Showing 30001 words to 33000 words out of 36747 words
Chapter 11 - GUBAR RAYUWATA BY FATIMA ABDALLAHI KANO .txt
bamu ga tashin hankali ba ."
Ya aje maganar cikin wasu zafafan hawaye da suka zubo masa , sannan ya maida kallon shi ga Sahid yana cewa, "Kai azzalumi ne mayaudari ka kashe Kalisa ka kashe mahaifin ka ."
Ya tun kude shi gefe
Sahid yana jiri ya ya tashi ya nemi hanyar fita ya hau mota ya tafi .Kai tsaye masaukinshi ya nufa wato hotel ya gyara jikinsa ya sauya kaya, kana yasha magani.
Kwanciya ya yi da nufin hutawa sai maganar Jafar take fado masa tana masa amsa kuwa .
"Kai azzalumi ne mayaudari ka kashe Kalisa ka kashe mahaifin ka."
Ya yi ajiyar zuciya ya tashi zaune, ya dauki mukullin motar shi da kafar shi mara lafiya da taji duka ya nufi gidan nasu .
Zuciyoyin su jafar tafasa suke yi matukar gaske, hakan ya sa suka fita domin daukar matakin da ya dace a kan Sahid.
Hauwa ce cikin wani babban falo suna hira da kawarta surayya
Hauwa ta zubawa Surayya idanu tana cewa, "Allah koh , ki ce sabon saurayi kika yi , shi kuma Faruk din fa."
Surayya ta kalli Hauwa tare da jefa mata wata harara tana cewa, "Shi fa soja ne, kuma wallahi ya kwanta mini a rai domin gaye ne Hauwa."
Hauwa ta ta'be baki tare da tashi tsaye tana cewa, "Kin ga ni tafiya zan yi , har akwai wani gaye da zai kuma shiga zuciyar ki bayan Faruk, wallahi kin bani kunya."
Surayya cikin dariya da zolaya ita ma ta ta shi tsaye tana cewa, "Wallahi duk sanda ya zo san had'aku ku gaisa besty ta."
"Mtwss." Hauwa ta ja tsaki tare ta bud'e kofar falon .
Lokacin ne wani farin mutum lukuti mai sanye da farar shadda ya turo kai , ba kowa ba ne kuwa fa ce ambassador.
Nan Hauwa ta gaidashi har yake tambayar mahaifin ta , nan take sanar masa yana gaida shi,
shima ambassador ya sake aika masa da sakon gaisuwa.
Haka Hauwa ta dawo gida.........
Anan bangaren su Zainab kuwa
Suna zaune a falo ita da yayan nata Ahmad, laptop ce a gabanshi yana dannawa
Zainab ta ce ,"Yaya Ahmad dan Allah ka yi hakuri ka bawa daddy hakuri, ka amson wayata, wallahi na tuba na canza."
Ahmad ya kalleta ya ta'be baki ya ci gaba da aikinsa
"Haba yayana Ahmad, wallahi na tuba ka kula ni mana , har abada babu ni ba HARUN."
Tsaki Ahmad yaja yana wurga mata harara "Dan Allah ki barni na yi aikina , ki bari ki kuma hankali da kanshi Dady zai baki."
Wayar Ahmad ce ta fara ruri , yana ganin mai kira ya dauka cikin farin ciki.
A yadda Zainab ta ga yayan nata yana waya tasan cewa Mahmud ne .
hakan ya sa yana gama wayar ta titsiye shi da tambaya, "Wa ne Yaya."?
Ahmad cikin farin ciki da washe baki ya ce ," Wallahi Mahmud ne , yana sanar min ya samu aiki a matatar mai ta kasa, abin ya farantan rai ."
Zainab ta yi murmushi tana cewa, "To yaushe zai zo."?
Ahmad ya jefa mata wani kallo yana cewa," To sannu , ke da ganin Mahmud sai Allah, sai dai ke ki shirya kije."
Ya cigaba da aikinshi
Duk atake Zainab ta shiga damuwa .
Bayan ya yi burkin motar shi a kofar gidansu, ya fito da kyer ya shiga cikin gidan .
"Assalamu alaikum."
Sahid ya yi sallamar a cikin gidan , wanda bai ga komai ba sai tabar ma a tsakar gidan , sallama ya sake yi a karo na biyu babu amsa .
Yanayin yadda yaji karshi shi na masa zugi da zafi ya sa ya nufi tabarmar da shirin zama
"Kar ka sake ka zauna mini a gida mugu azzalumi."
Cewar mahaifiyar shi data fito daga daki ,
a lokacin ne shima Jibril ya fito daga wanka .
Tsololo Sahid ya yi da baki yana kallan mahaifiyar shi dajin wannan furuci da ta yi masa
"Ka gaggauta fita a cikin gidan nan Sahid."
Ta kuma fada cikin kunci
Sahid ya daure ya ce ,"Mama da gaske ne baba ya rasu."?
Jibril dai bai ce komai kawai yana sauraransu
"Sahid ni mahaifiyar ka Binta , babu abin da zance maka tsakanina da kai , abu guda dana sani ka ci amana, kuma tana tafe domin cinka , ka je za ka gani."
Tana gama magana ta shige daki , Jibril ma ya shige dakinshi ya sanya kaya ya fita , yana fita ya ci karo da 'yan sanda tare da Umar da Jafar .
Kafin su yi masa tambayar ina Sahid, Sahid ya fito suka sashi a mota suka tafi .
Share and comment...............................📚
Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)
Editing❌
_________________________________________
Page 41 & 42
Hankalin Harun duk yabi ya tashi
ganin yadda wasu abokanshi da dama an turo musu sakon ni da yake tabbatar zasu tafi training amma shi Harun bai ga wannan sako ba ko tuntuba, hakan ya sa yake bibiyar inda matsalar take .
Anan ma Umar Allah ya ba shi sa'a sai dai ba ya so ya tafi training ba tare da yaga yadda kotu za tai ga Sahid ba ,
sai dai jafar ya tabbatar masa babu abin da zai gagare shi , tun da suna da kwararran lauya , ga kuma baba GARBA shi ma ya zo.
Haka dai Umar ya hakura ya tafi kaduna ba tare da ya so ba.
Maryam ce ta fito da gudu daga daki tana sheka amai , tana gama amai ta malale a wajen tana shure-shure .
Haka cikin gaggawa mahaifiyar ta , ta kira malam na lado suka tafi asubiti.
Yadda alakar Harun da surayya take , lokacin da yake sanar da ita matsalar da ya samu , har an tafi training babu shi , ya roki surayya alfarma data mika takardunshi ga mahaifin ta ambassador, domin ya yi magana da lu'utanal a kan shi.
Haka kuwa aka yi surayya ta karba , domin a halin yanzu ma takardun suna hannun mahaifin ta , amma har yau bai samu damar magana da lu utanal ba .
Allah sarki Maryam, lamarin dai har yanzu babu dadi , malam na lado da babarta sun shiga damuwa , haka dai dactor ya sa akai mata gwaje-gwaje , daga bisani ta samu bacci
Lokacin dasu Hajjiya, matar Alaji Kabiru da zainab suka zo dubata , har suka dawo bata farka ba, Zainab dai ta ji tausayin kawartata tana kuma mata fatan samun lafiya..
Fitowar ambassador ke nan daga gidansu Surayya,
ya hau mota rike da wasu takardu a hannunshi, sannan driver ya ja mota suka tafi .
Ambassador sake kallon wannan takardun na hannunshi ya ke yi , lokaci guda kuma yana sake mamakin yadda saurayin 'yar tashi Harun ya zama mai irin wannan mummunan hali da lu'utanal ya sanar masa.
Wanda lokaci guda yana sake tuna maganar da tafi tsaya masa a rai , da lu'utanal ya fada kamar haka .
"Lokacin da Hauwa ta zo min da zancen, sai da muka bibiyi rayuwar shi , muka tabbatar da zargin da ake masa sannan muka hana shi wannan dama , irin Harun mummunan tashin hankali ne zamansu cikin al'uma, kuma bugu da kari mu kara ba su gwarin gwiwa tare da basu aiki irin na soja , ambassador hakan ba mai faruwa ba ne."
Ambassador ya yi ajiyar zuciya bayan tunanin da ya gama .
Har suka isa cikin gida, ambassador jefi jefi abin yana damunshi , daga karshe yana shiga cikin gidan ya zauna a falo
Yadda matarshi ta ganshi haka , ya sa ta fara tambayar ko lafiya, nan take ya sa ta kira masa surayya.
Bayan surayya ta zo ya mika mata takardun Harun yana cewa
"Ki maza ki kira wannan yaron ki ba shi , kar na sake jin komai daga gare shi , hatta mu'amalar ku na wargaza ta."
Dauuu ta ji gabanta ya fadi
"Rabuwa da Harun kuma yanzu." Surayya ta fad'a a cikin ranta
ta kalli ambassador tana cewa cikin harshen turanci , "Dady me ya sa kuma ? Me yake faruwa."?
Nan take ambassador ya sanar wa da Surayya komai , da irin binciken da lu'utanal sukai a kan shi , har suka haram ta masa aikin soja."
Surayya ta yi matukar mamaki da jin hakan , abin ya matukar d'aure mata kai.
Tashi ta yi ta shiga daki da nufin kiran Harun ,
Amma sai ta fasa , ta kira Hauwa ta ce ta zo tana ji ranta.
Bayan Hauwa ta Harun Surayya ta sanar mata halin da take ciki , nan Hauwa ta sake tabbatar mata da waye Harun, ta tabbatar mata yaudara ce ta kawo shi, babu yadda Surayya ta iya ,
Ta kalli Hauwa tana cewa, "To yanzu mene abin yi Hauwa."
Hauwa ta ce , "Ki kira shi ya zo."
Ko awa daya Harun bai 'ba ta ba ya karaso
Ya shigo yayi parking da motar shi , sannan ya dauki waya ya kira Surayya.
"Ya zo."
Surayya ta yi maganar sa'ilin da ta kashe wayar tana kallon Hauwa.
Hauwa ta ce , "Ta shi mu je."
Surayya ta kwashi takardun suka fita .
Tun da ya hango su ya fara washe baki domin a lissafinsa
Surayya zata gabatar masa da kawarta ne , ya sa suka taho tare .
Suna karasowa Surayya ta sake had'e ranta , ammo sam Harun bai lura da hakan ba, domin yadda ya ga kawartata Hauwa zazzafa ya sa hankalin shi ya koma kanta yana kallonta sama da kasa.
Yadda Surayya ta lura da hakan ya sa ta sake jin tsanarshi ta kuma yadda da abin da aka fada mata.
Lokaci guda ya maida kallon shi ga Surayya yana cewa
"Annurin Rayuwata, barka da fitowa."
Tasssssss Ya ji saukar mari a fuskarshi
Da gigicewa da tsananin jin zafin marin da mamaki ya kalli Surayya , hannun shi dafe a kuncinsa .
Cikin turanci Surayya ta fara magana, "Kalle ni da kyau mayaudari, azzalumi ,na tsaneka Harun ."
Ta d'ago hannunta na hagu da ta rike takardun ta watsa masa
Sannan da yaren Hausa ta cigaba da cewa , "Sai ka kwashe su , kuma kai da aikin soja har abada. Allah ya mana tsari da kai yi waje ."
"Haba Surayya waya shiga tsakaninmu haka , ban yi muki komai ba , amma...."
Kafin ya karasa maganar ta sake shara masa mari tana cewa, "Matukar baka fita a gidan nan ba ka sake magana sai na sa an kulle ka."
Harun matukar mamaki ya rufe shi ya kasa gane dalili, idan ma shi mayaudari ne ta ya ta sani. Abin ya d'aure masa kai sosai.
Ya durkusa ya d'ebi takardunsa ya shiga mota ya tafi .
Surayya ta yi ajiyar zuciya tana kallon Hauwa.
Malam na lado yana Cikin tashin hankali , jikin Maryam babu kyau , gida suka koma sakamakon tabbatarwar likita cewa Maryam tana da ciki , sun shiga tashin hankali sosai
Tana matukar jin jiki sosai ko magana bata iya wa amma haka Malam na lado ya tsaya a kanta yana mata tsawa yana tambayar wanda ya yi mata ciki .
"Maryam yanzu wannan shi ne abin da zaki bar mana , cikin shege gidan malam guda." Mahaifiyar ta ta karasa maganar cikin kuka
"Wallahi kin bamu kunya kin cutar damu."
Maryam cikin radadi tana kuka tana kokarin magana ta fara neman yafiyarsu tana sanar dasu ba ba halinta ba ne ba kuma lefinta ba ne.
"To waye ya yi miki ciki Maryam." ?Malam ya tambaya cikin zafi .
Maryam tana gumi cikin jinya tana kuka ta fada musu yadda Harun ya yaudare ta .
"Lallai wannan yaron baisan gidan da ya zo ba , zan kuwa nuna masa ni Malam na lado malumtata ba a banza take ba."
Cikin huci ya karasa maganar
"Wallahi baba sam ba zan yi abin da zai cutar daku ba , daga karshe ake tabbatar min haka halinshi yake , ya yaudari mata da yawa, dah nasan zanga irin wannan ranar da na kashe kai na kafin ta zo."
Maryam ce ta yi maganar tana kuka , yayin da mahaifinta ya yaji duk tausayinta ya kamashi.
Haka ma mahaifiyarta ita ma ta fashe da kuka tana rarrashin Maryam.
"Allah ka gani na yi kokarin tsare amanar da ka bani ta Maryam, amma ga yadda ka tsaro lamarin ka."
Malam na lado ya fada cikin matukar rauni
Sannan ya kalli Maryam yana cewa, "Shi ya sa naso ya turo iyayensa , amma tabbas na yi sakaci , na yi babban kuskuren da bazan yafe wa kaina ba."
Share and comment...........................📚
Gubar Rayuwata⚡🌹
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)
Editing❌
_________________________________________
Page 43 & 44
Anan kuma cikin kotu an yi zama na farko tare da karanta irin tuhumar da ake wa Sahid, amma ya'ki yadda da wannan tuhuma , yana sanar da kotu babu wata cin amana da zai iya aikatawa ko handuma ,wanda har zata yi sanadin mutuwar Kalisa.
Jibril da babarshi ko kotun ba su halatta ba , haka alkali ya d'age shari'ar zuwa wani lokaci, tare da ba da belin Sahid.
Hauwa ce kwance kan kafar Hajjiya.
Hajjiya ta ce ,"Wai yaushe ne Abdallaah zai dawo daga Germany zamanshi ne fa ya sa bikin ku har yau ba rana. "
Hauwa ta yi Murmushi tana cewa, "Ai momy ya kusan dawowa, shi ma ya damu ya dawo fa."
Hajjiya ta ce ,"Ai gara dai ayi -ayi a wuce gun."
Hauwa ta ce ,"Yawwa momy kinga ashe wannan yaron Harun, wanda abokina Mahmud ya yi magana a kan shi , har Surayya yaje gunta."
Hajjiya ta yi dariya tana cewa, "Tabbb amma wannan yaro ko d'anbanza, yanzu shi ina Mahmud din."
Hauwa ta ce ,"Ba ya nan , amma ya ce idan ya shigo gari zai zo ya gaida Dady."
Hajjiya ta ce ,"To Allah ya kawo shi."
A halin yanzu kowa yana ta magana masu gulma da yamad'd'i suna ta yi cewa Maryam yar Malam na lado ta yi cikin shege , daga wanda zasu zagi ta da iyayenta sai masu Allah ya kyauta da fatan shiriya.......
Musamman yadda abin ya yi tsamari da suka koma asubiti aka tabbatar musu tana da cuta mai karya garkuwar jiki , nan malam hankalin shi ya sake tashi , haka suma almajiran malam duk abin bai yi musu dadi ba.
Haka ita ma Zainab ta sami wannan labarin, kuma an tabbatar mata da Harun shi ne wanda ya aikata mata wannan abu.
Zainab ta shiga wani hali tana ta kuka , yayin data tuna Lokacin da Mahmud yake shirin rabata da Harun take masa wani kallo, har ya kai ta wulakantashi , haka ta ringa kuka tsawon yini guda tana nadama .
A Yanzu babu wanda take son ji da gani idan ba Mahmud ba , amma yadda ta ga ba ta da damar , ya sa hankalinta ya sake tashi , cikin kuka ta nufi wajen Hajjiya ta sanar da ita komai kuma ta roketa da ta 'kar'bo mata wayarta wajen Alaji.......
"Umma yau ne za a zaman kotu na biyu." Jibril ya sanar da mahaifiyar shi
cikin mummunan 'bacin rai ta kalleshi tana cewa, "To mene."?
" Ba komai. " Ya ba ta amsa
"Ni tsakanina da Sahid kawai Allah ne zai mana hisabi , idan ma kotu ta sake shi ya dawo gidan nan ya ci gaba da zama , amman a ranar gobe akwai tsaiwa tsakanina dashi da mahaifin sa."
Jibril ya yi ajiyar zuciya yana jinjina dajin tsoron maganar mahaifiyar tasu."
Anan cikin kotu Lauyoyi sai musayar hujjoji suke , domin lauyan Sahid ya yi iya yinshi , har ya ke son gamsar da kotu cewa Sahid sam ba mai laifi ba ne bai kuma aikata wannan tuhuma da ake
masa ba .
Nan Lauyansu Jafar ya fara sanar da kotu manyan shaidu da kotu ta gamsu dasu , daga karshe haka Sahid ya rasa ta cewa har ya amsa tuhumar, yayin da lauyanshi bai iya kare shi ba .
Daga karshe lauyansu Umar ya nemi kotu data umarci Sahid da ya fito da dukkan dukiya da kadarori mallakin wannan marayu har wanda ya kashe ya fita birtaniya ,
Sannan lauyan ya mikawa kotu adadin kudade da kadarori da Sahid ya zaune."
Bayan alkali ya gamsu ya sanarwa da Sahid umarnin kawo wannan kadarori a zaman kotu na gaba........
Ana tashi daga zaman kotu Sahid asubiti ya wuce sakamakon ciwon kafarshi ,
Umar dai yana can , amma duk sanda akai zaman kotun yana bibiyar yaji yadda aka tsaya , wannan babbar shari'ar har gidan radio ake saurara..
"Malam wannan wacce irin rayuwa ce na shiga uku malam."
Mahaifiyar Maryam take fada cikin kuka yayin da take rike da gawar Maryam a hannunta .
"Malam Maryam ta rasu ta bar mana duniyar , ina zansa kaina , wallahi bazan yafewa wannan yaron ba , ya Allah ka ga yadda ya yi mana..." Ba tare data karasa maganar ba ta sake rushewa da kuka mai matukar gwanin ban tausayi .
Malam na lado shi ma baisan lokacin da wasu hawaye suka zu'bo masa ba , ya kalli