Showing 3001 words to 6000 words out of 20241 words

Chapter 2 - GAWA TAFE Book Complete Hausa Novels Writing by Mrs Sufi.txt

02 Feb 2025

2164

On2025




*©Zahra Royal Star*






*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*






*EPISODE 2*






"Bana buk'atar fita da kowanne jami'in tsoro, da'aAllah ku matsa ku bani waje na wuce"


Wani daga cikin jami'an tsoron ne ya d'an duk'a har k'asa yana cewa.


"Please Ranki ya dad'e Amal mai gida ne ya hana duk d'ayanku da zai fita, a tabbatar an basa wani jami'an tsoro koda mutum d'aya ne ya fita dashi, kiyi hakuri ga Anjali kuje tare please kar muyi laifi wajan mai girma Gwamna".
Wani tsaki taja tana duban Anjali dake gefenta, sanye take da kayan jami'an tsoro itama, dama kuma ita ce mai bata kariya, duk inda take to zaka ga Anjali a wajan.


Key d'in mota ta wurga ma Anjali ta duk'a k'asa ta d'auka, da sauri ta bud'e mata gidan baya ta zauna, ta maida murfin ta rufe ta zagaya gidan gaba wajan mai toki taja motar suka fice daga gidan.


Basu dad'e da fita ba su Faruk suka fito, su dama sunfi so idan zasu fita ayi masu Jiniya, jami'an tsoro suna take masu baya, sai idan zasuje wajan shashanci sune hatta kansu jami'an tsoron basu san lokacin da suke sab'ewa suyi tafiyarsu harsu dawo basu sani ba, saboda akwai b'arauniyar hanya a gidan gwamnatin, wadda sune kad'ai suka san da ita.




Kiiiiiiiiiiiii
"Ohhhh My God" Anjali ta furta da k'arfi.
mugun sauri Anjali taja wani uban birki motar ta tsaya, har Amal dake baya ta d'an bige da jikin Motar.


A yamutse cike da masifa Amal ta d'ago tana cewa.


"Wannan wane irin hauka ne Anjali?, baki da hankali ne so kike ki kashe ni da raina?".




"Ranki ya dad'e please kiyi hakuri dan Allah, wata Tsohuwa ce ta shigo mana gaba zata tsallaka titi ne".


Zaro ido waje Amal tayi cike da tsallar jin haushin ko wacece ta shige masu gaba, ta kai dubanta gaban titin ganin Tsohuwar har yanzu sai wani d'angyasa k'afa take had'e da sandarta tana dogarawa, har sun ma d'an bigeta tana k'ok'arin tashi da kyar.


Rai a mugun b'ace cike da tsanar talaka a cikin ranta Amal ta wani bud'e mota ta fito.


A wulakanci Amal ke kallon Tsohuwar ganin zata dafa masu mota tana son mik'ewa, Amal tayi saurin saka k'afar ta hanb'arar da Tsohuwar tana tofa mata miyau akan fuskarta tana cewa.


"Kee da'aAllah magidajiyar Tsohuwa kawai, saboda tsabar gidadanci irin naku na talakawa kawai ki shigo titi tsabar rashin hankali da wayewa, titin na gidanku ne da zaku rink'a hawansa kara zube haka?, sana karki sake k'azamin hannunki ya sake tab'a min Mota aikin banza kawai".


Amal ta k'are maganar tana nuna Tsohuwar dake d'uke a yanzu tana mata kallon tsallar mamaki.


Mutane da yawa sun tsaya suna kallon abunda ke faruwa, wasu y'an mata ne dake nesa da wajan suna tafe zuwa wajan suna cewa.


"Kee wa nake gani kamar d'iyar B Radda Gwamnan Jahar nan?".




"Yo ita ce mana, gata can tana wulakancin nata da ta saba, dama kuma na dad'e ina jin ana cewa duk Y'ay'an Gwamnan nan mai ci yanzu basu da mutumci wulakanci ne dasu, idan ka bari wata hud'd'a ta had'aka dasu, sai sun k'ask'astar da kai sun nuna maka kai ba kowa bane".


"Yo ubanwa zasuyi mawa, ai Mulki ba hauka bane wallahi, kuma suje ai duniya ce tafi Bagaruwa iya jima wallahi. Ki duba irin d'ibar albarkar da take ma waccar Tsohuwar miye laifinta? Dan kawai tazo tsallaka titi motarsu ta shawo Kai?, Ai suma da laifinsu tunda ba toki suke na kwanciyar hankali ba".


Irin wannan maganganun ke tashi a wajan.


Anjali ma fitowa tayi tana son yima Amal maganar abunda take ba dai-dai bane, amma tana shakkarta.


Tsohuwar da kyar ta mik'e wata mata na kamata Tsohuwar tana kallon Amal dake dod'e hancinta tana yamutse fuska ta ce.




"Uhuhmm yarinya kenan, kibi duniyar a hankali, saboda ba matabbata ba, ce ku guji ranar da zaki nemi taimakon wani kuma kina ji kina gani ya kasa taimaka miki har ki halaka kina ji kina gani da idon ki.....


"Ke kinga baiwar Allah ki rik'e wa'azinki na saba jinsa daga bakunan jama'a, dama ku talakawa ba abunda kuka iya sai y'ar k'aramar murya, wai dan kawaii aji tausayinku. Ke Anjali dalla shige muji, mubar wajan nan wari ma wajan keyi mtswww".


Ta k'are fad'ar haka tana shigewa motar da sauri, mutanan dake wajan sun saki baki da hanci suna jin d'ibar albarkar da wannan y'ar yarinyar ke masu.


______________________
"Baby na mike faruwa ne?, kin iso ranki duk a b'ace".


Kallon Faisal tayi tana narke fuska, ta kalli Anjali tana d'an b'ata fuska ta ce.


"Please Anjali d'an bamu waje ko?".


Matsawa Anjali tayi kawai tabar wajan bata ce komai ba, tana kallon yanayin wajan da suka zo d'in. Waje ne irin na shak'atawa, irin na Y'ay'an masu hannu da shuni ne kad'ai ke shawagi a wajan, kowa ka kalla yana ji da kanshi a wajan.




Kamo hannu Faisal Amal tayi a shagwab'e ta ce.


"Honey wata Tsohuwar banza ce ta b'ata min rai a hanyarmu ta zuwa wajan nan, wai mi yasa shi talaka fakiri ne ba abunda ya iya sai shashanci da k'auyanci, shiga fa tayi a gaban motar mu kawai ta wani hau titi sai ka ce titin na ubanta ne mtswwwww".


Murza hannunta yake yana sake shigewa mata, yana wani shinshinar wuyanta had'e da hura mata iska, a hankali taji ya had'e bakinsu waje d'aya, bata hanasa ba saima wani d'an murmushi da saki tana tallafo kansa itama.
Jama'a karku ce wasu sunma hangi miye suke yi, saboda da yawa wajan wayayyu ne, rayuwa ake kamar ta turawa, kowa ga gani a wajan d'an iskan kanshi ne.


Sakinta ya d'anyi yana jifarta da murmushi ya ce.


"Manta da wasu talaka Babyn, ya maganar tafiyarmu Gowa?".




"Ohh abunda na zo mu tattaunawa kenan, mu y'an gidanmu su Faruk mun gama tsara yadda za'ai tafiyar, kaga ni da kai sai Jasmi na kira wayarta itama zata zo nan zamu had'u yau zamu gama tsara yadda za'ai".


"Yawwa Baby ki shirya zuwanmu Gowa zaki bani kyautar.....


"Na sani ba sai ka fad'a ba ai"


Murmushi ya saki na shak'iyaancin yana kanne mata ido d'aya.




"Wow My friend ashe har kin rigani isowa?".


Zama Jasmin tayi tana fad'ar Hakan.


Tafawa sukai Amal ta ce.


"Shegiya K'awata wannan muguwar shiga haka, kina lokaci fa".


Dariya Jasmin tayi tana kallon wani D'an iskan wando data saka da wata y'ar riga ko cibiyarta bata rife ba.


Ta ce "kema kinsan bana son kaya masu nauyi just bana son takura. Yawwa wai yaushe ne zamu bar K'asar nan ne na K'usa fa Guys?".




"Maganar da muketa yi kenan, inaga bamu wuce cikin Satin nan gaskiya".


Fad'in Amal.




Jasmin ta d'aga kai ta ce "wai ina shegiyar nan ne Hanan?".




"Hhhh ai ko yanzu kin ganta wajan nan itama ai duk da ita za'ai tafiyar". Cewar Faisal


"Ki ce zamu rak'ashe da yawa a Gowa, Gowa zatai d'ibar Y'ay'an Manyan K'asar Nigeria".


Fad'in Jasmin tana murmushi da d'okin tafiyar.




*HANAN POV*




"Ke Farida kiyi saurin had'omin Copi, ina sauri ne zan fita pls".


Hanan ta k'are maganar tana zama d'aya daga cikin kujerun babban parlon gidan nasu, tana latsa waya, bata kalli inda Farida ke goge a parlon ba.


Farida da rawar jiki ta amsa tana shigewa k'aton kitchen d'in parlon. Duk da yawan ma'aikata dake kitchen d'in amma ita ce kad'ai suka yadda da girkinta, shi yasa tana aikatuwa a cikin gidan ba d'an kad'an ba.


Da rawar jiki ta k'araso inda Hanan take a zaune, rik'e da cofi na copin data had'u mata.


"Gashi Ranki ya dad'e an gama".


Hannunta ta mik'a again tana latsa wayarta ta amshi k'ofin dake hannun Faridar.


Kaiwa bakinta tayi tana latsa waya, kurb'a d'aya tayi da mugun sauri a zabure ta furzar dashi sai akan fuskar Farida.
A zabure Farida ta saki k'ara tana mik'ewa tsaye, domin taji zafin copin ta furzar mata akan fuskarta.


Hanan rai a b'ace tana nuna Farida da yatsa tana cewa.


"Kan uba, so kike ki kashe ni Farida?, kinji zafin abunda kika had'u min kuwa?, waike mi yasa komai zaki yi sai kinja an zagi ki?, wannan wane irin jakanta ce haka, ace mutum kullum sai ance baiyi dai-dai ba, sai ka ce wacce ke da Kwakwalwar kifi".


Zubewa Farida tayi a k'asa tana had'e hannunwanta waje d'aya alamar neman afuwa tana cewa.


"Kiyi haku......

"Dalla can rik'e hakurinki Malama".


Ta k'are maganar tana sakin kofin a hannunta ya fad'i k'asa ya tarwatse, ta nunata da yatsa ta ce.




"Ki kiyaye a nan gaba, idan ba haka ba kin san sauran, kuma ki fara shiri domin dake zanyi tafiya Gowa, domin ki rink'a min hidima a can, saura idan munje can d'in ma ki rink'a min Jakanta kamar yadda kike min nan".




Rasssssss Farida taji gabanta ya yanke ya fad'i lokaci d'aya, haka kawai taji gabanta ya ci gaba da bugawa, jin abunda Hanan d'in ke fad'i, bata san mi yasa taji ta tsani ayi tafiyar nan da ita, tasan zasuyi tafiya tabbas zasu bar K'asar zuwa shak'atawa amma b'ata tab'a tunanin cewa wai da ita za'a tafi ba, b'ata tab'a ganin irin haka ba ita kam, zaka je shak'atawa tsabar sangarta har sai ka tafi da mai maka hidima?




"Tsayuwar uban mi kike kuma a nan?".


Fad'in Hanan tana ma Farida wani duba.


Da sauri Farida ta katse tunanin data fad'a jiki na rawa ta ce.


"Yi hakuri Ranki ya dad'e".


Ta fad'i hakan tana barin wajan.


Anam ce ke sakkowa tare da Mom har Anam na kyarmar fad'in.


"Mom kinji miye waccar yarinyar ke fad'i ko?".




"Naji mana, to miye a ciki?, idan ta tafi da Farida, ai zata rink'a mata wasu abubuwan ne a can".




"Nooo Mom bai kamata ma ki bari taje wani yawan shak'atawa ba wallahi why Mom d......


D'aga mata hannu Mom tayi dai-dai sun idasa sakkowa k'asan ta ce.




"Kinga Anam bana ce miki ki daina shiga harkar da babu ruwanki a ciki ba?, so please ki kyale yarinya tayi yadda take so mana, kuma nake ganin ai ba ita kad'ai zatayi tafiyar nan ba, ita fa dasu Amal da kuma su Al'ameen Yayyunta, zasu tafi, kinga kuwa banga abun tada hankali ba ai".


"Mom ki ce kawai shashancinsu zasu tafi wallahi, ai duk inda aka sami su Amal dole akwai shashanci a ciki, Mom dan Allah kima Dad magana ya soke masu
Tafiyar nan, ni haka nan tunda suka fad'i tafiyar na ji kwata-kwata bata kwanta min ba, suyi hakuri da ita mana zuwa wani lokacin".


Hanan dake kallon Anam ji tayi kamar ta shik'e mata wuya, tsabar jin haushinta. Ji mata da'aAllah nason masu bak'in ciki k'iri-k'iri.


"Kinga ko Aunty Anam babu abunda ya sha miki kai da tafiyarmu, ai bamu ce dake zamu je ba dai ko?".


"Ki rufe min baki Hanan, ni yama za'ai nayi tafiya irin wannan daku Allah ya tsare ni wallahi, kuma zaki ci ubanki ne idan ina magana kina sak'o min wannan shegen bakin naki".


Kwab'e fuska Hanan tayi tana murgud'a mata baki.


Mom data zauna akan kujera tana d'aukar romot d'in Tv ta canza tasha tana cewa.


"Kwantar da hankalinki Autata babu wadda ya isa hanaku tafi Gowar nan, tama yi ta gama"




Sakin baki kawai Anam tayi tana duban Mom, can ta sauke wani lumfashi tana gyara tsayuwarta ta ce.


"To tunda dole ne ance tafiyar ta su, Mom karta sake ta ce zata d'auki Farida su tafi tare, domin banga dalilin da zaisa dole sai an d'auki Farida ba".


Wani kallo da Mom ta jefa mata ne yasa ta d'an had'e wani miyau daya tsaya mata a mak'oshinta, tana sake kallon Mom d'in.


"Anam kifa fita ido na rufe tom, da ita d'in zata tafi, ko ke ce kika d'auke ta aiki ne ban sani ba?"


"Ni Mom bani na d'auke ta aiki ba, am...


"Kinga zo ki wuce wajan aikinki ya fiye miki, domin b'ata ma kanki lokaci kawai kike a yanzu".


Ranta babu dad'i ta juya ta fice daga parlon.


Mom na kallon ta fita taja wani lumfashi duk da itama tafiyar bata wani kwanta mata ba, amma kamar an d'aure mata jijiyoyin jikinta da bakinta ta kasa furta ainafin abunda ke cikin ranta.


A hankali ta ce.


"Ace ayi mutum yayita shiga abunda babu ruwansa".




Hanan dake murmushin cin nasara ta rungume Mom tana cewa.


"Mom wallahi shi yasa nake k'ara sonki, bari naje su Amal na can suna jira na, zamu tattaunawa akan tafiyar da zamuyi Gowa".


"To sai kin dawo, am....


"Haba Mom karki ce komai, kawai sai na dawo d'in dai".


Ta k'are maganar tana kai mata kiss a goshi tayi saurin ficewa daga parlon, domin ta lura kamar Mom d'in na son yarda da maganar Anam d'in.


_______________________
*HARUN POV*


a hankali yake juya y'ar kujerar da yake zaune akanta.
Sanye yake da kakensa na Soja, wadda suka k'ara haska fatarsa Chocolate color, dara-daran idanuwansa ya lumshe yana sake bud'e so. Dokar daji ce suke, yak'i ne akai Babban gaske, daka kalli yanayin wajan da suke zaka shaida hakan, saboda gawawwakin dake yashe a wajan, da wasu tsirarun Sojoji dake wajan, sai wasu Gawawwakin Sojoji suma dake kwance a wajan cikin jini.


"Harun Yaya dai?".


Kallonsa ya kai inda yaji kiran nashi a hankali ya sake ware idanuwansa sosai akan abokinsa shima dake sanye da kaken Soja.


Cike da tsananin gajiya ya ce.


"Noo ba wani abu Captain Joha"


"Dole Harun jikinka yayi ciwo, ban tab'a ganin mai k'ok'arinka ta fanin yak'i ba, dubi fa irin mutanan da kashe wajan aikin nan, yama kamata muzo mubar cikin jejin nan gaskiya"


A hankali ya d'an mik'e akan kujerar da yake kai duk jikinsa jini ne sai wasu y'an ciwuka da baza'a rasa ba.


Kujerar daya tashi Joha ya kalla domin irin kujerar Mota ce data rugugguje ta fita daban, a dai-dai lokacin daya kashe wani d'an daba wadda ya addabi mutane da dama, sunsha artabu da Harun kamin Allah ya basa damar kashe sa, yana kashesa kuma ya fad'a kan kujerar yana sauke wani lumfashi mai cike da gajiya.


Ganin Harun d'in yayi nisa ya barshi ga jirginsu dake shirin tashi domin barin Jejin, da sauri da d'an gudu-gudu ya k'arasa inda yake, kusa a tare suka shige jirgin ya d'aga dasu suka bar cikin Jejin dake ci da wuta ga gawawwakin jama'a nan, sun bar wasu Sojojin na aikin jidar wa'inda suka rasa ransu a wajan.............


*GAWA TAFE*
(Zombies story)
On2025




*©Zahra Royal Star*




*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*






*EPISODE 3*




"Why Amal zaki je tsakiyar titi ki fito kina ma mutane tsawa?. Ki duba video yadda y'an adawa ke yad'ashi suna magana marar dad'i akai na da iyali why mi yasa?".


Fad'in Abbie dake tsaye yana nuna ma Amal wayar dake hannunsa ransa a b'ace yake maganar.


Amal kuwa dake tsaye shagwab'e fuska tayi tsabar ta saba masa sangarta ta ce.


"Sorry Abbie wallahi banyi hakan dan b'ata siyasarka ba, kasan talakawa ba abunda suka iya sai shige ma masu kud'i, kawai fa Abbie muna tafiya tsakiyar titi wata banzar Mata ta shigo mana gaba, ni kuma shine......


"Shine ke kuma kika tsaya tsakiyar titin kina d'iyar Gwamnan Jahar nan kina cece kuce da jama'a, kuma dama kin san magauta kiris suke jira su yad'a abunda bashi kenan ba. Yaushe ne tafiyarku Gowa?".


Wani murmushi ta saki na tsallar murna ta ce.


"Yesssss Abbie cikin weekend zamu tafi".




"Noo na dawo da tafiyar taku zuwa gobe, gara ki bar K'asar keda wa'innan Yayyun naki kuje can ku d'an huta, saboda maganar mutane akanku yanzu tayi yawa, gara ku tafi can, dan in kina ganin mutane irin na K'asar nan dole hakan zata rink'a faruwa, canfa duk masu kud'i ne ke zuwa K'asar shak'atawa, so kamar nawa kuke son tafiya dashi?"




"Wayyo dad'i Abbie Allah ya saka, Abbie kamar Million's......


Faruk ne ya yayi saurin katseta da shigowarsu kenan parlon suka ji maganar Abbie ta k'arshe inda yake tabbayar kamar nawa zasu ishe su tafiyar.


"Abbie kamar Million's biyar-biyar ko wannan mu ta ishesa nake gani ko guys?".


Ya fad'i yana duban su Amal da Al'ameen.




"Yesss Abbie saboda muda friend d'in da zamuyi tafiyar dasu"


Cewar Amal tana kallon Abbie dake kallonsu.


Abbie ya juya wajan P'A d'insa yana basa umarnin ya turowa kowannan su naira million shidda-shidda ta account d'in kowa daga cikinsu.


Wani tsalle Amal ta daka tana rungume Abbie jin harda k'ari yayi masu akan wadda suka tabbaya d'in.


Murmushi ya d'an saki yana cewa.


"But sai kun rink'a lura idan zaku fita cikin gari, kusan inda ya dace ku rink'a abubuwa, saboda yanzu sai kuga abu k'arami magauta na son mayar dashi babba, yanzu miye dan kawai kin fito kin tsawatarwa wannan Tsohuwar?, why mutane yanzu kamar jira suke su fara zaginka, dama nasan shirrin mak'iya ne kawai, sai ku kiyaye gaba d'ayanku, baima kamata kuna bi Local waje irin wadda zaku rink'a had'uwa da wa'inda basu san miye duniyar take ciki, just ku rink'a ma K'anwarku fad'a Faruk".


Da to suka amsa ya haye sama P'A d'insa yana take masa baya. Yana bin Y'ay'an gata da kallo, lallai giyar Mulki na d'ibar wasu mutanan, dubi dan Allah yadda yayi kyauta Millions shidda ga kowannan su, kamar yayi kyauta naira biyar.


Fad'in P'A d'insa a zuci yana bin bayansa yana maganar zuci.


_____________________
*1100pm Umaru Musa Yar'Adua Airport Katsina State Nigeria*




Gaba d'ayansu ne tsaye a filin jirgin.
Wasu matsiyatan kaya suka saka kusan zan iya cewa duk iri d'aya ne, saboda k'ananun kaya ne wadda sukai masu mahaukacin kyau.


Daga gefen Amal harda Anjali za'a tafi saboda ta rink'a tare mata wasu abubuwan, tana kula da ita, sai Jasmin.
Hanan ma tare suke da Farida wacce aka bata kwancan kaya, shigarta itama ta k'ananun kayan ne, dan dai ita ko ina a jikinta a rufe yake. Daka kalli yanayin fuskarta zaka shaida cewa ba dan tana so za'ai tafiyar nan da ita ba.
Domin sai da sukai uwar watsi da Inna Zubaida a sadda ta koma gida take shaida mata zasuyi wata tafiya da ita k'asar waje, ita gaskiya zata ce masu ta daina masu aikin, bazata wani bisu zuwa K'asar da bata sani ba, tafiyar ce kwata-kwata bata kwanta mata ba. Ai ko tasha zagi da kwashe albarka sai cewa mata take
"Sannu y'ar bak'in ciki irin tsiya dangin tsiya sannu kinji na ce. Ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login