Showing 6001 words to 9000 words out of 36747 words

Chapter 3 - GUBAR RAYUWATA BY FATIMA ABDALLAHI KANO .txt

Advertisement

ita ce Allah yake hanasu yi maka wasu abubuwan , mu da muke da Allah, Wallahi duk sharrinsu a kan zu zai tattare , kawai addu'a zamu cigaba da yi."


Alaji ya girgiza mata kai alamun yaji dad'in zancen ta yana cewa, "Gaskiya ne."


Kalisa ce ta shigo ta katse su da cewa ,"Momy Dady , abinci ya kammala ku taho ."


Alaji ne ya kalleta cikin kauna yana cewa, "Tom Kalisa Yanzu zamu taho."


Matsowa ta sake yi tana cewa, "Haba Dady tsawon yini fa kana azumi, kuma babu abin da kaci , ka dena biyewa momy ka taho mu tafi ." Ta ja masa hannu ya bita suka fita yana yiwa Hajjiya Maryam murmushi. Ita ma murmushi tai ta bi bayansu.


Duk sun zazzauna su baba anje , Nabila, Jafar , Alaji na fitowa gun kawai duk suka d'auke wuta kowa ya yi shiru , su Hajjiya Maryam su ma suka zauna , aka fara cin abinci amma abin mamaki da tambaya kowa shuru ya yi kamar wanda aka aikowa da mutuwa , jikinsu duk kasala ta ziyarcesa bayan sun gama cin abinci
sai aka fara kallon-kallo ba tare da kowa ya bar wajen ba .




Alaji Idris ne ya bud'i baki yana cewa, "Kalisa gobe ki sanar da Sahid ina san ganinshi."


Wani fad'uwar gaba taji ba zato ta shiga yanayi tana tunanin ba dai dady zai maganar aure ba .


"Kalisa ba ki ji mene na ce ba ne ".
Alaji ya fad'a


Da sauri ta kalleshi tana cewa," Naji dady ."






Sannan ya d'auke kai a gunta yana cewa, " Idan Allah ya kaimu gobe ,ina son magana da kowa da me nan bayan kun yi break fast. "


Maganar suka ji wani iri harsun fara tunanin meke damun Alaji yau .




Kawai ya tashi ya nufi d'akinsa , Hajjiya Maryam ajiyar zuciya tai tana binshi da kallo


Nabila ce ta kalli Jafar tana cewa, "Mene dady zai fad'a mana gobe , nifa har na fara jin tsoro ."


Baba Anje tace ,"Too Allah masani ku bari goben ta yi , Allah ya kai mu , mu kuma ji alheri."


Suka ce ,"Amin."








Washe gari da safe Aminu ya fara shirya kayansa domin komawa Adamawa inda yake karatu , bayan ya shirya kayanshi tsaf
Hajjiya da Alaji Kabiru suka fito sukai sallama har Alaji ya ba shi wasu kud'i


Sai Ahmad da Mahmud suka d'auki kayansa domin rakashi


Zainab ta kalli Aminu tana cewa, "To yaya Aminu Allah ya tsare hanya ya kula mana da kai ."


Aminu yace ,"Amin Zainabu ta."


Hararar kauna Mahmud ya jefa mata yana cewa,"Ni ba za a mini addu'a ba."
.


Murmushi tai mai jan hankali tana cewa, "To kai yaushe zaka tafi yaya Mahmud."


.Zaro idanu ya yi yana cewa, "Laaaaah ashe korata kike so ki yi ."?




Dariya tai tana cewa," Wallahi a'a yaya bari na koma ciki ."


Ta tafi yana bin ta da wani kallo....


Fitarsu ke nan sai ga Harun ya shigo aiko Zainab tana zaune taji sako ya shigo mata, "Ki fito gani a harabar gidanku."




Murmushi tai tana cewa, "Ya Allah, yau zan ga waye mai wasa da hankalina ."


Ta tashi ta sa hijab ta fita


duk ta duba harabar gidan amma babu kowa hakan yasa ranta matukar'baci




cikin ranta take cewa aikin banza kawai ta juya zata shiga gida ."






Jin murya tai ance ,"Ina za ki kuma gani a Bayan ki."




Tai sauri ta waiga don ganin wayeeeeee.






Comment d'ina a zube shi a private




Share , like and comment.................๐Ÿ“š




Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน
By






Fatima Abdallaah kano
( Autar marubuta )








editingโŒ






*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>




Page 9&10








"Dan Allah malam yi hakuri". Yarinyar ta fad'a tana kallon Mahmud
Murmushi ya yi yana cewa, " Babu komai laifina ne , kema ki hakuri, na gaji ne ga ciwon kai ."
Murmushi ta sake yi tana cewa, "Allah sarki , to idan ba damuwa ka shigo na rage maka hanya tunda naga kai ma hanyar tawa kayi ."
Mahmud ya ce ,"A'a wallahi karna bata miki Lokaci nan babban titi zan gangara."
Tace ,"Haba babban titi ai da sauran tafiya ka shigo kawai."
Ya bud'e kofar ya shiga tare da rufewa yana ajiyar zuciya
babu wanda ya ce da wani komai , har saida motar ta tsaya , ta fita ta bud'e gaban motar domin ganin matsalar, dogon tsaki ta saki , hakan ya sa Mahmud fitowa yana duba mata ,"Na ce da dady na tsani motar nan amma ya'ki saurarana ."Tai maganar cikin damuwa .
A lokacin Mahmud ya rufe gaban motar yana cewa, "Karki damu , shiga ki tayar mu ga ."
Ta shiga tasa key , aiko mota ta tashi suka ci gaba da tafiya
"Ki sauke ni anan ". Mahmud ya fad'a Murmushi tai ta fara kokarin parking,bayan tayi burki ne ta kalli Mahmud tana cewa," Sai dai bansan sunanka ba ."
"Sunana Mahmud. ke kuma fa ."
Ajiyar numfashi tai tana cewa, "Ni suna na Hauwa Muhammad Sadiq, ni 'yar gidan lu'utanan Muhammad Sadiq ce ."
Mahmud ya kafeta da idanun mamaki Lokaci guda kuma yana cewa, "Gaskiya na gode Hauwa Muhammad, amma idan ba za ki damu ba , ko zaki ban number ki ." ya mika mata wayarsa
Ta amsa tare da aje masa number ta a cikin wayar , Mahmud ya fito ya sake godiya ta tafi




Mi'ka ya yi yana cewa, "Tabb ka ga wata mota , yaran manyan ke nan ." Ya yi murmushi ya gangara domin tafiya gida.






Zainab ce kwance a kan kujerar falo suna waya da Harun , yake sanar mata fa zai jarabawar sojoji ta taya shi da addu'a
Ganin shigowar Mahmud cikin yanayin da bata saba gani ba ya sa ta tashi zaune , tare da sanarwa Harun zata kirashi .
Mahmud kusa da ita ya zo ya zauna , ya jingina kanshi a kujera tare da ajiyar zuciya .
"Yaya Mahmud lafiya kuwa."
Mahmud ya kalli Zainab da cewa ,"Zainab daga asubiti nake, wallahi tana da cutar nan." ya karasa maganar cikin yanayin damuwa
"Ina Ahmad."? Ya kalleta yana tambaya


Cikin jimami ita ma Zainab ta ce ," Wallahi bansan inda yayi ba , naga ya hau mota ya fita . To amma Yaya Mahmud yanzu mene abin yi ."
Mahmud ya gyara zama yana kallon Zainab ya ce ,"Zaki aure ni Zainab, kina so na."?


Jitai zuciyar ta tai wani irin bugawar tsoro
"Ni dai ina son ki , amma kiyi tunani." Ya tashi ya shiga cikin d'akinshi , Zainab tana bin shi da kallo
"Me ya sa yaya Mahmud yake mini haka , duk abin dake ranshi kawai fad'a mini yake ko kunya." Zainab tai maganar tana mamaki tare da sake kallon kofar d'akinshi


Kiran Harun ne ya katse mata tunani, ta tashi ta shige d'akinta, kai tsaye kan gado ta fad'a ta cigaba da waya dashi.










A halin yanzu Alaji Idris ya yi azumi guda 58 yana zaune a falo shida Hajjiya suna hira
"Wato Hajjiya kinga a kwana a tashi na kusan kammala azumi na , Allah ne abin godiya."
Hajjiya tai murmushi tana cewa, "Wallahi kuwa Alaji ai wata rana sai labari."


"Wallahi Hajjiya na yi dace da samunki a matata , duk wanda bai samu mace kamar ke ba , to abin tausayi ne ."


Dariya Hajjiya tai tana cewa, "Alaji ke nan ai ni ce na yi dacen miji wallahi , ni dai fatana Allah ya barni da kai."


Alaji Idris ya zaro mata idanu yana cewa, "A barki dawa? ai ko Allah bazai barni ba , sai dai kiji wufff na mutu ." Ya karasa maganar yana dariya


Ita ma Hajjiya dariya tai tana cewa, "To ai shi ke nan kowa na haka ne . To amma Alaji me zai hana kasha ruwa muje kauye a gaidasu , domin mun kwana biyu bamu je ba ."


Alaji Idris ya ce ,"Eh gaskiya ne wannan in sha Allah zamu je kuwa ." .....










Yanzu karfe 12 na dare , sai yanzu Uncle Yahaha ya tashi a bacci daga d'akin Fa'iza, yana tashi a firgice ya sakko daga kan gadon , Fa'iza dake kan kujeara sauri tai ta tashi tana kallonshi da cewa ,"Lafiya kuma ."
Ajiyar zuciya ya yi , sannan ya ce ,"Bansan zan yi bacci haka ba , ga shi dare ya yi , tafiya zan yi gaskiya. "


Ganin yana kokarin sa takalmi Fa'iza da sauri tasha gabanshi tana cewa, "Haba Yahaha dan Allah wanne irin tafiya kuma bayan dare ya yi haka kawai ka bari saida safe ." Ganin yadda take kwarkwasa ya sa yasha jinin jikinshi , ya fara mata magana cikin nutsuwa.
"Haba dai safiya , na bar kakata a gida ita kadai, kuma ban sanar mata zan kwana a waje ba , ni ban ta'ba kwana a hotel ba , kuma bugu da kari da mace ."


Shagwa'ba ta fara tana bubbuga kafafunta a kasa tare da girgiza jiki, "Ni gaskiya ka zauna ."
Shi kuma banza Uncle ya koma gado ya zauna jabar , "To shi ke nan na fasa tafiya , amma da sassafe zan tafi."
Wani dad'i ya kashe Fa'iza a tsaye ta karasa ta d'auko masa abinci .


Bayan ya gama cin abincin na wajen wasu mintina .
Fa'iza ta tashi ta jawo akwatinta
rigar jikinta ta fara kokarin cirewa
hakan ya sa uncle Yahaya saurin kauda kai ya kalli fuskar gado .
๐Ÿ˜‚ dariya ta yi tana kallonshi , tsat ta cire doguwar rigar , sannan tasa wacce bata kai wacce ta cire arziki ba , gadon ta hau ta zauna tana kallon Uncle


Uncle Yahaya yaji wani yarrr ,"Haba mene nasa irin wannan kayan kuma."


Dariya tai tana cewa, "Baby bana san yarinta , sai ka ce ba wani mara ilmi."


Hard'o wuyanshi tai tana cewa, "Wallahi ina san ka Yahaya aure nake son mu yi."
Duk ya rasa yadda zai da ita jikinshi ya fara rawa
"To shi ke nan naji sake ni."
Fa'iza ta sake shi tana murmushi








Lokacin da safiya tai , su Uncle Yahaya harda yin wanka sannan ya tafi gida wajen kakarshi domin ita kadai yake da ita.


Yana fita wayar fa'iza ta fara ringin tsaki taja sannan ta d'auki kiran .






"Yaya haka haba my baby zaki tafiya baki sanar dani ba , me ya sa ."
Daga can bangaren aka fad'a


Tsaki Fa'iza tai tai tana cewa, "Dole idan zani waje sai ka sani ne ."


Daga dayan bangaren cikin mamaki ya sake cewa ,"Kai Fa'iza ni ne fa , Abdul Salim ne ."


Dariya ta kwashe da ita tana sake tuntsurawa tana cewa dashi ,"To kana tunanin muryarka zata buya ne ,koba komai ai na yi saving numbobinka nasan kuma kai ne ."


Ya yi ajiyar zuciya tare da cewa ,"OK yaushe zaki dawo to."
Gaskiya ba yanzu zan dawo ba , domin babu kud'i a hannuna kuma ina san zan se wasu abubuwan in taho dasu ."




Abdul Salim ya yi murmushi yana fadin ,"Zan turo miki dubu dari ki yi hakuri da ita."


Fa'iza ta ce ,"Shi ke nan to ina jira ."


Abdul ya ce ,"To ko dai siyayyar aurenmu zaki fara ne."


Fa'iza tai tsaki tana cewa, "Wanne irin aure kuma , ni dai kasa min kud'in , sauran maganar sai na dawo."




Ya ce ,"To ba komai I love you. " Ya kashe wayar .






Shi Abdul Salim haifaffen dan legos ne da yake da gata , kuma dan masu fad'e aji dan manya, Yana son ya auri Fa'iza, bai taba lalata da ita ba , amma Fa'iza ba sonshi take ba , ya yi mata komai hatta gidan da take ciki a can shi ne ya siya , Saidai ba cikakken hankali gare shi ba , yana shaye-shaye , Kuma baya barin duk wanda ya zo masa da rainin wayo.






Harun ne zaune shi da Zainab a restaurant


Tun da ya sa idanunshi cikin nata bai cire ba , sai tunani yake kala-kala
Shin Zainab kuwa zata ba shi kanta , ko kuma maganar aure zai je da ita , to amma yasan Mahmud ba zai bari ba , hakan ya sa kawai yake jin gara ya yaudareta kamar yadda ya saba yiwa sauran 'yan mata.






Tom ni dai comment din na PC , share, like ...........๐Ÿ“š




Gubar Rayuwataโšก๐ŸŒน



By

Fatima Abdallaah kano
( Autar marubuta )







*AUTAR MARUBUTA CE*โœ๐Ÿป๐Ÿ‘ผ๐Ÿป
๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน__________๐ŸŒน_________๐ŸŒน
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐Ÿคฒ๐Ÿผ
<><><๐ŸŒน><><><>๐ŸŒน<><><>๐ŸŒน<><><><>๐ŸŒน<><><><><>๐ŸŒน<><>






Page 11&12








Zainab ganin yadda kallon ya mata รฑauyi , ya sa ta ta fara tsarguwa , ta kasa zama daidai .
"Harun lafiya kuwa kake mini irin wannan kallon."
Murmushi ya yi mara kunyan yana cewa, "Haba Zainab akwai abin da nake son sanar dake ."


Zainab murmushi ta yi tare da gyara zaman mayafin dake jikinta tana cewa, "To ka fad'a mini mana baby."


"Tom fatan kin shirya ji domin kalmar tana da zafi."


"Zafi kuma."
Zainab ta fad'a cikin mamaki


"Ina san ki."
Zainab ta kau da kai tana dariya


yayin da Harun ya ce ,"Ba fa abin dariya ba ne , Ina jin san ki a raina kamar zai fasa zuciya ta ya fito , Ina kaunar ki da dukkan yakini da sadaukarwa, fatan zan same ki cikin girmama soyayya ta da bata kulawa."
Ya karasa maganar yana duban cikin idanunta


"Ni ma ina san ka Harun , soyayyar da uwa takewa yaronta , soyayyar da bata da karshe kuma bata da misali , domin kai din Rayuwata ne ."


Murmushin farin ciki ya yi da jin wannan batun na Zainab
hakan ya sa ya fara fadin , "Gaskiya naji dadi Zainab amma ina mai sanar dake cewa Gobe zan yi tafiya zuwa gida wato garin Tiga zan gaida iyayena, domin fa kinsan anan gidan kanin ummanmu nake."


Murmushi ta yi Zainab da ya matukar kara fito da kyanta tana ce masa , "Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya , a kuma gashshemin da Umma ta."


"Karki damu my baby za su ji gaisuwarki Sarauniyar soja."
Ya yi maganar yana sara mata , ita kam ta yi masa dariya








Bayan malamin lissafi ya fita daga ajinsu Khadija
Ajin ya rufe da surutu yayin da wasu suke yin bitar lissafin


Laila ko rubutun ma batai ba ta yi tagumi idanunta sun kawo ruwa


Khadija ce ta dungureta tare da cewa ,"Haba Laila Adam mene yake damunki ne ."


Laila ta kalli Khadija tana cewa, "Wallahi ke ma kinsan Uncle ne , wallahi ina son shi , amma yanzu duk ba ya kulani , ko gani na ba ya yi , so yake ya juya mini baya , wallahi ina san uncle Khadija."


Khadija ta ce ,"Kuma babu abin da kika yi masa ."


Laila ta ce ,"Babu abin da nai masa Khadija, duk fa ya juyan baya."




Khadija ta ce ,"To ki bari anjuma ki same shi mana ."


Laila cikin fushi da bacin rai tace wallahi ko ganina fa ba ya san yi ."


Khadija ta ce ,"Tabbb ki ce dai akwai matsala. "






Yanzu dai Uncle Yahaya ko d'ar ba ya ji idan zai tafi hotel wajen Fa'iza
Domin kafin ya tafi makaranta ma ya sanar da kakarshi cewa ba zai kwana a gida ba yau , domin akwai aikin da zai , haka ta yi masa addu'a tare da fatan alheri....








Duk iyalan Alaji Idris zaune suke suna karyawa cikin farin ciki , domin Allah ya sauki Alaji Idris lafiya ya kammala azumi


wajen kwana uku ke nan


"Hajjiya kin san yau ne fa zami tafiyar nan zuwa kauye , da safiyar nan zamu tafi domin kinsan gari ne mai nisa kuma hanyar ba kyau ne da ita ba ."




Hajjiya Maryam ta ce ,"Alaji ke nan , ai na fika zumudi , domin tun dazu nasa Musa driver ya wanke mota , kuma ya zuba duk kayan abincin da za a kai musu."






Alaji Idris ya yi dariya yana cewa, "Eh lallai ki ce abin na yi ne , amma baba anje ba za ki ba ne ."?


Hajjiya tayi dariya tana cewa" Tabb ka ji Alaji da zance , baba mai jikin tsufa ina zata wannan garin , ai kam tayi zazzabi."


Dariya baba anje ta yi tana cewa, "Gaskiya kam ku je Allah ya dawo daku lafiya , ina nan dasu Nabila."


Jafar ya ce ,"Ai ko dai baba ki yi zamanki wannan garin ba abin zuwa ba ne kuma kauye ne."


"Ka ci gidan ku. Ina ce dangin ku ne ." Hajjiya ta yi maganar


Kalisa ce ta zumburo baki tana cewa, "Ni dai ina san zuwa momy."


Hajjiya ta ce ,"Ai na sani Kalisa danta Jafar da Nabila baza ai zumunci ba .


Alaji Idris ya mike da cewa ,"Hajjiya ki tashi mu shirya ina san har na dawo naje office. "


Ya shige ciki .






Bayan duk sun shirya suka fito harabar gidan
Duk suna musu a dawo lafiya


"Baba dan Allah karki bari yarannan su fita yawo , a kula dasu."


Hajjiya tai maganar cikin girmamawa tare da shigewa cikin mota


Sukai sallama suka tafi


yayin dasu kuma suka koma gida






Bayan wajen minti goma da fitarsu , sai ga GARBA ya shigo


Suke tabbatar masa Alaji sun tafi kauye


Garba ya koma yana takaicin rashin ganinsu domin ya basu sako zuwa wajen Shehu .




Bayan sun fito break Laila ta nufi staff don ganin uncle Yahaya


aiko yana zaune suna hira da wasu tsurarun malaman wanda duk kusan sa'anninshi ne
yana ganin Laila ta shigo ya had'e rai , hakan ya sa Laila Adam tasha jinin jikinta da 'ker ta karasa wajen shi ta tsuguna
Tun kafin ta kawowa ranta ta yadda za ta masa magana taji yana cewa, "Tashi ki tafi baki ganni da malamai ba ne."




Sau dubu nawa yake kiranta a gaban malamai ,amma yau yake wannan maganar, abin da ya zo mata kai ke nan


Cikin nutsuwa ta kalli cikin idanunshi da fuskar maraici ta fara magana da turanci ."Uncle dan Allah, wallahi na matukar damuwa da kai , mene na yi maka ."




Uncle Yahaya ya tashi ya fita waje
wani abu taji ya turnuke mata zuciya ta kalli sauran malaman wanda duk hankalinsu ba ya kanta , sannan ta tashi ta fita
Uncle yana can gefe yana waya ga dukkan alamu koma wayar me yake da mace yake yi


Laila ta sawa zuciyar ta wannan maganar


zafafan hawaye ne suka zubo mata , hakan ya sa ta kasa daurewa ta nufi aji tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login