Showing 18001 words to 20241 words out of 20241 words

Chapter 7 - GAWA TAFE Book Complete Hausa Novels Writing by Mrs Sufi.txt

02 Feb 2025

2165

ce Mom d'in ta mutu.


Da kansa yaja Motar, bayan yasa Mom a baya sai Anam data shiga tana rungume da Mom, da gudu yaja Motar suka fice suka bar y'an aikin gidan da zullimin abunda ke faruwa.


_____________________
*HARUN POV*


Babban d'akin taro ne na Hukumar Sojan K'asar Nigeria, gaba d'ayansu ne zaune a wani k'aton Table kowanne mutum dake zaune an aje masa ruwa a gabansa. Gaba d'ayansu sun mai da hankalinsu ne ga Shugaban Sojojin da yake masu wani mahimmin jawabi kamar haka.




"Mun had'a wannan mintin d'in ne, a bisa shugabannin K'asar nan da suka bada umarnin tura wasu daga cikinmu zuwa K'asar Goa".


Sai kuma yayi shuru yana sake kallonsu, wata Tv ce a gabansu tana tsaye yana nuna jikin Tv d'in yana sake kallonsu yana sake cewa.


"Wata annoba ce ta riski K'asar Goa, a yadda muka samu labarin cewa cutar ta gama ma K'asar Goa babbar illar da har suke neman taimako a k'asashen duniya, wa'inda suke da halin taimaka masu k'ofa a bud'e take, suna buk'atar Likitoci wa'inda suka san aikinsu, sai kuma Sojoji wa'inda suka kware ta fannin yak'i. To shugaban K'asar nan ya bada Umarnin mu tura Sojojinmu na nan k'asa Nigeria domin kai masu d'auki, had'e da Likitoci manya na K'asar nan. A labarin da naji cewa akwai Y'ay'an Manyan K'asar nan da suka tafi Goa bada dad'ewa ba, shi yasa abun ya shafi Manyan K'asar yasa har suka bada umarnin ayi gaggawar kai masu d'auki".
Ya sake d'an yin shuru yana dubansu gaba d'aya sun bada hankalinsu suna sauraran abunda yake cewa, sai d'aga kai suke alamar suna fahimtarsa sosai.


Ya sake nuna jikin Tv d'in dake a gabansu yasa wani manuni yana nuna yadda K'asar Goa ta fara komawa kamar Mak'abarta yana cewa.




"A nan zaku ga irin illar da cutar ke yi a jikin D'an Adam, cutar dai tana kama mutum ne idan mai cutar ya cije ka ko kuma yasa farcensa ya yakusheka, cutar tana sa ka rink'a cin naman mutum, akwai had'ari sosai a wannan tafiyar da muke shirin turawa wasu daga cikinmu.
Kai Captain Harun kai zamu tura had'e da Y'an group naku, domin Hukumar Soja ta yarda da kai da y'an term d'inka, tana da tabbacin baza ku bamu kunya ba, shi yasa ma kai tsaye muka yanke kune zakuyi wannan tafiyar".


D'aga kansa kawai Harun yayi alamar tabbatarwa, da amsawa Kuma.
Taron ya tashi a inda aka ware y'an group d'in Captain Harun ciki harda Abbakar da kuma Captain Joha, sai wasu kusan su goma Sha harda mace Maza sunfi yawa a ciki.


_____________________
Momma dake zaune sai rusa uban kuka take har jikinta na rawa tsabar tashin hankali, a rud'e Abbie ke mata magana yana cewa.


"Haba ya kamata ki daina kukan nan haka nan, nasa fa za'a tura Sojojinmu na K'asar nan had'e da Doctors domin cuto Y'ay'anmu, insha Allah babu abunda zai faru dasu ki kwantar da hankalinki kinji?".


Kuka ta sake rushewa da shi, tana kuka tana cewa.
"Wallahi hankali na bazai tab'a kwanciya ba, baccin gaba d'aya Y'ay'ana suna K'asar da wannan cutar ta b'arke da ita, ya za'ai na iya kwantar da hankalina?, kana fa gani aka nuno yadda idan mutum ya kamu da cutar yake cin naman D'an uwansa, wannan wacce irin cuta ce haka, ni ban tab'a ji ko gani ko labari akwai irinta ba, Innallihi wa'inna alaihir raju'on, nikam da nasan hakane bazan tab'a bari suyi wannan k'addarar tafiyar ba, dan......
Toshe mata baki yayi ganin yadda take magana cikin kuka har tana shid'ewa, cikin kwantar da murya Abbie ya ce.

"Mu dukanmu bamu da sani da abunda Allah ya hukunta faruwarsa ai, addu'a ya kamata mu bisu dashi, dan Allah kibar kukan nan haka nan karki sama kanki wata cuta daban Kuma".


Cikinsa kawai ta shige tana sake rushewa da kuka, domin tashin hankalinta gaba d'aya Y'ay'anta suna Goa.
Taji labarin an kwantar da Mom a asibiti kwata-kwata bata da kwarin gwaiwar zuwa asibitin dubo ta, ji take dama ita ce ta suma ko ta samu sassaucin abunda take ji a ranta, dan ita sadda ta riski labarin komawa tayi kamar wata zararra, da kyar aka samu ta hawaye suka fara subo mata, daga nan ne kuma ta rink'a kuka mai sauti kamar ba gobe.


_____________________
*ANAM POV*


Rik'e take da hannunsa Mom da farkawarta kenan Anam sai kuka take tana kiran.


"Dan Allah Mom karki sake suma, kina bani tsoro, kuma nima dani za'aje domin ceto y'an uwa na, yanzu nake samun kira da Hospital namu ana son ganinmu gaba d'aya, kuma ana ji dani a asibitin da nake aiki, nasan zaiyi wuya ba'a ce za'ayi tafiyar dani ba".


Rik'e hannunta Mom tayi da k'arfi tana girgiza kanta, Dad na kusa ya d'an rik'e d'ayan hannun nata yana dubanta jin tana cewa.


"A'a a'a ban yarda kije K'asar nan ba, kema so kike na rasa ki?, ban amince kije ba, itama Hanan nayi danasanin barinta zuwa, ashe dama abunda kike ji a jikinki kenan?, shi yasa kike ta k'ok'arin nuna min kar na bar Hanan taje, amma nak'i, bazan barki kije ba Anam bazan iya ba, idan na bari kika tafi kamar banyi adalci ba".


Hawaye take tana maganar, Anam ma wasu hawaye ne suka sake wanke mata fuska ta girgiza kanta tana cewa.


"A'a Mom dan Allah karki ce karna je, ina son nima nayi taimakon bayin Allah, ko Allah zai ji tausayinmu ya k'are Y'an uwana dake cikin k'asar da annobar take, please Mom ki gane abunda nake nufi, ba abunda zai faru dani Mom please".


Mom zata sake magana wayar Anam ta sake d'aukar k'ara, cirota tayi ganin Doctor Halisa ke kira yasa ta kalli Mom tana cewa.


"Ki gani ko Mom?, kirana ake daga Asibitin da nake aiki mitin ne na gaggawa zamu shiga, please Mom ki barni naje dan Allah"




Dad ne ya katse hanzairin Mom dake son sake turjewa ya ce.


"Please ki barta taje nima na barta taje insha Allahu zata dawo lafiya ita da Y'an uwanta".


Ba dan Mom taso ba ta d'aga masu kai kawai hawaye na sake zubo mata akan fuskarta.
D'auke idonta tayi daga Anam d'in tana zare hannunta daga na cikin Anam d'in.
Dad ne yayi ma Anam alamar ta tafi kawai zaiji da Mom d'in, dan sun lura Mom bata gama amincewa da Anam d'in taje Goa ba.


____________________
Gaba d'ayan Doctors ne a zaune a wani d'akin taro a asibitin da Doctor Anam ke aiki, kusan ita d'aya ake jiran isowarta wasu har sun fara jin zafin ta, ciki harda wata Doctor Asiya sai cika take tana batsewa, a inda har ta fara surutu ita da wata K'awarta Doctor Sa'adha tana kallon k'ofar d'akin turon da suke tana cewa.


"Wai ya za'ai anzo an wani aje mu akan wata can bata k'araso ba, mi yasa baza'ai mana jawabin abunda ya taramu ba?, ko kuwa dole sai shafaffiya da mai d'in can Anam ta zo za'a fara?, dan wallahi na tsane ta, ta cika iyayen tsiya da son asani".


D'an tab'e baki Doctor Sa'adha tayi tana gyara zaman gilashin idonta, tana d'an yin magana k'asa-k'asa yadda ita da Doctor Asiyar ne kad'ai zasu ji ta ce.


"Ai ko zaman jiranta ake yi yanzu, danni nima fa wallahi haushi take bani, ashe ba ni kad'ai ce ke jin kwata-kwata batai min ba".
Asiya zatai magana Anam ta fad'o d'akin, kamar an jefota.


Doctor Fahat ne ya kalleta kusan shine shugaban asibitin, dan shine ma zaiyi bayani akan abunda ya tarasu.


"Mi ya tsayar dake ne Anam?, kin bar mutane a zaune".


"Am sorry Doctor Fahat, wallahi an kwantar da Mom d'ina ce a asibiti, ga abubuwa da suka cakud'e mana a family namu, amma yanzu na iso zamu iya fara abunda ya taramu".


Nuna mata wajan zama yayi ta zauna ya d'an kallonta cike da sonta da birgewar da take masa.


Su Doctor Asiya dake gefe kusan a tare suka tab'e baki.
Tana zama Doctor Halisa dake kusa da ita ta d'an mata rad'a a kunne wadda yasa Anam d'an sakin murmushi kad'an.


Gyaran muryar da Doctor Fahat yayi ce yasa gaba d'ayansu suka mai da hankalinsu gare shi.


"Kamar yadda kuka sani a safiyar yau ne muka ji labarin wata Annoba ta kunno kai a K'asar Goa, wacce ta hallaka mutanan k'asar da yawansu, dan hakane manyan k'asar Goa d'in suke neman taimakon manyan Doctors wa'inda suka san aikinsu had'e da taimakon Hukumar Soja, ga duk K'asar dake son taimaka masu k'ofa a bud'e take. Mun samu umarnin cewa shugaban k'asamu Nigeria ya bada Umarnin tura Sojojinmu had'e da Doctors a kowanne asibiti dake fad'in k'asar nan zasu iya bada kamar mutum uku, abunda yasa mukayi gaggawar taraku a nan kenan, mun rigada mun gama zab'ar wa'inda za'ayi tafiyar dasu, ga duk wadda muka je muka dawo lafiya dashi, shugaban k'asa ya ce zai bada gagarumar kyauta wacce zata girgiza mutum, dan haka mun zab'i Doctor Anam had'e da Doctor Halisa sai kuma Doctor Asiya sai kuma ni da za'ayi tafiyar".


Shuru wajan ya d'auka kamin kuma a fara y'an k'ananun maganganu, wasu sunji haushin cewa bada su aje ba, domin jin cewa ai shugaban k'asa yayi albishir d'in zai bada gagarumar kyauta, kyautar ce kawai da suka ji za'a bada ta rud'e su, sai cece kuce suke akan wa'inda aka yanke dasu za'aje, wasu ma kai tsaye suke maganar son kai aka nuna a cikin wa'inda aka zab'a za'ayi tafiyar dasu.


Sai da Doctor Fahat ya d'an buga table d'in dake gabansa, sana suka yi shuru.


"Idan akwai wadda yake da magana k'ofa a bud'e take, ga duk wadda aka zab'a idan baida ra'ayin zuwa zai iya fad'a a canza wani a madadinsa".


Kowa shuru yayi domin wa'inda aka zab'a kowa dama so yake aje dashi.
Doctor Sa'adha ce ta tab'e baki ita ce farkon tashi ta fice daga d'akin taron tana jin zafin ba'a sa da ita ba a tafiyar.


Doctor Asiya ce ta take mata baya, domin suna d'asawa da ita.


"Haba k'awata ya da haka Kuma?, ba'a gama taro ba kin tashi".


Tsayawa Sa'adha tayi tana kallon Asiya kamin ta ce.


"Dole zaki ce haka man, tunda kin san an zab'e ki a tafiyar".


"Noo wallahi na so asa dake a ciki, amma dan Allah kiyi hakuri, ni kwata-kwata ma jikina ne yayi sanyi, kamar na ce ma fasa zuwa ma, kinga fa inda zamu kamar lahirarmu ce muka kai kanmu, kinji bayanin da Doctor Fahat yayi ai?, wa'inda suka kamu da Cutar fa cin naman mutum suke da ransa fa, abun ya d'an so ya bani tsoro, ba dan naji za'a bada number yabo ga duk wa'inda akai tafiyar dasu aka dawo lafiya su za'a basu kyauta had'e da number yabo, wallahi da ba abunda zaisa na amince ayi tafiyar dani".


Wani tsaki Doctor Sa'adha ta saki tana bankama Doctor Asiya harara, tayi gaba tabar Asiya da sakin baki.


Au yanzu haushinta take ji duk bayanin data tsaya tayi mata?, gani take kamar bak'in ciki Sa'adhar ke mata dan kawai an zab'e ta, ita kuma ba'a ce da ita ba.


Tab'e baki Asiya tayi tana d'aga k'afad'arta, alamar Doctor Sa'adhar taji dashi dai.


______________________
*Umaru Musa Yar'Adua Airport Katsina State Nigeria*


Gaba d'aya Hukumar Sojojin Nigeria ne had'e da Kwararrun Likitoci wa'inda aka tantance zasu tafi zuwa K'asar Goa, wadda K'asar Goa d'in ta riga da tasan da zuwansu a yau d'in, sosai kuma suka jinjinama Nigeria d'in a bisa taimako na farko da aka fara kowa masu, Nigeria ce ta farko wacce ta fara amsa zata turo mutananta domin taimakon k'asar.


An riga da an shirya tarbarsu a can, da duk kayan aikin da zasuyi anfani dashi.


Da sun sauka kai tsaye gidan shuban K'asar Goa d'in za'a sauke su, domin a fadar shugaban k'asar ce kawai Zombies basu gama cimmata ba, amma suna gaf shiga fadar shi yasa suka nemi taimakon K'asashen duniya.


Jirgin Sojojin Nigeria ne ya fara tashi kamin kuma Jirgin Doctors nasu Anam ya d'aga sararin samaniya shima.


Su Anam jirginsu na d'agawa ta kama sauke ajiyar zuciya, jin wani bala'in tsoro yana rufe mata gangar jiki, kai bama ita d'aya ba dukkansu sai yanzu ne suke jin anya basuyi gaggancin amincewa shiga K'asar da annoba ta gama halaka mutanan cikinta ba kuwa?.


A wajansu Harun ma kusan hakane, Abbakar kuwa akwai bak'in k'uduri a ransa na son kawo k'arshe Captain Harun a wannan tafiyar yayi ma kansa al'k'awarin bazai tab'a bari Harun ya dawo da ransa ba............




*Tofa jama'a masoya na masoyin wannan book d'in nawa, laifin dad'i aka ce k'arewa, a nan duka-duka na kawo k'arshen Free pages, Maza-maza ka-ki tura kud'inka domin karanta ci gaban labarin, yaya za'a kwashe a wannan tafiyar dasu Captain Harun suka yi had'e dasu Doctor Anam?, shin zasu dawo da ransu kuwa?, shin wai ma zasu had'u da y'an uwansu a k'asar Goa?, K'asar da ke da yawan jama'a, ya za'ai su fara neman su lokaci d'aya?.*
*Kai nima fa zanso sanin ya zata kasance a wanga book wallo.*




*GAWA TAFE, NA KUD'I NE AKAN NAIRA D'ARI HUD'U KACAL #400, DAGA EPISODE 9TO10, ZAI TSAYA FREE PAGES D'IN, KARKU BARI A BAKU LABARI, SALON LABARIN NA DABAN NE, BA SAI NA TSAYA INA MAKU DOGON SHIRHI BA, KUMA KUN RIGA DA KUN SAN AL'K'ALAMINA BAYA RUBUTUN BANZA*




*Zaka iya turo kud'inka ta wannan number d'in*👇
8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank


Saika turo shaidar biya ta wannan number d'in 👇
08130479973

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login