Showing 18001 words to 21000 words out of 24103 words
Chapter 7 - WASU MAZAN Part 1 Complete By Ummu hibbat .pdf
ya had'a kowa da alheri." Ko da jin wannan batun na ta sai Awaal ya zaro idanu yana fad'in, "Haba Samha yanzu sai ki
iya rabuwa da mijinki ki watsa farin cikin yaran ki saboda kawai wani abu da yake zuciyarki?"
"Tabbas Awwal, wannan shi ne abu mafi sauki da zanyi domin na ceto rayuwata daha halaka!
Zama da kai tabbas halaka ce zallah. Yara kuma Allah ya raya mun su."
"Haba, ta ya zaman zai zama halaka me na rage shi da ke. Komai ina miki ko da kij fita ba lalle
ki auri wanda zai baki gata irin wanda na baki ba."
"Na sani, baka rage ni da komai ba. Amma fa ka gaza ba ni farin ciki a gidanka. Na sani Awwal
ko da na fita ba lalle na samu na miji da yayi min gata kamar ka ba. Ko kuma wanda zai inganta
rayuwata kamar yadda ka min ba. Ko wanda zai girmama iyayena kamar yadda ka girmama su
ba. To amma ka sani dukkan wannan abin da kayi min matukar ba zaka iya ketarar dani daga
wutar Allah ba basu da amfani a gare ni ranar lahira. Gwanda mu rabu na koma gida na auri
talakan da zai nemo mana cin yanzu ya nemo na ajima. Abun so shine ya zama min katanga
daga wutar da Allah ya tanadar wa dukkan matan da suka kasan ce mage da wuri a gidan aure.
" Cab! Samha ki sauya tunani wallahi ki nutsu ki yi hakuri dani in sha Allah zan sauya zakiyi
farin ciki sosai da sosoi a rayuwar da zamuyi gaba."
"Sauyawa fa ka ce min Awwal. Shin har akwai wata sauyawa wacce zaka yi wacce ban sani
ba? Ba ga irin sauyawar ta ka ba. Ina gida ina zamana ka je ka dawo dani ka ce ka sauya,
amam kuma sai ga irin abin bak'in cikin da ka kuma shuka min. Ni dai na sanar maka iya
gaskiya ya ne wallahi. Domin na lura ba zaka tab'a sauyawa ba. Haka Allah ya halicce ka don
haka sai ka sama mana sauki. "
"Na san har kullum ba kya iya fahimtata Samha ke dai maganar ki guda d'aya yace wallahi ko
da yause akan wannan za'a tsaya ake jin kanmu da ke? Ke yanzu wannan ba abin kunya bane
a gareki a ce shi ne silar mutuwar auren ki?
" Tambayata kake? Wai tambayata kake wa zai aure ni? Bari ka ji duniya tana fad'i kuma Allah
ya san cewa domin gudun sab'a masa na ke dukkan wannan abun. Baya ga haka da ba abin da
zai sa na ce zan rabu da kai. Awwal wallahi ina sonka! Son da ba zan iya misaltamaka ba, ni
nasan irin wahalar da zan sha a lokacin da zan raba kaina da kai. Sai dai ka sani yin hakan
tabbas shine mafi alheri a gare ni da yaran nawa ma gaba d'aya. Domin ko su yaran nawa ba
zasu so yau a ce ga uwarsu tana aikata wani abu mafi muni ba, ko kuma a koma ga Allah suka
an yi min hisabi zuwa ga wuta. Yaran nan uku ne fa, ka san inda zaka kai su ai ba sai ma
sanar maka ba. Don haka kawai kayi abin da na ce maka kawai shi ne mafi sauk'i. Domin babu
wani uzuri da zan yi maka anan gaba. In sha Allah zaka smau daidai kai ka aura . ni ma kuma
Allah ba zai barni haka ba tun da ba butulci na yi ba. Sai ba tabbata na yi akan bauta masa.
Kuma ya bamu damar yin haka a lokacin da irin wannan matsalar ta faru."
Lumshe idanu sosai Awwal yayi yana jin dukkan abin da Samha take fad'i, wani irin b'acin rai
yake ziyarta zuciyar sa wanda bai san ma me zayyi ya huta ba. Shi kam baya jin zai iya rabuwa
da Samha, kuma ya san ba zai iya abinda take so ba. To yanzu ina mafita cikin wannan lamarin
na sa. Ajiyar zuciya ya sauk'e ya sauk'a a kan gadon ya wuce bayin da ke cikin d'akin yayi
wanka tare da alwala ya fito ua hau sallaya ya fara shirin tayar da sallah. Jin fad'uwar abu
abayan sa ya sa shi da katar da sallar. Juyawa yayi. "Innalillahi wa'inna 'ilaihirraj'un." Shi ne
abin da ya furta.
Ganinta zube kamar sumammiya shi ne abin da ya tayar masa da hankali. Gefe guda kuma
haushinta ya kama shi saboda a ganin sa wannan 'yar matsalar ba wata matsala ba ce da zata
sa kanta cikin damuwa har ta yanke jiki ta fad'i. Jijjigata ya yi shiru. Ganin haka sai ya koma
bayin ya samo ruwa ya fesa mata sai ta kawo lumfashi. Kallonta yayi cike da b'acin rai ya ce,
"Wallahi Samha abin nan ya ishe ni sam! Taya zaki zo kina tayar min da hankali akan wannan
abin."
Lumshe idanu ta yi ba ta ce komai ba ta yunk'ura ta hai gadon ta kwanta ta yi lamo kamar me
bacci. Ganin ta yi haka shi ma bai sake ce mata komai ba ya wuce ya kwanta. Ko da asuba ta yi
ta yi wanka ta yi sallah ba ta kuma yi masa magana ba ta fi ce, ta yanke shawarar fita cikin
sabgarsa kawai tun da ta lura sam ba zai tab'a fahintar ta ba. Idan ta kawo masa abinci sai ta ajjiye a dining ta koma d'akinta. Haka idan dare yayi baya tarar
da ita a falo ta ajjiye masa komai ta shiga har ta rufe ita da yaranta. Shi ma Mu'azzam ya jima
rabon da yanga har yake tambayar Awwal ko ta kuma koma wane, amma ya tabbatar masa
tana nan. Sai ana gobe zai koma gidan hajiya sannan suka had'u suka gaisa . washe gari da
yamma ya tattara kayan sa ya koma gidan hajiya saboda yau ta dawo daga tafiya. Ita ma
Samhan da washe garin ranar taje ta yi mata sannu da dawowa. Ko da dare yayi Awwal ya zo
ya d'auketa yana tambayarta ko suje gidan abinci na Arraudah su ci abinci ne yaga kamar bata
ci komai ba. Ban za ta yi masa bata ba shi amsaba har sai da ya maimata sannan ta ce masa ta
k'oshi. Ko da suka k'arasa gida falo suka yad'a zango ita da yaran shi kuma ya wuce d'akinsa.
Bayan wani lokaci kad'an ya fito ya zauna a falon ya fara yiwa yara wasa har da dariya. Ganin
haka ya sa tsam! Ta mik'e ta bar falon ta koma d'akinta. Da kallo ya bita bai ce komai ba. Bayan
sun gama zaman ya ce kowa yaje ya kwanta. Dakin sa ya shiga ya kwanta yana ta mazarin
yadda zai b'ullo mata saboda ba ya son irin wannan zaman sam. Mik'ewa yayi ya nufi d'akinta,
adaidai k'ofar d'akinta ya tsaya sakmakon jin.........
15
Jin sautin muryarta cikin kuka shi ne ya dakatar da shi daga shigar, yana kuma jin yadda take
rokon Allah a kansa. Ta na cewa, "Ya Allah wannan zaman na gidann Awwal na gaji da shi,
Allah kai ne she da ba ina k'in zaman ba ne don wata mafuta ba, sai dai na tseratar da rayuwata
daga fad'awa halaka. Allah ina son Awwa, idan har zai zama irina Allah a sauya shi. Idan kuma
ni zan iya zama irin sa to Allah a mai dani. Ya rabb! Idan hakan duka ba za su samu ba Allah ka
raba wannan auren domin na tseratar da mutuncina. " Tana gama fad'ar hakan ta kuma
fashewa da kuka . jin irin addu'o'inta sai duka jikin sa ya yi sanyi. A hankali ya bud'e k'ofar
d'akinta ya shiga, bai yi magana ba ya je kusa da ita ya zauna.
Kallon ta yayi yaga yadda hawaye suka jik'e mata fuska, tausayi da soyayayyarta duka sai suka
lullub'eta. Kafad'ar sa ya jingina da ta ta. Ya ce, "Me kike yi har yanzu baki kwanta ba."
"Sallah nake yi ko ba ka gani ba ne?" Ta bashi amsa cikin kuncin zuciya. Bai ce komai ba yayi
shuru yana sauraran fitar lumfashinta. Can kuma sai ya ce, "Ki zo muje d'akina mu kwanta."
"Ba zanje ba Awwal, har sai ranar da ka k'ara k'arfin injin batirin motarka. Domin ba yadda
za'ayi a ce kullum idan muka hau ta wuce da kai inda kake son gani amma ni kumata gaza
kaini."
Daga haka Samha ta mik'e ta bar wurin bata jira amsar da zai bayar ba. Shi kuwa a zuciyarsa
sam kunya ce ta lullub'e shi. Bai san sanda Samha ta falle haka ba har ta ke iya sanar masa
wad'annan maganganun. Mik'ewa ya yi bai ce uffan ba ya bar d'akin.
Bayan gari ya waye Samha ta had'a komai ta koma falo ta zauna tana jira ya dawo daga kai
yara a makaranta ta tanmbaye shi za ta je gida domin bikin Yaya yusuf ya k'arato kusa. Bai jima
ba kuwa ya dawo ya wuceta ya fara cin abincin sa. Ganin haka ya sa ta je inda ya ke ta zauna.
Tana zama ya ce, "Ina kwana." Mamaki ya ba ta sosai, domin kullum ita ce take gaidashi ya
amsa cikin gadara yau kuma shi ne yake gaisuwar. Amsawa ta yi tare da fad'in, "Ina son ka ba
ni dama na je gida,Saboda shirye-shiryen bikin Yaya Yusuf."
Kallon ta yayi sai ta sunkuyar da kanta k'asa.
"Babu damuwa amma ni zan kaiki kuma zan d'auko ki, ba zan so kiyi tuk'i kina cikin damuwa
ba."
"Uhm." Shi ne iya abin sa Samha ta furta kawai ta mik'e za ta bar wurin.
"Ina kuma zaki je?" Ya furta cikin k'asa da murya. "Zanje na gama aikina da wuri ne."
"Okay ba damuwa, sai dai baki karya ba kamar."
"Ba na jin yunwa yanzu." Ta fad'a tare da barin wurin don kar ma ya kuma mata wata
tambayar. Kitchen ta koma ta fara shirya abincin da za ta tafi da shi gida. Bayan ta kammala
komai ta had'a kayan yaranta wanda idan aka kaisu anjima za ta sauya masu.Shiryawa ta yi
cikin wata atamfa mai ratsin ja da kuma launin ruwan hanta. Haka jilbab d'in ta ma ruwan hanta
ce, takalmi ma haka. Hoda ta sanyawa fuskarta kawai da man leb'e sai turare da ta banbad'a
tunda tafiyar daga ita sai mijinta kuma gidansu za ta je. Jilbal d'in ta saka ta d'auko gilashin ta
na ido ta fari ta saka. Tana tsaye gaban madubi ya bud'e kofar ya shigo. Kallonta yayi sai dai
zuciyarsa ta buga. Ganin irin kyawun da ta yi ga kuma k'amshi me d'adi wanda yake shak'a.
Hak'ik'a Samha ta daban ce kuma tabbas ya san yayi dacen mace ta kyakkawa ga ilimin addini
ga kuma tsafta ga iya girki. Sai dai matsala guda ta hana su su fuskanci juna. "Ki zo mu tafi idan
kin gama. Kuma ki kashe komai ma wutar lantarki."
Da to ta amsa masa ta yi yadda yace d'in. Bayan sun rufe gidan sun shiga mota sun fita suna
hanya ya kalle ta tare da fad'in duka wannan turaren da ta saka don zata je gidannan ne? Amsa
da ba shi da saboda gidan ne. Shiru yayi bai kuma cewa k'ala ba ganin yadda ta had'e fuska ta
juya kai gefe. Har suka isa tukunna ta kalle ahi tare da fad'in. "Za ka shiga ne ko sai ka dawo?"
Sai ya dawo ya ba ta amsa. Fita ta yi ta shiga gidan inda ta tarar da su anti dija da maryam
duka sun zo su. Farin ciki sai ya mamaye mata fuska amaimakon damuwar da take ciki. Gaida
kowa ta yi aka amsa mata sanna ta zauna tare sa ajjiye fulasan hannunta. "Baba ya na ciki ne
anti Maryam?" Ta tambaya. Yana ciki suna ba ta amsa. Don haka kai tsaye sai mik'e ta wuce
d'akinsa domin gaida shi. Can ta samu Mama da yaya Yusuf suna zaune. Da farin ciki Baba ya
dube ta yana fad'in "Mamana ke ce a gidan ?" "Eh wallahi Baba yanzu muka zo. Su ma
gaisawa sukayi har da su yaya sannan ta koma wurin si anti Dija. Suma zaune suna hira amma
kuma sai suka ga sam hankalinta kamar baya tare da su kamar da ka sancewarta mai surutu.
Anti Maryam ta dube ta. " Samha, me yake damun ki ne?"
Jin tambayar ta yi a bazata. Don haka sai ta d'ago kai ta ce..........
16
"Me kiga gani?" "A'a naga sam baki da walwala sosai ne."
Aunty maryam ta ba ni amsa. "Aunty kawai dai ciwon kai nd yake damuna." Carab! Aunty dija
take cewa aunty maryam ko dai ciki ne dani. Murmushi kawai na yi domin ba ta san halin da
nake ciki bane shi ne kawai. Muna tsaka da zaman mama ta zo tare da kayan akwatin yaya
muka fara dubawa. Kaya ne na gani na fad'a masu kyau da tsada. Mama na kalla na ce, "Mama
yau she yaya ya kud'ance haka ne? Irin wannan kayan haka, lalle wacce zai aura ta more da
kaya masu kyau da tsada."
Murmushi Mama ta yi tare da cewa, "Ai ya jima yana tara kayan sa shi yasa, kuma da yake
yanzu yana aiki shi ne yasa siyan na k'arshen aka siya masu tsada."
"Ai kuwa ya kyauta ko ba komai za mu kai kaya ba raini. " murmusawa auntys suka yi suna
yaban kyan kayan har muka gama aka maida. Ko da yamma ta yi Yaya ya shigo gida muka
masa murna ya sanar damu idan har akwai abin da muka san ana saka wa mu fad'a ya sayo a
saka kafin lokacin. Sanar masa muka yi komai ya yi yadda ake buk'ata. Muna tsada da
tattaunawar kuwa k'annen mahaifiyar mu suka zo si ganin kayan. Suma ya bawa sukayi aka
maida suka tabbatar komai ya yi. Bamu rabu da su aunty ba har sai bayan magrib sannan suka
tafi gidajen su. Ina zaune ina zaman jiran tsammani mama take tambayata ya batun jinnu tana
sa ran dai ba na ganin komai yanzu? Amsa mata na yi da komai lafiya yanzu kam sai dai abin
da ba za'a rasa ba. Kafin ta kuma magana muka ji Sallamar yaya da Awwal sun shigo, kansa
bisa k'asa ya gaida Mamanmu muka fara shirin tafiya gida wansa har su Ameera sun fara shirin
bacci da yake ba wutar nefa kuma ba abokan wasan kowa ya tafi da yaransa. Tayar da su duka
na yi muka yi sallama da mama. Ya ya ne ya kama hannun yaran ya kaisu mota. Sallama suka
yi da Baba da yake k'ofar gida a zaune. Nima sallama na yi masa muka tafi. Muna cikin mota ya
dube ni ya ce, "Manyan k'anne biki sai k'aratowa yake. Ni yanzu sati nawa ya rage?" Kauda kai
na yi gefe sannan ma amsa masa da cewa, "Sati uku ne."
"Ki ce abin ya zo zamu sha bikin baban yaya ."
"Haka ne kam."
Na bashi amsa.
Daga haka bamu kuma wata magana ba har muka je gida. Koda muka isa na kai yara d'akinsu
kowa ya kwanta sai na fito na yi hanyar kitchen domin na dora masa wani abu tunda mu munci
abinci shi kuma bai ci ba. Tare ni yayi tare da fad'in "Ba sai kinyi abinci ba, na zo da abin da zan
tab'a anjima ki zubamin yana teburin abinci. " Da to na amsa masa na koma d'akina na kunna
datar wayata sai kuma na tuna banyi sallar isha ba. Don haka sai na mik'e na je nayi alwala na
yi sallah na yi addu'a na kammala. Falo na fito na zauna na kunna kallo na fasa chaty d'in,
labarina na kunna a wayata na ajjiye wayar a kan babbar kujera ina kallah kamar tv. Na yi nisa a
kallon ina daidai inda maryam takewa mainasara shag'waba a asibiti. Duka sai na ji sun burgen,
dama ace ni da Awwal ne haka muke kashe juna da kallon k'auna. Wani murmushi ya yalwatu
kan fuskata wanda ban san ina yin sa ba. Ji na yi an d'auke wayar, idanuna na d'ago na kalle
shi tare da fad'in lafiya?"
Kallona yayi cikin ido sanna ya d'auke kansa. "Samha wannan da kike kallah fa shirine, karfa
kina sakawa ranki damuwa ki b'ata zaman auren ko saboda ganin soyayar film."
"Awwal, daman na tab'a ce maka ina buk'atar soyayyarka? Ko kuwa ka ga ana haska
mu'amalar aure anan? Ni fa bana son irin haka ka bani wayata ban shiga sabgar ka ba kaima
ban buk'aci ka shiga tawa ba. Tunda ba wani laifi kaga ina aikatawa ba.
" Samha dole na shiga sabgarki tunda ni mijinki ne."
"To maza na san dai maganar ba ta wuce ta abinci ba, muje na zuba maka abin da ka kawo
anan aka fi kauri!" Na furta cikin d'aga murya.
"Me kike cewa haka? Kina nufin iya ka cin abinci na iya kenan?"
"Wannan fa kai ta dama ni kazo ka ba ni abin da zan zuba maka kawai."
Bai ce komai ba ya isa wajen firji ya kawo ledoji. Ko da na bude kaji ne masu rai da lafiya
gasassu dayar ledar kuma da ya ciro a firjin kayan sanyi ne masu sanyi. Murmushi ne ya kufce
min domin Allah ya yi ni da kwad'ayin kaza. Filet na d'auko na zuba masa na ajjiye tawa awani
filet d'in na maida guda zan rabawa yara da safe. Zama na na fara ci ba ko jira. Awwal ya gama
gane ni sosai, da zarar yaga ina cikin fushi da wannan