Showing 3001 words to 6000 words out of 23314 words
Chapter 2 - KANO TO JIDDA BOOK COMPLETE DOCUMENT by Zahra Muhammad Mahmud--.txt
ya ɗaukesu dukansu,kowacce cike da kewar gida,bama kamar suhaima,da ita kaɗaice yar garinsu.
muje zuwa.
surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*Maki gani ya kauda idonsa👇*
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
*DEDICATED TO ZAHRA BUKAR(ALLAH YA SAUKEKI LAFIYA,AMEEN)*
*9-10*
Washe gari da safe,bayan sunyi sallah,wanka sukayi sukaci abinci,sannan hajiya duniyar sama ta kwashesu zuwa wani boutique.
Suhaima se murna take ta ɗauka zasu gurin Annabi ne,ganin sun tsaya abakin boutique ne yasa tagaza yin shuru tace
"Hajiya don Allah yaushe zamuje mukaiwa Annabi ziyara,naji ance anan yake?"
Wata uwar tsawa hajiya ta dakamata sannan tace.
"uban waye yace miki,duniyar sama na siyo yanmata dan suzo sukai ziyara madina,?to in mafarki kike kiyi saurin farkawa,atafiyata,nafarko baa aure,kuma baa zuwa masallacin harami,bare kuma kiyi tunanin zuwa madina,basu na kawoki kiyiba,dan haka ki kiyaye,dan duk wacce takarya dokata wlh hukuncinta haukacewane kunde ji na gaya muku"
Bayan sun shiga ta siyo musu kayanne,suna hanyar komawa gida,suhaima bata daddaraba tasake cewa.
"To hajiya me muka zo yi anan don Allah?"
"kunzo karuwanci ne"cewar hajiya tana tauna cingum.
👀👀👀👀haka suhaima take waresu,kana daga bisani,tace bakinta na rawa.
"hajiya ni mahaifiyata tace bata yafeminba inna aykata zina kuma tarasu"
Daidai lokacin suka iso gidan.
suna fitowa hajiya tabata amsa da cewa.
"yaro man kaza to ay baki saniba yau ko uwarkice hajiyar sama tasa kuɗi tasiyota zuwa nan kasar,to wlh,dole tayi abinda nasata bare ke"
Tasssssss,suhaima ta ɗauke hajiya da wani lafuyayyan mari,sannan tace tana kuka.
"ni kika siyo ba inna taba,baki da hurumin yin magana akanta,sabida bata da alaƙa da fasiƙa irinki,ina jure komai amman banda wulakanta mahaifiyata"taƙarasa zancan tana kuka,
ga mamakinta memakon taga hajiya taji haushi,se kawai taga tayi dariya tace.
"you will fay for it"
Dayake suhaima come ce,bataji me hajiya tace ba,binsu tayi abaya zuwa cikin gidan.
Su hajiya sun rigata shiga,ayko tana shiga taji anrufeta da duka.
Yanmatane su biyar majiya ƙarfi,sukaimata shegen duka,seda takasa motsi,sannsn hajiya tas suka kaita wani ƙaramin daki suka wurgata ciki suka kulle,
Suhaima jitayi ana taɓata ,da sauri ta buɗe idonta tana kallon me taɓata
wata yar matashiyar budurwace,wacce zasuyo sannin juna,itama kyakkyawacd ba laifi.
Kama suhaima tayi ta tasar da ita zaune ta jinginata da jikin bango,
da kyar suhaima tace.
"wacece ke,me kikeyi anan?"
kuka yarinyar tasa tace.
"sunana sajida,ni yar bauchi ce a nigeria,watarana nafito zani makaranta,se wasu mutane suka saceni,suka kaiwa wata hajiya wai ita uwar mabuƙata,shine aka kawoni nan jiddah da sunan zanyi karuwanci,to danaki amincewane shine suka sani aɗakinnan,suna ganamin azaba iri iri,watana shida kenan a ɗakinnan,sesun ga dama suke bani abinci,nasan kema kin amincewa da kikayine yasa suka kawoki nan"
rungume juna sukayi suna kuka suna rokon Allah yakawo musu ɗauki.
Wasa wasa seda suhaima rayi wata uku a ɗakin tare da sajida.
yau gidan shuru alamar kowa yatafi fasikancinshi.
jin karar bude kofar ɗakin dasuke ciki sukaji hakanne yasa dukansu suka natsu.
Wata yamushashshiyar matace tashigo ɗauke da kwanaon abinci wanda ko basu faɗaba sunsan nasu ne.
Dungura musu abincin tayi sannan tace
"shegu yan iska masu taurin kan tsiya,gaku mata har mata amman kunki ku mori rayuwarku."
Suhaima da sajida kallon juna sukayi sukayi alama da ido,ay miƙewa sukayi atare suka rufe matar da duka,basu kyaleta ba seda suka mata jina jina,sannan suka fice da gudu daga ɗakin,koda suka iso falo ba kowa,dan haka waje sukayi,da gudu.
koda megadi ya gansu be cemusu komaiba,danbesan,antsaresu ba,dan haka buɗe musu ƙofa yayi suka fice a 360.
gudu suke bilhakki da gaske,duk da basu san inda zasuba amman basu dena gudunba.
muje zuwa.
surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
*Maki gani ya kauda idonsa👇*
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*DEDICATED TO ZAHRA BUKAR*
*11-12*
Gudu sukeyi,basu tsayaba seda sukaje jikin wani dogon gini,sannan suka tsaya kalle kalle.
Can suka hango wata mata wacce da gani sunsan yar nigeria ce.
Da gudu suka nufeta,sunaso ta taimakesu tamaidasu gida.
"Ayya na tausaya muku,amman kuyi hakuri inkaiku kuyi ayki tukuna seku,samu kuɗin jirgin komawa gida".
Cike da faraa,suka amince suka bita.
Dayake matar ita a makkah take,dan haka mota suka hau,daga jiddah zuwa cikin garin makkah.
Koda suka isa gidan matar,sunsha mamaki,domin shima cike yake da yanmata,yara da manya,sannan ga kekunan guragu nan kala kala.
Abinci tabasu sukaci,sannan takira wata halima tace mata.
"anjima inzaku harami,kutafi da wainnan,kinga zaa kara samun kuɗin sadakar"
sude su suhaima basu san manufarta ba.
Suna zaune,halima tazo da bandeji,tasa su suka dora hannayensu a kafaɗarsu ta ɗaure guiwar hannun da bandejin,sannan takawo kalar jini ta shafa akasan.
bame cewa ba yanke musu hannun akayiba,sude se kallon abun mamaki suke.
Mamakinsu be ƙaruba seda aka kawo musu keken guragu akace,su hau.
ba musu suka haye,wasu suka turasu zuwa harami.
Suna cikin tafiya,duk wanda yagansu se yabasu sadaka,ayko suna zuwa daidai,wani hotel,me suna land premiar,suka haɗu da yankame.
Suhaima se gani tayi,sauran sun kwasa da gudu,dan haka itama,sauka tayi akan keken,ta ruga da gudu,itako sajida kamin ta gudu har sun kamata,ihu take tana tsillewa dan batasan inda zaa kaitaba.
Suhaima leƙowa tayi daga inda ta boye,taga ansaka sajida a mota,fitowa tayi da gudu dan itama akamata,amman ina kamin ta ƙaraso sunja motar suntafi.
tsugunawa tayi agurin tanata rusa kuka,daga karshe tamike ta cigaba da tafiya tana share hawaye.
Dayake lokacin aykin hajji ne garin na makkah cike yake da baki.
Suhaima cigaba tayi da tafiya,har ta iso wani guri dataga jamaa da yawa se shiga sukeyi,kyan gurin da tsarinshine yasa suhaima shaawar shiga ciki taga kome ake gani.
Tana zuwa zata shiga da takalminta,taji wani megadin ƙofar yana faɗin,"haram haram"nuni yaymata data cire takalmi ba musu tacire,ya miƙo mata wata farar leda,tasaka aciki,sannan ta rike a hannu ta shiga.
Dayake gangarane,haka suhaima ta dunga tafiya kanta akasa,kamar ance ta ɗago kanta.
ALLAHU AKBAR.
Arba tayi da ɗakin Allah yayiwa sama rumfa.mutsike idonta tashigayi nason tabbatarwa ba mafarki takeba.
ay tunda taga dagaske shine seta fashe da kuka,t juya tafice zuwa waje tasha wahala kamin tasamu bahaushiyar data nuna mata gurin alwala.
alwala tayi tadawo,gurin kaaba.
Dayake batasan ya akeyiba,ita gurin kaabar kawai tanufa,dan ko alwala tayine,sabida tanaso ya amshi rokonta da gaggawane.
da kyar tasamu ta isa jikin kaabar,tunda taji hannunta yataba ta,se kawai ta rushe da kuka tana faɗin.
"Allah na daɗe ina wahala arayuwata,ka kawomin agaji,ya Allah,nagaji,katausayamin haka,nima baiwar kace ya Allah"ta ƙarasa adduar tana kuka.
********
Suhaima seda ta kwashe tsawon sati guda acikin harami,tana maimaita wannan adduar,alwala da tsarki kawai ke fito da ita,abinci ko ana raba sabil na dabino da madara,su take ci.
Yau jummaa,rana ta buɗe sosai agarin na makkah,bayan an idar da sallar jummaa ne,suhaima tafito,wajen haramin sabida tanaso ta siyi riga da kuɗin sadakar da aka bata ranar da aka kama sajida.
Tana fitowa,taita tafiya,tarasa mezatace inta shiga shagon,dan ita batajin larabci.
Wasu gungun mata,ta hango,zaune,jikin ginin bindau,da sauri tanufesu,sallama taimusu,suko suka amsa amman azatonsu balarabiyace,dan haka se suka mata larabci.
ido taware atanta tace dama akwai baƙaƙen larabawa,tunda tagade fatarsu baƙace.
Dakyar tace musu ita bahaushiyace,don Allah tanason siyan rigane batasan mezatace.
Wata acikin matanne,ta juya tayiwa yar uwarta magana da larabci,seta juyo tacewa suhaima.
"amman ke bakuwace ko?"
kai suhaima ta ɗaga mata.
murmushi matar tayi sannan tace.
"karki damu ki bini ni kuma namiki alkawari insha Allahu,zan samar miki ayki,aguri me kyau,yadda zasu dunga biyanki duk wata,inkin amince kibini muje,amman ba anan garin nake zauneba,ni ina riyad ne"
Suhaima da sauri ta amince,ayko guri tasamu tazauna jiran matar,har tagama abinda zatayi,suka nufi tashar mota,suka hau,mota zuwa riyad.
muje zuwa.
Surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*KHALEESAT HYDAR FACEBOOK NOVELS GROUP,NAGODE DA SOYAYYARKU GARENI,ALLAH YATSAREKU CIKIN TSAREWARSA AMEEN,*
*ZAKU DUNGA YIN HAKURI DA ABINDA YA SAUWAKA,BA KODA YAUSHE ZAN DUNGA TYPING BA,NAGODE DA ADDUOINKU MASOYANA*.
*DEDICATED TO ZAHRA BUKAR*
*13-14*
Tafiyace me tsayi tsakanin makkah da riyad,dan haka sun jima kamin sukai.
Kamarde sauran,shima gidane me ɗauke da yawan mutane mazauna nigeria.
Tunda suhaima taje garin hankalinta akwance yake,sabida dankalin turawa kawai suke soyawa su fitar dashi,waje su siyar,hajiya murja sunan wacce takawo suhaima riyad,tana da kirki sosai kuma akwaita da tsoron Allah.
Sannu ahankali,suhaima har tasoma jin larabci,kamin wani lokaci taƙware dayin yaren,shiyasa take yawonta ko ina batare da ƴan kamen tikari sun kamata ba,sabida harshenta har ya karye,ko hausarta bata fita da kyau,sannan kamanninta babu mecewa ba balarabiya bace.
Watan suhaima biyar tare da hajiya murja,rannan da safe suna zaune sega,wata aminiyar,hajiya murja tashigo,me suna hajiya safiya.
fuskarta ɗauke da murna ta faɗo gidan,har tana tuntuɓe,amman bata damuba faɗi take.
"hajiya murja,fito,yai nasamo kabar me daɗi,fito fito"
da sauri hajiya murja ta tari aminiyar tata tana faɗin.
"akbirni kawata,meyafaru,kinsa nafara murna tun kamin naji"
guri suka samu suka zauna,sannan hajiya safiya tace.
"Dama gidan,sarki Abdulaziz Assa'udi ne,aka kama maaikatan gidan da laifin yunƙuri kashe ɗanshi,tahanyar bashi guba,to shine aka kori kowa,to yanzu sababbin maaikata suke ɗauka,kuma kinsan basa ɗaukar baƙar fata,shine nace ko zaki gwada kai suhaimanki ko zaa dace su ɗauketa,tunda aykine me kyau,"
"Gaskiya naji daɗin wannan labarin,sede,abu ɗaya,wlh banaso suhaima tayi nisa dani,sabida,tabani labarinta gaba ɗaya,tausayinta nakeji,ina gudun nakaita,makkah bayan nataho kuma sugano ba balarabiya bace,asamu matsala,"
Murmushi,safiya tayi sannan tace.
"inbanda abinki suhaima ay tasan hanya,insuka korota seta dawo,nan,nide namata shaawar aykin wlh,ki daure kawai mu kaita mu bita da addua"
Ayko da kyar hajiya murja ta amince.
Sati guda tsakani,suka shirya suhaima zuwa makkah,da kuka suhaima ta amince da aykin,dan itama batason yin nisa da hajiya murjan.
Koda suka isa masarutar,sun tadda mutane jibge ana musu screening,dan haka suhaima tahau layi,amatsayin me share share.
Koda akazo kanta ashe bata saniba se kana da takardar zama ɗan kasa,ido ta dunga warewa inda tace tamantoshi a gidansu dake riyad.
Kyan suhaima da kwarjinintane yasa mutumin yasa sunanta amatsayin me shara agidan batare da katin ba.
ganin sunanta yashigane yasa ta dawo gurin su hajiya murja sukayi sallama,sr kuka sukeyi,ahaka suka rabu,bayan hajiya murja taba suhaima ɗayar wayarta,sabida sudunga gaisawa.
Bayan angama tantancrwa ne aka shigar dasu suhaima cikin gidan,aka gabatar dasu ga alummar,gidan,daganan akaba kowa,ɓangarenshi,daze dunga kula dashi,cikin ikon Allah ɓangaren,babban ɗansarkin mesuna.
*SHUREIM ABDUL'AZEEZ AS-SA'UDI* ,ya faɗo acikin bangaren da suhaima zata dunga gyarawa,kuma dama duk inda,aykinka yake to anan ɗakinka yake,amatsayinka name kula da gurin.
Danhaka,ɓangaren aka kai suhaima,aka bata ɗakinta,mecike da kayan more rayuwa,kamar bame aykiba.
********
Hajiya duniyar sama sanda ta dawo tasamu labarin su suhaima sun gudu ba ƙaramin baƙinciki tayiba,ranta sosai ya ɓaci.
Hakanne yasa takira bokanta dake ƙasar indiya,tashaida mishi tanaso ya haukata suhaima da sajida,
alkawari yamata inda yashaida mata,yana da ayyuka sosai agabanshi,amman ta jira bayan wata shida ze kammala yashiga nata.
bata damuba,sabiɗa tasan boka guru maharaja da cika alƙawari
Anashi ɓangaren kuwa,boka guru maharaja,yaune waadin daya dibarwa,duniyar sama,dan haka tuni yashiga ɗakinshi na yin tsafin domin aywatar da nufinshi.
Wanda yay daidai da shigar suhaima masarautar makkah amatsayin hadima agidan.
Sajida kuwa bayan ankamata,sijin aka kaita,watanta biyu aciki,aka sakata,ajirgi,zuwa nigeria.
a kano aka sauketa,kuma bata da kuɗin mota hakanne yasa ta ɗauki drop din mota zuwa bauchi.
Sosai iyayenta sukayi murna da komawarta gida bayan sun cire ran sake ganinta,sukai taaantar hajiyar sama da tawagarta.
muje zuwa.
surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*dedicated to zahra bukar*
*15-16*
Yau da wuri suhaima ta tashi,ta ɗauki injin shara da mopping ta nufi ɗakin yarima.
Da sallamarta ta,shiga sede bakowa adakin.
Ba abunda yafiba suhaima mamaki,kamar ganin ɗakim kamar bame hankali aciki,sabida mugun dattin dayayi,wadrope a buɗe,kayan daya cire gasunan zube aƙasa wasu akan gado.
Tattara kayan wankin tafara yi takaisu cikin worshing marchine,tazuba ruwa da omo,sannan ta kunna,ta dawo taci gaba da aykin ɗakin.
Ranar suhaima tasha wuya sosai,dan kwalema tayiwa ɗakin,harda canjawa gado gurin zama,sannan tasa sabon bed shit,kayanshi ko data wanke shanyawa tayi suka bushe ta zauna ta gogesu tas,sannan,ta kwaso na cikin wardrope ɗin gaba ɗaya tasake sabon shiryawa.
kamin wani lokaci ɗakin yafito fess kamar bashiba.
Koda tashiga toilet nanma ta tarar dasi boxsize dinshi da singlet,jibge aciki baa wankeba,a kunyace suhaima ta kwashesu takai,worshing marchine suma tawanke ta goge masa,ta feshesu da turare ta shirya masa.
Koda ta koma ɗakinta wanka tayi ta gasa jikinta sannan tayi sallah,ta nufi kitchen dan samawa cikinta abinda zata ci.
Sabida gidan komai a adalce sukeyi,kowanne ɗan ayki a ɓangarenshi akwai,kitchen da store daze dunga girka abinda yakeso yaci ba takurawa.
Koda suhaima taje kitchen dambun coucous tayi wanda yasha naman kaza da kayan lambu.tuni,ɓangaren nasu ya buɗe da ƙamshi.
tana gamawa,ta juye a kula,sannan tazuba wanda zataci ta fice daga kitchen,tanufi ɗakinta,tazauna taci tasha ruwa,tabi lafiyar gado.
***********
Shi ko Shureim tunda ɗakinshi yayi datti yadena kwana agidan ya tattara abinda yake buƙata,yakoma kwana a hotel,dan baze iya kwanan ɗakinba.
Yau yana tasowa daga office har ya shiga lifter zuw Ɗakinshi,sekuma kawai yaji yanason zuwa gidansu,dan haka fasa hawa saman yayi yadanna ta dawo dashi ƙasa.
yana sauka yashiga motarsa zuwa gidansu.
A aladar gidan basa zaman falo,dan haka be tarar dakowaba,ɗakin mahaifiyarshi yanufa.
me suna hajiya fatima,a kishingiɗe yasameta,me mata tausa tana matsa mata ƙafarta.
Nufarta yayi da sauri yarungumeta ya sumbaceta,ita kuma ta shafa gashin kanshi tana samasa albarka.
kan kujera yaje yazauna,suna hira,duk da cewa shureim miskiline na bugaw A jarida,wanda magana ke matuƙar tsada agurinshi,amman baya yiwa mahaifansa.
"Shureim ina kashige kwana biyu bana ganinka?"inji mahaifiyarshi cikin harshen larabci.
"Ummi wlh ɗakina yayi masifar dattine,ni kaina kunyar ɗakin nakeyi,shine kawai yasa natare a hotel acan nake kwana,tunda ankori yan aykin gidan"shima ya bata amsa da lataɓcin.
Murmushi ummin tayi sannan tace.
"Kaide akwai shiririta,to ay ankawo wasu maaikatan jiya,kuma kaima antura me kula da ɓangarenka,nasan angyara komai yanzu,kaje kaduba inbeyi maka ba base a canja kayan ɓangaren gaba ɗayaba"
Taɓe baki yayi sannan yayiwa ummin tashi sallama yanufi ɓangaren nashi.
Tunda yake betaɓa jin ƙamshin dayakeji aɓangaren nashiba yanzu,kamshin turare ganida ƙamshin girki,tuni cikinshi ya juya,alamun yanajin yunwa.
Kasa jurewa yayi yanufi kitchen ɗin,ba kowa se cooler buɗewa yayi wani tiririn ƙamshine ya daki hancinshi,da sauri,ya ɗauki plate ya juye abincin aciki,ya ɗauka yanufi ɗakinshi.
Abinda yagani ba ƙaramin mamaki yabashiba,inbanda ƙamshi ba abinda ɗakin yake komai naciki yadawo sabo,wardrop ɗinshi yanufa acan yasha makurar mamaki,ganin komai a wanke a goge se ƙanshi sukeyi.
toilet ɗinshi yanufa acanma yasha kallo,besan sanda murmushi ya kubce afuskarsa ba,a fili ys bayyana.
"ko waye yayi wannan aykin ba balarabe bane,sabida su basu saba da wahalaba,,musamman nacikin birni bankiba kona kauyem zasu iya kwatantawa, nasan koma waye to tabbas namiji ne,dan mace bazata iyaba"
da wannan bayanan nashi yaje yazauna yafara cin abincin,ji yake kamar kunnenshi ze fita,dan daɗi sam babu tafarnuwa aciki,shidama yatsani tafarnuwarnan,dande kawai yazamar musu tamkar aladarsu ce cinshi.
Shureim duk yawan abincin seda yakwasheshi tas yasha ruwa,yamiƙe ze fice ji yayi ya gaji dan hska lafiyar gadonshi daya gaji da haɗuwa yabi,yayi kwanciyarshi tuni bacci yayi awon gaba dashi.
*********
Tunda daga wannan lokacin,kullum suhaima seta girka abinci me rai da lafiya ta haɗa harda shureim sabida ta fahimci inta rage s kitchen yana zuwa ya cinye,dan kullum taje gyara ɗakinshi seta fito da plate.
tsawon wata guda kenan,tana ɗawainiya dashi,tuni yamurje,har wata kiba yayi,ga ɗakinshi kullum cikin gyara,gashi be taɓa ganin me aykin nashiba,kuma bedamu dason ganin me aykinba dan azatonshi namiji ne.
Yau tunda suhaima ta tashi kanta ke ciwo,dakyar ta cire kayanta,ta ɗaura towel tashiga wanka,adaddafe tagama wankan ta ɗauro towel ta fito,tana fitowa tayanke jiki ta faɗi aƙasa.
Tsawon kwanaki biyu kenan shureim,bega angyara mishi ɗakiba,kuma baa dafs mishi abincinba,wanda yasan da baa fashi.
hakanne yasa yashiga damuwa,nason sanin halin dame aykin nashi yake ciki.
Suhaima ko tunda ta faɗi bata tashiba seda ta kwans biyu ahaka,cikin dare ta tashi a haukace,tuni tayi fatali da towel ɗin dake ɗaure jikinta,se buga kanta take a bango tana zage zage.
Shureim cikin bacci yaji ana buge buge,a firgice ya tashi,silifas yasaka yafito,falo ananne yafahimci aɗakin me kula dashine abun yake faruwa.
Da gudu ya nufi ɗakin,yatura yashiga,ganinta tsirarane,yasa yayi saurin dakatawa gamida runtse idon shi yana fadin.
"Auzubillahiminashshaidanirrajeem"
itako suhaima se buga jikinta take da bango,har ta jiwa kanta ciwo,ganin zata illata kantane,yasa shureim daurewa ya ƙarasa inda take ya riƙeta,nanfa dambe ya kaure,ita ala dole seta kwace,inda shi kuma ya gwada mata ƙarfe,ta hanyar rungumeta gabaɗaya ajikinshi.
Se gurnani takeyi kamar tsohon zaki,ɗaukarta yayi gaba ɗayanta,yanufi ɗakinshi,da ita se son kwacewa takeyi,amman ya hanata.
koda yakaita ɗakin,ɗaureta yayi da ƙafar gado sannan yakoma ɗakinta,ya ɗauko doguwar riga da dogon wando,har ze fita ya hangi wayarta jone ajikin charge,cirota yayi yaga tana da missed call har guda goma.
Da sauri ya koma ɗakinshi,likacin saura kaɗan ta kwance daga daurin daya mata,da sauri yaƙarasa inda take,sunci uban dambe kamin yasamu yasaka mata kayan,
yana gama sakamata,yafara rera karatun qurani,cikin zazzakar muryarshi akunnenta,sannu a hankali tafara gurnani,da buge bugen,zuwa can kuma seta zube jikinshi sharab alamun tayi bacci.
kan gadonshi ya ɗorata,ya gyaramata kwanciya,sannan yanufi ɓangaren mahaifinshi,domin sanar dashi abinda ke faruwa.
muje zuwa.
surbajo for life.
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*KANO TO JIDDAH*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Dedicated to zahra Bukar*
*17-18*
Yana zuwa ya samu mahifin nashi zaune yana cin tuffah,
Bayan ya gaisheshine yashaidamishi abinda ke faruwa.
Akiɗime sarki yake tambayarshi.
"taya haka tafaru,yanzu yarinyar tana ina?"
"Tana ɗakina tasamu bacci"
"muje in ganta"cewar sarki yana miƙewa.
Ɓangaren Shureim ɗin suka dawo tare,koda yaga suhaima sosai yatausaya mata,kallonshi yamayar gun shureim yace.
"bata da wayane,ay yana da kyau asanar da yan uwanta halin da take ciki"
Da sauri shureim yaje yaɗauko wayar suhaima yakawo masa.
Number hajiya murja suka kira bugu ɗaya ta ɗauka dan dama gaba ɗaya a firgice take na rashin jin suhaima kwana biyu
jin muryar namijine yasa hajiya gigicewa tana tambayar waye cikin harshen larabci
"Shureim sunana,dama anason ganinki da gaggawa a inda me wannan number take ayki,sabida kwana biyu kenan bata da lafiya"
salati hajiya take tana ƙarawa bakinta har rawa yake gurin bada amsar gatanan zuwa.
kamin hajiya tazo,sarki sawa yayi aka maida suhaima wani ɓangare na musamman aka kunna mata karatun qurani
cikin dare hajiya ta iso batare da tsoron komaiba sabida tana da igama.
Gurin kwana aka bata kamin gari ya waye.
hajiya ta kasa bacci burinta kawai tasan halin da suhaima take ciki.
Washe gari seda rana tafito sannan Sarki ya buƙaci agabato masa da hajiya murja.
Rusunawa tayi tagaisheshi,sannan tanemi guri ta takure.
"baiwar Allah meye haɗinki da yarinyar nan,gaskiya nakeso kisanar dani"
Hajiya murja batare da tsoron komaiba ta faɗamishi duk abinda tasani gameda suhaima,harda labarin suhaima nacan nigeria da suhaiman ta bata.
Sarki seda yashare kwallah na tausayin suhaima,daga haka sawa yayi aka nemo manyan malamai,suka shiga saukewa suhaima qurani me girma.
tsawon sati guda aka kwashe ana mata karatu,cikin ikon Allah aljanun suka fara magana,malaman basuyi kasa a guiwaba,gurin ci gaba da karatun,har suka samu aljanun suka fita.
kowa se hamdala yakeyi nasamun nasarar samun lafiyarta,
Sede tunda tasamu sauƙi kuma se bata magana sede nuni take da hannu.
Shureim inyasata agaba yana kallo har beso yadena,tunda yaji labarinta yaji takwant mishi arai,d mahaifinshi ze amince da ba abinda ze hana be nemi auranta ba,dan harga Allah suhaima tana cikin jerin irin matan dayakeso ya aura,wato mata wainda suke da rangwamen gata,domin yatallafi rayuwarsu.
Hajiya murjace tacigaba da kulawa da suhaima agidan sarki batare da tsangwama ko takurawaba.
tsawon watanni biyu takwashe tana kulawa da ita,sumul tawarke maganace kawaide har yanzu batayi amman babu inda yake mata ciwo.
Ganin hakane yasa