Showing 81001 words to 84000 words out of 84748 words

Chapter 28 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.pdf

23 Mar 2025

4980

"Suraj kai yaron kirki ne ban so ka bi mummunan tafarki da Muhammad ya bi, duk abin da ya
yi maka ka yi hak'uri ka bishi da addu'a shiriya wata rana koda bana duniya zai yi nadama abin
da ya aikata maka.
Kar ka k'ullace d'an uwan ka Suraj banaso ka bi son zuciyar ka kaman yanda shi ya bi, kada
ka biyewa rud'in zuciya zata iya rusa maka kyawawan halayyen ka Suraj......
Wata irin nadama ce ta lullu6e Uncle fuskar shi ta jik'e sharkaf.....da gumi ya yi shiru yana
kallon barrister A ya kasa furta koda kalma d'aya ne.
**----**-**-----**--** Aliyu da su Daddy tun kafin su k'arasa layin gidan Jamal, suka ci karo da
motar barrister A a gefen hanya duk gilasan ta a farfashe.
"Suka k'ara shiga tashin hankali fiyye da farko suna cikin wannan halin, sai ga Jamal ya kira
Aliyu nan da nan ya bashi labari iya abin da ya sani.
Sosai hankali Aliyu ya k'ara tashi da ji cewa uncle Suraj da momma ke da sa hannu ga dukan
matsalolin da suke ciki.
Cikin wani irin yana yi Aliyu ya ce "kar ka yi yunk'uri tun k'arasu ku jira mu a bakin hotel d'in
za mu zo da police saboda is very risk zuwan mu batare da jam'ian tsaro ba.
Jamal ya ce Shikenan ku yi sauri Aliyu saboda bamu da wadattacen lokaci komai zai iya faru.
Kaitsaye su Aliyu suka wuce police headquarter batare da 6ata lokaci ba DPO da kanshi ya
had'a team suka dauki hanyar Emmaculete hotel in da suka had'u da Su Jamal motar Nafisat
matar uncle Suraj tana gaba su na biye da ita tare da Jami'an tsaro.
"Bangare su barrister Z da ke daure a upstairs cikin taimakon Allah Sa'eed ya yi dabarar
kwancewa, jikinsa yana rawa shiga kwance su barrister Z bayan ya kwance su, malam ya ce ku
taimaka ku danne Maryama nayi gaggawa yi mata ruk'iya ban mu sani ba ko za mu fita wurinan
a raye ba. Ina fatan ta dawo hankalinta kafin mugaye mutane nan su gama yanke hukunci abin da za su
yi mana.
barrister Za ta ce haka ne malam ya kamata maryama tasan abin da ya faru da ita.
Babu 6ata lokaci malam ya shiga yi mata ruk'iya Baaba laraba ya tasaka d'an kwalinta ta
toshe mata baki, kada ajiyo ihun ta a k'asa.
"Uncle ya d'ago jajjaye idanuwanshi masu cike da zallan nadama ya bud'i baki da zai yi
magana, momma ta bankad'o k'ofa ta shigo hannunta rik'e da 'yar k'aramar bindiga.
Yayin da yaran Uncle Suraj suke biye da ita saboda ta ri ga da ta siye su da kud'ad'en da ta
zo da su.
Daga Uncle Suraj har Barrister A suka mik'e tsaye cikin kad'uwa, kafin Uncle ya dauki pistol
d'inshi da ke ajiye akan kujera har Momma ta k'araso kusa da shi, cikin fushi ta dauke shi da
rikitattace mari a kumatun shi na hagu yana d'agowa tasake dauke shi da wani a kumatun shi
na dama. Uncle Suraj ,ya d'ago dafe da kumatu yana kallonta baki bud'e,
Tsawon lokaci ya dauka yana kallon nata kafin ya ce "Ni za ki mara Zaituna??

Cikin tsananin fushi har tana had'awa da huci ta ce "Ba wai iya marin ka kawai nayi ba Suraj
har rayuwarka sai na raba ka da ita, ba ka za6i ka tozarta ni a idon duniya ba, ni kuma zan
tabbatar da na tura ka k'iyama.
Da sauri Barrister A ta nufe momma muryar ta tana rawa ta ce "kar ki yi haka momma
Uncle ya yi nadama abin da ya aikata, kuma ki sani daga ke har shi masu laifi n.....
Bata k'arashe magana ba momma ta dauke ta da bahagon mari, tasa bindigar hannunta ta
daketa a goshi tsananin zafi ya ratsa tun daga tafin k'afarta har zuwa tsakiyar kanta, take ta
sulele k'asa goshin ta yana zubar da jini.
Duk da haka Momma bata bar ta ba bin ta yi tana duka had'e da saka k'afarta tana surin ta.
Gani haka yasa Uncle ya zabura zai kai ma barrister A dauki, kafin ya k'araso wajen su
Momma ta saita shi da bindigar hannunta batare da tunanin komai ba ta sake masa harsashe a
gefen cikin shi, k'arar bindiga tare da sautin ihun Uncle Suraj suka karad'e ciki da waje falon.
A matuk'ar rud'e barrister A ta yunk'ura ta tashi da kyar, tare da kiran sunan Uncle ta nufi
wajen da yake kwance cikin jini, kafin ta kai hannunta ta ta6a shi, ita ma momma ta hal6e ta a
kafad'arta ta dama harsashen ya ratsa fatar jikinta tare da huda k'ashin ta, cikin k'araji da
kururuwa ta fad'i kusa da Uncle Suraj wanda yake fitar da numfashi sama-sama. Cikin rashin Imani balle tausayi Momma ta kalle Oska ta ce "Osaka je ka zo min da
Maryama, yanda na rasa M Ardo ita ma ba zan barta ta rayu da shi ba.
Yi maza ka zo min da ita so nake naga su uku suna daukar rai sannan ne zuciya ta za ta lafa
da tuk'uk'i da take min.
An gama Hajiya yanzu nan zan cika aiki, amma key yana wajen oga Suraj.
Zo ka caje shi maybe key d'in yana cikin ajihun shi, da kyar Uncle ya bud'e bakin shi ya ce
"Zaituna don Allah ki kyale su kar ki cutar da su ni ne nayi miki laifi, ki yi duk yanda kika dama
da ni amma su ki kyale su.
Oska ya kwashe da dariya had'e da dauke Uncle da mugun suri sai da kanshi ya bugi kujera,
ya duk'a ya ciro key gaban aljihun rigar sa.
yana magana dariya mugunta ya haura sama jin takon tafiya an nufo d'akin yasa Sa'eed ya
dauki kujera ya la6e bayan k'ofa, Oska yana bud'e k'ofar Sa'eed na sauke masa kujera aka
yayin da Malam ya buga masa wani kofin silver da ya tarar a d'akin, Oska ya kwalla k'ara ya
fad'i igiya suka saka suka daure shi. "Sa'eed ya dauki bindigarsa ya wuce gaba malam yana binsa a baya yayin da barrister Z take
bin bayan malam, abayanta kuma Baaba ce da Maryama wacce ta warke sumul....ta dawo
hankalinta.
"Kafin su sauka k'asa suka jiyo jiniya motar police sai kawai suka tsaye cakk.....su na jiran su
ga abin da zai faru.
Momma wacce jin k'arar jiniya police ta gigita ta duk tabi ta rud'e, ta Kalle d'aya daga cikin
yaran ta ta ce "na shiga uku kaman police ne suka zo?"
Ba kama ba ce Hajiya su d'in ne don haka kowa ya yi ta kanshi saboda ba mu da wadattace
bullets da za mu yi fad'a da su, kowa ya kare kansa da bullets d'in ya rage mishi.
Wani irin gumi ya karyowa momma duk ta bi ta tsorace tana kallon yaran ta, suka nufi
window suka lek'a gani yawan police d'in da ke kewaye da su yasa suka, karaye gudun kada su
afko musu su kashe a banza yasa d'aya daga cikinsu ya kalli sauran 'yan uwan shi ya ce duk
mai so ya cigaba da numfasawa, ya yi surrender saboda babu hanyar fita anan wuri.

Yayin da a can waje DPO yake sanar musu da su mik'a kansu ta ruwan sanyi saboda suna
kewaye da police babu hanyar fita su yi surrender kawai.
"Babu 6ata lokaci suka nufi k'ofar fita kowane su hannunshi sama, da gudu police d'in suka
k'araso wajensu suka buga musu handcuffs tare da zuba su cikin motarsu duk abin da yake
faruwa su Aliyu su na tsaye a wajen gate saboda police sun hana su k'arasowa ciki.
"Momma ta Kalle Uncle Suraj ta fashe da kuka cikin muryar kuka ta ce "Ka cuce ni Suraj ga
shi ta sanadin ka zan yi mutuwar k'ask'anci, Allah ya isa tsakanina da kai.
Uncle wanda ke fitar da numfashi da kyar ya ce kar ki zarge ni Zaituna "kwad'ayin ki ne ya
jawo miki.
A fusace Momma ta nufe shi tasake halbin shi dai-dai lokaci da police suka shigo falon "ki
ajiye bindinga kafin na hal6e ki!
Cewar d'aya daga cikin police d'in, tsabar rud'ewa yasa Momma ta juyo batare da wani tunani
ba ta halbi policemen d'in a k'afa, Wanda ke bayan shi babu 6ata lokaci ya sake mata bullets a
cinya ta kwalla ta fad'i k'asa a tunanin ta kashe ta za su saboda haka ta sake lalla6o bindigar ta
da ta fad'i, kafin police d'in su iso wurinta tasake kai musu halbi Allah ya taimaka bullet d'in ba
wanda ya sama huda k'ofa, gani yanda take da taurin kai yasa wani daga cikinsu ya hal6e ta a
chest tasaki wahalalle k'ara tare da kwantawa numfashinta sai ya yi sama ya sake dawowa
k'asa.
"Daga nan police suka shiga caje gidan, a upstairs suka tarar da su barrister Z suka nu na
d'akin da suka daure Oska aka fito da shi.
Su Kuma suka biyo bayan police d'in tun kafin barrister Z ta k'arasa sauka k'asa ta hango
barrister A kwance cikin jini bata numfashi, Aminaaaa.....tasa ki wani irin ihu mai k'arar gaske
gaba d'aya ya karad'e gidan.
Daga can gate Aliyu da su Daddy suka jiyo ihun nata, Aliyu da Abba suka danno da gudu
zuwa cikin falon duk iya k'ok'arin DPO nagani ya hana su shiga falon hakan bai samu ba, domin
ture shi Aliyu ya yi yana shiga ya hango barrister Z rungume da ita tana wani irin kuka.
Wani irin duhu ne ya mamayewa ganin sa k'asa d'aga k'afafun shi ya yi zuciyar shi na
halbawa da sauri-sauri kar dai a ce sun kashe mini Amina?"
Tambayar da ya yi ma kanshi kenan kafin ya lalla6o amsa gaba d'aya su Daddy suka shigo,
saboda d'aya daga cikin policemen ya lek'a waje ya sanar da su za su iya shigowa Abba yana
kyalla ido ya hango jini rabin ransa yana zuba ga ta kuma bata numfashi, ya kwalla razanane
ihu da mugun gudu ya isa wajenta Sai lokaci Aliyu ya yi ta maza ya nufi wurin ta yana zuwa ya ciro ta daga cikin Abba, cikin tashin
hankali ya nufi waje da ita.
Zee-zee da Meena tare da Teema suka nufi momma su na kuka abin ka da uwa da 'ya'ya, su
kadai ne rungume da ita.
"Daddy yana talla6e da uncle yana kuka tare da fad'ar "ka yafe min d'an uwana duk ni ne
sanadin jefa ka cikin wannan hali.
Da kyar Uncle ya furta na yafe maka Yaya nima don Allah domin na cutar da kai ba kad'an
ba, na aikata zina da matar ka har mu ka haifi Teema don girman Allah ka ce ka yafe min.
Daddy ya girgiza kanshi yana kuka mai tsanani ya ce na yafe maka, ni ma ka yafe min.
Na yafe maka Yaya don Allah ba don ni ba ka kulamin da Teema da Al'amin.
kuka ya ci k'arfin Daddy kasa cewa komai.

motar asibiti [ambulance] ta iso ta kwashe su zuwa Abj hospital, kafin a fara treatment d'in
Uncle Allah ya kar6i ran sa Daddy kamar zan yi hauka gaba d'aya hankalin su ya tashi cikin
nasara aka cirewa Barrister A bullets d'in jikinta, saidai numfashinta da bai dai-daita ba dole aka
wuce da ita ICU aka sanya mata oxygen ita ma momma an cire mata harsashen saidai tana
under police custody.
*Few hours later*
Momma ta farfad'o sai faman rusar kuka take yi, ga tsananin azabar injury da ke jikinta ga shi
sai faman rok'o take yi a kira mata Daddy tanaso ta rok'i gafarsa, hakan yasa nurse d'in ke on
duty tayi mata allurar bacci.
Lokaci da Aliyu ya ji cewa ba momma ce ta haife shi ba maryama ce saura kiriss....ya yi 'yar
k'aramar hauka shi kan shi Daddy ya girgiza da jin wannan sabon al'amari, yayin da Maryama
ta rungume Aliyu tsam....a jikinta tana gunji kuka duk wanda ya gansu a lokaci dole ya tausaya
musu, saboda abin ya zama musu goma da goma uncle Suraj ya rasu ga barrister A
unconscious, Shiyasa Aliyu ya dawo kaman wani zarare.
Da kyar Abba ya rarrashe Aliyu ya amince suka tafi gida saboda yanda ya gigice ya shiga
damuwa yasa Abba ya dawo tausayin shi musanmman ya hango ta cikin idanuwanshi yanda
yake tsintsan so Barrister A.
Sai a washe gari Daddy ya samu kar6a gawar Uncle Suraj, aka wuce da ita Yola cikin 'yan
uwa da abokan arziki da yake ba kowa Daddy ya gayama musanbabbin mutuwar tasa ba.
Ana gama jana'izzar sa Aliyu ya juya Abj Daddy kuma sai dai aka yi sadakar bakwai.
"Cikin hukunci ubangiji barrister A ta farfad'o, yayin da jikin momma ya rikiceDaddy yana rik'e
da hannunta tana kuka had'e da rok'on gafara Aliyu kan kasa jure kallonta ya yi yafice daga
d'akin suna cikin wannan halin d'a momma ta baro a Nijar yana jariri a baiyana da photon ta tun
tana budurwa duk da yanzu girma ya kamata hakan bai hana su Sheda ta ba. Tashin hankalinsu ya k'aru a lokaci da Ibrahim ya gabatar da kanshi a matsayin d'a da ta
haifa, tabbas ga kamanu shi d'aya da Momma babu ko tambaya kasan ita ce ta haife shi duk da
tana cikin mayuwaci hali bai hanata rungume Ibrahim tana kuka tana rok'onsa gafara.
Cikin dare Momma ta ce ga garin ku nan, rai bakon duniya su Zee-zee sun ci kuka kamar ba
gobe dole suka dangana.
Yayin da Daddy yake dorawa kan shi laifi abin da yafaru akan momma da Uncle Suraj, a
cewar shi da bai zalinci Uncle Suraj ba duk haka bata faru ba.
***---***----*****
*FIVE MONTHS LATER*

Barrister A sanye da night gown light pink tafito daga bedroom dinta zuwa na Aliyu, koda ta
shigo yana wanka.
ta bud'e closet ta ta fito masa da kayan shi tana shi shiryawa a luggage d'in da za su yi tafiya
zuwa los angeles a cikin k'asar California, in ka ganta kaman bata yi ciwo ba ta warke sumul
ta6o kawai ya rage shima tana amfani da magani 6acewar ta6o sannu-sannu zai 6ace.
Aliyu ya fito daga wanka d'aure da brown towel iya waist d'inshi, Barrister A ta d'ago tare da
wanke shi da k'ayattace murmushi shima ya mayar mata da marni yana zuwa kusa da ita ya
fizge Coat d'in sa da ta dauko da nufi sakawa a trolley, ya zauna daff....da ita tare da rungumo
ta yana rad'a mata "Wifey I miss you so much I really need you in my bed right now kar ki ce

ah'a Baby kin sani nayi hak'uri almost five months please.....
Kafin ya k'arasa ta had'e bakinta da nashi ta shiga ba shi wani irin zazzafan French kiss,
sosai Aliyu ya rikice ya dimauce tuni ya yi undressing d'inta ranar ta gurzu kaman first night
d'insu.
Ta 6agare Daddy ya had'e kan iyalinshi yayin da Maryama ta had'e kan yaran ta yanda take
kulawa da su Zee-zee za ka dauka ita ce ta haife su, musanmman Teema da ta dawo 'yar
gaban shi kowa sonta yake yi, tuni ta daina k'arya iskokai dama depression ne ya yi mata yawa,
yanzu kuma batada sauran damuwa. "Daddy ya kira lawyer shi da na Uncle Suraj aka raba dukiyarsa kashi biyu ya mallakawa
iyalin uncle, rayuwa ta dawo musu sabuwa saboda hatta da Ibrahim d'a Momma Daddy ya
dawo da rik'onshi hannunshi, ya bashi aiki a kamfaninsa.
*LAX LOS ANGELES INTERNATIONAL AIRPORT*

Ahankali suke takowa daga steps d'in jirgi Aliyu yana gaba sanye da white long suit jacket
k'afarshi na cikin Chelsea boots.
Yayin da barrister A take sanye da brown frock jacket tare da stirrup trouser, k'afarta na cikin
velvet ankle boots ta yane kanta da siririn scarf
kallo d'aya za ka yi musu ka gano cikkaku masoya ne musu masifar k'aunar juna, da yake jirgin
na su da dare ya yi landing ga wani masifaffen sanyin garin ya yi musu marhaban.
"kowane su yana janye da luggage suka fito wajen airport texi suka hau zuwa, hotel d'in da
ya yi musu booking tun kafin su iso suna zuwa batare da 6ata lokaci ba aka nuna musu room
dinsu irin suite dinan ne ya kama sai masifar tsada.
Washe gari da yamma lis....suka fita yawon bud'a ido a wani had'adden wurin hutawa, mai
suna frank national park & beach.
Bayan sun zauna waiter ya kawo musu menu suka za6i drink d'in da za'a kawo musu,
saboda ba su ji yunwa.
Wayar Aliyu ya yi ringing gani Daddy ne kira yasan za su tattauna ne akan abin da ya shafi
business, maganar su zai dauki longtime yasa Aliyu ya mik'e neme wurin da ba zai dame
mutane ba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login