Showing 15001 words to 18000 words out of 20241 words

Chapter 6 - GAWA TAFE Book Complete Hausa Novels Writing by Mrs Sufi.txt

02 Feb 2025

2163

Motar yana komawa daga bayansu cikin hikima, k'arfe ya samu ya daddage iya k'arfinsa ya rink'a sauke masu shi a bayansu wani a tsakiyar kai, nan take suka zube a sume, domin su kansu su Faruk d'in sun lura idan ba b'are masu kai kayi ba ya rabe gida biyu, to kuwa ba mutuwa suke ba, suma ne suke kawai da an d'auki lokaci zasu tashi.


Sauke k'arfen yayi yana sauke ajiyar zuciya yana dafe da bayansa, sai jan iska yake a bakinsa, suna kallonsa cike da tausayi.


Shiga motar sukai gaba d'aya, sai Doctor d'in nan dake tsaye bai da alamar ma zai shiga motar sai hawaye yake, ga Zombies dake sun rufe unguwar a yanzu, domin duk inda wani mutum yake kamar k'amshinsa suke jiyowa duk nisansu dashi kuwa k'amshin zai kai har inda suke.


Suna kallonsa Al'ameen ya kwala masa kira, zaro ido sukayi ganin Doctor d'in nan wacce Zombies suka gama bidirrinsu da ita, ta mik'e ta koma Zombie itama.


Jikinsu ne ya kama rawa ganin duk yadda Zombies d'in nan suka ji mata ciwoka a jikinta duk d'aukarsu mutuwa zatayi amma ji yadda ta mik'e itama ta zama irinsu.


Suna gani Doctor d'in nan ya nufi inda yake yana hawaye yana tsaye inda take, harta k'araso ta cin masa kawai ya wani rungumeta, ita ko dai-dai wuyansa ta kafa masa wani uban cizo tana wani irin gunji had'e da gurnani.


Juyowa tayi dashi saitin da suke, suna jin ihunsa had'e da mik'a hannunsa yana alamar a ceceshi, sai ihu yake ita kam har lokacin bakinta yana wuyansa sai tsotsar jininsa take had'e da yago fatar wajan tana ci.


Yo ko kallonsa sun sake yi, Faruk ya tayar da Motar jin su Jasmin suna cewa.


"da'aAllah Faruk ja mota muje, kaji d'an rainin wayo Malam, a sadda muke kiransa ya dawo mu tafi ba k'i yayi ba, sai da yaji azaba zai wani nuna a taimakesa yake, ai ga k'auna nan ya gani, nikam banga wadda zai zama Zombies ba na kashe kaina akansa ba wallahi".


Gaba d'aya samarinsu ne suka dubesu, ba wadda ya sake magana, dan suma kusan zan iya cewa abunda ke zuciyarsu kenan, kowa tashi ta fishsheshi ake kawai.


Wani irin matsiyacin gudu Faruk keyi dasu, dan duk inda suka bi suka wuce Zombies ne keta shawagi a cikin garin Goa, sai mutanan da baza'a rasa ba a mab'oya, amma duk wadda idonka zai gane maka shi a tsakiyar garin to ya riga da ya zama Zombies.




Wani munafikin burki Faruk yaja har saida su Farida
Dake baya suka bige da jikin Motar. Hanan dake dafe da goshi inda ta bige ta d'ago tana niyar magana kawai idonta ya hasko mata wasu dondonzon Zombies da suka tare masu gaba, yawansu ya zarce masali ma, dan tsananin yawansu basa jin zasu iya bi ta kansu.
Ko wanne ka kalla daga cikinsu ido a waje ga wata irin zufa data rufe masu jiki gaba d'aya, yadda kasan an watsa masu ruwa a jikinsu.
Kowa ya kasa magana sai bakunansu dake bud'e a hangame tsabar tashin hankali.


Anjali ce tayi k'arfin halin fisgo magana daga bakinta tana cewa.


"Faruk kabi ta kansu kawai, Allah zai bamu ikon wuce su da yardar shi".


Tayar da motar yayi yana bata wuta, sosai yaja da baya kad'an kamin ya jata da k'arfi yabi ta kan Zombies, amma duk da haka wasu sun watse wasu ko sai da suka manne a jikin Motar.


Sai da ya rink'a jijjiga motar had'e da samin wata bishiya ya rink'a goga motar a jiki ne wasu wadda suka mak'ale suka zube suna wani irin ihu.


D'aga kai Farida tayi jin yadda wani Zombies ke buga tsakiyar motar da suke ciki yana daga can samanta ya mak'ale sai gunji yake da gurnani kamar wani Zaki.


Faruk yaja birki bai tsaya ba, cike da kwarewa ya rink'a juyo da Motar wai dan dai Zombie d'in nan daya mak'ale ya fad'o k'asa, duk sun jigatu sun wahala, saboda uban gudun da ake dasu, gashi sai wurwura su ake cikin Mota, da kyar Allah yasa ya fad'o ta gaba Faruk bai tsaya ba yabi ta kansa ya latse suna iya jiyo ihunsa.


Gaba d'ayansu sauke ajiyar zuciya sukai, duk da sun san zasu iya gamuwa da wani iftila'in zombies d'in a gaba, domin sun san duk inda zasu shiga a yanzu Zombies sun gama karad'e gaba d'aya K'asar Goa.


Motar ce kawai suka ga ta tsaya tak'i baya bare gaba, Faruk sai sun tayar da ita yake amma ina.


Wani tsaki Faruk ya saki had'e da kai ma sitiyarin Motar wani naushi yana cewa.


"Ohhh My God, mai d'in Motar ne ya k'are, ya kamata muyi hanzarin sauka daga cikinta, kar wata masifar ta rufe mu muna ciki".


Ai kamin ma ya dire maganar gaba d'aya sun b'alle marfin Motar suna ficewa daga cikinta.


Sai da suka gama sakkowa suna dube-duben inda ya kamata su fara nufa a yanzu kuma.


Wani company nin yin shinkafa suka ci karo dashi Al'ameen ya nufi wajan yana fad'in.


"Kuzo muje ko mun d'an huta a cikin wancan Company d'in da nake gani a gabanmu".




"Kai kam Al'ameen ai bamu ga hutu ba, ni wajan ne ma bai wani kwanta min ba, dan Allah mubar wajan nan".


Fad'in budurwarsa dake mak'ale dashi, sai wani waige-waige take, idonta a waje na tsananin tsoro.


Ko magana bai mata ba suka biyo bayansa domin suma a mugun gajiye suke.


Shiga sukai cikin Company nin suna kallon irin illar da Zombies sukai a cikinsa, kusan GAWA tafi a k'irga suka rink'a cin garo da ita ta mutane gasu nan cikin jini, gashi wajan yayi wani irin shuru sai wata iska dake busuwa a wajan, wacce saita sa mutum tsorata dan ji kake shuuuuuuuuuuuuu kamar kana cikin Mak'abarta nan, kai gaba d'aya ma garin haka ya koma.


A hankali Farida ke tsallake Gawar mutane tana ware idonta waje, zuciyarta na bugawa wasu hawaye na tsananin tausayin kanta dama wa'inda suke tare dasu, duk da tasan sune suka ja masu wannan shiga masifar.
A haka kuma idan ka ce zakai magana su ce zasu rufe ka da fad'a, sufa ta lura ma wasu daga cikinsu har yanzu ba nadama a tare dasu.


Kamar jira ake Farida ta tsallake wata Gawar mace dake yashe a k'asa.
Budurwar Al'ameen ce a bayanta, ta zo tsallaka gawar da Farida ta tsallake kawai kamar saukar aradu gawar nan ta tashi tana rarumo k'afar budurwar tana k'ok'arin kai mata cizo.


Wani uba-uban ihu ta saki wadda yasa gaba d'ayansu toshe kunnuwansu, domin ihun da mugun k'arfi ta sake sa, wani irin ihu take tana kiran sunan Al'ameen.


Duk ya gama rud'ewa ya rasa ta inda zai fara kawo mata d'auki shima.


Su Jasmin ko da Hanan k'ara matsawa suke daga inda suke suna dafe da k'irjinsu dake bugawa sosai na tsallar tsoro da wata irin razana da sukai.


Wata k'arar ta kuma kwalawa a sadda taji saukar hak'oran matar akan k'afarta, wani shegen zafi da rad'ad'i ne yayi ma Kwakwalwar kanta dirar mikiya, ta saki wata k'arar tana kiran.


"Wayyo Allah na shikenan ta kashe ni wallahi, shikenan nima na koma irinsu, na shiga uku wannan wacce irin masifa ce, Allah ya isa tsanina dakai Faruk duk kaine silar shigowarmu wajan nan, ashe ajalina na cikin wannan company nin, wayyo Allah na, wayyo wayyo wayyo".


Matar ce ta mik'e tana gunji kamar Mage ta samu b'era tana niyar sake kai mata wani cizon suka ji k'arar saukar wani k'arfe da Al'ameen yayi nasarar samu a wajan basu lura ba ya kwad'a mata shi a a tsakiyar bayanta, tana sake juyowa garesa tana niyar kamosa shima tana son kai masa cizo had'e da d'an wani ihu da gunji irin nasu na Zombies idan suka ji azaba.
Ya d'aga abunda ya kwad'a mata ya sake kwad'a mata shi a tsakiyar kanta, sai a lokacin ta zube a sume.


Kamo hannun Budurwar tashi yayi yana mik'ar da ita.
Sai aikin kuka take domin ita kam tasan nan da wani lokaci zata koma Zombies.


Wani kallo Jasmin take binta dashi batai wani nauyin baki ba wajan cewa.


"Tsakani da Allah Al'ameen asan yadda za'ai da wannan budurwar taka, Fisbilillahi wallahi bazata zauna damu ba, haka kawai bamu ankara ba ta zama irinsu ta zo ta ce zata farmaki wani daga cikinmu, nifa gaskiya a yanzu ban yarda da kowa ba, tunda k'anwarku ta mutu, to ya kamata kowa ma aka ciza to ku kyale shi kawai wallahi".


Rushewa da kuka budurwar tayi tana bak'in cikin abunda Jasmin ke fad'a.


A zuciye ta nufi inda Jasmin take tsaye tana cin kwalar rigarta tana cewa.


"Ashe Jasmin kece mutum ta farko da zaki fara gudu na?".


Wani d'an iskan kallo Jasmin ta jefa mata, tana saka hannunta ta yakice ta daga jikinta, tana nunata da yatsa ta ce.


"Karki sake wannan jikin naki ya ce zai sake tab'a jikina, kuma baki ji miye na ce tun muna a cikin mota a hanyarmu ta zuwa wannan wajan bane?, ke ko uwata ce ke na rantse da Allah yau sai mun raba hanya dake, bare babu uwar da muka had'a dake".


Cike da tsananin mamakin Jasmin Farida ke kallonta, tana zare ido waje, uwafa?, anya Jasmin nada hankali kuwa?, bata gudun itama gobe a cije ta?, amma ta manta da hakan, sai wani tayar da jijiyoyin wuya take, sai ka ce tana da tabbas d'in ita Zombies d'in Allah ba zai basu sa'ar su cije ta ba.


Cike da bak'in ciki da jin zafin Jasmin budurwar ta wanke ta da wani Mari, wadda Jasmin ta zabura a kid'ime domin Marin yazo mata a bazata ne, bata lura da lokacin data d'aga hannu ta kai mata marin ba.


Dafe k'uncinta tayi tana fiddo idonta waje bata tsaya b'ata lokaci ba wajan d'aga hannunta itama tana sauke mata wani gigitaccan mari har biyu wadda ya ci uwar nata zafi wadda tayi mata.


Ganin suna son had'a jiki suyi dambe yasa Al'ameen shiga tsakiyarsu ransa a mugun b'ace yake cewa.


"Wai mi yasa ku mata k'aramin tunani ne da ku?, miye abun fad'a muna cikin wannan halin?".


Nunata Jasmin take da yatsa a yadda take magana zaka san lokaci d'aya ta tsani budurwar Al'ameen d'in, fad'i take.




"An gaya miki ni sakarya ce dolowa irinki, da zan tsaya ki mare ni ban rama ba, ai ko ko uwar data haifeki tayi kad'an ta ce zata mari Jasmin bata mara ba, ki kiyaye a nan gaba".


Abu biyu ya taru yayi ma Budurwar nan yawa ga zafin cizon da aka danna mata, ga bak'in cikin ta kusa komawa Zombie, ga kuma tsanar Jasmin da take ji idan batayi sanadiyar zamowar Jasmin Zombie ba, ko tayi sanadiyar mutuwarta, to gaskiya bata haifo ba, hankalinta bazai tab'a kwanciya ba.


Wani kukan kura Budurwar tayi, Jasmin bata ankara ba Budurwar ta kamo wuyan Jasmin dai-dai fatar wuyanta tasa farce ta yakoshi Jasmin d'in, wacce bata lura da yakoshinta tayi ba, dama gashi tana tara farce zak'o-zak'o a hannunta.
Kuma dama tasan tunda yanzu jinin jikinta ya gama kamuwa da cutar, to tana da tabbacin idan ta yakoshi mutum a yanzu zai iya zama Zombies shima a ko wanne lokaci.


Jasmin zata kai mata duka a baki Faruk ya hankade Jasmin daga wajan, har yanzu Jasmin bata ji wani zafi ko rad'ad'in ciwon da Budurwar ta ji mata ba.


Fahimtar hakan da budurwar tayi ta saki wata shegiyar dariya, wacce tasa su Farida mamakinta, kai har Jasmin d'in, batayi gigin nuna mata wata illa da tayi mata ba, sai ma nunata da take da yatsa tana dariyar tsananin mugunta.
Gaba d'aya Jasmin sai taji ta tsargu, ta kama duba jikinta, amma babu abunda ta gani a jikin nata.


Kamar jira ake kawai sukaga budurwar an fyad'ata da k'asa, jaa da baya suka kama yi gaba d'ayansu, suna kallon yadda take komawa lokaci d'aya, jikinta ya kama sauyawa yana komawa color blue, jijiyoyin jikinta sun fito rud'u-rud'u, fatar jikinta ta koma ruwan toka.
Farida tana kallon yadda take wage baki tana ihu lokacin da k'asusuwan jikinta ke kakkaryewa, hak'oranta sunyi wani masifar tsini, na gaban bakinta.
Wata irin mik'ewa tsaye tayi tana layi, kanta ya jirkice kafafuwanta ma haka.
Da gudu suka fara ficewa daga company nin, kusan zan iya cewa Jasmin ce farkon arta na kare.
Sauran suka take mata baya.
Kamar jira ake su fara fita, suka fara ganin Zombies masu yawa suna fitowa daga wasu sassa na company nin, kota ina kamar zaro su ake suna fitowa suna niyar fitowa daga cikin company nin.
Faruk ne yayi azamar idasa ficewa kusan shine k'arshe, yasa iya k'arfinsa yana son rufe k'ofar company nin, domin idan wa'innan Zombies d'in suka fito da suke gani suna b'allowa daga cikinsa, to komai na iya faruwa.
Al'ameen ma ya taimaka masa da kyar suka datse k'ofar Zombies na gaf k'arasowa wajan k'ofar.
Suna jin lokacin da suka iso bakin k'ofar suna bubbuga k'ofar a hankali suna suna girgiza k'ofar da son b'allata.
Kamar ance Faruk ya waiga yaga wani k'aton duram mai cike da fetur a cikinsa.


Da sauri ya k'arasa inda yake yana ma Al'ameen alamar ya taimaka masa.


Bai san abunda yake nufi ba, sai da yaga Faruk d'in yasa inda duram d'in yake iya k'arfinsa ya jirkitar da Duram d'in fetur d'in da ke ciki ya fara malale k'ofar Company nin.
Ja da baya suka soma yi sosai Faruk ya d'akko wani dutse na k'ank'ara iya k'arfinsa ya irink'a had'e dutsen da d'an uwansa, suna bada wani sauti, can saiga wuta suna kawowa, idan ya had'esu waje d'aya.

Suna bada wutar yayi tsalle ya jefar dasu a cikin fetur d'in daya malale a k'asa.


Ai ko nan take wuta ta fara ci a wajan, kamar wutar daji ta fara kamawa da yawa tana nufar cikin company nin.


Suna tsaye nesa da wajan suna gani a sadda wutar ke k'ara ci sosai harta kama cikin company da yawa suna iya jiyo ihun Zombies dake ciki, had'e da kururuwarsu.


Wutar har wani tashe take sama, saboda zuwa lokacin ta gama kama gaba d'aya wajan, har sai da su Faruk d'in suka had'a da d'an gudu suna son barin wajan................




*GAWA TAFE, NA KUD'I NE AKAN NAIRA D'ARI HUD'U KACAL #400, DAGA EPISODE 9TO10, ZAI TSAYA FREE PAGES D'IN, KARKU BARI A BAKU LABARI, SALON LABARIN NA DABAN NE, BA SAI NA TSAYA INA MAKU DOGON SHIRHI BA, KUMA KUN RIGA DA KUN SAN AL'K'ALAMINA BAYA RUBUTUN BANZA*




*Zaka iya turo kud'inka ta wannan number d'in*👇
8130479973 Fatima Rabi'u Opay bank


Saika turo shaidar biya ta wannan number d'in 👇
08130479973


*GAWA TAFE*
(Zombies story)
On2025




*©Zahra Royal Star*






*ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION*




*EPISODE 9TO10*
*END OF FREE PAGES*






*G.R.A. Estate Residential Area, Katsina State Nigeria*




*ANAM POV*




Da mugun gudu Anam ta sakko k'asa tana duban Mom dake tsaye hankali a tashe rik'e da waya a hannunta, sai kiran waya take amma ana cewa wayar a kashe.




"Mom wallahi nima sai kiran wayar Hanan nake ita da su Faruk amma a kashe, ya za'ai su bi su kashe wayoyinsu wannan wane irin hauka ne haka Mom?".


Mom dake cikin halin rud'ani itama ta sake gwada kiran nasu again a kashe, sauke wayar tayi kawai tana dafe kanta ta kalli Anam tana cewa.


"Please Anam ina cikin rud'ani, ki barni da abunda nake ji, gaba na fad'uwa yake amma kinzo kaina sai hayaniya kike min".


"Haba Mom nima fa hankali a tashe yake, ya kamata ace tun sadda suka isa su kira mu ko?, amma har yanzu shuru"




D'aga kanta Mom tayi ganin Dad ya shigo Parlon a rud'e yana kallon Anam duk ya rud'e yana cewa.


"Maza-maza Anam kunna min Tv, an kira ni waya wai na kalli Labarin duniya na yanzu da ake haskawa akwai matsala da alama".


Gaba d'ayansu gabansu ne ya yanke ya fad'i bare Mom ido a waje take bin Dad da kallo ta kasa cewa komai.




Hannun Anam na rawa ta d'akko romot tana kunna Tv had'e da kamo tashar labarin duniyar.


Muryar mai labaran ce ta karad'e parlon a inda yake cewa.


"A labaran namu na yau zaku ji cewa a K'asar Goa wata muguwar annoba ta kunne kai a gabashin k'asar gaba d'aya, a inda yanzu haka cutar na dad'a yad'uwa kamar wutar daji, a inda shugabannin K'asar ke bada labarin cewa suna buk'atar taimakon K'asashen dake kusa dasu, kai harma da K'asashen duniya baki d'aya, a inda suke buk'atar kwararrun Likitoci wa'inda suka kware ta fannin aikinsu, domin suna son gano maganin da zai warkar da wannan Cuta, sai kuma buk'atar Sojoji wa'inda suka kware ta fannin yak'i domin yak'in wa'inda suka riga da sun gama kamuwa da ita wannan annobar, wacce idan mutum ya kamu da ita cutar yake cin naman mutum d'an uwansa. To sai dai muce Allah ya kyauta, kuma Allah yasa K'asashen duniyar suji Koken K'asar Goa domin tallafa mata wajan iyakance wannan annoba data riske su in.......
Kamin ma su idasa jin k'arshen labarin Mom ta sulale a k'asa a sume.
Anam dake kusa ta lura da ita ce ta saki wata gigitacciyar k'ara had'e da bazawa da gudu tana tarbo Mom a jikinta.


Kuka ta rushe dashi tana jijjiga Mom.


Dad kansa ya d'auki zafi yama rasa miye ya kamata ya farayi, dole su zauna da Gwamna da kuma, shuban K'asa, asan yadda za'ai suma su tura Sojojinsu had'e da Doctors domin cuto Y'ay'ansu dake a K'asar Goa.


Zufa kawai ke yanko ma Dad ba shiri ya cire babbar rigarsa, ya nufi inda Mom take da hannunsa ya kinkimeta sai waje.


Mutanan dake cikin gidan, ganin Dad ya fito da Mom a hannunsa bata motsi, yasa gaba d'ayansu rud'ewa ga Anam dake biye a bayansa sai rusa uban kuka take kamar wacce aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login