Showing 84001 words to 84748 words out of 84748 words

Chapter 29 - Gidan Rina Book Complete Jidda Aliyu.pdf

23 Mar 2025

4978

Tun lokaci da ya shigo wurin tayi bala'in daukar hankalinsa, sai faman kallonta yake yi sanye
yake da blue jeans tare black hoodie kanshi dauke da pcap Dr Joel Kenneth kenan matashin
likita da tauraro sa ke haskawa a yanzu Joel d'an kwalisa ne mai ji da kud'i da kyau.
Iyayyen shi 'yan asalin Nigeria ne zama ne ya kawo su California tun yana yaro suke a k'asar
shi kadai iyayyen nashi suka haifa.
Mahaifinshi ya mutu kusan shekaru goma kenan hakan yasa mahaifiyarsa ta koma Nigeria a
yanzu tana zaune ne a d'aya daga cikin gidaje da mahaifinshi ya bari a Abj, shi ma yana
daff....da komawa Nigeria.
Tun ya shigo yake kallon barrister A k'asa hak'uri ya yi ya mik'e ya nufi wajenta cikin husky
voice dinshi ya ce "hey......beautiful!
Barrister A ta d'ago kad'an ta kalle shi saura kirisss....ta kwalla ihu sakamakon yanda ta
tsorata tare da bud'e idanuwanta, ba don long necklace mai dauke da cross da ke sanye da
wuyan shi da tace Aliyun ta ne.
Tabbas ba ko tambaya tasan wannan twin brother Aliyu ne, saboda tsananin kamanun su

kuma kafin momma ta mutu ta sanar da cewa abokin haihuwar Aliyu bai mutu ba ranshi ta jefar
da shi.
Cikin tsadadd'en turancin shi ya ce zan iya zama.
Cakk.....barrister A ta mik'e tsaye ta shiga rarraba idanuwa ko za ta hango Aliyu, can.....ta
hango shi tafe tun kafin ya k'araso ya ga wani k'ato tare da matar sa hakan yasa ya k'ara sauri
da yake iya bayan shi yake iya hangowa.
Yana k'arasawa dai-dai Joel yana jiyowa karaf.....suka had'a idanuwa sauri kad'an kowane
su ya saki fitsari a wando, Joel ya fi Aliyu shiga firgici saboda bai san yana da d'an uwa ba
saboda iyayyen shi shi kadai suka haifa sa6ani Aliyu wanda bai dauki dogon lokaci ba ya dawo
cikin natsuwar shi, bai san lokaci da ya rungume Joel ba. Duk da Joel bai san alak'arsu ba sai kawai ya tsince kanshi da k'amk'ame Aliyu d'in.
Bayan sun saki juna Aliyu yake mishi bayani ba wai haka kawai suka yi kama ba, su Twins ne
Joel ya 6ata tun yana jinjiri hatta da 6th finger irin na Aliyu Joel yana da shi.
Shi kanshi Joel ya yarda da abin da Aliyu ya fad'a duk da ana kama a duniya amma
kamanun shi da Aliyu, dole ta kasance ta jini ce.
Babu 6ata lokaci suka nufi gidan Joel d'in inda ya kira mahaifiyarsa mrs Kenneth domin ya ji
daga bakin ta, da yake a vidoe call ya kira ta ya nuna mata Aliyu ya kuma sanar da ita abin da
ya sanar da shi.
Nan take ta fashe da kuka cikin kuka ta sanar da shi gaskiya mr Kenneth adopted dinshi ya yi
a gidan marayu kasancewar bashi haihuwa, amma ya sani har gobe tana kallonshi a matsayin
d'an su tana kuma taya shi murna gane biological parents dinshi da ya yi.
Tsabar farin ciki da kuma suna so su yi surprising family su yasa washe gari suka dawo
Nigeria tare da Joel.
Lokaci da Umma maryama tayi arba da d'anta da ta fidda ran gani saida ta suma aka yayyafa
mata ruwa ta farfad'o, Daddy ranar kamar zai yi hauka.
*AFTER THREE MONTHS*

A cikin watani uku abubuwan farin ciki sun samu a M Ardo family, inda Joel ya kar6i musulunci
ya tashi daga Joel zuwa Abdulrazaq sai cikin da Barrister A take dauke da shi na tsawon watani
uku.
Burin Daddy ya cika iyalinshi sun kammala kuma suna cikin farin ciki.
Bayan wata biyar barrister A ta haihu ta sami baby boy, ranar suna ya ci sunan Uncle Suraj
saboda tunawa da Uncle yasa.
"suna kiran shi da Aiman rayuwar Barrister A da Aliyu gwanin ban sha'awa kullum k'ara k'aunar
Juna suke yi.



*TAMMAT BIHAMDILLAH*

_ANA NA KAWO K'ARSHEN LITTAFIN GIDAN RINA KUSKURE DA KE CIKI ALLAH YA
GAFARTA MIN, IDA NAYI DAI-DAI ALLAH YASA YA AMFANI AL'UMMAH MUSULMI_

Sai mun had'u a cigaban novel d'ina mai suna *ZAZZAFAN KISHI*




Jeeddah Aliyu





Jeeddah Aliyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login