne ya iso duniya lafiya,se kuka yake tsanyarawa,balaben usuli,babu inda yabaro ubansa,zuwa can wani sabon ciwon ya turnuƙe suhaima,ba jimawa yar kyakkyawar yarta ta mace ta kunno kai cikin hukuncin Allah,itama ta iso duniya se kuka sukeyi.
Yaran kyawawane na bugawa a jarida,namijin tamkar shureim haka itama macen,babu inda suka baroshi.
Nan maman haule ta wankesu tas ta naɗesu azannuwa sabida babu kayan da za saka musu,tayiwa suhaima wanka tabata abinci taci sannan ta rakata gidansu ɗauke da kyawawan yaranta.
wani yaro tasa ya tura kurar ruwan zuwa gidan su suhaiman.
*********
shureim faɗuwar da yayice ta haddasa mishi paralise,seda ya kwashe watanni biyar yana jinya sannan ya warke,
Yana samun sauƙi ya kafa rigimar se yatafi nigeria,sabida yasan babu wata kasa da suhaima zataje sama da ita.
Fafur sarki yaki amincewa,sabida shureim be taɓa zuwa nigeria ba.
Ayko nan shureim yatashi hankalin kowa, Akan abarshi amman sarki yahana sabida beson ya rasa ɗansa kuma magajinsa.
To ana hakanne suhaima ta haihu a nigeria.
muje zuwa.
surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*BILKISU U HAMZA NAGODE ALLAH YA ƘARA GIRMA DA DAUKAKA,#AUNTY HALILOSS ANA TARE NO MATTER HOW HARD THE SITUATION IS,JUST KEEP BURNING THE LIGHT,*
*Dedicated to Zahra Bukar*
*47-48*
Lantana ranar jitayi kamar ansata a aljannah dan mugunta,daɗin dataji beda iyaka dan haka makwabta tashiga yiwa shela.
Ayko nanfa gidan yacika damƙam anzo ganin yayan zina
Suhaima ko rungume yayanta tayi ta hana kowa ya ɗauka gamida rufe fuskokinsu.
Se dare gidan ya watse.
Ga sanyi anayi,suhaima se ƙara rufe yaranta takeyi gudun kar sanyi yamusu illah,
Mahaifintane yakawo mata tabarmarshi da bargonshi da filo dayake kwana akai yabata yace ta dunga kwantar da yaran tana rufesu.
Shida kanshi yamusu huɗuba bayan ya tambayi wanne suna takeso asa musu.
Kanta tsaye,tace
"AbdulRahman da AmatulRahman"
ayko haka yasakamusu suna,dan yace koma taya suhaima ta samar da yaran shine sila,da beyi watsi da rayuwarta ba hakan bazata faruba,shiyasa memakon tsana shi tausayinta yakeji.
Washegari da asuba lantana tafito tafara balai akan azofa aɗrmebo mata ruwa,suhaima na shirin miƙewa se taji baffanta ya fito ya tafi da kurar.
Kukane ya kuɓcewa suhaima tana rungume da yaranta take faɗin.
"me yasa habibi kayimin haka?,meyasa kakase gane niba fasiƙa bace?,meyasa kakasa shaidata?,meyasa?" ta ƙarasa maganar cikin kuka.
Gari be gama wayeba sega hanne tazo gurin suhaimar bayan sungaisa tace mata.
"innace tace nazo na tayaki ɗaukar yaran kizo tamuku wanka tun ɗazu ta kwashe ruwan"
kukane ya kwacewa suhaima data tuno tata innar.
Haka suka tafi gidan su hanne.
suna zuwa toilet suhaima tashiga inna tamata wankan jego,sannan tasata ta zauna a ruwa.
Bayan sun fito inna ta wanke yaran,sannan ta ɗauko rigunan data siyo musu jiya da yamma tasaka musu.
duk da rigunan bamasu tsada bane amman,sunyi musu kyau.
Daga ƙarshede suhaima a gidan ta zauna inna na kulawa da ita har seda tayi arbain.
su twins ko irin masu girman,agir dinnanne,sunyi yan lukutaye dasu abunsu,gasu da wayo.
Bayan suhaima tayi arbainne takoma gidansu,taci gaba da bauta,dan bazata juri ganin mahaifinta nayiba.
ya hanata yace tabarshi shi yayi amman fafur taki amincewa.
Ruwa kawai take barinshi yana ɗebowa,amman tallah tuni ta koma bakin aykinta.
in zata tafi,seta goya twins,ɗaya agaba ɗaya abaya,innar hanne ce ta koyamata irin goyon.
Se tasaka hijab ɗinta ta rufesu ahaka zasuje sugama yawo arana su dawo.
Duk wani haske da suhaima tayi tuni ya dishe,sabida wahala.
Yau tun cikin dare Abdulrahman yake kwara amai,ga zazzafan zazzaɓi daya rufeshi,se kuka yakeyi,
Hankalin suhaima inyayi dubu yatashi tarasa inda zatasa kanta Allah Allah take gari ya waye.
Ayko bakwai abakin chemis din rabiu dan me gari yamata.
Duk saurinta seda ta samu layi,sabida chemis din shine kamar asibitinsu,dayake babbah ne.
Layin tashiga har yazo kanta.
Koda tashiga yagama dubashi,maganin dubu daya yarubuta mata.
kuka suhaima tasamishi akan yaymata bashi zata biyashi,buɗar bakinshi se cewa yayi.
"keko suhaima din Allah haka kikaje kika gama rabawa larabawan abun kyauta basu baki komaiba se tukuicin yayan zina?"
maganar ta doketa amnan tunda neman taimako takeyi dole ta bashi amsa a saukake.
"wlh kabiru yaran nan bana zina bane,zaku tabbatar da hakanne ranar da mahaifinsu yabiyo sahunsu"
"nufinki aure kikayi acan?"
Da sauri suhaima tace,
"Aure nayi,to mijina ne yasakeni shiyasa nadawo"
"tunda yasakekine to inga takardar sakin".
dayake da handbag dinta ta tafi ba musu,ta zuge ta ɗauko katin Atm se alokacin ta lura akwai wasu takardun kanana aciki ,duka ta ɗauko ta miƙawa Rabiu.
Amsa yayi yana dubawa,yana dariya,sannan yace.
"Suhaima ay wannan ba takaddun saki bane,takardun cire kuɗine akowacce ƙasa kake inkaje zaka cire kuɗin dake cikin asusun ajiyarka"
ido kawai suhaima take warewa,dan bata yarda da batun na rabiu ba.
ganin bata yarda bane yasa yace.
"kinga bari inbaki maganin kije kibashi,anjima inkina da lokaci inna tashi daga ayki,kizo muje kano a duba miki aga ko nawane aciki,da duk wani bayani zasuyi miki"
se yanzu hankalinta ya kwanta,dan ita lafiyar ɗanta yafi mata komai.
maganin yabata ta dawo gida,taba Abdurrahman,sannan taimusu wanka itama tayi,ta goyasu suka tafi tallah.
bayan ta dawone,taje gurin rabiu shima lokacin yatashi,dan haka a motarshi ya dauketa honda civic,suka nufi kano.
Tafiyar awa guda ce takaisu bakin wafer.
Da kyar suka samu suka samu wanda ze musu abinda yakawosu,baa sha wahala ba sabida a takardun harda pin number da accaunt no,dan haka,mutumin nagama dubawa ya ɗago yace musu.
"da akwai kuɗi aciki har kimanin naira miliyan dari dari"
"miliyan ɗari?"rabiu da suhaima suka haɗa baki gurin tambaya.
Tabbatar musu da hakan yayi.
suhaima sabuwar soyayyar mijintace takamata,wato yabatane dan beson tasha wahalar rayuws.
Dubu ɗari uku suhaima tasa aka ciro mata,sannan suka baro gurin.
Kasuwa tasa yakaita,nanfa ta dagargaji siyayya,tasu twins dinta,harda gidan sauro ta siya musu,da madara da cerelac,daduk wani nauin abinci na yara me gina jiki.
suturu kuwa tasiya musu su ba adadi,da pampers duk ta jidar musu,da takalma,da sabulan wanka dana gyara gashinsu,dayake gashi garesu sosai irin na larabawa.
seda takashe dubu ɗari biyu a siyayyarsu,sannan taba rabiu dubu talatin,se godiya yake mata,sabida yaji dadinsu.
haka suka kamo hanyar laminkwai,gab da magriba suka iso.
lantana na zaune se gani take ana shigo da kaya,har aka gama shigewa dasu ɗakin suhaiman.
wani baƙincikine yaziyarci zuciyarta,take tasha alwashin seta sace kayan.
Bata gama tunaninba,sega suhaima dame gyaran ƙofa,tasa yasakamata kuba a kofar,ta yadda duk balai bame shigar mata ɗaki.
shiga tayi ta ware komai,sannan ta kafa musu katifunsu da gidan sauronsu.
dubu ashirin ta ɗauka takaiwa maman hanne,sannan tamata bayanin komai,godiya taimata sosai gami da sa albarka.
a ƙofar gida tasamu mahaifinta,tamiƙs masa dubu arbain sannan tace masa.
"Baffa ka ɓoye kadunga cin abinci me kyau don Allah ko gobe suka kare kamin magana zan ƙara maka,kadena yiwa matarka biyayya sabida abun duniya kaji don Allah"
murnar da yayi bata da iyaka,dan azahirin gaskiya sabida kuɗi yake bin umarnin matarshi,dan yasamu nacin abinci.
Cikin kankanin lokaci,baffa ya sauya duk abinda yakeso yakeci,ba abinda yadameshi da girkin lantana.
su twins tuni sun fara iya zama,Abdurrahman dayake yafi ƙiriniya har yafara son yayi rarrafe.
Yanzu suhaima inzataje tallah se takaisu gurin maman hanne,dan bata dens tallan bane sabida masifar da lantana take zubawa mahaifinta.
sabida hankalin baffa ya kwantane yasa taci gaba da tallan.
ɗakinta kullum arufe yake ba damar lantana taimata sata.
kuɗinta insuka ƙare rabiu ne me zuwa ya ciromata wasu yakawo mata.
amanar rabiuce tasa suhaima ɗaukar miliyan guda tabashi,ya faɗaɗa chemis ɗinshi.
Watannin su twins bakwai suka fara rarrafe,abun gwanin shaawa.
*******
Saudiyya
Ba irin neman da baayiwa hajiya murja a riyad ba amman baa sameta ba hankalin shureim sosai yakara tashi,
hakanne yasa ya tuno da sabuwar dabarar dazatasa abarshi yatafi nigeria
Yau wani ɗan matashin yaƙi ya balle agidan sarki.
Shureim ne ɗauke da wuƙa a hannunshi,ze cakawa kanshi,idan baa barshi yatafi nigeria ba.
duk yadda sarki yaso ya ajiye wuƙar amman ina yaki,maimakon hakama har yafara yanka hannunshi jini na zuba,ya ɗaga ze caka acikinshi kenan,sarki yakwallah kara yana faɗin.
"na amince ka shirya katafi!!!!!"
da gudu ya wular da wukar yaje yarungume mahaifinshi yana kukan farinciki.
A Ranar ofishin jakadancin saudiyya dake nigeria suka bada sanarwar,zuwan ɗan sarkin saudiyya sarkin gobe da yardar Allah ze iso nigeria,.
Nan danan fadar shugaban kasa tafara shirin tarbarsa.
Shiko shureim da kyar ya amince se washe gari ze tafi,cikin dare gaba ɗaya angama haɗa komai na tafiyarshi kama daga escote dade sauransu.
washegari da misalin karfe goma na safe jirgin sama mallakin masarautar saudiyya,ya ɗaga da shureim da maƙarabansa,daga filin jirgin sama na garin zuwa kasar nigeria.
garin masoyi baya nisa.
muje zuwa
surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Kungiyar matan aure na garin bauchi naga sakonku nagode sosai,Allah yasa ku ɗore da aywatar da abunda kuka fahimta a gidajenku,na Aure Ameen*
*dedicated to zahra bukar*
*49-50*
Gaba ɗaya titunan dake Abuja jamian tsarone ta ko ina,yayinda helicopters keta shawagi asama.
Ƙarfe biyar na yamma jirgin saudiyya ya sauka a airpot a Abuja.
Shureim ne yafara saukowa,sanye yake da farar jallabiya,ya ɗaura rawanin larabawa yayinda idonshi ke ɓoye cikin baƙin glass.
Tawagar shugaban ƙasace ta iso da sauri,shugaban ƙasa yatarbeshi,tare ds ambasadon saudiyya na nigeria.
Acikin tawagar shugaban ƙasa,Akwai minstan mata,hajiya salbiyya Adam itama taje tarbar shureim,Ministan kuɗi,Hassan Atk shima baa barshi abayaba,can daga gefe nahango tawagar ,Mufarka mata suma sunyo ƙungiya guda ƙarƙashin jagorancin admins ɗinsu,zinnira da Hameeda.
Kalli iya kallonka bazaka taɓa hango ƙarshen masoyan surbajo da suka cika airport din domin tarbo shureim ba.
Kai Abun rukuni rukuni ne,sanda shureim ya ɗags idonsa ya hangi yawan alumar Khaleesat hydar novels,kimanin mutum dubu sabain da uku,sunzo tarbarshi ay kawai se hawaye yafara zuba a idonshi,dan be taɓa tsammanin nigeria haka suke da karrama baƙiba,se yau.
Nanfa jamian tsaro suka kasa suka tsare suka hana kowa isa gareshi.
jerin gwanon motocine suka ɗaukesu zuwa vila,yayinda,Tafeesu novels,da m kaoje novels,da da da da da🤣suka mara musu baya da gudu.
Sabida cunkoson mutanene yasa motocin basa sauri,sun jima kamin suka samu suka isa vila.
Shureim da kyar yayi bacci washe gari ko,yace,anunamishi kano,danshi Azatonshi kusane daga inda yake.
Nande ya fayyacewa shugaban ƙasa abunda yakawoshi,sosai yatausaya masa,hakanne yasa shugaban ƙasa ya umurci minister yada labarai Hajiya Zahra Surbajo yace,tasa afara cigiyar suhaima ta kowacce kafa ta sadarwa,
Kwanaki uku aka kwashe ana sanarwa harda kyautar,kujerar makkah da maƙudan kuɗi gaduk wanda yasanar da ganin suhaima.
Shide shureim gani yake in aka kaishi kanon zefi ganinta da wuri,dan yariƙe sunan kanonne tun ranar da hajiya tabasu tarihinta.
har tsawon sati guda shuru kakeji.
Shureim duk yatashi hankalinsa.
Sabida yace a kano takene yasa aka fo tsaurara bincike abirni da kauyukan kanon.
********
Rabiune zaune A chemist ɗinshi yana duba marasa lafiya,yayinda gefe ɗaya kuma yake sauraron redio.
Wata murya yaji rangaɗeɗiya,tafara da cewa.
"Assalamu alaikum jamaa masu sauraro barkanmu da sake saduwa daku acikin shirinmu na filin cigiya da sanarwa,wanda ni Autar hajiya zan jagoranta,A shirin namu na yau zakuji kautukan da akasaka gaduk wand yanemo wata matashiyar budurwa me suna suhaima yar jahar kano,suhaimade ta baro saudiyyane a ranar........ Zuwa gida nigeria,suhaima farace me matsakaicin tsawo,sannan suhaima tana ɗauke da ciki a lokacin tahowar tata,ansaka kuɗi wuri na gugan wuri har naira miliyan goma,da kujerar makkah,ga duk wanda yabada sanarwar inda suhaima take,ga wanda Allah yasa yadace da ganinta,se ya tuntubi minister yada labarai akan nombobi kamar haka,08093235..🤣Allah yabada ikon ganinta akan lokaci Ameen".
jikin Rabiu har rawa yakeyi wajen zaro wayarshi a aljihu,gurin kwafe number,yana gamawa yayi dialing.
ba jimawa aka ɗauka,sabida dama layin sabo aka saka sabida hakan.
Nandanan Rabiu yashaida yasan inda take,batare da bata lokaciba yabada Address.
sallamar kowa yayi yanufi gidan su suhaima.
Ayko yaci saa tafito zata tafi tallah kenan.
cikin mutunci suka gaisa,sannan yace.
"Yau kinada babban baƙo,nikuma yau nayi byebye da talauci"yaƙarasa maganar yana dariya.
Itama dariyar tayi,sannan tace.
"wanne irin babban baƙo kuma rabiu?"
"nima wlh bansaniba ammande nasan tabbas yau zamuyi baƙi a garinnan"
"To Allah yasa baƙin na Alkhairine"
"Ameen,sannan yaude don Allah ki haƙura da zuwa tallan nan ni zan siye duka"
Dariya tayi ta ɗauka da wasa yake se gani tayi ya sauke abincin yafara bawa yara sadaka,yana gamawa,yaciro kuɗinta yabata.
Godiya tayimasa sosai,sannan ta koma cikin gida.
Lantana taji takaicin dawawor suhaima da wuri shiko baffs yaji daɗin hakan.
*********
Sanda labarin ganin suhaima ya isa fadar shugaban ƙasa shureim kafa ba takalmi yakwasa da gudu yafita waje dan ya ɗauka anzo da itane.
koda yaga babu ita ido kawai yake zarewa kowa se mamakin irin son da yake mata suke.
dakyar ya kimtsa,aka hsɗashi da jamian tsaro suka hau jirgi zuwa kano,daga kano gomnatin kano tashirya mishi motoci na alfarma,ana bugamasa jiniya,ƙarƙashin rakiyar minister yada labarai zahra surbajo,da shi kanshi gomnaɓ kanon,suka nufi garin lamin kwai.
muje zuwa.
Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Wayyo masoyana kuyi haƙuri surbajo nasonku aduk inda kuke,nafeesa Abdullahi,baze yiwu surbajo tasa numberta a page ba sede ke ki rubuto taki kituro, da yardar Allah zata iso gareni,bama keba duk wani masoyina dayakeson hulɗa dani ya rubuto numbersa yaturo,zasu iso gareni kuma insha Allahu zan nemeku,banaki saka number na bane dan tsoroba kawai de dan jaddada tsarone nagode*
*dedicated to zahra bukar*
*51-52*
Duk inda suka wuce kallonsu akeyi,sabida motocine sunkai guda Ashirin jere akan titi.
Sannu a hankali suka iso garin na laminkwai,dan haka sauka sukayi akantiti,sukabi jar ƙasa zuwa cikin garin.
Wuyan shureim kamar ze tsinke sabida ƙara masa tsawo dayakeyi.
Yan garin sunga abun da basu taɓa ganiba,sabida suna hawa titin jar kasar lamin kwai ɗin,
Escote suka firfita daga motocinsu suna gudu aƙafa,motar da shureim yake ciki kuwa,escote ɗin larabawa kowa sanye da bakaken suit,fuska manne cikin bakin glass,kunne maƙale da bluethood,hannu ɗaya cikin riga riƙe da bindiga.
Wallahi koni tsarin yaminni.
Mutanan garin kiɗimewa sukayi,ganin fararen fata a ayarin tafiyarne,yasa alumar garin fara rawar murna.
Domin a tunaninsu man fetur ne a garin nasu,shine akazo a haƙo,yayinda wasu kuma tunaninsu yafi karkata akan service ne ya faɗo garin.
Hakanne yasa kowa ya shiga adduar Allah yasa agidansa ya faɗo.
acikin masu tunanin service ɗinne harda lantana,addua tayita ba adadi akan Allah yasa a gidansu ya faɗo.
Suna isa garin ƙofar gidan me gari suka tsaya,dama tuni rabiu yana binsu abaya.
me gari rawaninshi har yana faɗuwa sabida kiɗima,danshi azatonshi yan taadda aka gano a ƙauyen nasa.
Nan aka buɗew su Shureim ƙofa suka firfito,shureim kallon garin kawai yake yana mamakin ta yadda suhaima zata iya rayuwa acikinshi.
Number rabiu aka fara kira da sauri yafito tsakiyar filin,yana ɗaga hannunsa.
kofar fadar me gari kuwa tacika damƙam da mutane yan ganin kwakwaf su lantana ne agaba gaba,ta baro suhaima gadin gidan.
Shiko baffa bayanan yaje ɗaurin aure kwanar ɗangora,na yarinyar abokinshi.
Shureim ganin rabiu amatsayin wanda yasan inda suhaima take da sauri yakamosu ya riƙe yana tambayarshi tana ina.
Duk yadda akaso ya kwantar