Showing 42001 words to 45000 words out of 84748 words

Chapter 15 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.pdf

23 Mar 2025

4972

her clothe ya yi mata naked ya tsaya yana kallon nakedness
d'inta.....he wearing a wicked smile duk lokaci da yaso yaci zarafinta kwanciyar wulakanci yake
da ita cikin muryar kuka momma ta ce don Allah Jarumi kayi hak'uri....don't treat me like this"
"Ya d'ago da fuskarshi da ke lullu6e da masks ya ce "you made a huge mistake na sanarda
wani sirrina don haka ina da damar da zan yi treating naki yadda nakeso.
"Tana ji tana gani ya shiga sarrafata kuma irin na mugunta d'inan ga momma jiki yafara nauyi
dama makeup ne yake 6oye tsofanta....lol.
Haka ya Jarumi ya cigaba da shagalinshi ita kuma tana kwance kaman gawa saida ya yi son
ranshi, sannan ya barta abin takaici ta tashi ta tsinto tufafinta da ya zubar a k'asa tasaka.
"Cikin kaukausar murya yafara magana wato yanzu na fahimci reni yafara shiga tsakanina da
ke Zaituna, kin manta waye ni da Kuma abinda zan iya aikatawa idan mutum ya kuskure min.
Zan miki gargadi na k'arshe wallahi.....wallahi Zaituna kinji na rantse idan kika sake plans dina
na tsawon shekaru masu yawa ya rushe ki saka aranki kin zama gawa.
"Da mugun tsoro momma take kallonshi, shi kuwa ko a jikinshi ya cigaba da zazzaga mata
ruwan bala'in.
Tunda na fahimci kwakwalwarki batada amfani na canza plans d'ina ba kuma zan sanarda ke
ba, saidai na baki umarni ki bi idan kuma kika kuskure sai na lahira yafi ki jin dad'i tashi maza ki
6acemin da gani tsohuwar banza tsohuwar kilaki.
"Ta tashi jikinta yana rawa ta dauki car key d'inta tafice cikin wani irin tafiya kaman wacce tayi
tangard'e.
"Tana shigowa main parlour ta iske Daddy tare da Teema zaune yana sauraren shirmeta,
suna arba jikinta ya dauki mugun rawa kaman daga sama taji sautin muryarshi yana cewa
"Zaituna daga ina kike?"
"Cikin rawar murya tafara magana abinka da marar gaskiya Du.....biya.....
Dubiya?"
Ya tambaya sounding very angry momma ta gyad'a kanta.

"K'arya kike yi Zaituna ba daga dubiya kike ba, koma daga ina kike Allah yana ganinki.
Daga haka bai k'ara furta uffan ba ya dawo da ganinshi akan Teema.
"Momma tayi shiru saboda babu bakin magana, jikinta sanyi lak'asss.....ta nufi upstairs yayin
da Daddy yabi bayanta da kallo yana jin wata irin tsanarta tana haurowa a k'asan zuciyarshi.
*****---****----*******
"Tun daga dowawarsu daga asibiti yake zaune a gida bai sake fita ba, sai kulawa ta
musanmman yake bata.
"Ko motsi kadan tayi sai ya tambayeta hannu ne?"
Ita kuma ta gyad'a kanta har wani sabuwar shagwa6a ta tsiro da shi ta dinga matsar hawaye
k'arya.
"sallah kadai ke fitarda shi daga gidan, lokaci da ya dawo daga sallar isha'i ya bi ta flat d'in
momma domin ya sanarda ita barrister A ta k'one.
"Koda ya shigo bata falon k'asa sai kawai ya nufi bedroom d'inta da ke upstairs ya sanarda ita,
ba yabo ba fallasa tayi mishi fatan Allah ya bata lafiya ba.
Falon Daddy ya wuce ya isa ga kujera ta kusa da wacce Daddy yake zaune ya zauna yana
gaidashi "Daddy barka da hutawa!
"Ya amsa da yauwa sultan ya jikin matarka?"

Taji sauki Daddy!

Madallah ka kula da ita sosai.

"Insha Allah Daddy!
Daga haka suka yi shiru yayin da Aliyu yake karantar yanayin mahaifin nashi, sai yaga kamar
akwai damuwa atattare da shi ya ce "Daddy naga kamar akwai abinda ke damunka,
musanmman lokaci da na shigo sau uku ina sallama kafin ka ji kayi nisa a tunani "don Allah
Daddy meke damunka?"
Asanyayye Daddy ya yi murmushi ya kalle d'an nashi ya ce "ba komai sultan gajiya ce kawai.
Kallonshi kawai Aliyu ya yi amma ba don ya yarda ba, ya mik'e had'e da cewa sai da safe
Daddy!
Har ya kai bakin k'ofa Daddy ya kirashi sultan...!
Na'am Daddy amsa had'e da juyowa.
Zo nan.
Daddy ya yafitoshi da hannunshi na dama.
''Dawowa ya yi ya zauna inda ya tashi yana kallon mahaifin nashi atsanake.
"Sultan inaso kayimin wani alk'awali ko bayan raina bazaka warware shi ba.
"Inajinka Daddy!
Cewar Aliyu cike da fargaba jin abinda mahaifin nashi zai fad'a.
Sultan inaso kayi min alk'awali komai runtse bazaka rabu da matarka ba, za ka zauna da ita
cikin dad'i ko akasin hakan.
Murmusawa Aliyu ya yi yana shafar gemunshi ya ce "Daddy idan wannan ne bakada matsala
da ni, nayi maka alk'awali komai wuya komai dad'i ina tare da Amina.

"Masha Allahu.....yarona naji dad'i wannan furuncin naka Allah ya yi maka albarka, ya baka
ikon rik'e alk'awali.
Aliyu ya amsa da ameen summa ameen!
Cike da farin ciki Daddy ya ce tashi ka tafi ka gaida min da ita, kafin na shigo da safe na dubata.
Za taji Daddy!
Ya tashi yafice.
Lokaci da ya shigo bata falon k'asa sai kawai ya wuce d'akinshi ya yi wanka, ya shirya cikin
pyjama saidai bai rufe bottoms d'in rigar ba sai uban k'amshin dolce & gabbana perfume yake yi
kai tsaye bedroom d'inta ya nufa alokaci har tayi wanka tana sanye da cotton night gown mai
d'an siriri hannu wacce da kad'an ta wuce cinyoyinta. "Yana tura k'ofa ta d'ago suka had'a idanu ya yi tsaye jikin k'ofar, yana aika mata da shu'umin
kallo.
Kasa jure kallon nashi tayi sakamakon wani irin bugawa da zuciyarta ke yi.
Ya k'araso ya iso gabanta ya durk'usa, ta shak'i dadd'add'en k'amshin turarenshi wanda gaba
d'aya ya lullu6e k'ofufin hancinta ta lumsashe idanuwanta. Hannunta mai ciwo ya rik'o yana
kallon ciwo, kafin ya dawo da ganinshi akanta cikin tattausan lafazi ya ce "ya kike jin hannu
yanzu?" Rausayarda kanta tayi tana kallon wani gun daban, ta ce da sauki.
"Murmushi ya yi had'e da mik'ewa tsaye batare da dauke idanuwanshi akanta ba ya ce "tashi
muje kici abinci.
Nagode Yalla6ai amma bana jin yunwa.
Tafad'a had'e da sadda kanta k'asa.
"Ya 6ata fuska sosai alamar ranshi ya6aci, duk da haka sai ya tsince kanshi da controlling anger
nashi ta hanyar sassauta murya alamar rarrashi ya ce "ki daure Amina ko kad'an ne kici idan
baki ci ba, bazan zan ji dad'i ba.
Yadda ya yi magana ya yi masifar burgeta tayi murmushi had'e da mik'ewa ya wuce gabanta ta
bishi abaya.
"Da kanshi ya yi mata serving da yake ga hannunta na dama ta k'one sai ta rik'e spoon da
hannun hagu, saidai bata taji dad'in rik'on spoon d'in ba.
"Gani haka yasa ya kar6i spoon daga hannunta ya shiga feeding d'inta, goganyar taku ta
bud'e ciki ta narki abinci kaman ba ita bace ta ce ta k'oshi.
ragowar abinci da ta rage ya ci sai faman kallonshi take yi idan ya d'ago suka yi four eyes,
tasake mishi murmushi shima ya mayar mata da martani murmushin nata.
Yana kammalawa ya tattare plates ya kai kitchen.
Ya nufo cikin falo idan ya hangota zaune maganinta ya dauko da bottle d'in ruwa, ya bata tasha
sai faman yatsine fuska take yi shi kuma yana mata sannu.
Around 10:30pm tayi mishi sai da safe ta nufi bedroom d'inta bata jima da kwanciyar ba,
bacci ya yi awon gaba da ita.
Aliyu ya jima zaune har lokaci kwanciyarshi bacci ya yi, ya mik'e ya koma bedroom dinshi saidai
sam ya kasa bacci sai faman juyi yake yi, nan take tunanin ya fad'o mishi bai kamata ya barta
ita kadai ta kwana ba, dole ya kasance tare da ita karta falka tsakiyar dare ta buk'aci ruwa ko
wani abun daban. daga k'arshe ya tashi ya nufi d'akinta ya tasaki sa'a bata rufe da key ba.

Yana murd'a handle k'ofar ta bud'e ya kutsa kai, duk da d'akin yana dauke da diff light hakan bai
hanashi gani kyakyawar fuskarta ma'a6ociya kwarjini ba.
"Sam bai yi tunanin kwanciya kusa da ita ba ya dauki two pillows ya jefa kan rugs carpet ya
kwanta, sai dai kuma ya kasa bacci domin wannan shine karo na farko da ya kwanta ad'akinta,
ya jima sosai kafin ya samu bacci ya dauke shi.
"Can tsakiyar dare ta falka don ta gyara kwanciyarta ta shak'i k'amshin turarenshi da ya
gauraye d'akin, ta tashi zaune ta hango shi kwance kan carpet da sauri ta yaye duvet da ke rufe
da jikinta ta zuro fararen k'afafunta k'asa, sannan ta mik'e tsaye ta isa wurinshi ta durk'usa
tashiga bubbuga hannunshi had'e da kiran sunanshi. A hankali ya bud'e idanuwanshi ganinta a durk'ushe yasa ya tashi zaune yana murtsuke
idanunshi asanyaye ta ce "Yalla6ai don Allah tashi ka koma kan gadon ka kwanta.
Ya girgiza kanshi ya ce "ki barni anan ya isa yana k'ok'arin komawa ya kwanta, Ta marairaice
murya kaman za ta fashe da kuka, tasake cewa don Allah yalla6ai ka tashi ba don ni ba.
Ko dai kana tsoro kar na dameka da snoring ne...?ni sai na kwanta k'asa sai kai ka hau gado.
"Murmushi ya yi batare da ya furta uffan ba ya mik'e ya hau gadon ya kwanta, yayin da tayi
tsaye tana kallonshi.
"Zo ki kwanta barrister banaso kallon nan naki mai kama da na tuhuma.
"Tayi murmushi batare da ta musa ba ta isa kusa da shi ta kwanta, yaja duvet ya rufa musu ya
shak'i k'amshin turarenta ya lumsashe idanuwanshi bayan ya sauke zazzafar ajiyar
zuciya.[7/27, 12:04 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA
KUD'I NE IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER* 0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619

DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA

*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```

*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```

*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``

*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN

*SLIMZY*:- IZZATA

*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO

*GIDAN RINA*



*25*


Suna gama waya agurguje ta shiga wanka.
"kafin tashiga bathroom saidai ta nemo disposed cup, tayi fitsari aciki duk da har zuwa lokaci
atsorace take.
Musanmman lokaci da tazo fitsari a cup d'in tana kammala wanka tafito daure da towel ta d'ebo
layoyin inda ta ajiye su ta shiga bathroom ta zubesu a k'asan tiles , jikinta na rawa saboda
tsananin tsoro ta dauko cup d'in fitsari gabanta na fad'uwa ta juye fitsarin akan layoyin, abinda
bai fi 20 seconds ba hayyak'i ya turnuk'e gaba d'aya bathroom sai kace gobarar wutar nepa. A rikice barrister A ta balla da gudu ta nufi k'ofar fita.
"Har ta rik'e handle sai kuma taja birki tayi tsaye a k'asan zuciyarta, ta ce bari dai na tsaya
naga abinda zai turewa buzu nad'i.
Masu iya magana nacewa matsoraci bashi gwani.
Yayin da hayyak'i ya dinga bin window bathroom d'in yana fita da yake gilashi window a bud'e
yake sai net ne kawai arufe, tanan ciki net ya dinga fita har wurin ya washe kaman hayyak'i bai
wanzu ba.
Gani haka yasa barrister A tadawo cikin bathroom din ga mamakinta sai taga babu layoyin, sun
zama hayyak'i.
"Naunauyar ajiyar zuciya ta sauke tana mamakin faruwar wannan al'amari, sai yau tak'ara
yarda da furuncin malam bahaushe da yake cewa tsafi gaskiyar mai shi.
Ba shakka irin wannan sihiri sai mai k'arfin imani sai kuma wanda Allah ya tsare.
"Ruwa zafi ta d'ebo ta wanke wurin duk da haka saida ta kunna tap na ruwan sanyi tak'ara
wanke wurin sannan tafice.
"kayanta tasaka tayi sallah had'e da neman tsarin Allah daga shed'anun aljanu da mutane.
Tana zaune downstairs falo su Zee-zee suka dawo daga school ko apartment d'insu basu shiga
ba suka yo nata, sosai tasake musu fuska anan suka ci abinci sai santi da yaba mata suke yi.
"Cikin siga ta kwarewa da aikinta take tambayarsu dangane da ciwon Teema, basu kawo
komai aransu ba suka shiga bata labarin duk abinda suka sani akan ciwon nata, har magani da
momma take bata mai wari saida suka gayamata.
"Tattara bayanan nasu tayi ta adana a kwakwalwarta.
"Kamar yadda tafaru jiya hakan ne yasake faruwa, lokaci sallar la'asar ya yi tai sallah su kuma
suna zaune suna kallo.
"A wannan karon tasha alwashin tambayarsu, kasancewar lamarin gidan yanzu ya dawo abin
tsoro agareta.
"Yan matan momma dukanku kuna menstruation ne?"
Cikin rashin damu da tambayarta ta Meena ta girgiza kanta, had'e da cewa a'a....me ki ka gani

matar yaya?"
Gani nayi lokaci sallah har yana k'ok'arin wucewa, amma ba ku tashi ku ka yi ba.
"Kusani ba k'aramin bala'in bane musulmi ya dinga wasa da lokutan sallah, especially sallar
la'asar.
"Bambancin musulmi da kafiri shine sallah, miyasa za ku dinga wasa da ita?"
Jikinsu ya yi masifar sanyi kunya ta lullu6esu, da suka tuna ba koda yaushe suke cika sallah ba.
Idan suka yi sallar asuba ba lalle bane su yi azhar da la'asar ba, sai sun zo kwanciya suke yi
sallar isha'i, ranarda suke ji k'arfi sai su ranka gaba d'aya amma zance na gaskiya sallah bata
damesu ba.
"Saboda momma ya kamata tayi musu fad'a sai akayi dace ita ma ba koda yaushe take yi ba,
sai tayi mata dad'i.
Daddy kuma ba mazauni gida bane balle yasan wainar da suke toyawa, kuma uwa-uba suna
da k'arancin ilmin addini.
Gani yana yin da suka shiga yasa barrister A tayi amfani da wannan damar, ta shiga yi musu
nasiha da tsoratar da su da irin azabobin da Allah[S.W.T] ya tanadarwa masu yi wasa da sallah.
Sun tsorata ba kad'an ba sun kuma yi nadama, cike da jin dad'i barrister A ta ce ku tashi ku je
kuyi, ku dage ku rok'i gafarar ubangiji domin shi mai yafiya ne.
"Godiya suka yi mata sannan suka nufi bathroom, domin yin alwala ta bi su da kallon tausayi
saboda tayi imani rashin dace da uwa tagari ne ya janyo musu hakan.
"around 9:30pm Aliyu ya shigo gidan tun safe da ya fita sai yanzu ya dawo, lokaci da ya shigo
main parlour tana d'akinta da ke upstairs bai nemeta ba ya wuce nashi bedroom ya yi wanka, ya
shirya ciki three quarter da rigar armless farare as usual yana k'amshin suave perfume karo na
farko da ya ji yana son ganinta, shiyasa ya nufi d'akin nata ya turo k'ofa ya shiga da sauri ta
waiga waya manne a kunnenta ga alama tana waya koda ya shigo, tsaye ya yi ya jingina jikinshi
a jikin k'ofa yana mata kallon nan nashi na k'asan ido.
"I'll will call you later tafad'a had'e da hanging up, sannan ta dawo da ganinta akanshi "sannu
da zuwa Yalla6ai...bansan kadawo ba ya office?"
Ta ya za'a yi ki sani bayan kina d'aki a k'unshe kamar amaryar k'auye.
Tunda yafara magana bai dauke ganinshi akanta ba.
K'ayattace murmushi ta yi kafin ta ce waya sani ko ni amarya k'auye ce.
Ni dai mu tafi na ba ka abinci maybe ba ka ci komai ba tun breakfast.
Ya tabe baki yana cigaba da kallonta ba ko kyaftawa, mamaki ne ya kamata ko me yake kallo a
jikinta ta bi jikinta da kallo boomshort ne a jikinta sai top mai k'aramin hannu iya cibiyarta bai
k'arasa rufe bombom d'inta ba sai gashinta da ya sha gyara tasake shi ya sauka a shoulders
d'inta, iya ganinta bata ga wani abu a jikinta da yake kallo ba saidai in reni hankalinshi ne ya
motsa.
"6ata fuska tayi ta dubeshi still yana mata mayattace kallonan nashi gira d'age sai taga
kaman yana yinshi ya sauya a zaman da tayi da shi bata ta6a ya yi mata irin wannan kallon ba.
"Yalla6ai.....lafiya"
Da sauri ya kauda fuska had'e da furta nothing"
"Cike da mamaki ta ce "nothing....then why are you looking at me like stranger?"
juyawa ya yi batare da ya bata amsa ba, jikinta ya yi sanyi kodai akwai laifi da tayi mishi batare
da tasani ba.

"ko don ya ganta da bomshort ne?"
Ta6e baki tayi da tayi niyyar doura kimono akan kayan nata, amma yanzu tafasa ko ba komai za
taji dad'i indan ya cigaba da kallonta.
"Saida tak'ara fashe jikinta da turare sannan ta sauko k'asa yana zaune a dining area talla6e
da kumatunshi, I'm sorry Yalla6ai na barka kana jira tana magana ne had'e da daukar plate tayi
mishi serving ta tura gabanshi.
"Ajiyar zuciya ya yi yana cin abinci lokaci zuwa lokaci yana mata fitinanne kallonshi, mai jefata
cikin wani yana yi abinda yake k'ara daure mata kai idan yana da magana me zai hana ya furta
ba ya fitine ta da kallo ba.
Gani kallon nashi ba mai k'arewa bane yasa ta mik'e za ta bar mishi wuri, ya had'e rai ya ce
ke....koma ki zauna ai ban sallame ki ba.
Ya k'arasa magana yana cije lips dinshi.
Komawa tayi ta zauna ya ce ya akayi ne naga ba ki ci abinci ba, ko kin k'oshi ne?"
D'aga eyebrows d'inta ta yi ta ce bana jin yunwa.
Ya ta6e baki ya cigaba da cin abincinshi, yana kammalawa ta tattare plates ta shigarda su
kitchen ta wanke, koda tadawo main parlour ya koma bedroom dinshi da ke sama, bata yi k'asa
da gwiwa ba ta bishi yana zaune a gefen gado yana waya.
Ya dauki dogon lokaci yana magana a wayar, kafin ya yi hanging up ya dawo da ganinshi
akanta.
Ya mik'e ya shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login