Showing 18001 words to 21000 words out of 36747 words
Chapter 7 - GUBAR RAYUWATA BY FATIMA ABDALLAHI KANO .txt
ta fad'a bayan ta amsa sallamar
Umar ne ya fara magana yana kallon Kalisa cikin kauns
"Tun da har yau babu labarin Sahid a kan me zamu zauna to baba , mun fita neman kud'in da za a mata aiki , kuma a halin yanzu mun sami dubu dari biyar ."
Nabila ce ta ce "To yaya Jafar me zai hana mu siyar da gidan da muke ciki."
Jafar yayi ajiyar zuciya tare da cewa "Nabila komai fa yana hannun wannan azzalumin babu takardun gidan ."
Umar ya yi ajiyar zuciya
Kalisa ce cikin wata muryar tsananin wahala ta ce "Akwai takardun wani gidan momy da dady ya bata , nasan zamu sami kudaden da zasu isa idan aka siyar."
"Alhamdulillah Allah mun gode maka." Baba ta yi maganar
Jafar ya ce aiko ba wasa za a yi ba yau za a siyar dashi in sha Allah komai zai tafi daidai."
Umar ya ce "In sha Allah kuwa."
Kalisa ta kira Umar kusa da ita cikin kasa da murya ta ce "Ina matukar kaunar ka."
Koda yaji hakan sai ya ja da baya cikin tausayi da wasu hawaye a cikin idanunsa
Sannan ya dago ya kalleta ya ce "Ni ma ina kaunar ki Kalisa zaki samu lafiya in sha Allah."
Baba anje ta ce "Allah kai ne abin godiya, ka bawa Kalisa lafiya."
Nabila ta amsa da "Amenn." tare da sake cewa "A gaskiya ya kamata a sanar da baba Garba duk ba su san abin dake faruwa ba."
Baba anje ta ce "Gaskiya ne za a sanar dasu."
Sallama da aka yi ne ya sa duk hankulansu ya koma kan kofar
Mahaifan Sahid ne suka shigo
nan aka basu wajen zama zamansu ke nan Kalisa ta fara shure- shure
hakan ya tayar da hankalin kowa saida aka kira dactor Aisha
bayan ta zo ta mata abin da ya dace har ta samu bacci .
Cikin tashin hankali malam Aminu yake tambayar dactor "Yarinya meke damunta haka."
"Baba tana dauke da mummunan ciwo a cikinta, kuma kullum tsanani yake karawa , sannan da fari kasar waje za a kaita , amma a halin yanzu an sami asubitin da za mata aikin , kud'in ne ba su samu ba , kuma ni gaskiya babu abin da zan iya mata kawai aiki take bukata , sannan a gwajin da mukai dalilin accident din nan karfen da ya tsagata ta sami cancer., Amma in sha Allah da zarar an mata aiki komai mai wucewa ne ."
Bayan ta gama ta musu sallama ta fita
Malam Aminu ya ce "In sha Allah."
Umar ya yi ajiyar zuciya yana cewa da Jafar "Mu je a nemi dillalai wannan ba abin zama ba ne Jafar."
Jafar ya ce "To yaya Umar."
Ya tashi cikin kasala da matukar damuwar da yake ciki .
Kafin su kai ga hanyar fita wani saurayi ya shigo cikin d'akin tare da sallama, nan take malam Aminu ya shaida shi ya caf ki sunan shi
"Sani."
Saurayin ya amsa tare da gashshe shi , sannan ya kalli Jafar yana cewa "Don Allah ka yi hakuri tun shekaran jiya MD Sahid ya bani sako a company amma ban kawo ba na mance ."
Ya Ka rasa maganar yana ciro wata takarda da aka sata a gidan sirri ya ba shi .
Ya musu sallama ya fita, kowa mamaki ne ya rufe shi har Kalisa da ba komai take iya ganewa ba.
Bayan ya bud'e takardar ya karanta a zuciyar shi , bayan ya gama ya yi shiru , yayin da ya barsu cikin tashin hankali dalili kuwa sun ga tashin hankali a tare dashi .
Mahaifiyar Sahid ce ta bude baki tana cewa dashi "Yaro mene a ciki me ya aiko haka."
Jafar ya kalli Kalisa cikin tsananin tashin hankali
Yadda Umar abin ya yi masa ciwo kawai ya karbi takardar ya fara karantawa shima a zuciyar sa
Bayan ya gama irin yanayin da ya shiga har yafi na Jafar
"Haba dan Allah wai mene wannan yaron ya rubuto kun yi mana shiru." Cewar mahaifiyar Sahid
Baba anje ta karbi takardar ta bawa Nabila.
"Nabila dan Allah karanta mana sun bar mu a duhu." Baba ta yi maganar cikin damuwa
Idanunta fal da hawaye ta karbi takardar cikin rawar jiki
muryarta na rawa ta fara da cewa "Assalamu alaikum.
Kalisa ku yi hakuri amma a halin yanzu babu wani kud'i da zaku samu duk da naku ne , ba zan baku komai ba balle ku fita kasar waje, a halin yanzu nayi biza ina birtร niya kuma ina da hakki cikin dukiyar Alaji Idris don haka na tafi na ci nawa .Sai wata rana."
Cikin mummunan yanayi Nabila ta aje karatun tare da tashin hankali
"Na yi asarar haihuwa , Sahid mutumin banza ne wallahi, Allah wadaran ka." Mahaifinsa ya yi maganar cikin kuka
lokaci guda kuma ya fad'i kasa
Hankalin matarshi ya tashi , hakan ya sa duk su Umar suka yo kanshi , da gudu Nabila ta fita kiran likita tana zuwa wajen doctor Aisha ta turo wasu nurse zuwa wajen shi .
Bayan sun kanshi daki cikin hanzari ita ma dactor ta shigo dakin domin taimakon gaggawa .
Zuuuu duk suka fita Nabila da Kalisa aka bari a dakin .
Lamarin yana dukansu , a can daga waje kuwa mahaifiyar Sahid kuka take tana cewa, "Wallahi shi ke nan malam mutuwa zai , zuciyar shi ta buga , yaron nan duk irin hidimar da Alaji Idris ya mana bai gani ba , Allah wadaranka Sahid, ka yi asara ka kashe mahaifin ka , wallahi ba zan yafe maka ba."
Baba anje ce ta fara bata hakuri cikin rarrashi "Ki yi hakuri , ba mutuwa zai ba , babu abin da zai same shi ."
Ta fusge jikinta a jikin baba anje tana cewa "Ni nasan halin malam wallahi, shi ke nan malam sai mun taho." Tana gigicewa da kuka
Ran Umar da Jafar duk ba dadi , Allah ne yasan ciwon dake ransu .
Dactor Aisha tana nuna kwarewa , yayin da tai saurin masa abin da yake bukata hakan ya tabbatar mata yana da rai .
Yayin da daya a cikin nurse din ke shiran sa masa ruwa ne , ya fara fisge fisge sai aman jini.
Nan doctor Aisha ta dawo kanshi .
Anan waje kuka kawai matarshi take , cikin kukan ta kira yayan Sahid take fad'a masa malam Aminu ya mutu, cikin tashin hankali ya fanno asubitin.
Zama ta yi dirshen tana ta kukanta , har baba ta gaji da rarrashi .
Sannan sai doctor Aisha ta fito tare da nurse din .
"Ba sai kin fad'a mini ba nasan ya mutu ๐ญ jeki abin ki." Matarshi ta yi maganar cikin kuka
"Likita ya ake ciki ya jikin nashi ."?
Jafar ya tambaya yayin dasu baba duk suke jiran amsa
likita Aisha ta fara magana" Ku yi hakuri Jafar , mun yi iya yin mu dan cetar ransa , amma Allah ya amshi abinsa."
Dauuuuu suka ji zuciyoyinsu na wani dukan dubu dubu na tsantsar tashin hankali.
Aisha suka wuce suka basu guri .
"Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un.Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un. Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un"
Baba anje ta fada cikin tashin hankali, su Umar duk sun kasa cewa komai
Ba a dade ba danta Jibrin ya karaso asubitin, shi ma , aiko su Jafar cikin wannan tashin hankali suka bisu kauye har saida aka shiryashi aka sallace shi sannan da aka kaishi suka dawo wajen dare.
Allah ya sa mu dace
Share and comment..........................,..๐
Gubar Rayuwataโก๐น
By
Fatima Abdallaah kano
(Autar marubuta)
___________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*โ๐ป๐ผ๐ป
๐น__________๐น_________๐น__________๐น_________๐น
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐คฒ๐ผ
<><><๐น><><><>๐น<><><>๐น<><><><>๐น<><><><><>๐น<><>
Page 25 & 26
Duk da Kalisa ba ta ce komai ba amma tabbas zuciyar ta babu dadi tun d'azu take kuka , anata rarrashinta amma ta kasa iya dena kuka .
A washe gari bayan sun sayar da gidan , dactor Aisha take tabbatar musu dole Kalisa a fitar da ita domin da tun da fari a matakin ciwon na farko an san abinyi shi ne za a mata aikin anan.
Haka dai basu ji dadi ba , amma gwarin gwiwar da suke samu Kalisa zata samu lafiya ,
Duk yau wani farin ciki suke yi domin zuwa gobe Kalisa za a fitar da ita India
wajejen yamma kuwa sai ga Baba Garba , aiko nan ya yi ta musu fad'a a kan rashin sanar dashi da wuri .
Jibril magana d babarshi a kan Sahid
Bayan magariba ta dauko kai Baba anje da farin cikinta ta ce "Nabila ta shi ki tafi gida ki shiryawa muku duk kayan da zaku bukata domin kinsan jirgi ba ya jira ."
Nabila ta ce "To baba bari naje gidan , su ka yi sallama tafi.
Yau dai a 'kallah duk sun sami farin ciki , domin yadda suka saki fuskokinsu abin farin ciki ne , sai dai ma mutuwar mlm Aminu ce duk wani bacin ran.
10:02 na dare
Baba anje ta fad'a a ranta " Nabila dai gida zata kwana ke nan , to Allah ya sa ta zo da wuri , ai Jafar ma na gidan shi da Garba ."
Jafar ma yana komawa gida babu wata-wata ya kwanta domin ya matukar gajiya .
Washe gari da safe
Laila ta samu lafiya har barrister Adam ya sama mata makaranta ta ci gaba , haka ta ci gaba da Rayuwar ta cikin aminci da kaunar iyayenta .
A 'bangaren Uncle Yahaya kuwa shiri yake zai koma Lagos wajen Fa'iza, domin ya sanar da ita halin da yake ciki , hakan ya sa ta turo masa kud'i domin ya koma kusa da ita , tun da dai yanzu ba kowa yake dashi ba .
Aiko yau din nan zan tafi lagos ๐ด๐
"Karfe nawa jirgin zai ta shi." ? Baba ta tambaya
"11."
Jafar ya bata amsa a gajarce
"To amma Nabila ina ta shiga ne , ko abinci take yi ne , tun jiya ban zata zata kwana a gida ba sai ga shi ta kwana kuma har karfe 9 shiru."
Baba anje ke nan
Jafar ya ce "Ai na yi zaton ma anan ta kwana domin jiya banganta ba ."
Darammm a zuciyar Kalisa da Baba anje
Kowa shiru ya yi yana sake-sake cikin ranshi , Jafar ya ciro wayarsa a aljihu ya ya nufi numbar Nabila domin kira,
wayar ko shiga ba tai ba balle ya sa ran jinta
Jin sallama duk ya sa hankalinsu ya koma kofar shigowa
"Assalamu alaikum".
Suka amsa sallamar tare da wani yanayi a cikin furkarsu
Baba garba ne ya shigo , shi ma yadda ya gansu ne ya sashi tambaya
" Ya haka , ko lafiya na ganku haka."? Ya karasa maganar ya na zuzzura musu idanu,
"Nabila ce ba a ganta ba."
Jafar ya ba shi amsa
"Subhanallahi kamar ya kuma Jafar."?
Tun kafin Baba Garba ya yi magana , Umar ya shigo yana tambaya
Duk shiru sukai kawai suna jin abin a ransu,
" Bata kwana a gidan ba ne ko ya". ?
Baba Garba ya yi maganar yayin da ya katse musu sake -saken su."
A wannan karon ma dai Jafar ne ya fara magana "Ni wallahi ban sani ba , jiya na gaji hakan ya sa ina shiga gida na kwanta."
"Kuma ba ta makota."? Baba anje ta jefawa Jafar tambaya
Jafar cikin takaicin yadda kowa shi yake tuhuma ya fara cewa " Ba mu tabbatar ba kawai mu fita mu duba." Ya karasa maganar tare da fita bai jira kowa ba .
A jiyar zuciya Kalisa tai , ba tare da ta ce komai ba
amma kana iya hangar tashin hankalinta a furkarta .
Bayan Uncle Yahaya ya sauka a legos, yabi wannan adireshi na Fa'iza ,wato inda gidanta yake , babu jan lokaci ya sami gidan
"Assalamu alaikum."
Uncle Yahaya ya yi sallamar a gidan Fa'iza tare da takatsan-tsan din kamar ba gidan ba ne , ba tare da ya kuma sallama ba ya ringa duban gidan yana lekawa
Jin muryarta ne ya tabbatar masa tabbas ya zo gidan masoyiya
"Haba baby, ni daya ce fa a gidan , daga ni sai kai , sannu da zuwa."
Ta karasa maganar yayin data aje buta tare da jan bandakin data fito .
Ajiyar zuciyar farin ciki ya yi yana gyarawa jakar kafadarsa zama yana cewa "Ga kyakykyawata farin cikina yau a gabana."
Wani irin kallo Fa'iza tai masa tare da kashe ido , lokaci guda kuma tana kai hannu tana karbar jakar tashi."
Suka nufi daki suna shiga dakin wayarta ta fara ruri , tabbas tasan Abdul ne , hakan ya sa bata bi ta kanta ba ,
shi ma Yahaya ko tayin daukar kiran bai mata ba , domin ga dukkan alamu bai ma jiba , saboda wani shegen kallo da yake binta dashi .
To ga dai Uncle Yahaya a lagos
Ko ta ina zai fara , kuma ya zai rayu
Ga kuma bangaren Kalisa, har yanzu babu labarin Nabila, da Sahid, ga ciwonta kullum abin tafiya yake , ko Kalisa zata sami lafiya?
Ga kuma bangaren Zainab da Mahmud, ga mutumin ku Harun .
Tofa duk ba za mu ji yadda abin zai kasance ba ,sai mun had'u a
A tare da ni Fatima Abdallaah kano
Wato Auta ga marubuta
Mu had'u a kashi na biyu karku mance fa ๐
Share and comment..................................๐
Gubar Rayuwataโก๐น
By
Fatima Abdallaah kano
. (Autar marubuta)
______________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*โ๐ป๐ผ๐ป
๐น__________๐น_________๐น__________๐น_________๐น
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_๐คฒ๐ผ
<><><๐น><><><>๐น<><><>๐น<><><><>๐น<><><><><>๐น<><>
Page 27 & 28
Duk hankalinsu ya gama tashi matukar gaske, har magariba ta yi amma babu labarin Nabila , da tananan sun tabbatar yanzu Kalisa tana India, amma duk inda ya dace a duba kuma a tambaya an yi , sai dai babu wani cigaba.
Allah ya kawo sauki da mafita , haka rayuwar take, kowa da kalar tashi kaddarar.
Washe gari
Jibril ne zaune kusa da mahaifiyar shi yana rarrashinta , tun da garin Allah ya waye take kuka
Cikin tausayin mahaifiyar tashi Jibril ya ce "Babata dan Allah ki jure wannan jarabawar , wallahi komai mai wucewa ne ."
Cikin rashin gwarin gwiwa ya karasa maganar
Cikin kuka tana face majina tana gogewa da zaninta ta ce "Wallahi Jibril kaninka ya yi asara duniya d lahira , domin ba zan yafe masa, ya je indai duniya ce , wanda ba su zo ba ma jiransu take , sai ta sashi kukan da babu hankicin da zai share masa."๐ญ
Ta kuma fashewa da kuka
Jibril duk ya kasa cewa komai domin zuciyar shi shi daya yasan zugin da take masa .
Kasar waje
Sahid ne ya fito daga asubitin kashi yana dingishi , guri ya samu ya zauna
iska mai dadin gaske ce ke kai wa tana dawowa , ga duk kan alamu yana jin dadinta fiye da su mazauna kasar
Lokaci guda kuma ya hade rai yana magana shi daya , yayin da ya hango wani gurgu bisa keke ana turashi
" Allah ka raba mu da wannan masifar kawai a yankewa mutum kafarsa ,
wannan asubitin za su min komai ba sai na koma Nigeria ba , Allah sarki babata da na ce ciwo zata daukon magani ,
ni da na koma Nigeria sai na yi aure na haihu da baturiya ,daga nan ma Pakistan zan wuce."
Ya aje maganar yana kallon ambulance din da suka shigo asubitin.
A d'azu jikin Kalisa ya rikice sosai da sosai , nan hankalinsu ya tashi
sun yi kokarin fitar da ita , amma Kalisa ta ce bazata bar kasar nan ba ba tare da tasan halin da kanwarta ke ciki ba .
Duk da an sanar da 'yan sanda amma har yanzu ba ta sauya zani ba
Fitar kannen Umar ke nan daga asubitin , su biyu mace dana miji
macen tana kuka da wannan yanayi data gansu a ciki. To ya za ai da lamarin ubangiji
Umar ya matukar ramewa sosai , su baba anje ma ba a cewa komai ga su Jafar da Garba , abin dai sai wanda ya gani.
Jingum suka yi duk din su a dakin
wayar Jafar da take ruri ne kawai ya sa ake jin wani sauti
da kasala ya cirota a aljihunsa tare d amsa kiran yana karawa a kunne .
Koda jin wata kakkausar murya ce ke magana hakan ya sa ya tashi tsaye , yayin da duk hankulansu suka dawo wajenshi
Da alamar