Showing 1 words to 3000 words out of 24103 words
Chapter 1 - WASU MAZAN Part 1 Complete By Ummu hibbat .pdf
Duk da irin saurin da nake yi bai hana na tsaya na jira shi ya fito ba. Kasancewar ina girmama
dukkan abin da ya sha fe shi. Kusan rabin awa kafin ya fito.
K'afafun sa da ya zuro na zubawa idanu ina kallo, yadda halittar k'afar ta cika kai ka ce shi ne
ya zana abarsa.
Bayan haske da k'afar take da shi ta kasan ce tana wani irin walwali mai d'auk'ar idanu. Duk da
hannu bai tab'a ba tabbas ma'abocin kallonta ya san fatar zata yi laushi. Shadda ce sanye a
jikinsa mai launin ruwan toka.
Haka hular kansa take ita ma. Fuskarsa kuwa sai walwali take kamar hasken wata daran
goma sha biyar. Sajen fuskar kuwa kai ka ce wani mai ya kwaranya a wurin yadda yake shek'i
da walwali.
Amma duk da wannan yanayi na fuskar sa bai sa ya cika cif ba, saboda kowacce halitta
cikar kyaunta tana k'ara cika a lokacin da fuskar ta kasance cikin murmushi.
Kallon gatsali na yi masa cike da jin haushin sa yadda yake jin kansa kamar wani na mijin kirki.
A zahiri kuwa cewa na yi; ''Sannu da fitowa bombino."
Halin na sa ya yi mini wanda ya sa ba, wato k'in amsa magana a kan lokacin ta. Sai chan
sannan ya bud'e karamin bakin sa ya ce dani. "Yawwa, muje na sauk'e ki a school tunda ba ki
fita ba."
"Idan ka kaini kuma da wacce mota zan dawo? Ai gwanda na je da motata." Na furta cikin
sakin fuska . Bai kalle ni ba ya fara shirin fita daga falon sai da na mik'e ina bin sa sannan
yace; "Wanda ya kaiki ai zai iya d'auko ki."
Ban tanka masa ba na wuce na je na shiga motarsa ya shiga shi ma ya ja muka fita mai gadi ya
rufe k'ofa.
Tafiyar kurame mukeyi ni da shi ba wanda ya kuma yiwa d'an uwansa magana. Daidai bakin
makarantar mu ya ajjiye ni wacce take anguwar ta'alawa a cikin garin gaidam. Ha'islamic ita ce
makarantar da nake zuwa karatun addini duk ranar asabar da lahadi. Ina fitowa kuwa idanuna
cikin na nabila k'awata da maryam sun kusa k'arasowa bakin get d'in makarantar. Murmushi na sakar masu na kulle masa motar sa ya ja ya tafi. K'arasowa sukayi muka gaisa
suna ta min tsiya da matar mijin ta, sunan da suke k'irana da shi ke nan.
Ban ce da su uffan ba na wuce suka rufa min baya.Muna shiga muka hangi malamin tauhidin
mu ya shiga ajinmu. Da sauri muka k'arasa dukanmu muka shiga ajin. Karatu ya mana
sannan ya d'aura da mana nasiha ya fita.
Yana fita kuwa adama me dambun kifi ta wangale bakin robar dambu da nufin mu siya.
Jujjuya shi na yi na dubi k'awayena na ce da su kowa ya d'au d'aurin naira d'ari-d'ari zan ba ta
kud'in.
Ko da jin haka tuni adama ta yarfa tafi tare da fad'in; " Ahayye! Ka ga manyan mata masu aji
sun bayar da yawa an cika masu aljihu." Idanu na zaro sosai nace; " Adama, muna cikin
islamiyya kike cewa haka?"
" Yo mene ne a ciki tunda dai gaskiya na fad'a, ke ni wallahi kina burgeni irin yadda mijin ki
yake ji dake d'innan." Adama ta fad'a tana kaimin dukan wasa kan cinyata.
Gab'a d'aya sai kunya ta lullub'eni na sunkuyar da kai k'asa, cikin zuciyata kuwa ji na yi wani
irin d'aci ya mamaye min ita sanadin yadda kowa yake min kallon macen da take more rayuwa
a gidan bombino. Da sun san irin tashin hankalin da nake ciki da ba za su ce haka ba. Su
kuwa su nabila tuni kowa ya washe baki suka d'auki na su d'aurin suna sha suna saka min
albarka tare da cewa adama; "Wallahi ke dai kin shiga uku da shegen b'aran-b'aramarki, sai
kinje wataran kin manta kinyi a gaban malam tukunna."
"Ke rufa mun asiri! Da ranar na fita ta taga kuwa. Yadda malam yake min kallon nutsatstsa."
Adama ta fad'a tana rik'e haba.
Kafin su kai ga bata amsa malamin da yake mana tafsiri na alku'rani ya shigo. Don haka tuni
muka nutsu muka gyara zama .
Misalin k'arfe shabiyu na rana aka mana fatiha muka fito muna hirarakin mu wanda muka
saba yi na raha da juna.
Kamar an ce na d'aga idanuna na kalli bishiyar da take k'ofar makarantar na hango shi zaune
cikin motar sa yana latsa wayarsa.
Maryam tace; "To Samha anan zamu rabe ga chan mijinki ya zo d'aukar ki don haka ba ni
littafina na tafsiri mayi magana ta wasaf." "Ke kam ki barmin mana na je na duba sosai tunda
na wa ya b'ace k'asa ko sama." Na fad'i haka ina marairaice fuska."Kayya sa! Ai kawai ba ni
abina kiyi hak'uri saboda kanki ya fi nawa ja kin sani sosai."
Sanin halin bombino zai iya juya motar sa ya tafi idan na tsaya b'ata lokaci tuni na b'ata
kayanta na na wuce ina murgud'a mata baki ina harararta Na ce; "Sannu me kan dankali."
Ko da na shiga cikin motar da sallama na shiga ina kallon yadda yake danna wayar sa cikin
nutsuwa, amma kuma bai ko waiwayo ya dube ni ba bare ya amsa min. Wani k'arago me tauri
na ji ya tsaya min cikin mak'ogwarona ga wasu kwallah da suka cikamin idanu kasancewa ta
mai saurin kuka. Jin ya tayar da motar shine ya tabbatar min da cewa lalle ba zai tanka min sallamar ba. Ba
wata tafiya me nisa mukayi ba muka zo gida da yake muna anguwar laa'anti da zama
Bayan me gadi ya bude mana mun shiga har zai wuce na ce; "Yanzu Awwal halinka na yiwa
mutun banza har ya kai ka fara k'in amsa sallama?"
"Au daman ce miki a kayi dole sai an amsa sallama a zahiri tukunna kake da ladan?" Ya ba
ni amsa.
Ban ce komai ba na wuce d'akina na cire kayan makarantar da yake jikina.
Tunanin abin da zan dafa mana nake kasancewar yaran nawa suna gidan hajiya
mahaifiyarsa, chan duk ranar juma'a suke tafiya sai lahadi za su dawo da yamma saboda
makaranta. Ganin zaman tunanin zai sa na b'ata lokaci sai kawaina wuce madafa na dora jalof
d'in taliya wacce ta ji kayan miya da bushashshen kifi . Kunun aya na had'a mai rai da lafiya ta ke na gama komai kasancewar na yi amfani da gas
ne. Kan daining table na shirya komai .
Ganin Awwal zaune kan d'aya daga cikin kujerun falon yana murmushi sai na ji farin ciki ya
kamani . Da yake ba ni da zuciya wajen biyan bukatar zuciyata kuma ganin yara basa gida na
ce bari na yi amfani da damata.
Cikin sauri na shiga toilet na fesa wanka na kwara turaren wanka mai k'amshin gaske a jikina
na fito na saka kaya masu kyua riga da wando wanda ko mak'iya su ka kalla tabbas ya san na
yi kyau kayan sun zauna min daram. Mai me kamshi na shafa na saka hoda da lipstic na sanya
wata hula kalar kayan na sake feshe jikina da turare masu kamshi. Da yake na yi alwala daman, sallaya na d'auka da hijabina na fita falo domin muyi jam'i idan a
gida zayyi.
Ina fita kuwa na tarar ya shimfid'a sallaya ya kalli gabas yana shirin tayar da ikamar sallah,
bayan sa na shimfid'a na bisa mukayi sallah har muka sallame. Bayan addu'o'i sannan na ta
shi na lunke hijabina na ajje kan hannun kujera tare da sallayar na gifta ta gabansa ina wani irin
taku wanda dukkan wani mai lafiya idan akayi masa haka tabbas na san zai ji a cikin jikin sa. Tun kafin na ida zama na ke jiyo takunsa ya nufo ni zuwa wurin daining table d'in. Har wani
runtse idanuna nake yi ina jin yau de kam na gama da shi tabbas na san hak'ata zata cimma
ruwa.
Jin shiru shine ya ba ni damar bude idanuna na hamgoshi yana gyara labulen wurin. Duk sai
na ji jikina yayi sanyi sosai . Abinc na zuba masa na zuba nawa na saka mana cokali na zauna
tare da fad'in bismillah. Wuri ya samu ya zauna ya kalle ni da halamun murmushi ya ce, "Sannu
da hidima." Har cikin zuciyata na ji dadin yabon duk da cewa ba yau ya fara ba, saboda abin ya
zame masa kamar sabo ko na ce sara.
Har muka gama cin abincin ina satar kallon sa ina kallon yadda idanun sa suka sauya kala
zuwa launin ja a maimakon farare kuma yana lumshe min su da wani irin kallo wanda na
tabbatarwa da kaina tabbas hak'ata zata cimma ruwa.
Sai dai kash! Yana gama cin abincin ya mike ya wuce falo ya kwanta kan kujera yana ta
zabga hamma . Ko da na gyara wurin na zauna gefen sa naga yadda zamu kaya na d'auki rimot
na tv na kama tasha sai ji nayi ya ce, "Don Allah Samha bacci zanyi kije falon ki kiyi kallon
mana." Wata mahngurbar damuwa ta ziyarci ziciyata kamar na zuga masa zagi na mik'e a fusace na
ce; "Ko baka fad'a ba tabbas zanyi hakan!" Har ina had'a hanya na wuce uwar d'aka na fad'a
gadona tare da barkewa da kuka.
Me Awwal yake nufi da ni ne? Ba shi da ishashiyar lafiya ne ko kuwa dai ina da matslane
wacce za ta hana shi ya sauke hakkin da yake kansa? Wace rayuwa ce hakan? Kullum a ce miji
yana guduna sai rabon haihu ya zo sannan zamu zam abu guda? Idan har ba ni da lafiya ko ina
da matsala tabbas ya kamata na ga haka a lokacin da k'addarar haihuwa ta kawo shi wurina.
Idan kuwa haka ne Awwal shi ne da matsala ba ni ba, to amma ta ya zan iya magance wannan
matsalar cikin sauki? Idan na ce zan rabu da Awwal kan wannan dalilin to ta wacce siffa zan
bayyanawa iyayen nawa matsalar? Saboda magana ce me girma. Haka zalika yadda 'yan uwa
da dangi da sauran mutane suke ji cewa na fi kowacce mace sa'ar samun miji na gari da kulawa
ba zasu gamsu da magana ta ba.
Musamman idan aka duba yadda Awwal yake da k'ira da karfi da kwarjini ga yanayin idanun
sa sak na kwaratan da suka kware wajen kallon matan mutane a titi. Duk da cewa na shi idanun
kalar su ce haka. To don haka zayyi wuya abin da zan fad'a ya zauna akan al'umma.Kuma idan
har na ce zan bar Awwal na barshi ba tare da d'aukar wani mataki ba tabbas rayuwata tana
cikin hatsari. Domin d'ayan biyu ne. Ko na tabbata cikin b'akin ciki ko kuma na zama mage da wuri. Da irin wad'annan tunanin
bacci yayi gaba da ni.
Ban farka ba sai kusan hud'u saura.
Don haka alawala na shiga toilet na yi na tayar da sallah ba tare da na fita falo ba. Bayan na
idar ne na fita domin na je kitchen na d'aura girkin dare.
Yadda na barshi yana baccin asara haka na tarar da shi. Har zan tayar da shi sallah a
zuciyata na ce barshi shi ya sani yayi ta baccin tunda shi ne ya koreni.
Ina chan ina aiki na ji motsin yana sallah a falo. Dan haka da na fito falo na zauna ina jira abin
da na d'aura ya nuna, har ya idar da sallah ya dube ni.
"Wai daman kin farka amma baki tayar
dani na yi sallah ba? Ya ce da ni.
"Kai fa ka ce na barka kayi bacci, tunda baccin ya fi komai mahimmanci a rayuwarka me zai sa
na ta she ka daga bacci?" Na bashi amsa cikin fusata.
Kallona ya yi ya kauda kai sannan ya ce. "Lokuta da dama kina fad'amin kalamai marasa
d'adi ina hak'ura amma abin ya fara isa ta fa."
"Au iya kalamai ne ma? Ai da sauki tunda ba cutarwa!" Na ba shi amsa na wuce kitchen
Shuru ya yi yana nazarin, chan kuma sai ya mik'e yana fad'in; "Yau zan kawo k'arshen rainin
nan naki Samha!"
Ya fad'a da k'arfi ta yadda zan iya jiyowa....
2
"Hummm! Ka yi ka gama wallahi indai baka sauya haliba kad'anne ka gani."
Na furta ta yadda ba zai jiyo ba. Aikina na saka a gaba har na kammala na gyara ko ina ina
faman had'a gumi, don haka falo na koma na zauna ina shan ac har na huce. Ana shirin yin
sallah na shiga toilet na watsa ruwa tare da alwala na fito na saka wata doguwar riga mara
nauyi ta yadda ba zanji zafi ya takuramin ba ko da an d'auke wuta, tunda sai ya ga dama zai
kunna mana inji yau kam yana ji da bala'i.
Bayan na yi sallah ina zaune ina lazumi ban ji motsin shi ba hakan ya tabbatar min da baya
gidan tun da mukayi magana sanda nake kitchen, kan kujera na koma na zauna ina jiran na ji
da me zai dawo amma shuru. Sai kawai na mance da batun sa bayan na yi sallar isha na hau
online muka fara bitar karatun mu da k'awayena na school. Jin shigowar motar sa ce ta sa na kashe datar domin na ga zuwan sa.
Hankalina na maida kan tv ina kallo sai na ji ya yi sallama, ina juyawa tare da amsawa na ga
kawu habu k'anin mahaifiyata ya rufa masa baya suna shigowa.
Cikin zuciyata na ayyana ke nan k'arata ya kai.
Zamowa na yi daga kan kujerar ina fad'in; "Kawu barka da zuwa, kaine a tafe ke nan?"
Wani kallo ya watsamin tare da fad'in, "kin ci gidan ku Samhatu! Kinji ko, wato ke da muke
ganin kin fi kowa hankali cikin 'yan uwanki ashe ba haka bane. Yanzu Samhatu mene ne kika
rasa a gidan yaron nan Awwalu, kin samu ci sha sutura walwa kina makaranta, yaron nan har
da mota ya siya miki, duk fad'in garin ku mata na wa ne kuke da mota? Ke baki ga wannan ma
darajawa ba ce. Alheri kuwa kaf! Family kowa ya san da shi. Yaran ki duka sun banbanta da na
sauran mutane, wajen sutura da walwala. Ku ci me kyau ku sha me kyau akwai abin da kike
nema fiye da hakan"
Wallahi ki shiga hankalinki, kiyi wa mijinki biyayya karna kuma jin ya kawo kashenki."
Lumfasawa na yi tare da juyawa na kalli shi me kai k'arar sai na ga wayam ba shi ba
labarinsa ashe ya wuce d'akinsa. Cike da damuwa na ce; "Kawu ka yi hakuri zan kiyaye hakan
in sha Allah."
"Yawwa da dai ya fi miki dai a wannan zamanin zaman auren shine rufin asirinki."
Ya fad'a tare da juyawa zai fita a falon daman ko zama bayyi ba. Awwal ne ya fito ya bi bayan
sa yana fad'in Kawu bari ma maida kai gida .
Fita suka yi na koma falo na zauna gajaf a kan kujerar na ce, "Zaman aure ko zaman girki?"
Sanin ba ni da amsa shine ya sakani na bud'e data na cigaba da karatuna.
Kusan goma na dare sannan ya dawo, abinci na je na zuba masa na ajjiye a gabansa nima
na zuba nawa. Da bismillah muka fara ci, can sai na dube shi na ce, "Ka kai k'arata wurin Kawu
maimakon ka zauna da ni ka tambayeni dalilin faruwar hakan. Ko da yake kasan amsar kawai
rashin girmama auren ne da kuma rashin soyayya." Har muka kammala cin abincin bai kulani ba sai da ya zo tafiya ya ce dani, "Ina jiranki a
d'akina, kuma karki wuce shad'aya baki zoba."
Yana gama fad'ar haka ya fice abin sa zuwa d'akinsa.
Da sassarfa na bi hanyar d'akina ina ganin duhu-duhu saboda zallar damuwar da nake ji a
zuciyata, anya kuwa Awwal ba zai saka min hawan jini ba? Yanzu wannan wacce irin rayuwa ce
haka? Hummm! Allah ka shiga lamarina. Na furta a cikin zuciyata.
Shirya kaina na yi cikin shiri na musamman, ina addu'a araina Allah ya sa na yi kwanan farin
ciki.
Ko da na tura k'ofa yana kwance ya juya min baya wanda hakan kusan ya zame masa sabo.
Ko kunyata ma yake ji ban sani ba, domin kuwa Awwal matukar ya zo da wata b'ukata to
mungama had'e idanu da shi sai kuma yinin ranar wajajen yamma. Ni fatana Allah ya sa ba
rabon wani cikine ya kawoni yau ba, saboda a yanzu a halin da nake ciki mafita ya kamata na
nema ba wai na cigaba da haihuwa da shi a wannan halin ba