Showing 6001 words to 9000 words out of 24103 words
Chapter 3 - WASU MAZAN Part 1 Complete By Ummu hibbat .pdf
ganin yadda lumfashinsa yake harbawa sosai da sosai.
Ni kuwa hawaye tuni ya wanke mun fuska da jin kalmansa, dukkan lokacin da za'a furta mini
kalmomi irin haka to suna ratsa min zuciyata na ji kamar a wata duniya nake.
Ka sa cewa da shi uffan na yi kawai sai zauna daram .
Shi ma zaman ya yi ya kuma cewa, "Samha ki ce wani abu mana."
Gyara zama na yi sosai na ce, "Yaya, wallahi baki ya yi k'an wajen furta kalar kaunar da nake
maka sai dai na ce komai wuya muna tare in sha Allah.
Da haka mukayi ta hira jar kusan magrib sannan ya tafi na koma gida. D'aki kai tsaye na wuce
na kwanta kan gadon mama, haka kurum kalaman sa suke dawomin a zuciya ina hawayen da
na gaza na farin ciki ne ko akasin sa? Wasa gaske soyayay ta yi nisa tskaanina da Isa
kwatsam wata rana muna zaune inda muka saba zance sai ga yaya Harun ya dawo daga tafiya,
duban mu ya yi bayyi magana ba ya wuce. Sai dai irin kallon da yake min shi ne ya sanya na ji
duk hankalina bai kwanta ba. Ganin na shiga damuwa sai Isa ya sallame ni na koma gida.
Bayan sallar isha mama tace min baban mu yana k'irana.
Zuciyata sai da ta harba da jin k'iran duk sa cewa ban san akan mene ne kiran ba. Baban mu
mutum ne me sauk'in kai wani lokaci kuma me fad'ane. Ya kasan ce laccara ne mai koyar da
ilimin lissafi, mahaifiyarmu ita k'ad'ai ya aura, ita kuma mu biyar ta haifa. Yaya Yusuf shine
babba, sai Yaya Sadik ya ke binsa, sai kuma Aunty hannatu Sai Aunty Dija, Sai ni autar su. Kuma dukan su sun kusa kammala karatun su kuma kowacce acikin su an saka mata ranar
aure wacce rana guda ce za'ayi bikin.
Yaya Yusuf kuwa bayyi aure ba bare Kuma Yaya Sadik.
"Samha!"
K'iran da mama ta yi min ne ya sa na mike da sauri na saka hijabina domin na amsa k'iran da
baba ya min.
Ko da na shiga falon sa duka yayyuna suna zaune a gaban babanmu. Wani irin fad'uwar gaba
ce ta riskeni da na ga irin Kallon da Yaya Yusf yake min.....
5
Wuri na samu na zauna daga gefe guda na fara gaidasu d'aya bayan d'aya. Abbanmu ya dube
ni ya ce, "Mamata, kinga yaron nan da yake zuwa wajenki, idan har da gaske kina son shi yana
sonki to maza ki ce ya turo da iyayen sa, saboda idan har da gaske yake zan had'a aurenki da
sauran 'yan uwanki ne tunda saura k'iris ya rage ki gama kya cigaba da karatun na ki a gidan
sa."
"Ajjiyar zuciya na sauke ina jin wata kunya tana lullub'eni. Yanzu kuma taya za'ayi min aure ban
yi jami'a ba? Kuma shi kansa Isa ba ni da tabbacin zayyi auren yanz.....tswar da Yaya Yusuf ya
daka min ce ta sa na firgita na d'ago da idanuna na du be shi.
" Ba magana aka miki ba ne ki ka yi shuru! Ko akwai abokin wasan ki anan?"
"A'a Ya ya, in sha Allah zan sanar masa da zarar ya dawo."
"Yawwa Mamana hakan ya kamata ayi, ta shi kije abin ki."
Abbanmu ya furta.
Mik'ewa na yi har ina sassarfa na bar wurin na koma d'akin mama.
Ban san me suka tattauna ba ni dai naga su Aunty sun dawo sai murna suke suna tsalle.
Kwana uku rabona da Isa kamar ya ji labarin abin da ya faru ko kuma nake son sanar masa,
kuma ba ni da waya bare na k'ira shi.
Haka na HaKura
Ranar monday muna tafiya makaranta ni da k'awata muka ga ganshi ya wuce a mashin bai
ganmu ba, sai sannan na samu nutsuwa da na tabbatar da lafiyarsa kalau. Haka mukayi
karatun amma duk hankalina yana kansa, har na fara jin damuwa ta mamaye min zuciyata.
Domin bai saba kwana biyu bai ziyarce ni ba, ko kuma ya aikomin da sak'on wasik'a. Amma
shuru sam ba kansa kuma lafiyar sa kalau.
Ko da muka dawo gida yamma ta na yi muka tafi islamiyya ni da yayyuna,
Sai wajen shida aka ta she mu, Aunty Dija ta dubeni ta cd, "Ke wai me ya same ki ne tun da
rana na ganki wata k'ala?"
"Babu komai kawai kaina ne yake ciwo."
Na ba ta amsa. Sai ta ce da ni ya kamata daga mun koma gida na sha magani kar abin ya yi
nisa.
Da to na amsa mata muka ta fi gida. Muna zuwa na tarar da takardar da nake saka ran
zuwanta ta wasik'a yaro ya kawo bana nan.
Har ina washe baki na mance a gaban su Mama na ke. Su kuwa su aunty Dija kallo suka bi ni
da shi. Ta kardar ta amsa na wuce d'akin mama na fad'a kan gado wani shauk'i yana d'ibana
tun ban bude ba.
"Abar k'aunata abar sona, sanyin idaniyata annurrin zuciyata, macen da babu kamarta binni
da k'auye. Hak'ika zuciyata ta azabtu da rashin ganinki, hancina ya yi kewar k'amshinki.
Idanuna sun yi kewar ganinki. My Samha, bakina ba zai iya sanar miki da tarin k'aunar da nake
miki ba. Na san kinyi mamaki da jina shuru ban zo ba, ina mai baki hakuri da hakan, hakan ya
faru ne sakamakon rashin lafiyar da nake fama da shi. Yanzu haka ina asibiti a kwance. Tun
ranar da na ganki ban tsaya ba saboda baba yana jirana a ranar. Daga masoyinki Isa."
Ina kammala karantawa na rugume takardar a k'irjina na fashe da kuka ina fad'in, "Daman na
san zayyi wuya ace kana lafiya baka zo ba."
Allah Allah nake gobe ta yi na fita makaranta daga an tashi goma na je na duba shi tunda ba
nisa da makarantar.
Bayan munyi sallar magarib duka muka hallara karatu a falon baba, anan ma sai da aka
ritsani da tambaya amma ban ce komai ba. Saboda da zarar an fara min tambaya daga bakin
mutanen da ya wuce biyu sai naji kuka yana zuwamin ni haka nake daman.
Da sassafe na shirya na fita makaranta, tun kafin mu shiga aji na sanar da Kulsum zata min
rakiya asibiti dubiya.
Ta amsa min da to ba damuwa. Muna karatu ina duba agogon Ta kusa dani da yakr ita ce mai
buga k'ararrawa. Wata irin mummunar fad'uwar gaba ce ta riskeni na fara ambaton sunan
Allah.
Ana fita kuwa ban bari mun ci komai ba na d'auki kaltum muka fita, muna shiga ba mu sha
wahala ba da yake d'akin maza ba shi da nisa sosai. Sai dai abin da idanuna suka ganemin ne
ya sani tsyawa cak!
Wasu maza ma gani suna rike da hannun isa ba ya iya ko lafiya an d'aura shi a kan kujerar da
ake tura marasa lafiya za'a kaishi wani waje. Wasu hawaye na ji masu zafi suna zirtatowa daga
cikin idanuna. Yana d'ago da kansa muka had'a idanu. "Samha."
Ya furta cikin sark'ewar murya. Ban iya amsawa ba saboda idan na ce zanyi magana kuka
zanyi. Da yake maganar a hankali ya yi nima dan ina ganin bakinsa ne na san me ya fad'a ba
wanda yaji, sai kawai suka tura shi suka tafi da shi. D'akin tiyata na ga sun nufa ni dai ban san
me za'ayi masa ba. Kaltum ta yi yin duniya mu tafi na ce sam! Ina nan ta koma kawai ni sai na ga fitowar su. Da
k'yar ta lallab'ani muka fara tafiya, bamuyi nisa ba na ji an k'ira sunana daga bayan mu, cikin
san in san me k'iran ya sa ni na yi saurin juyawa.......
6
Ina juyawa sai na ga abokin Yaya Yusuf ne, gaida shi na yi ya amsa ya na tambayata wa ye ba
lafiya. Duburburcewa na yi, sai Kaltum ta yi wuf ta ce, " Rakoni ta yi dubiya." Wani sanyi na ji da
jin batunta ina me farin cikin kub'utar dani da ta yi, domin kuwa mutum ne me bin kwakwaf,
kuma na san zayyi wuya bai sanar da Yaya Yusuf had'uwar mu ba. Shi yasa gaba d'aya na gaza nutsuwa. Da haka dai muka wuce shi a wurin, ko da muka koma
school d'in ban fahimci komai ba har aka ta shi. Ina zuwa gida kuwa na yi sauri na yiwa mama
bayanin cewa na raka Kaltum dubiya Asibiti gudun kar Yaya Yusuf ya tuhume ni. Kamar kuwa
na san haka za ta faru, bayan magrib yana shigowa gida tambayar da ya fara min kenan.
Amsar da na bashi tilas ta sa ya hak'ura.
Bayan mun kammala karatun dare sai na koma d'akinmu domin na lallab'i zuciyata da damuwa
da take damunta. Yayuna suka sani gaba da tambaya dole na sanar musu gaskiya tunda ba ni
da wanda suka fi su a yanzu. Aunty Dija ta rik'e hab'a tare da fad'in, "Ohh Allah, yanzu Samha
har kinyi girman da za kiyiwa soyayya kuka?" Ban iya bata amsa ba kawai na ci gaba da kukana.
Haka na kwana cikin damuwa ina jin yadda zuciyata take bugawa da sauri da sauri. Da wuri
na shirya muka tafi School domin yau so nake kafin a shiga aji ma na duba shi. Muna shiga
cikin asibitin sai muka ci karo da wasu daga cikin danginsa suna zubar hawaye, cike da
damuwa na tare wata daga cikin su ina tambayar ta ko lafiya, tare da ce mata ina Isa ya ke ya
kuma jikinsa.
Amma shuru ba amsa. Ganin na kid'ime sosai shi ne ya sa wata daga cikinsu ta ce min, "
Yarinya kiyi hak'uri yanzunnan Isa Allah yayi masa rasuwa, kuma har ya kusa rasuwa yana
fad'in sunan wata Samha, wannan shine abin da ya damemu. Muna son mu san ko wacece ko
tana binsa bashi ne yake so ya ce." Tun da ta fara maganar na ji wani irin abu ya sauk'a a jikina me kama da tafashashshen ruwan
zafi ya gigita dukkan nutsuwa ta. Wata furgitacciyar kuwwa na saki na zube sumammiya.
Ban san me ya faru ba
Sai da na bud'e idanuna na ganni a kwance a gadon Asibiti, gefena Kaltum ce da wani wanda
ban san shi ba.
Ganin na farka ya sa Kaltum cewa, "Alhmdulillah! Samha don Allah bud'e idanunki sosai, ba
gaskiya bane abin da ta fad'a."
Girgiza kai nayi wasu hawaye suna kawo ziyara kan fuskata masu zafin gaske, tare da wani
mummunan ciwon kai da yake ratsa dukkan jikina.
"Kaltum." Na k'ira sunanta cikin raunatacciyar murya.
Amsawa ta yi tare da matsowa kusa dani sosai. "Ai ba yadda za'ayi bai rasu ba su ce ya rasu.
Tabbas Isa ya rasu ya barni da tarin k'aunar da nake masa, ya bar zuciyata da muradin son
ganinsa, ya barta da batutuwa da nake son na furta masa. Ina jin ceqa tabbas ba zan yi nisan
kwana ba zan mutu." "Haba ke kuwa, me zai sa ki ce haka? Idan Allah ya karb'i wani bawa ba yana nufin wani bawa
ba zai rayuba sai da wannan d'in."
Na ji sauk'ar maganganunsa a cikin kunne na.
Ban ba shi amsa ba saboda ganin ya min kwarjini, sai Kaltum ce ta ce da shi, "Haka ne."
Sannan ta dube ni ta ce, "Samha wannan mutumin shi ne ya taimake ni da motarsa a lokacin da
kika fad'i har zuwa bakin titin da d'akin nan yake. Kuma shine ya tsaya a kan mu ganin ba kowa
kusa damu har aka baki kulawa ta musamman." Kai na jinjina sannan ta dube shi na ce masa, "Mun gode sosai."
"Babu komai." Ita ce amsar da ya ba ni.
Har wajen azahar ina kwance a gadon asibiti na ce wa Kaltum lalle lalle ya ka mata mubar
asibitinnan tun kafin asirina ya tonu, domin ta san halin 'yan gidanmu indai mutum ya aikata
wani abu a b'oye to ya shiga uku. Bare kuma ni da na zo duba saurayi duk da cewa ya bar
duniya ban sani ba ko alhinin hakan zai sa a rageni da fad'an idan anji. Da to ta amsamin ta dubi wannan bawan Allah da ta ce ya taimakemu tace masa zamu tafi
gida gaskiya saboda akwai matsala.
Ina ji ya tambayi Kaltum mene ne matsalar ta sanar masa komai ba ta b'oye mishi ba. Jinjina kai
ya yi ya fita can sai suka shugo shi da wani likita ya du ba ni ya kuma tabbatar masa da zamu
iya tafiya, amma da sharad'in na kula da shan magani. Da to ya amsa masa Na ta shi zaune
Kaltum ta taimakamin muka fita. Bayan mu ya bi yace da Kaltum idan ba damuwa zai kaimu
gida saboda yanayin jikina ba kwari, kuma ko mashin muka hau ba zamu samu nutsuwa ba.
Ba ta yi masa musu ba kasancewar ta san ban cika son hawa mashin ba in ba dole ba. Ban yi
musu ba ni ma saboda na san ba zai cutar damu ba in sha Allah, tunda har ya taimake mu.
Don haka muka shiga motarsa ya d'akko mu har wajen layinmu na ce ya tsaya anan mu
sauk'a.
Bai musa ba ya tsaya tare da min fatan samun lafiya.
Fita muka yi nida Kaltum muka do shi gida, sai dai ina d'ago da kaina na yi idanu hud'u da
Babanmu da Yaya Yusuf suna zaune k'ofar gida suna kallonmu ni da Kaltum. Wata irin fargaba
ce ta riski zuciyata wacce sai da ta yi sanadiyyar zubar wasu hawaye daga idanuna tare da
fad'in "Na shi ga uku na kaltum. Dubana ta yi tace karna damu ta san abin da za ta ce kawai na yi maza na goge hawayena.
Gogewa mukayi muka k'arasa inda su Babanmu suke fuskokin su duka cike da alamar
tambaya.
Firgigit na dawo daga duniyar tunanin da na tafi jin ana ta bugamin k'ofar dakina. Muryar
Ameera da na ji shine ya tabbatar min da sub dawo a makaranta ko abinci ban samu na yi
musu ba. Da sauri na bud'e k'ofar na yi musu sannu da dawowa na ce su je suyi sallah ina
zuwa zanje kitchen, sauri sauri na shiga na d'aura mana jalof d'in taliya domin zan fi saurin
gamawa. Ina tsaka da girkin sai na ji kamar motsin mutum a bayana. Sauri na yi na juya domin
ganin waye ne. Awwal ne tsaye ya ware min hannaye da nufin na zo ya rungume ni. Mamaki fal
ya mamaye min zuciya, "Wai anya Awwal ne kuwa? Ko dai mafarki nake yi ne?" Na tambayi
kaina. Cikin tsoro nake kusantowa gareshi tare da k'okarin murmusawa saboda zuciyata idan ta
samu abin da take muradi, mancewa take da dukkan kuskuren da Awwal ya turnuk'amin.
Sai dai ina zuwa daf da shi zan fad'a jikin sa ya ja gefe na gwaru da bangon wurin, take
bakina ya fashe a wurin. Shi kuwa juyawa ya yi bai ce komai ba ya fice. Mamaki da Al'ajabi
sune suka saka ni na gaza cewa komai. A halin yanzu a furgice na ke da wurin ma sosai. Da
kyar na iya kammala komai na fita a kitchen d'in, sai dai ina zuwa falo na ci k'aro da shi zaune
yana min murmushi. Wata kyakkawar ajiyar zuciya na sauke wacce ta yi sanadin da Awwal ya
kalle ni ya kuma mun murmushi. Sakin abincin na yi na wuce d'aki da mugun gudu na rufe ina
salati domin tabbas na san na yi gamu.
A falo kuwa Awwal ne zaune yayi dariya son ransa tare da fad'in Samha zan koya miki
hankali.............
7
Wani irin tsoro sosai ya riski zuciyata, damuwa da tunanina Allah ya sa ba gamo na yi ba. Ina jin
yadda su Ameera suke bugun k'ofar suna cewa na bud'e Abban su ya dawo abincin bai zube
ba. Fad'in ya dawo shine ya kuma rikita ni. Ke nan da gaske dai gamon na yi ba Awwal bane.
Cike da damuwa na yunk'ura na bu de k'ofar na fita zuwa falo ina rak'ub'ewa kamar wata
munafuka. Kallon sa na yi ya had'e rai gyam yana hakimce a kujera amma ba wacce na barshi
ba. "Tabbas wannan shi ne Awwal mijina." Na furta a cikin zuciyata. Domin Wancen Awwal d'in
ma'abocin murmushi ne, na wa kuwa ga kalar sa nan. "Wai tsayuwar me kike ne ba zaki zuba
mana abinci ba!" Ya fad'a cikin tsawar da ta yi sanadin zaburata izuwa dining. Abin ka da mai
zaman jiran kiris.
"Tofa! Yau kuma wani sabon salo kika zo da shi gidan." Awwal ya fad'a.
Ban kula shi ba har na je na gama zuba komai na zauna ina ganin yadda suke cin abinci cikin
kwanciyar hankali amma ni kuwa sam bani da ma kwanciyar hankali bare na yi tunanin wata
aba wai ita yunwa. Ganin ba na cin abinci ne ya sa Ameera ta fara cewa, "Mama, ki ci abinci
mana ya yi dad'i fa." Kallon ta kawai na yi na gyada kai na kalli inda Awwal yake zaune yana cin
abinci bai ko kalle mu ba. Ina ganin ya mik'e ya yi hanyar d'akin sa na bi shi. Domin ji nake
matukar ya ta fi to aljanin sa zai fito. Ganin ina bin sa ne ya sa ya juyo tare da fad'in , "Malama
lafiya kike bi na?"
Turus! Na ja na tsaya na rasa abin fad'a. Ina ganin ya ci