Showing 1 words to 3000 words out of 20241 words
Chapter 1 - GAWA TAFE Book Complete Hausa Novels Writing by Mrs Sufi.txt
*GAWA TAFE*
(Zombies story)
On2025
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
*EPISODE 1*
*General hospital Katsina State Nigeria*
"Innallihi wa'inna alaihir raju'on, Farida waye ya take ki da mota har hannunki ya k'arya haka?"
Kuka Farida kawai keyi mai cike da tsananin rad'ad'in zuci da azabar da hannunta ke mata.
Kwance take akan gadon marassa lafiya, irin na asibitin. Hannunta ta kalla ganin yadda ya kunbura har yayi fushi da waya, wani miyau mai zafi ta had'e a mak'oshinta tana kallon abokiyar zaman Mahaifiyarta wacce duk ita ce silar shigarta cikin wannan wahalar, domin da baccin bata d'ora mata tallar da bata so ba, da duk hakan bata faru ba.
"Inna Zubaida wani ne a mota ya bige ni, kuma bai tsaya ba, yayi tafiyarsa, sai wasu Mutane k'alilan ne suka kawo ni asibitin nan"
"Dalla can rufe min baki, ai ni wallahi ni ce kika jama asara, yanzu ubanwa zaije wajan aikin ki? Kin kuma san inda kike aikin nan bafa mutumci ne dasu ba, kuma na rantse bazaki ja min salalan tsiya ba, domin idan aka kore ki daga gidan Alhaji Sammani B Radda Mai Naira ai na shiga uku na, dan haka yanzun nan kima tashi ki kama hanya mu wuce, dama tallar baifi ta wuni d'aya kike zuwa min ba, shine yanzu kinje kin shige ma titi kinja masu hannu da shuni sun bige ki kin barni da aiki".
Wata doctor ce da tun maganar Inna Zubaida ta farko take kallonta cike da mamaki, ta kasa hakuri ta kalleta ta ce.
"Baiwar Allah amma da alama bake ce kika haifi wannan yarinyar ba ko?. Domin da ki ce kika haifeta bazaki fara mata zancen rashin zuwanta wajan aiki da zatai na y'an kwanaki ba. Ke burinki kawai ta kawo miki kud'i kawai, baki gudun ma ace yau anje wani ya lalata mata rayuwa gaba d'aya?, miye zan.......
"Ke Kinga baiwar Allah, babu ruwanki a cikin sha'ninmu, ina ruwanki? Ke ke rik'eta ko ni? Ko kuwa ke ke d'aukar cinta ko shanta?. Kinga Malama ki sallame mu ma mu wuce gida".
Inna Zubaida ta k'are maganar tana hararar likitar kamar idonta zasu fad'u.
Girgiza kanta kawai likitar tayi tana sake duban Inna Zubaida ta ce.
"A sallame ku ai bai taso ba, saita samu sauk'i tukunna".
Rai a b'ace cike da da harguwa Inna Zubaida ta fara cewa.
"Ai ko kun samu mai biya mata magani, domin na rantse da Allah ko sisina bazatai ciwon kai ba, yawwa, gara ma ku sallame mu wuce a'ato, idan ma baku bamu sallama ba, yanzun nan zamu wuce sai naga ubanda ya isa ya hanamu tafiyar".
Likitar zata sake magana aka bud'e k'ofar d'akin aka shigo.
Shuru tayi tana kallon wacce ta shigo d'in.
"Doctor Halisa mike faruwa ne"
Kallonta Halisa tayi tana cewa.
"Uhuhmm wannan matar ce marar imani mana, Doctor Anam an kawo wannan yarinyar da k'araya a hannunta wani shima marar imanin ya bigeta, ko tsayawa baiyi ba yayi tafiyarsa ya barta, shine wasu bayin Allah suka kawota asibitin nan, mun samu da kyar an gyara k'aryar hannun nata, shine ta bada number wannan matar an kira ta mai maikon ta zo ta nuna tashin hankalinta, sai ma ta fara cewa zata jaza mata asara mine-mine, da dukkanin alamu ba ita ce ta haife ta ba in......
"Kinga Malama dan Allah babu ruwanki a ciki, miye na wani tsayawa ki gaya mata abunda ya shafi rayuwarmu ne, kawai ku bamu sallama mu wuce inda dare yayi mana, ni wallahi bana son shiga sharra ba shanu".
Inna Zubaida ta k'are maganar tana banga masu harara gaba d'aya.
Wani duba sosai Doctor Anam tayi ma Inna Zubaida kamin ta matsa kusa da Farida dake hawaye har lokacin tana kallon abunda Inna Zubaida keyi.
Ta ce "ki daina kuka kinji?, zaki iya gane motar data bige ki, ko number motar?".
Da shashshekar kuka Farida ta ce.
"Na dai rik'e sunan da na gani a jikin Motar".
"Yawwa fad'a min miye kika gani?".
"Naga ansa *Al'ameen Galadima B Radda* a jikin Mo.....
Saurin yin shuru tayi jin yadda Doctor Halisa tayi saurin fad'ar sunan data kira.
"Tabd'i jam ubanwaye bai san Y'an gidan B Radda ba, dan ubanki ubanwa ya kaiki sallaka titi kinga irin motocin Y'ay'an Gwamnan Jihar nan zasu wuce, baccin baki da halkali ai gidan da kike aiki ma gidan K'aninsa shashasha ke dan......
"Haba baiwar Allah ki bita a hankali mana?".
"Ke Kinga baiwar Allah babu abunda ya shafeki Dani, kuma da kike mata tabbayar ta rik'e number mota ko sunan dake jikin number Motar, mi kika isa kiyi ma wadda ya turmusheta a titin?, kina dai ji babu ubanda bai san Y'an gidan B Radda ba, sune fa da Nigeriar gaba d'aya, Y'ay'an k'usoshin k'asar nan ne fa, ita fa ba y'ar kowa ba ce face y'ar gidan Malam Dauda Mai Faci, dan haka karki sake ki wani sa mata rai da d'aukar mata mataki akan abunda ya faru da ita. Ke kinga Farida maza tashi mu wuce gida, mun gode da irin taimakon da kukai mata".
Ta idasa maganar ta kamo hannun Farida mai lafiya ta jata keee suka fice daga asibitin gaba d'aya.
"Kashhh wallahi Allah wasu basu da tunani da hankali, ai ta bari taji miye zaki ce ne ko, bata san kema y'ar gidan wuce ba".
"Uhuhmm".
Doctor Anam ta ce kawai tana cire rigar doctors dake a saman kayan data sa.
Tana duban Doctor Halisa ta d'an dafe kanta.
Kamin a hankali ta ce
"Na rasa miye yasa Y'ay'an Daddy B Radda suke haka, kodan sunga ubansu shine akan muk'amin Gwanan Jahar nan why zasu rink'a taka duk wadda suka ga dama ne?".
Dafa ta Halisa tayi tana sauk'e numfashi ta ce.
"Banga laifinsu ba, amma abunda suke yayi yawa gaskiya, kiyi hakuri akan abunda zan fad'a dan na sani da ciwo tunda Y'ay'an K'anin Mahaifinki ne, amma su guje ranar da zasuyi muguwar nadamar da bata da anfani wallahi. Kinga kamar ke babu wadda ma zai kalle ki a yanzu ya ce ke y'ar wani ce a K'asar nan, baki d'auki kanki komai ba, aikin dake gabanki shine kawai kike, shi yasa wallahi kike sake birgeni idan ma kin fad'a ba babu wadda zai ce ke y'ar gidan B Radda ce".
Shuru kawai Doctor Anam tayi domin ranta sosai ya b'ace akan abunda yake faruwa a cikin family nasu.
_____________________
"Why Dad mi yasa su Faruk B Radda da su Al'ameen G B Radda zasu rink'a d'aukar kansu da nesa haka ne?, wata fa yarinya ya bige da mota amma ya wuce kamar wadda ya bige Dabba ba D'an Adama ba, rayuwa zata tafi a haka ne?".
Dad dake zaune akan Darning table su duka Y'an gidan ne, Anam Sai K'anwarta mai bi mata, sai Mom ita dake zaune daga gefen Dad.
Ya d'an zare gilashin idonsa yana duban yarinyar ta shi zaiyi magana Mom ta rigasa.
"Anam shin wai ina runki da rayuwar su ne?. Suyi yadda suke so lokaci ne, ni banga wani aibun abunda suke yi ba, matsayi ne Allah ya basu d'aukaka ce Allah ya basu, girma ne Allah ya basu kud'i ne Allah ya basu, sana haka zalika kema dukkanin abunda ya basu kema Allah ya bawa naki Mahaifin, kema kiyi yadda kike so mana, amma sai wani tauye kanki kike kin hana kanki shak'atawa, kin hana mutane su san wacece ke, kin wani je asibitin talakawa asibitin Gwamnati kina aiki kamar ke haba, wallahi idan na tuna wannan abun karki ji yadda nake jin haushinki sosai, shi yasa ta wani wajan K'anwarki Hanan tafi ki sanin mi cece rayuwa da matsayinta".
Tab'e baki kad'an Hanan tayi tana cewa.
"Mom ai ni banzan iya zubar da class d'ina kamar yadda Aunty Anam ke yi ba wallahi, ina banga d'an talakan da zai raina ni na kyale shi ba wallahi"
"Ke da'aAllah rufe ma mutane baki a nan wajan, ansa dake ne marar kunya? Duk ba halinku d'aya da su Ameen d'in ba, duk ba dake suke zuwa yawan banza aje waccar k'asar aje wannan k'asar kullum kune y'an yawo K'asashe k'ashe, kuma wallahi Allah kin kusa daina fita kwata-kwata ma kuwa".
Cewar Anam rai ba b'ace tana kallon Hanan dake turo baki gaba.
Mom ta dafa Hanan ta ce.
"Rabu da ita kinji Autata babu wadda zai hanaki shakawata wallahi, kema ai ba hanaki akai ba, kece kika tauye kanki, dan haka bazai yuwu kuma ki ce zaki tauye wani ba".
Dad dake kallon kowa a cikinsu yayi shuru, Anam ganin Dad shurun nasa yayi yawa yasa ta kwab'e baki tana cewa.
"Uhum uhum haba Dad ka ce wani abu mana, kayi shuru".
Murmushi ya d'an saki kad'an kamin ya ci gaba da cin abincinshi hankalinsa kwance ya ce.
"Ni duk banga abunda tada hankali ba Anam, kiyi rayuwarki yadda kike so, suma ki barsu suyi yadda suke so, kinga dai ni K'anin Babansu ne, banda ikon ce ma ubansu gashi-gashi, kuma kinfa san bana son shiga harkar wasu, so please kima daina d'akko irin wannan damuwar kina gaya min please".
"Yawwa Dad shi yasa nake sonka wallahi, baka da takura ko kad'an, amma Aunty Anam kin cika shiga abunda babu ruwanki a.....kwaffffff
Anam ta bige bakin Hanan dake maganar.
Tab'e baki Hanan tayi da sauri ta saki wani kukan sangarta, domin ba wata bigewa ba ce Anam d'in tayi mata, amma shine harta wage baki tana sakin kuka.
Tashi Mom tayi tana kallon Anam ta ce.
"Kinga Anam daga yau gaskiya karki sake d'akko damuwar wasu ki kawo ta cikin gidan nan, kije can ke ta shafa, tunda ke ce kika je can cikin talakawa kika d'akko ta, karki sake bigar min yarinya akan wasu talakawa can".
Juyawa Hanan tayi zata bar wajan Darning d'in kawai suka ci k'aro da Farida mai aiki.
Tassss
K'arar mari ya k'arad'e wajan.
Da mugun sauri Farida ta dafe k'uncinta tana rik'e hannunta wadda ya samu karaya tana jin wani zugi da rad'ad'i domin bata lura bane ta sawo kai wajan, suka yi karo da Hanan, hasalima Hanan d'in ce ta bangaje ta har tana bangaje mata hannun data kare dashi, amma shine kawai ta d'auke ta da mari.
"Ke wacce irin dak'ik'aya ce ne? Ku wai rayuwarku komai zakuyi sai kunyi na rashin hankali da gidadanci ne?, idan kikai wasa zakiyi ta bakin aikin ki wallahi shashashar banza kawai".
"Dan girman Allah Ranki ya dad'e kiyi hakuri, wallahi banga kin sawo kai bane, ai da bama zan biyo ta inda kike ba".
"Dalla can ni rufe min baki".
Hanan ta k'are maganar tana sakin wani dogon tsaki ta wuce ta tana jefa mata kallo irin na k'as-k'anci.
Anam zatai magana Mom tayi mata wani kallo wadda yasa dole ta shanye abunda take son fad'a d'in.
Dad kuwa tashi yayi ko a kwalar rigarsa ya haye sama, domin shi baiga wani aibun abunda Hanan d'in tayi ba, danya saba ganin hakan a wajanta ko Mom, Anam ce kawai baya ganin tana ma masu Aiki tsawa kota kyare su.
Farida ta d'ago, sai fuskarta ta cika da mamaki ganin Doctor Anam, tunda ta fara aiki tsawon sati biyu a gidan, basu tab'a had'uwa ba, sai a asibiti sai kuma yanzu data san cewa y'ar gidan ce.
"Keeee dalla can ubanmi kike kuma a tsaye har yanzu? Da ba zaki fara aikin daya kawo ba?".
Cewar Mom data mik'e tsaye itama.
"Kiyi hakuri uwar d'akina"
"Da anyi magana kiyi hakuri, rik'e hakurinki Malama. Sana miya hanaki zuwa da wuri yau?, kina so ki rasa aiki ne?".
Da sauri Farida ta fara girgiza kanta bakinta na kyarma ta ce.
"Dan Allah Haj kiyi hakuri, wallahi ina kan hanya ta ta zuwa gidan nan Mota ta kad'e ni, shine yasa banzo da wurin ba, kin gani Haj har karyewa nayi amma a ha......
Saurin yin shuru tayi ganin Mom ta d'aga mata hannu tana cewa.
"Kinga Malama dakata please, wannan keta shafa, bana son yawan surutu kin sani, ki fara aikin dake gabanki kawai".
Ta k'are fad'ar haka ta bar wajan itama, aka bar wajan daga Anam Sai Farida tsaye.
Sauke ajiyar zuciya Farida tayi wasu hawayen tausayin kanta da duk wadda yake cikin hali irin nata, na aiki k'ark'ashin wa'inda basu san darajar D'an Adam ba, dole yasha wahala irin haka.
Jin an rik'o hannunta yasa ta d'an firgita, sai kuma ta ja wani dogon lumfashi tana kallon Doctor Anam data rik'o hannun nata.
"A madadinsu ina mai baki hakuri kinji?, yanzu a hakan kika taho aiki?".
"Uhuhmm Haj kenan ai babu komai rayuwa ce fa, karki damu idan ma banzo ba wahalar da zan sha a gida ai sai ya fiye min alkhairi gara na zo nan d'in kawai. Ashe Ranki Ya dad'e ama gidanku nake aikin rashin sani?".
"Uhuhmm ai tun lokacin da kika fad'i sunan Dad nasan gidanmu kike aiki, ban dai nuna bane kawai".
"Lallai Ranki ya dad'e wallahi halinki ya banbanta da saurin Y'an Family naku, ke kam kinji dad'i abunki, Allah yasa ki d'ore da halin nan naki".
A cikin zuci kawai Anam ta amsa da amin.
Da sauri Farida ta d'an zabura ta ce.
"Ranki ya dad'e bari na fara aikin nan, na barki lafiya".
Ta k'are maganar tana tattare darning table d'in duk da hannunta d'aya bata iya aiki dashi, haka take cije baki da kyar take k'arfafa ma kanta gwaiwa take aikin, domin idan ma bata yi ba tasan abunda zai iya faruwa da ita, to gara taji wannan azabar da hannunta ke mata zai daina ne na d'an lokaci ne.
_____________________
*Government House Katsina State Nigeria*
"Asabee!! Asabee!!"
Da mugun sauri har Asabe na tuntub'e ta k'araso wajan tana zubewa k'asa akan gwaiwowinta.
Bakinta na kyarma wajan cewa.
"Ranki ya dad'e ga ni".
"Ke wai wacce irin jahila ne? Sau nawa zance miki a rink'a goge kujerun nan sau biyar idan aka tashi? Dubi d'akin nanma wani k'arni nake ji, hatta toilet d'in nan bai min yadda nake so ba".
"Dan Allah kiyi hakuri Ranki ya dad'e za'a sake aikin yadda kike so kiyi hakuri".
"Mtswww, wallahi daga yau idan na sake fitowa na iske ba dai-dai ba to ki kuka da kanki".
"Baza'a sake ba Ranki ya dad'e da yardar Mai Sama".
Wani Tsakin Amal tayi tana zama kan gadonta wadda ya gaji da had'uwa iya had'uwa.
Danna wayar take saiga Sa'ade wata mai aikin ta shigo da rawar jiki, a k'asa ta duk'a ta fara cire mata takalmi ta kama k'afar tata ta saka cikin wani ruwa da yaji kayan k'amshi da turaruka, tana wanke mata k'afar, had'e da yanke mata farce, tana yi tana taka tsantsan sai ka ce tana wanke kwai.
D'an rantse ido da sauri Amal tayi jin kamar dan zafi a k'afar tata, d'agowa tayi tana cewa.
"Keee Kee Kee Sa'ade baki gani ne ke?, ke makauniya ce ne?, ki rink'a yin abu da hankali mana, na kusa asa a sake min ke tunda naga kullum so kike kiji min ciwo haka kawai a banza".
Jiki na rawa Sa'ade ta ce.
"Haba uwar d'aki na, kimin rai dan Allah kiyi hakuri za'a gyara wallahi".
"Mtswww na dai gaya miki".
"Wallahi naji ranki ya dad'e za'a kiyaye"
Sake mik'a k'afar tayi Sa'ade ta ci gaba da yi mata yadda take so. Sun shafe kusan awa d'aya ana wanke k'afa kad'ai, ita ko sai faman danna waya take tana cin biskit mai d'auke da wata irin Zuma a ciki da Madara had'e da wani lemo da aka aje gefe guda.
Ta d'auki kusan awa uku kafin ta gama shiryawa gaba d'aya ta sakko k'asa.
Kallon su Faruk tayi tana d'an tab'e baki ganin yadda suka ci ka Darning table d'in da surutun su.
K'arasowa tayi tana taku d'ai-d'aiya, kamar wacce ke tsoron taka k'asa.
Kallon K'anwar tasu su Ameen suka yi har suna had'a baki wajan cewa.
"Wow My K'anwa dole ne ki rink'a cizon gayu fa, shi yasa muke ji dake a family namu ke da Hanan Allah kun san miye kuke yi fa,
Banda waccar Anam d'in ita kwata-kwata bata waye ba wallahi".
"Uhuhmm"
Kawai Amal ta ce ta ja kujera ta zauna tana aje y'ar k'aramar jakar hannunta had'e da key d'in mota dake hannun tana kallon su ta ce.
"Shi yasa ai bama jituwa da ita, sai ka ce Y'ar daji kwata-kwata bata da class Aunty Anam, wallahi tana bada mu, ni k'ara jin haushi na ma, ta rasa inda zatai aiki wai sai asibitin marassa gata".
Al'ameen ya d'an tab'e baki yana cewa.
"Ai ita hakan da take ba wani abu bane take gani a tunaninta wai hakan shine wayewa, so take muma mu koma irinta fa".
Da sauri Amal ta ce "ai ina itama tasan bazai yuwu ba, babu yadda za'ai na iya zama irinta, domin ni bana son raini ko kad'an a cikin rayuwata, bazan iya bari wani d'an talaka ya zo dai-dai dani ba wallahi"
Faruk ne ya d'an sauk'e lumfashi kad'an kamin ya d'an d'age k'afad'arshi kad'an ya ce.
"Ku manta da zancanta please. Wai ya maganar tafiyarmu Gowa ne? Yaushe kuke ganin zamu yi tafiyar nan ne?".
"Wow Y Faruk kasan harna sha'afa da tafiyar nan ma?. Kan uba zamu fa rak'ashe a Gowa d'in nan fa, ina son yanayin K'asar, shi nida Jasmin da Hanan zamuyi tafiyar nan, sai kum....
Al'ameen ne ya katse Amal da cewa.
"Sai kuma wannan ana can Saurayin nan naki nasan zaki ce".
"Ke ma fa Amal ta wani wajan kina kwafsa mana fa, kina biye wadda bai kai Mahaifinki kud'i ba, waye ubansa a k'asar nan, kamata yayi ki samo D'and'anan wani K'usa a k'asar nan, amma sai kika b'ige ga Wannan gyu d'in Faisal".
Cewar Faruk.
"Uhuhmm Y Faruk bazaka gane ba, Faisal yayi ne, wai baku ganin tsananin kyansa ne da gayunsa, yayi kota ina yana da class shi yasa nake sonshi, kuma ai shima ubansa yana da kud'i kawai dai bai kai kud'in nawa uban bane, shine kawai kuke ganin ya kwafsa".
"Hmmm shikenan dai nima da tawa budurwar zanje yawon shak'atawar nan dole ne na kira Hana da ita za'a wannan tafiyar".
Fad'in Al'ameen.
Ai ko Faruk najin haka yayi saurin cewa.
"Ohhh D'anwaken zagaye za'a min kenan?, ai ko nima dole ne zamu tafi da tawa Babyn Jonal".
Tab'e baki Amal tayi tana kallon Faruk ta ce.
"Ka rasa wacce zaka rink'a ma'ala da ita sai Kristan?".
"Uhum Amal kenan sunfi dad'in sha'ani ai".
Shuru sukai jin Momma ta sakko wajan, masu aiki ne suka masu suka fara zuba ma kowa abinci suka fara ci, suna wasa da dariya da Momma saika rantse cewa ba ita ce ta haife su ba, domin kwata-kwata jikinta bai nuna hakan ba.............
*GAWA TAFE*
(Zombies story)