Showing 12001 words to 15000 words out of 24103 words
Chapter 5 - WASU MAZAN Part 1 Complete By Ummu hibbat .pdf
fatan Allah ya sa zuwa dare na ji alheri. Misalin tara na dare na wuce
d'akina na kwanta ina saka rai da tsammanin kira daga gare shi idan magani ya fara aiki. Amma
shiru har na fara jin bacci, kamar dai wasa baccin ya yi gaba dani sai da asuba na ji yana buga
min k'ofa.
Ko da na farka ma ga lalle maganin nan bai masa komai ba kawai sai na fashe da kuka. Na
jima ina yin kukan kafin na je na yi alwala. Sallah na yi na zauna ina lazimi har gari ya fara
haske. Daga nan kuma na wuce madafa.
Takwas a makaranta ta yi min rai na duka a jagule
Adama ta dube ni, "Ke kuma Samha me ya sa me ki yau?"
"Me kika gani."
Na ba ta amsa.
"Kawai yau na ga ba kya walwala ne."
"Au to wannan ai ya na faruwa ga kowanne mutum, saboda wani lokaci ka ji kana walwala wani
lokaci kuma ka ji ba son magana. Wannan kawai shi ne."
"Haka ne kam, to yanzu dai ina kayana su ke? Ko an siye?"
Dariya na yi ta dole da na tuna ba amfanin da maganin ya min, ciro su na fara yi a jakata ina
ajjiye mata akan bencin da muke zaune. "Adama ba ta gari matar amma wata ta d'auki k'ulli
guda na mazan ta ce na tambayo mata kud'in sa kuma wai ta ce ba shi da kyauma."
Na k'arashe maganar ina galla mata harar wasa.
Dariya Adama ta yi har da shewa tare da fad'in, "Haba wa! Ai kuwa dai maganin me kyau ne,
sai dai idan shi mijin ne ba abin arzik'i a gare shi."
Kallon ta na yi da mamaki na ce , " Lalle Adama, to mene ne amfanin siyan maganin? Daman
ba don a gyara ba ne?"
Dariya ta yi har da bugar cinyata ta ce, "Ke malama saurara na yi maki baya ni da kyau! Shi fa
maganin mata da maza da ki ga gansu dukan su, Ana amfani da sune idan an d'an gaza ko
kuma ka ji ka sauya daga yadda ka ke da, amma batun wai kana mara kuzari ka zama me
kuzari d'ari bisa d'ari, to ba zayyu ba. Sai dai idan baka sa kuzari ya d'an taimake ka. Idan kuma
kana da shi ne za ka k'ara sai ya hautsina ka har a arasa gane maka. Wanna shi ne. Ko kuma
shi me son ya yi amfanin da magani ya zama ya gane wanda yake masa amfani sosai."
"Hummmm! Adama yau she kika san duka wad'annan bayanan?"
"Ke zauna can, dukkan sana'ar da zanyi sai na yi bincike a kanta."
" To yanzu dai ya kamata ki sayi ko guda ne saboda a gyarawa baban Ameera, ita kuwa
wancen ki ce ta bayar da dubu guda."
Idanu na zaro da jin kalmar dubun da zan biya ta asara tun da ba wani abun da ya min
maganin. Na ce, "Ke Adama yanzu wannan abin ne dubu? "
"Tabbas kuwa, don ma ta ce bai mata ba ne da har da d'ari biyar za ta biya."
"Cab! Lalle kam, zan kawo miki gobe idan na amso."
Na ba ta amsa. Turo min wasu kalolin zuma ta yi gaban tare da cewa lalle sai ma siya guda wai
tana da kyau idan na siya zan samu alheri.
Dariya kawai na yi na tura mata kayanta na sanar ma ba yanzu ba don tafiya zayyi ma shi yau
zuwa damaturu.
Na sanar mata hakan ne kawai don ta barni da abin da yake damuna. Ina cikin wannan halin
idan na ce zan sha wani abu kuma ai yau sai dai na tallata kaina, na fad'i hakan cikin zuciyata
tare da istigfari.
Da yake Salma bata zo na ana ta shi na koma gida, sai dai ina shiga na tarar da wani abun
mamaki.......
10
Ko da na shiga cikin falon tsayawa na yi cak! Sakamakon ganin mu'azzam zaune a falo shi
kad'ai yana mun murmushi.Mamaki fal ya kama zuciyata
To shi kuma me yake yi ana shi kad'ai? Ban gama mamaki ba na ga Awwal ya fito a d'akin sa
yana fad'in yawwa ga tanan ma ta dawo. Karfin halin na yi bayan mamakin ya gushe na shiga
cikin falon ina k'ak'alo murmushi, zama na yi daga d'aya daga cikin kujerun ina fad'in, "Sannu
da zuwa. Yau kai ne ka kawo mana ziyara?" Murmushi ya yi ya ce, "Eh fa ziyarar bazata mijinki
ya jawo ni har ta tsawon sati guda. Dam! Na ji zuciyata ta harba da batun satin. Ina tsaka da
tunanin Awwal ya dube ni ya ce, " Ki yi sauri ki shiga kitchen ki daura mana abin da zamu saka
a cikin mu. "
Da to na amsa na gaida bak'on na wuce d'akina na cire kayan inifom d'in, atamfa riga da sket
na saka sai na samu wani mayafi mai kauri na saka ta yadda ba zai bayyana jikina ba. Kitchen
na wuce na barsu suna zaune suna hira. Sauri na yi na d'ora mata shinkafa da miya ta kayan
d'anye wacce za ta ji nama. Cikin iko na ubangiji cikin miti arba'in tuni har na gama komai. Ina
had'a kunun aya sai ya shigo kitchen d'in ya same ni tare da fad'in ban gama bane shi fa yunwa
yake ji. Kallon sa na shagala da shi yadda ya min kyua kamar yau na fara ganin sa, Awwal ya
cika na miji wanda Allah ya yi masa kyau da k'ira, ga kuma ilimi ga arziki. Amma sai dai kash!
An rage shi da wata matsala babba wacce ita ce cikar jin dad'in ko wanne bawa. Jin ya kuma
yin maganar duka sai ya saka min kasala a jikina har na ke jin kamar na je na rungume shi.
Kallon sa na yi cikin yanayin da ba zan iya tantancewa ba tare da kashe masa murya cikin wani
irin salo me wuyar fassara na ce, "Bombino, don Allah kar ka bari soyayar ka ta yi min illah a
zuciyata, wallahi ina jinka a zuciyata sosai. Ina fad'ar haka wata kwalla ta cika min idanu ganin
ko motsi bayyi ba. Ji na yi kamar ya ba ni wata dama ce hakan ya sa na je na rungume shi ko
zan ji salama a cikin zuciyata. Kasak'ai ya yi yana jina bai ce komai ba kuma bai motsa ba bare
ya rungume ni da hannnayan sa. Jin na saka hannayena bisa kansa ne ya sa ya fara ja da baya
yana kok'arin raba ni da jikinsa. A daidai wannan lokacin kuma na ji muryar mu'azzam yana
fad'in, kun shanyani da yunwa kun zauna soyayya ko? Jin sautin sa tuni Awwal ya yi fatali da ni
gefe ya fice. Wata irin kunya da nadamar abin da na aikata suka rufe ne, domin irin haka bana
sanin na aikata sai bayan faruwar abun, kuma hakan ya samo asaline daga yanayin da nake
ciki game da shi. Kayan na fara fita da shi zuwa falo ina ta sun kuyar da kaina kasa kamar
munafuka har na had'a komai na jere a dining. Dukan mu sallah mukayi sannan na yi wanka na
kuma shiryawa muka hallara a teburin cin abinci. Muna zaune bayan na zubawa kowa muna ci
shi sarkin kunya kansa k'asa ba ya ko dagowa yana yiwa mu'azzam zance, ya yin da shi kuma
mu'azzam duka hankalin sa akaina yake yana ta satar kallona. Ni kuwa yau ban tsinci kaina da
jin haushin sa ba, saboda ko wacce mace burin ta mijin ta ya kalle ta idan ta yi ado, amma shi
ya duk'ufar da kai kamar me tasbihi shi kuwa yana kalle masa. Har muka kammala cin abincin
nan bai d'ago da idanun sa ya dube ni ba. Don haka nima fa gaba d'aya nutsuwata ta koma kan
mu'azzam har na fara maida masa da martanin murmushin. Bayan mun kammala na koma
d'akina sai kuma na ji ban kyauta ba sai na fara istigfari ina neman yafiyar Allah. Jin shigowar
sa bai sa na kalle shi ba domin na san shi ne da ikon zuwa a wannan lokacin. Kallona ya yi sau
d'aya da na d'ago ya sauke ya ce da ni, hajiya ta yi tafiya ta sati guda kuma ba zai iya barin
mu'azzam da ba shi da mace ba tare da k'anwar sa wacce ba aure a gida ba hakan akwai
hatsari. Don haka mu'azzam zai zauna anan tsawon sati kuma baya son zaman hira ko da baya
gida iya ka ta da shi kawai gaisuwa da ba shi abinci a duk lokacin da ya bukaci hakan. Mamaki
ya kamani sosai da jin wai da gaske satin zayyi. Lalle Awwal zai kawo mana damuwa cikin
zaman mu wacce ta fi ta baya yawa. Domin da zaman sa gidan nan gwanda can, tun da ba su
san ya abin yake ba . ta ya zai kawo min k'ato gida bayan ya san ba iya min ya ke ba kuma ya
ce mu zauna haka kawai. Jin na yi shuru ina tunani a zuciyata ya sa shi cewa, "Dake na ke fa."
Kai na d'ago na dube shi na ce, "In sha Allah."
Da ga haka ya juya ya fice a d'akin. Ban kuma fitowa ba sai da na yi sallar la'asar kafin nan na
fito zan d'aura girkin. Ina fitowa na wuce kitchen sai na ji kamar motsi a falo sai na juya,
Mu'azzam ne zaune yana ta aikin kallon film d'in labarina maimai ci na su sumayya da fresido.
Da sauri na wuce shi domin bai ganni ba. Aiki na ke tuk'uru ina son na gama da wuri domin ina
da wani program na da k'awayena a wasaf da zanyi. Karfe biyar dai-dai. Ji na yi kamar motsin
mutum, ko da na juya mu'azzam ne ya tsaya yana k'are min kallo. Dam! Na ji zuciyata ta harba,
"Wannan kuwa ya san me yake yi?" Na furta a zuciyata. Sosa kai ya yi ya ce, "Ase dai kina
kitchen d'in, ina zaton ma ko kina bacci ne shi ne na ce bari na d'aura shayi saboda ni
ma'abocin shan sa ne sosai. To dunda kina nan kya dafa min idan kin gama.
Sai da ya k'arkare da batun sanna na ce masa, " Okay ba damuwa zan had'a maka."
Da to ya amsa tare da juyawa ya fita. Bayan na gama da na fito baya falo don haka sai na yi
sauri na zauna a falo na d'auki wayata domin ba na so su fara bana kusa. Ina hawa kuwa am
fara da gabatarwa, don haka duka hankali na ya tattara akan wayar. Ji na yi kamar an tsaya a
kaina, don haka sai na juya na ga ya sake mun murmushi, "Wai matar me kika samu ne a waya
ina ta sallama baki san ma ina yi ba." Ya tambaye ni cikin shagwab'e fuska. Na bude baki da
nufin ba shi amsa kawai sai na ji motsin bude k'ofar falo, ko da na juya Awwal ne ya shigo.Kai
tsaye bai ko kalle mu ba mu'azzam yana fad'in har ka iso ke nan, bai amsa ba kai kawai ya
gyad'a yawu ce, ganin haka tuni ni ma na koma d'akina. Ko a wajen cin abinci su na zubawa ni
kuwa d'aki na tafi na ci na wa a can. Sai wajen goma na dare Awwal ya min tex yana nema na a
d'akin sa. Shiryawa na yi na tafi zuciyata tana ta taradadin abin da zai ce. Ko da na je ya jima
bai kula ni ba har sai da na gundura da zaman kafin ya ce, "Yau yau na saka doka har kin fara
karyata? Wai baki lura mu'azzam yayi rayuwa a turai ba ne? Shi shigewa mace ba komai ba ne
a wurin sa , amma duk da haka ba zan iya jurar irin haka ba. In kin sa ba zaki kiyaye dokata ta
daga yau zaki na wuni gidanku har sai ya tafi."
Kallon sa na yi na ce, "Kai ne fa ka kawo shi, kuma shi ya shigo falo ya same ni ba ni ba.
Idan har ba baka yarda da kanka ba na mene ne ma kishin? Ai ina ganin abin da kake so shi za
kai wa kishi."
"Samha! Ya k'irani cikin wani irin yanayi na b'acin rai. Kallon sa na yi tare da rike masa hannu
domin na san masifa ce zayyi na ce, " Don Allah ka bar wannan zancen da za kai, ka fuskanci
matsalar mu ita ce abin dubawa ba wai wani batu da kai da kanka ka kawo shi ba. Ba ni da
burin da ya wuce a ce yau ka zama cikakken na miji." Kallona ya yi ya kasa ce min komai, na d'ora da cewa, "Ta ya zaka kawo min wani gardi cikin
gida ka ce mu zauna tare da shi bayan ka san matsalarmu Awwal?"
Ka sa ko da motsin kirki ya yi ya sunkuyar da kansa sannan ya ce, "Samha fita min a
dakina......
11
Shuru na yi ina ganin yadda yake dad'a matse idanun sa gan baya son ya bud'e su. Fita kawai
na yi tare da fad'in, "Ina dai sa ke tuna maka." Daga haka na fice zuwa d'akina. Shi kuwa
Awwal a b'angaren sa ya na jin ta fita ya bude idanun sa tare da cewa, "Oh Allah Samha ta
fitsare ba ta jin kunyata sam! " Gadon sa ya haye yana na zarin kalaman ta tare da jin haushin
sabon halin da ta zo masa da shin
San da ya auri Samha yarinya d'anya sharaf da ita bata san komai ba shi ya koya mata
komai, amma yau wai shi take ikirarin baya isarta? Ko da ya fad'i maganar sai da ya kuma kulle
idanunsa, domin lamarin kunya ya ke ba shi matuk'a. Wanka ya shiga ya yi, bayan ya fito ya
zauna abakin gadon yana latsa waya cikin intanet ya kutsa yana nazarin halayyar mata wai a
tunanin sa ko a kwai wani hali da mata suke da shi ne wanda Samha ta gani ta d'auko bai sani
ba. Amma har ya gama bai ga wasu daban ba. Ganin zaman ba shi da amfani ya sa ya haura
gadon sa ya kwanta, can kuma sai wani tunani ya zo masa, yadda Samha ta raina k'ok'arin sa
ya kamata ya nuna mata shi fa ba lalatacce ba ne. Da wannan tunani ya cire kunya ya wuce
d'akinta. Ita kuwa baiwar Allah tuni har bacci ya fara d'aukarta cike da mafarkan da ta saba. Ji ta
yi ana jan yatsun k'afarta kamar a mafarki kamar a zahiri. Farkawa ta yi ta gansa tsaye a kanta.
Don haka cikin mamaki ta ta shi zaune. Domin ta ya jima bai zo d'akinta ba sai dai ta je wurin
sa. Kafin ta yi magana ya hayr gadon ya juya mata baya tare da lumshe idanunsa. Ganin haka
tuni ta ji wani sanyi a ranta ta san ya zo ne ya bata hakkin ta. Baya ta juya ita ma domin ta
amshi sak'on da zai bayar. Jin sa a bayanta ya rungume ta hakan ya sanyata farin ciki sosai da
zak'uwa da yanayin. Wasa gaske dai Samga yau ta tsinci kanta cikin yanayi na jin d'adin abin
da Awwal yake mata. Sai dai kash! Ana zuwa inda ta fi so da k'auna fa ya jibgemata yana
numfarfashi. Domin ji yake a wurin sa ya yi babbar bajinta. Wasu siraran hawaye ne suka fara
safa da marwa a fuskarta tare da fad'in, "Awwal mene ne kuma haka? Don Allah ka ci gaba,
wallahi zan iya mutuwa yau kam idan baka ba ni farin ciki ba."
Jin batun ta ba k'aramin mamaki ya ba shi ba. "Samha yanzu dukkan wannan k'okarin da na yi
har yanzu ban rufe bakin ki ba? Yadda na bawa kaina wahala domin rufe miki ba ki da kuma
sanya ki farin ciki a she banyi ba? To wallahi ina baki shawara tun wuri idan ma wasu suke zuga
ki kina shan wasu abu domin ki k'ure mijinki to ki daina. Kuma ki sani wallahi ba zan kuma iya
wani abu haka kawai gobe na ka sa fita ba."
Yana gama fad'ar hakan ya fi ce a d'akin ya bar Samha cikin matsanancin hali. Birgima take
iya birgima har ta wantsalo a kan gado tana cikin damuwa bata sani ba.
Jin ta bugu da bangon d'akin ya sanya ta dafe wurin tare sa saurin mik'ewa ta koma gadon tana
dafe mara tana hawaye. Ganin zaman bazayyi ba ya sa ta fita tana dafe bango domin ta je
kitchen ta duba lemon tsami ta sha ko za ta samu sauk'i. Duhu duhu take gani da yake idanun
ta tsabar wahala ba ta iya bud'esu sosai. Tana shiga tana lalume ta ji ta lalumi mutum dai'dai
marar sa. Jin abin ba irin na su ba shi ne ya sanyata d'an k'ara bude idanunta kad'an tare da
lumshe su. Ita da 'yarmaye ba maraba. Shi kuwa Mu'azzam yana kwance yaji marar sa ta dame
shi da damuwa don haka ya san dai ba za'a rasa kayan shayi ba. Kuma daman ya sa ba tun a
gidan su kullum abin ya dame shi haka ya ke fita ya had'a kayan sa ya sha ya samu sauk'i. Jin
an dafa wajen har sai dai ya ji yana shirin sumewa. Domin abu ne da bai tab'a ji ko aikatawa ba.
Sake jigbe masa ta yi tare sa rungume shi tsaf a jikinta tana fad'in, "Me kake yi kuma anan
Awwal? Wallahi Awwal yau idan na mutu tabbas kai ne