Showing 6001 words to 9000 words out of 20241 words
Chapter 3 - GAWA TAFE Book Complete Hausa Novels Writing by Mrs Sufi.txt
ko ko kina mutuwa kina farfad'owa billahir azim Farida sai kin bisu ko da bangon duniya ne kuwa, shi uban naki da bai da aikinyi sai Faci ba gashi can a bakin titi ba, kullum ba abunda ya iya sai maula, ni ce dai rufin asirinku gaba d'ayanku, to wallahir azim baki isa ba, garama tun wuri ki fara shirin tafia, ke baccin ma baki da tunani da hankali za'aje dake k'asar waje kina wani k'i, tsabar dama ke ta daji ce, ba abunda kika sani sai k'auyenci, yo ina laifin wadda ya ce zai kaika inda baka tab'a zuwa ba ko a mafarki, baki tab'a tsammanin zaki fita wata k'asar waje ba, ke ko Niger wannan dai ta kusa damu, ubanki baida arzik'in kai ki, bare ance k'asar turawa zakuje".
Inna Zubaida ta dad'e tana zagin Farida kamar zata rufeta da duka.
K'arshe dole Farida ta yarda da tafiyar, tana kuka ta koma gidan aikin nata, tana tunanin da Mahaifiyarta na raye wallahi tasan ko za'ayi mi, bazata tab'a bari taje ma aikatau d'in ba, bare harta had'u da wa'inda basu san darajar mutum ba, bare kuma ace za'ayi wata tafiya da ita.
"Keee wai wacce irin sakarai ce ne, komai sai ance kiyi ne? Ko kuwa komai sai an nuna miki yadda zakiyi? Tsabar k'auyenci irin naki?".
Fad'in Hanan tana banka mata harara.
"Kayi hakuri Ranki ya dad'e banji miye kike cewa ba?".
"Ya za'ai kiji mi nake cewa, tunda kin lula duniyar k'auyenci, sai wani bin mutanan wajan nan kike da ido".
K'asa tayi da kanta, ita harga Allah tana dai kallon jama'a ne amma wani abu can take tunani a ranta, ba wai kallon mutanan wajan ba.
"Sai ki mai da hankalinki sosai za'a fara kiran sunaye, idan kinji naki Zaki iya biyo bayanmu, bana son yawan magana na gaya miki".
"Insha Allah Ranki ya dad'e za'a kiyaye".
Tsaki kawai Hanan taja tana k'ara gyara y'ar jakar dake hannunta irin ta gayu, sai wayar da take shirin sakata a ciki.
Amal ta kalli Hanan ta ce.
"Ashe kema haka kike fama da irin gidadawan mutanan?".
Ta k'are maganar tana kallon Farida da kanta ke a k'asa tana jinta.
" Wallahi fa kin dai gani, ai ni uban mutum nake ci wallahi a zauna lafiya, domin ni bana d'aukar shashanci".
"Hhhhh haba k'awata, nima sai ka ce baki san wace ni ba, ni ai inaga na fiki rashin d'aurkar raini wallahi".
Dariya zaku saki a tare suna kai dubansu wajan su Faruk da wanne cikinsu yake nanik'e da budurwarsa, sai ka rantse ka ce wasu ma'aurata ne.
Suna cikin haka aka fara kiran sunayen fasinjojin jirgin, wadda zai d'aga k'arfe sha biyu dai-dai.
Gaba d'aya kusan sune suka fara shiga jirgin kwansu da kwarkwatarsu Y'ay'an manyan k'asar ne, abun kamar had'in baki ma, babu wani d'an tagajan-tagajan a cikin jirgin.
_____________________
*ANAM POV*
A hankali Doctor Halisa ta dafa kafad'ar Anam cike da mamakin yadda ta dad'e tana mata magana amma shuru ba amsa, shine yasa ta d'an dafa kafad'arta.
D'an firgita tayi tana dawowa yaccinta.
"Lafiya kike kuwa Anam?"
"Uhuhmm da sauk'i dai Halisa"
Zama Halisa tayi tana duban Anam d'in cike da mamaki tana aje wasu takardu dake rik'e a hannunta ta ce.
"Mi yake faruwa ne?".
Sauke ajiyar zuciya Anam tayi tana zare wani abun Doctor's dake rataye a wuyanta kamin ta ce.
"Akan Family namu ne kawai, wai wata tafiya suka shirya kawai don suje yawan shak'atawa, wai yau da safe har Dad yake ma Hanan kyautar Million biyar, why Fisbilillahi kamar Hanan y'ar haka da ita za'a rink'a mata kyauta Million biyar?".
Zaro ido waje Halisa tayi tana had'e wani miyau a zuci take cewa "wayyo Allah dama nice a matsayin ku".
A fili kuma ta d'an maze tana cewa.
"Tabd'i jam gaskiya anaji da Hanan d'in nan taku, to ai ni Doctor Anam banga abunda shiga damuwa ba a nan".
Wani kallo Anam tama Halisa tana cewa.
"Amma wallahi ban tab'a tunanin jin haka daga gare ki ba, da nasan abunda zaki ce kenan da bazanyi gaggancin sanar dake damuwa ta ba, haba baki da K'anwa ne a gidanku Halisa?, kamar Hanan ana bata irin wannan mak'udan kud'ad'en, ya za'ai bazata lalace ba, gata tana mace, dama ace namiji ne wannan komi yayi ido ne, ita fa?".
Bata san hawaye take ba sai da taji saukar hannun Doctor Halisa akan fuskarta tana d'auke mata su.
Jiki a sanyaye Halisa ta rik'e mata hannu ta ce.
"Ko kad'an ba abunda kike zargi bane, ni a nawa tunani kawai ki bita da addu'a shine ya kamata, dama a gida ana samun zakka a ciki, ki rink'a sata a cikin addu'o'inki insha Allah komai zai wuce, zaki ga kamar batayi ba insha Allah".
Sauk'e lumfashi Anam ta rink'a yi saboda hawayen dake mata zuba sai ma wani k'ara gudu da suka rink'a yi.
Rungumeta kawai Doctor Halisa tayi tana d'an bubbuga bayanta.
_______________________
*HARUN POV*
Gaba d'aya d'akin taron ne aka d'auki tafi, jin an kira sunan Harun.
A hankali cike da natsuwarsa ya tashi yana nufar inda shugabansu na Sojoji ke tsaye cike da izzarshi yake tafiya mai jan hankali da class.
Kai tsaye inda shuban nasu yake ya tsaya yana Sara mashi.
Wata number yabo shugaban ya d'akko ya ratayama Captain Harun, yana saka masa aka sake d'aukar wani tafin mai k'arfi sauran Sojoji dake tsaye kuma suka Sara masu.
Number yabo aka basa mai girma tare da k'arin matsayi mai girma a cikin Sojojin.
"Mtswww"
Kallon na kusa dashi Captain Joha yayi wadda sarai yaji tsakin da ya saki a lokacin da shugaban Sojojin ke k'ara gode ma Harun tare da jinjina akan namijin k'ok'arin da yake yi ta fannin yak'i.
Joha ya kasa hakuri ya kalli Abbakar ya ce.
"Abbakar ya da tsaki kuma?".
"Mtswww nifa na tsani bawan Allahn can wallahi, ace komai sai shine zai zo na d'aya, komai za'asa dashi shine akan gaba, sai kace ba tare Muka zo dashi Hukumar Soja ba, matsayinmu d'aya dashi ada amma yanzu ya k'are mu".
Wani murmushin gefen baki Joha ya saki yana kai dubansa inda su Captain Harun suke tsaye, a yanzu ya amshi abun magana yana d'an jawabi cike da muryar nan tashi mai kauri had'e da natsuwa.
"Banga abunda Captain Harun ya tsare maka ba Abbakar, sai nake ganin kamar hassada kike masa kana bak'in ciki da ci gaban da Allah yake basa ne, ya kamata zuwa yanzu ka daina duk wannan indai akan Harun ne zaka mutu da ciwo a ranka kuwa".
Wani dogon tsaki Captain Abbakar ya saki cike da jin zafin Captain Harun ya mik'e ya bar masu wajan, yana ji a ransa ko wuk'a ya samu ya sami dama kuma zai iya kashe Harun wallahi.
Captain Joha ya bisa da kallo yana masa Add'aur shiriya, duk da ya kasance shi ba addini d'aya suka had'a ba, baya bak'in ciki da d'aukakar da Allah yayi ma abokinsa, ko da da rana d'aya ne kuwa, duk da cewa kusan matsayi d'aya suka fara aiki a tare a Hukumar Sojan, amma gashi yanzu Captain Harun d'in ya kare su nesa bama kusa ba, bai tab'a jin wani abu saboda da haka ba, ace sai d'an uwansa wadda suke addini d'aya ne yake jin haushinsa haka.
Kusan abokai ne harda Abbakar d'in Kuma duk tare suka zama Sojojin.
______________________
*Airport Rd, Dabolim Goa*
A hankali Fasinjojin jirgin daya sauka a filin jirgi dake K'asar Gowa ya sauka a dai-dai k'arfe takwas na dare.
Gaba d'aya suka fara fitowa d'aya bayan d'aya.
Kusan zan iya cewa Farida ce k'arshen fitowa ita da Anjali suna rik'e da akwatunansu gaba d'aya.
Farida ba abunda take sai tasbihi ga Ubangiji wadda shine mamallakin komai dake cikin duniyar nan tamu da kowa a cikinta, gaba d'aya garin Gowa ya tafi da imanin Farida, tsabar yadda ya had'u iya had'uwa, zata iya rantsewa da Allah b'ata tab'a ganin garin da yake dad'in ace zaka shak'ata kamar Gowa ba, lallai bata ga laifinsu Amal da suka dage sai wannan K'asar zasu zo yawan shak'atawa ba, K'asar tayi kyau kam iya kyau, an tsarata ta tsaru.
Garin kalle-kalle Farida harda su tuntub'e saura kad'an ta kife a k'asa, tsawar da Hanan ta buga mata ce ta kusan sata idasa zubewa a k'asa bata shirya ba.
"K'auyencin zaki fara nuna mana ko?, ki natsu ki shiga hankalinki wallahi Farida".
Da rawar jiki Farida ta d'aga kanta maganar ma ta kasa, da gudu ta k'araso inda wasu motoci suke parking a wajan.
Motoci ne sunkai biyar ko wanne ya hau wacce yake da ra'ayi dama kuma tarbarsu aka zo yi.
Farida kanta ai bai k'ara kwancewa ba sai da taga sun iso wani matsiyacin Hotel wadda tunda take a duniya b'ata tab'a ganin irinsa ba.
Hotel ne amma yadda kasan kana cikin gidan ubanka.
Kai zata iya cewa babu ce kawai babu a hotel d'in, iya had'uwa D'akunan da suka kama sunyi kyau na k'in k'ari.
Kowanne cikinsu tare da wa'inda suka taho suka kama d'akuna.
Su Faruk da Baby's nasu d'aki d'ai-d'aiya suka kama kowanne, sai kuma Amal da Faisal d'aki d'aya, abun ya so ba Farida mamaki tunda dai ai take ganin ba ma'aurata bane, amma su ko a jikinsu, ita da Anjali aka kama ma d'aki d'aya, ita kanta Hanan sai yanzu ne ma Faridar ta lura da wani saurayi da Hanan ta taho dashi, ita wallahi da duk bata lura dashi ba, sai yanzu da ake shirin had'a d'aki d'aya dashi d'in.
Ita kam yau tana ganin ikon Allah, sufa a haka gani suke wayewa ce ba wani abu bane kwana d'aya da namiji wadda ba maharramunka ba ko?.
Irin wannan tunanin take a zuciyarta.
A cikin daren sai da suka d'an huta, kamin suka fara shiga wanka aka fito aka d'auki wani shegen wankan, ana shirin fita yawo tun a ranar.
Duk d'aukar su Anjali sai zuwa safiya zasu fara fita yawon, sai kawai suna zaune aka buga masu k'ofar d'aki suna fita Amal ta basu umarnin su fito zasu d'an fita daga gari ne a kamin gobe da safe ayi mai gaba d'aya.
Da mamakinsu taje ta sanar da Farida.
Farida harta fara wani wahalallan bacci taji an tayar da ita.
Ba dan ta so ba ta fito suka iske su suna jiransu.
Hanan sai fad'a take tana masifar sun barsu a tsaye sai ka ce wasu sa'anninsu.
Basu da ikon cewa komai suka shige mota suka nufi cikin garin Gowa.
Sunsha yawo cikin daren, kamar bazasu dawo makwancinsu ba.
Iya gajiya Farida ta gaji ai nun, amma ba damar nunawa, tana kallon Anjali ita ko a jikinta, tunda zan iya cewa ta saba dama da irin hakan ita.
Kiiiiii
Gaba d'aya motocin suka ja birki.
Fitowa suka rink'ayi gaba d'aya suna kallon motar su Amal dake gaba ita da Faisal wadda sune suka ja birkin suka tsaya.
"A'a ya naga kunja birki mi ya faru ne?".
Fad'in Jasmin.
D'an kallon ta Amal tayi tana zare hannunta daga na Faisal dake kallon abunda ke gabansu wani Kare ne tsaye a wajan saura kad'an su take sa ma.
Tsaye yake sai kunji yake bakinsa yayi daje-daje da wani bak'in jini, idonsa kuwa jawur kamar garwashin wuta, kamar Kuma wuta naci a cikinsa.
Farida tana kallon yanayin Karen gabanta ya yanke ya fad'i har sai da ta d'an ja baya tana addu'a a zuci, haka kawai taji mugun tsoro Karen.
"Wallahi wai Kinga wani Kare ne ya shige mana gaba, shine yasa muka ja birki saura kad'an mu take sa ma Allah ya tak'aita"
Fad'in Amal itama tana mai do dubanta wajan da Karen yake ganin Faisal ya nufi inda yake yasa ta d'an ja da baya tana sake cewa.
"Kaii kaii Honey please karka matsa inda yake, kasa dutse ka jefesa ya bamu waje kawai mu wuce dan Allah, ni haka nan ban yarda da Karen ba".
Haba ai baima jita ba nufar Karen kawai yake yana wani murmushi irin ya saba da Karnukan nan yana cewa.
"Haba Baby ba abunda fa zai faru, baki ga Karen turawa bane babu ruwansu da fad'a ma bare suji ma mutum ciwo".
Ya k'are maganar zai kai hannunsa jikin Karen.
Kamin ya kai hannunsa jikinsa kawai kamar an harbo Karen yayi wani kukan kura ya fad'a jikin Faisal yana kafa masa hakura a dai-dai k'afarsa.
Wani bala'in ihu mai k'arar gaske Faisal ya saki, jin wata azaba da tayi ma Kwakwalwar kansa sallama mai shirya ba.
Gaba d'aya zaro ido waje sukai wasu na komawa baya, Farida ko wani zawo ne taji yana shirin zubo mata.
Da kyar wasu Y'an Sadda suka k'araso wajan, suka kori Karen daga wajan yayi cikin daji yana lashe jinin daya tsotsa a jikin Faisal.
Faisal da kyar ya mik'e idonsa jawur na tsabar azaba tunda yake bai tab'a jin cizo mai zafi da rad'ad'in azaba irin na wannan d'an iskan Karen da ya cije sa ba.
Da kyar Amal ta rik'e masa hannu yana d'angyasawa, suna ta masa sannu, sai dai kawai ya girgiza kai yana d'aga masu hannu alamar yaji.
Kai tsaye Wani Babban Asibiti suka nufa dashi domin gyara masa cizon da Karen yayi masa, domin harya fasa masa fata sosai sawon hak'oran Karen b'aro-b'aro a cikin k'afar Faisal inda ya kai masa cizo.
Doctor's sunyi mamakin yadda wajan da Karen ya cije sa yake komawa wata color daban, wani irin bak'in jini wajan ke zuba.
An masa allurar bacci tare data kashe rad'ad'i domin Faisal wani ihu ya rink'a masu na cewa wajan na masa wani irin azababben rad'ad'i, dole tasa Doctors yi masa allurar kashe zafi.
Amal sai kuka take kamar wacce aka ce ma mutuwa zaiyi...........
*GAWA TAFE*
(Zombies story)
On2025
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*
*EPISODE 4*
*V.M Salgaocar Super Speciality Hospital Goa*
Zaune suke a d'akin jinyar da aka kwantar da Faisal, sunyi jingum jigum kowa da abunda yake tunani a ransa.
Hanan ce ta d'an matsa kusa da Amal dake zaune bakin gadon da aka kwantar da Faisal wadda yake wani dogon bacci har zuwa biyu na dare Shuru kake ji bai farka ba.
"Ya kamata wasu daga cikinmu suje Hotel d'in da muka sauka su d'akko mana kayan anfani, ba zai yuwu mu kwana gaba d'aya a asibitin nan ba".
Fad'in Al'ameen yana duban su gaba d'aya.
Hanan data k'arasa inda Amal take ta ce.
"Ni gaskiya ina nan nida K'anwata sai dai kai ka tafi kaida Garl d'inka"
Shuru ya d'anyi, haka kawai yaji baya son tafiya ya barsu, cikin k'arfin hali Al'ameen ya dafa kafad'ar Faruk yana cewa.
"D'an uwa da kai zamu wuce ne ko kana nan?"
"Why not mu zauna gaba d'ayanmu zuwa safiya, sai mu wuce mu dawo?"
*Farida & Anjali POV*
Su Farida dai na daga waje k'ofar d'akin da aka kwantar da Faisal suna kallon yanayin asibitin.
Wata y'ar hayani ce ta fara kusanto inda suke, hakan yasa da mugun sauri Farida ta zabura ta mike da kyar Anjali ta rik'e mata hannu ganin tana neman banka masu cikin d'akin jiyar.
Zaro ido waje tayi tana kallon Anjali tana cewa.
"Wallahi Anjali kwata-kwata hankali na ya kasa kwanciya da inda muke, ke gaba d'aya ma K'asar ce bata kwanta min ba, ki duba ki gani daga isowarmu har wasu abubuwa marassa dad'i sun fara faruwa damu fa, yanzu ki dafa k'irji na kiji yadda yake bugawa da k'arfi har ya wuce misali, zuciyata da ruhi na dank'are suke da tsoro na rasa mi yasa Hakan".
Sauke wani gajeran lumfashi Anjali tayi tana jin wani iri a ranta kamin ta ce.
"Kusan nima zan iya cewa ina jin kaso mafi girma da fargaba a raina, duk da ba yanzu ne karo na farko dana bar K'asar Nigeria ba, no a ko da yaushe muna tafiya irin wannan da su, amma wannan sai nake ji ta banbanta da sauran, kwata-kwata, bana jin tafiyar a raina, ki natsu insha Allah babu abunda zai faru kinji".
Suna cikin magana wasu Doctors guda biyu suka nufo inda suke tsaye, zasu wuce hankalinsu a mugun tashe da harshen turanci Anjali ta ji kamar suna cewa.
"Akwai babbar matsala a cikin gari ya kamata ayi gaggawar kulle hospital d'in nan, kamin matsalar ta shigo ciki".
Hankali a mugun tashe d'ayar keba d'aya amsa daga cikinsu tana cewa.
"Akwai fa marar lafiyar da aka kawo yanzun nan D'an Sanda ne wai wani mahaukacin Kare ya cijesa a hannunsa, kuma da alama kamar Karen shine ke son yad'a wata cuta, dan yanzu haka ance cikin garin Goa ba lafiya cutar da Karen ke yad'awa ce, yaje ya sake cizon wata mata ita kuma matar ta tafi gida ciwo nata cinta, k'arshe kawai mijina ta kama tana cizo had'e da yagar naman jikinsa tana ci, a labarin dana na gani ma ta cinye rabin gagar jikin mijin nata fa, hatta Yaronta k'arami ta cije sa, amma ance shi ya gudu dashi da ita ne suka rink'a cizon mutane har cutar ta fara yawa a cikin gari, shine ina cikin kallon abunda ke faruwa kika shigo min da maganar ana son kulle hospital d'in nan gudun kar cutar ta iso cikinsa, to amma fa......
Tsaye suka tsaya inda su Farida suke, Farida sai zare ido take tana binsu da kallo ganin yadda suke magana hankali a tashe suna rik'e da hannun juna, tana dai jinsu ne amma kwata-kwata bata fahimtar yaranda suke yi, sai Anjali dake jin komai tana fahimtar su, itama k'irjinta sai bugawa yake, idonta da hankalinta kacokam yana gare su, ta tsaya sake da baki tana jin abunda suke cewa ji take abun kamar a cikin film ko labarin wani littafi.
Farida ce ta kamo hannun Anjali tana d'an girgiza ta tana cewa.
"Dan Allah kina jin miye suke cewa?, naji a jikina kamar abun suke fad'a ba alkhairi bane, kamar zai shafe mu ne, dan Allah ki sanar dani miye suka tattauna a Kai".
Zatai magana taga d'ayar Doctor d'in ta ce.
"Ohhh my God kina nufin wadda aka kawo yanzun nan shima cizon Karen ne?, to ai wannan d'akin ma wadda aka kawo shima cizon Kare ne an masa allurar bacci ne shine ma zanje