Showing 66001 words to 69000 words out of 84748 words
of plans d'inta.
Daniel ya bud'e mata gate ta nufi parking lot tayi parking motarta tafito tare da Teema, saida ta
kashewa Daniel gargad'i kada koda kuskure ya fad'awa momma ita tafita da maryama.
Koda ta shiga falonta k'arfe 12:40pm gaba d'aya kwakwalwarta ta toshe tana buk'atar ta ware
lokaci na musanmman da zatayi tunanin mafita.
"Kitchen ta nufa ta dauko ruwan roba masu sanyi, bata ko nemi cup ba ta balle murfin robar ta
kafa bakinta saida ta kusan shanye fiyye da rabin ruwan sannan ta ciro robar daga bakinta ta
direta akan fridge, tasaki ajiyar zuciya koda tafito daga kitchen bata ga Teema ba murmushi tayi
tana girgiza kanta, abayyane ta ce Teema kenan ke da iskokanki kuna buga wasanku mai kyau
da tsari yanzu ni kuma yanzu ne zan fara nawa wasan
_Readers ku zuba ruwan comments ni kuma gobe na zuba muku long typing_
Jeeddah Aliyu
[7/27, 12:23 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
*GIDAN RINA*
*36*
Da k'arfi momma take danna horn kamar gaba d'aya za tashi unguwa, da gudu Daniel yafito
daga band'aki ya bud'e mata gate.
Tsabar tashin hankali da take ciki yasa ta kasa k'arasawa parking lot sai daf da barandar shiga
flat d'in maryama tayi parking, tafito daga cikin mota da wani mugun sauri tanufi k'ofar da zai
sadda ta da main parlor maryama manya-manya d'uwawunta sai wani 6al...6al...6al suke yi da
yake gown d'in shadda ne a jikinta, gaba d'aya d'uwawun nata sun kwashe rabin rigar shiyasa
ta tsangale sai kace Rukayya Dakaratu ta shiga gaba tana biye...lol..
Garin sauri ta hau barandar ta taka wrong steps da yake sai ka taka kusan five steps kafin ka
hau barandar.
Saura kad'an tafad'i duk da haka, ita sam bata damu ba murad'inta tayi four eyes da maryama,
jikinta yana rawa ta ciro key daga handbag d'inta sau biyu key d'in yana sa6ulewa daga
hannunta yana fad'uwa.
Da kyar tayi nasarar tattara natsuwarta waje d'aya ta bud'e k'ofar, tun da ta jefa k'afafunta cikin
falon bataci karo da Baaba ba tasan akwai matsala tak'ara mulmula manyan mazaunanta masu
barazana yaga rigar jikinta, ta nufi d'akin da maryama take ciki k'ofar da tagani a bud'e ya haifar
mata da mummunan fad'uwa gaba, duhu ya maye ganinta miyau bakinta ya kafe batasan lokaci
da tayi fad'uwa 'yan bori ba da6asss......su kansu d'uwawunta da zasu yi magana da sai sun yi
mata Allah ya isa saboda ta azabtarda su ba kad'an ba.
"Da rerrafe ta k'arasa shiga d'akin duk da tasan a rufe ta barshi hakan bai hanata duba
bathroom ba, ko Allah zai sa kwakwalwarsu ta toshe kaman nata sun 6oya a bathroom nan ma
taga wayam....da gudun bala'in tafito compound ta hango Sa'eed yana wankewa barrister A
motarta, nan ko rahoto yake dauka. "Ta shiga kwalla masa kira kai Sa'eed!
Sa'eed!
"Banza ya yi da ita kamar bai ji ba sai wak'e-wak'ensa yake, gani haka yasa ta nufi wajensa
yana ganinta ya cire earpice d'in kunnenshi ya durk'usa hannunshi rik'e da brush d'in da ake
wanke tayoyin mota da shi.
"Wata kafira harara tafara wulga masa tana fad'in kai wane irin bagidaje ne sa'eed?
Tun d'azu nake kwalla maka kira amma kai hankalinka yana ga wankewa k'anwar uwarka mota,
sai kace ubanta ke biyanka salary ko ubanta kake ma aiki ban saniba?"
Sa'eed ya girgiza kanshi ya ce Allah ya huci zuciyarki Hajiya, kunnayena suna doshe da
earpice shiyasa ban ji kiran naki ba don Allah kiyi min afuwa.
"Mtssss....taja dogon tsaki tare da fad'in dama tambayarka zan yi ko kaga lokaci da wani ko
wata yafita da mahaukaciyar gidanan?"
"Sa'eed ya yi shiru na 'yan dak'ik'u kafin ya ce auuu....Hajiya kina nufi Teema gaskiya banga
fitarta ba s....
Shut up.....!
Jahilar tsawa da momma ta daka masa yasa shi saurin had'iye sauran kalamansa, ya ja da
baya yana kallonta a tsorace saboda shi da kanshi yasan ya ta6o _*GIDAN RINA*_
"Sa'eed yanzu don bakada mutunci 'yar tawa ce za ka kira da mahaukaciya...? Ba shakka duk
yanda akayi da jaki sai yaci kara.
kana gidan ubanta a k'ark'ashin inuwarsa, kana ci kana sha da gumin ubanta shine don
b**ubanka za ka kira 'yarshi da mahaukaciya.
"Don Allah Hajiya kiyi hak'uri wallahi na zata ita kike nufi, saboda ita kadai ce muke da a
gidanan mai irin wannan lalura amma kiyi hak'uri ki gafarce ni tuntun6en harshe ne.
"Tuntun6en harshe uwarka ko na ubanka yau sai kabar gidanan, tunda bakada kunya har za
ka iya duba tsabar idona duk kwarjini nan nawa ka kira 'yata mahaukaciya wallahi sai kabar
gidanan bak'in munafuki.
"Afakace Sa'eed yake harararta yana yatsina a zuciyarshi kuma sai rama zaginshi yake ya ce
ka ji ja'ira wai kwarjininta da wannan shegiyar fuska kaman dudduge kuturu, sai shegen fari
fuuu...kaman jan kosai ga ki nan babbar munafuka da wasu shegun d'uwawu kaman na masu
rawan makosa. Kai...!
Don ubanka mikake fad'a ne?
Na ga sai musu-musu kake da baki, ko zagina kake yi?"
"Zagi kuma..?
ya maimaita yana wani zare idanuwa, tare da fad'in Allah dai ya kauda 6aci rana Hajiya.
Rashin sani ma'anar maganar ta sa yasa taja tsaki mtsss....tanufi bakin gate tana cigaba da
zaginshi hade tak'ara jaddada masa sai yabar gidanan.
"Duk yawan masifar da ta dinga zazzagawa Daniel bai sa yafad'a mata ba sai cewa ya yi bai
ganta ba.
Bayan ita da Aliyu ba wanda ya fita daga gidan.
A fusace tanufi flat d'inta yayin da Sa'eed ya bita da murmushin mugunta har da yi mata gwalo.
***----*****----****
Ta bangare barrister kuma ta kira barrister z ta bata labarin abinda ya faru, yayin da barrister z
tak'ara tabbatar mata da cewa gobe zata zo da malam tana gama waya da ita Aliyu ya kirata
video call, wani shegen dad'i mai kama da ice cream ya ziyarceta tana kallo har kiran ya tsinke
bata yi receiving ba, wai ita adole aji take ja...lol. "Wani kira na sake shigowa da ya yi kusan tsinkewa sannan tayi picking. kyakyawar fuskarshi
ma'abociyar kwarjini ta bayana a screen d'in wayar yana zaune akan resting chair da ke gidan
Daddy na lagos.
"Hey.....my lazy lawyer how you're feeling now?"
Sanyayye murmushi tayi tare da fad'in I'm feeling better Yalla6aina ya gajiya flight hope ka ci
abinci ba ka zauna da yunwa ba?"
"Gajiya flight na wartsake ta a conference hall tun zuwana muke meeting ban wuce one hour
da fitowa ba, shiyasa sai yanzu na samu damar kiranki.
"Allah sarki my hubby da ina kusa da kai da nayi maka massage.
Ta k'arashe magana tana masa dariya.
Murmushi ya yi tare da shafa sumar kanshi ya ce
Aminaa....!"
Na'am!
Ta amsa masa anatse
"I miss you so much yau kadai duk naji wani iri ji nake kamar na bud'e idanuwana naganni kusa
da ke, I miss you & how close we used to be I miss how much you used to care about me, I
miss the time we spend together bakina ba zai iya fad'ar yanda nayi kewarki ba saidai kawai ya
misalta I miss you a lot I wish to open my eyes to see you standing beside me. "Lumsashe idanuwanta tayi sosai kalamanshi suka ratsa jinin jikinta, ta fad'ad'a murmushin
kan fuskarta tare da fad'in I miss you so badly Yalla6aina nima ji nake kamar nayi tsuntsuwa
nagani kusa da kai ba abinda yake fad'ar min da gaba a duk lokaci da na tuna cewa ni kadai
yau zan kwana a gidanan. Ta karashe magana tana share hawayen shagwa6a mai cike da zallan kissa.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "I'm sorry wifey wallahi the trip is very important to
me da nadawo gobe amma don't worry, it won't take long its just one week, I would be back so
stop crying kin ji Babyna..?
Ta share 'yan budaren hawayenta tana dariya, knocking d'in da taji anayi da yasa ta ce hubby I
have a visitors bara na bincika za mu yi waya anjima saboda bangaji da kallon wannan
kyakyawar fuskar taka ba.
"Nima haka Babyna.
Yafad'a tare da katse kiran.
Tana bud'e k'ofa suka had'a idanu da uncle Suraj sai da taji mummunan fad'uwar gaba, ta
k'irk'iro murmushin dole ta ce Barka da zuwa uncle Suraj!
"Yauwa the best lawyer in the world!
Cewar uncle Suraj yana mata wani shegen murmushi mai wuyar fassarawa.
Ita ma murmusawa tayi batare da ta tanka mishi ba.
"May I...?
Yafad'a yana nuna hanyar da tare da hannunshi.
Yes of course ta karashe magana tana mai juyawa cikin falo, ya biyota a baya.
ruwa da Juice mai sanyi ta kawo mishi ta nemi kujera da ke nesa da shi kad'an ta zauna.
"Ya gyara zamanshi kafin ya ce ya gida barrister ya akaji da bankad'o sirrinka Jama'a...?
Ai barrister kuna k'ok'ari ba kad'an ba, samun masu yi aikin Allah irinku sai an tona sannu da
hidintawa Jama'a my beautiful daughter in law!
Dariya tayi sam bata kawo komai aranta ba saboda ya saba da yi mata irin wannan wasa, sai
kawai ta ce uhm....uncle kadai baka rabuwa da abin dariya ni fushi ma nake yi da kai.
Ta karashe magana tana 'yar k'aramar dariya
"Shiru ya yi yana kallonta wanda sai mai hankali zai gano idan kallon nasa ya dosa, ya saki
k'ayattace murmushi ina neman afuwa tun kafi nasan laifi da nayi amma fad'amin laifi da nayi
my beautiful daughter in law na k'ara bada hak'uri?"
"Dariya barrister A tayi ta ce wato uncle shine ka turamin miji Lagos kai kuma ka dawo Abuja,
wannan ai rashin adalci ne.
"Zaro idanuwa uncle ya yi tare da rufe bakinshi da tafin hannunshi yana dariya, ya ce kai my
beautiful daughter in law na fahimce kina daff...da sussuta min yaro to karki damu bari na kira
Yaya M Ardo na fad'a masa kince ya dawo miki da mijinki kina k'ewarsa.
"Sosai take dariya yayin da dariyarta ta tayi wufff.....da imani uncle ya shagala iya shagaltuwa
da kallonta, tana maida ganinta akanshi ya yi sauri kauda fuska yana shafar munafuki gemunshi
mai kama da na balagagge bunsuru had'e da wani ja'irin murmushi.
Ta ce rufamin asiri uncle da wasa nake.
"Ya mik'e tsaye tare da cewa ni zan tafi dama Zaituna ce ta kirani wai tanemi maryama sama
da k'asa bata gannta ba shine nakeso nasamu bayanai daga gareta, ta yanda akayi har tayi
sakaci maryama tafita daga gidanan saboda inaso nakai report wa 'yan sanda kinsan 6atan
mutum ba k'aramin abu bane, musanmman ita maryama da ke dauke da lalura ta ta6in hankali. "Shiru barrister A tayi gabanta na fad'uwa duk tayi wani iri fuskarta ya nuna rashin gaskiyarta
a fili, har tayi niyyar ta fad'awa uncle ita ce ta dauke maryama sai kuma taga rashin dacewar
hakan gara ta jira zuwa gobe idan malam ya zo, maybe adace maryama ta dawo cikin
hankalinta sai tafad'a masa yayin da uncle Suraj ya kafeta da idanuwa yana karantar yana yinta
anatse.
"Gani yadda yake kallonta yasa tattaro natsuwarta wurin d'aya ta ce wai Uncle wacece
maryama nan?
Sunanta kawai nakeji ga bakunan jama'a har yau banta6a ganinta ba.
"Uncle ya yi bazawarin murmushi na gefen baki ya d'age girar ido ya ce ba kisanta ba ko?"
Ta gyad'a kanta tana mai cigaba da murmushi yak'e.
karki damu my beautiful daughter in law za ki santa very soon saboda ina ji a jikina bata yi nisa
da mu ba kawai kiyi fatan aganta.
Bari na wuce akwai musu jirana a office gashi kuma inaso na biya police station.
Shikenan uncle Allah yasa aganta sai anjima a gaida gida.
Batare da ya amsa mata ba ya nufi k'ofar fita da sauri.
"Sa'eed yana fitowa daga band'aki Daniel na budewa uncle gate yafita.
"Ya bi gate d'in da kallo cike da takaicin rashin sanarda uncle abinda yafaru na nemansa da
suka yi a d'azu.
Jeeddah Aliyu.
[7/27, 12:23 AM] Jiddah Aliyu: *DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA NA KUD'I NE
IDAB KANA SO SAI KA TUNTUBE WANNAN NUMBER*
0813943903
*SAI KA TURA SHEDAR BIYANKA GA WANNAN NUMBER*
08166177830
*ZA KA IYA TURAWA WANNAN NUMBER KATIN MTN*
08039424298
*SHEDAR BIYANKA KATINKA GA WANNAN NUMBER*
07084161619
DA D'UMID'UMINSU DAGA ALK'ALUMA SHIDDA
*JIDDAH ALIYU*:-```GIDAN RINA```
*A'ISHA DANSABO*:-```BURIN ZUCIYA```
*KHADIJA AHMAD KDEEY*:-```DA CIWO A ZUCIYATA``
*RAHMA MUH'D RUFA'I NALELLE*:- HAYATUDEEN
*SLIMZY*:- IZZATA
*SAFIYA GALADANCHI*:- TANA K'ASA TANA DABO
_Assalamu Alaikum masoya masu bibiyar novel dina wasu daga cikinku sun kirani wasu kuma
sun turomin message sun yi min nuna damuwarsu na rashin gani new update, wanda suka yi
min texts ban yi reply ba su yi hak'uri abin ne da yawa nagode kwarai da gaske da
KULAWARKU_
*37*
*AM ARDO CONTRACTUAL & BUILDING MATERIALS NIGERIA LIMITED*
_*LAGOS NIGERIA*_
*Time:-1:30pm*
Daddy da Aliyu suna gabatarda meeting da employers d'in kamfaninsu, a conference hall da ke
cikin company. text ya shigo wayar Daddy bai duba wayar ba saida suka fito daga meeting.
Ya bud'e text d'in abinda ya gani ya yi matuk'ar girgiza hanta cikinshi, da sauri yafito daga
office dinshi ya nufi na Aliyu agaugauce ya sanarda shi zai wuce Abuja Maryama ta6ata.
Yatsine fuska Aliyu ya yi tare da fad'in haba Daddy ya za'a yi ka tafi a yanzu bayan kasan irin
mahimmanci da project d'inan yake da garemu, da irin mak'udan kud'i da zamu samu please
Daddy ka bar zance tafiya nan koda zuwa jibi ne, uncle suraj yana Abuja na tabbata zai yi
handling komai kamar kana nan. A fusace Daddy ya ce rufemin baki Sultan tun kafin na kwashe ka da mari project d'in banza
project d'in wofi, saboda neman duniya sai na kasa tafiya nasan halin da matata take ciki ka
shiga taitayinka da ni banso ka k'ara kwatata yi min irin wannan zance idan har kai ba zaka iya
handled komai sai tare da ni sai ka bari babu dole mtsss....ya k'arashe magana da jan dogon
tsaki bai ko saurare abinda Aliyu zai ce ba ya bude k'ofa ya fita ko gida bai koma ba ya wuce
kaitsaye airport.
***---****---*****---***
*Abuja*
*Time:-10:00am*
Barrister A tana tsaye a kitchen tana ba ma 'yan aikinta umarni abinda zasu girka mata a
matsayin breakfast, suka jiyo wani shegen heavy knock ta Kalle Bintu ta ce "Bintu je ki gani
wanene ke min knocking da sassafe nan.
Bintu tana bud'e k'ofa taga momma a tsaye jikinta sanye da sleeping dress, sai d'an wani
siriri scarf da ta yane kanta da shi ta ce "ina kwana momma?"
Wulak'antattace kallo ta watsawa mata tare da sa hannayenta ta tureta gefe, ta shigo cikin falon
ranta a 6ace ta shiga kwalawa barrister A kira "ke Amina!
Amina!"
Kina ina fito ki fad'amin ubanda ya baki izzini dauke maryama daga gidanan?"
Jikin barrister ya dauki rawa ta zazzaro idanuwa cabdijam....wane munafuki ne ya fad'a mata
ni na dauke Maryama.
A fusace momma ta shigo kitchen d'in tashiga k'arewa Barrister A kallo mai cike da tsana, yayin
da barrister A ta tsareta da nata idanuwa ba alamar tsoro babu yabo ba fallasa ta ce "ina kwana
momma?"
"Ke saurara bak'ar munafuka alguguma har ni za ki nemi ki tonawa asiri, wallahi kiyi kad'an
fad'amin menene hujjarki na dauke maryama daga gidanan?"
Rolling idanuwa Barrister tayi hankalinta kwance ta ce "wai saboda kawai ki sami hujja momma
kika shigo min a hargitse.
ni wallahi na dauka ma gobara kika yi, Kalle kayan jikinki momma wannan sam bai dace
tsohuwa kamanki tana yawo da sleeping dress a farfajiyar gida ga katti bila adadin kiyi ma
kanki fad'a mana.
Ba ma wannan ba wane munafuki ne ya gayamiki ni ce na dauke maryama?"
Sororo da baki sake momma take kallon barrister A kafin tayi kwafa ta ce "kiyi katon kuskure
Amina kuma tabbas sai kiyi nadama mafi muni a rayuwarki, ki rasa wanda za ki k'aluballanta sai
ni tanuna k'irjinta da yatsa ta girgiza kai ba ki san wacece ni ba.
Shiyasa kika yi min kutse don tsabar iskanci kina tambayata wanda ya gayamin ke kika dauki
maryama to a Cctv camera naga lokaci da kika fita da ita ke da Teema da bak'in munafuki nan
Sa'eed.
"mtsss.....Barrister taja tsaki tare da fad'in wacece ke momma? Face bak'ar azzuluma
muguwa, kina matsayi mace kuma uwa amma bakida imani balle tausayi ko kad'an a zuciyarki.
kuma Cctv ki ya gayamiki k'arya ni ban dauki maryama, saboda haka don Allah ki fita ki bani
wuri banso