Showing 9001 words to 12000 words out of 24103 words
Chapter 4 - WASU MAZAN Part 1 Complete By Ummu hibbat .pdf
gaba da tafiya na kuma binsa har
muka shiga d'akin sa. Zama ya yi a bakin gadonsa don haka na yi saurin zama gefen sa tare da
rungume shi k'am k'am na ce, "Bombino, don girman Allah kai ni gidan hajiya, wallahi ba zan iya
zama a gidannan ba. Ko kuma ka kaini gidanmu amma wallahi zai illata ni." Chakume fuska ya yi ya fara ki ci niyar raba ni da jikin sa ya ce, "Samha mene ne haka wai? Ki
bar jikina fa ban son rashin hankali, wa ye zai illata ki a cikin gidan bayan mu kad'ai muke a
cikin gidan?" "A aljanin ka wallahi! Aljanin ka ne zai ka she ni ." Na ba shi amsa tare da
rushewa da kuka. Madubi na kalla sai kuwa na ga Awwal a ciki yana murmushi. Sam na mance
cewa ni da shi duka muna agaban madubi ne . Wata uwar k'ara na sa ka tare da zubewa a jikin
sa sumamma. Wuraren la'asar sakaliya na farka na ganni kan gadona ni guda ina kwance
zabura na yi na yo falo na tarar ba kowa domin na san yaran duka suna islamiyya. Da
sauri-sauri na rufe gidan na shiga gidan mama Aisha mak'ociyata na kai mata ziyarar dole. Hira
muke amma sam hankali na baya kan zancen, har ta fuskanci ina cikin matsala. Ko da ta
tambaye ni me yake faruwa da ni na ce mata ba komai. Ana shirin k'iran sallah na fito na zo zan
bud'e gida sai ga Awwal ya dawo da yara. Don haka tare muka shiga da su, sai sannan na ce
da Ameera ta rakani kitchen na daura abinci. Shi dai kawai kallona yake yi.
Haka muka d'auki tsawon mako biyi kullum cikin fargaba nake rayuwa a cikin gidan duk da
cewa ban kuma gamo da aljaninn Awwal ba. Ko makaranta ba na iya zuwa har su adama suka
min waya na sanar musu zan fito satin gaba.
Satin gaba da ya gabata na samu zuwa makaranta amma sam ba na cikin nutsuwata, saboda
ban gama sakin jiki da gidan ba, kuma ga shi ina cike da matsananciyar sha'awar da ta ke son
ta fi k'arfin tunani da hankali na. Ina mamakin kaina idan aka cire kwanakin da na yi jinyar
jinnunna kullum sai na ta shi cikin dare na sanarwa Allah a mai dani kalar Awwal ko kuma shi a
mai da shi kalata. Amma sam ban samu sauyin ko guda daga ciki ba. Sai ma yadda na fuskanta
abin na wa kullum ci gaba yake yi. Daga makaranta gidanmu na wuce ranar wurin mamata
domin ko ba komai ya kamata ta san halin da nake ciki.
Ko da na sanar mata halin da nake ciki game da Aljanin Awwal. Murmushi Mama ta yi tace dani
kawai na tsorata ne ba wani aljani abin da take so dani kawai na rik'e addu'a.
Haka dai muka yi ta tattaunawa tana k'ara sanar min wasu addu'o'in da ban san su ba na
neman tsari da jinnu. Misalin biyar na koma gida na saki jiki na shiga kitchen d'in da rabon da
na shi ge shi ni kad'ai tun ranar da abin ya faru. Bakina cike da addu'o'i har na kammala komai
na dawi falo na kunna k'iara'ar alkur'ani mai girma sautin suratun bak'ara daga bakin Aramma
malam Abdurrahman Yola. Yana yi ina bi har lokacin sallah ya yi Awwak ya dawo da yara.
Haushin sa ne ya kamani ta yadda yake yawo zulum-zulum cikin maza yana amsa sunan su,
alhalin shi rakosu ya yi. Bayan munyi sallah sai muka ci abinci da yarana ban da shi saboda ya
fita. Aikin gida na taimaka musu suka yi har aka kira sallar isha. Sallah muka yi sannan na kaisu
d'akin su ka kwanta. Ita kuma Ameera a kusa d'akina nata d'akin yake.
Falo na dawo ina zaune ina kallon tashar zee aflan wani indiyan fim ake haskawa na soyayya
na yi nisa sosai da shagala a cikin kallon sa yadda jarumin yake nunuwa jarumar kulawa da
soyayya shine ya ba wa zuciyata damar aikewa da kwakwalwata katin gayyatar dawomin da
bara bana..... Yaya Yusuf ne ya kalli Kaltum ya tambayr ta daga ina muke kuma waye ya sauke mu. Baba
kuwa bai ce komai ba ya tsaya na k'are min kallo. Duk na firgice amma kuma da jin amsar da
Kaltum ta fara bawa Yaya sai na samu nutsuwa. "Bayan mun fita munje makaranta sai na ce
da Samha ta rakani na siyo biro a wani shago bakin titi, muna fita sai wannan me motar Allah ya
kawo tsautsayi na buge Samha amma kuma bata ji ciwo ba sai suma da ta yi saboda firgici.
Ganin haka ya sa aka shigar da ita mota nima na shiga ya kaimu asibiti aka bata kulawa. Ko da
ta farfad'o aka tabbatar ta samu nutsuwa kuma bata da wata damuwa shine aka sallame mu,
sai ya kawo mu gida Samha ta ce ya sauk'e mu bata son ku ji kar hankalin ku ya ta shi."
Kaltum na kaiwa karshen zancen ya ya Yusuf ya mike a fusa ce tare da fad'in, "Kuma shi ne ya
biye mata ba zai zo gida ya bayar da hakuri ba? Zaki iya gane lambar motar sa?" Ya tambayi
kaltum. Wani sanyi na ji ya ratsa zuciyata yadda na ga yaya Yusuf ya yarda da maganar kaltum.
"Gaskiya ba zan iya ganewa ba, saboda agigice na ke wallahi." Kaltum ta bayar da amsa.
Ya ya Yusuf ya ce, "Baba bari na bi sawun sa ko zan tarad da shi ."
"Aa Yusuf bar shi kawai tunda dai har ya kaita asibiti an duba lafiyarta ai zance ya k'are. "
Fa sa tafiyar yayi ya juyo ya kalle ni ya ce, "Yanzu ba in da yake miki ciwo?"
Kallona na kai gare shi na ce, "Eh Yaya."
To shi ke nan ku shiga ciki kawai. Ya bamu amsa. Shiga muka yi muna Sallama ba kowa
tsakar gidan don na tabbata su aunty ba sa gida mama kuwa a wannan lokacin ta na Sallah da
na filfili.
Muna shiga d'akinmu na fad'a gado na fashe da kuka na ce, "Yanzu Kaltum shi ke nan na rasa
Isa? Isa ya barni da duniya wayyoa zuciyata , Kaltum Isa ya mace ya barni da tarin soyayyar sa
a zuciyata."
"Haba Samha ki yi shuru mana kar wani ya ji ya gane gaskiyar da muka b'oye. Ki yi hakuri
yanzu ba lokacin kuka bane, lokaci ne da zakiyi masa addu'a, a yanzu Isa yana can yana amsa
tambayar da mala'iku suke masa... Ko da jin haka wani sabon kuka ya zo min na danna kaina
cikin fulo ina yin sa gudun kar wani yaji ya tambayi ba'asi. Haka dai kaltum ta lallab'ani ta bar gidan. Kusan kwana biyar da faruwar hakan Babanmu ya
k'irani ya kuma sanar min na sanar da me zuwa wurina fa idan ya zo. Sanar masa na yi da ya
rasu ma shi baya duniyar, hankalin Babanmu kwarai sai da ya ta shi da jin mutuwar Isa. Fatan
rahma ya yi masa sannna ya yi mun addu'a da fatan samun wanda ya fi shi. Kwanaki na wucewa watanni na shud'ewa shekaru na taruwa. Kwatsam watarana aka turo
yaro aka ce ana sallama da ni a k'ofar gidanmu. Koda na fita sai da zuciyata ta buga saboda
ganin me k'iran........
8
Ganin sa ba k'aramin tayar min da hankali ya yi ba, domin ya dawo min da mutuwar Isa ne
sabuwa dal! Cikin zuciyata. Wannan bawan Allahn nan ne da ya temake ni a lokacin mutuwar
Isa. Kamar me sand'a na k'arasa wurin sa da sallamar da da kyar ake iya jiyota a gare ni.
Amsa min ya yi cikin farin ciki sannan ya gaidani tun kafin na gaida shi. Amsa masa na yi cike
da jin kunyarsa, saboda ni ce ya kamata na gaida shi .
Shuru muka yi dukan mu na wani lokaci sai can kuma ya ce dani, "Tun da na ta fi na gaza
samun sukuni, ina ta tunanin ko ya jikin ki. Amma sam zuciyata ta gaza samun sukuni shine na
ce bari na zo na duba lafiyarki."
"Ayya, gaskiya na gode sosai da kulawarka Allah ya bar zumunci."
"Amin." Ya amsamin ya kuma tambayata Kaltum. Sai na sanar masa tana gidan su yau ba mu
had'u ba. Mun dan tab'a hira kafin ya yi min ban kwana ya tafi ni ma na koma gida.
Daga haka wasa gaske k
Duk bayan wasu kwanaki sai ya zo mun gaisa har ranar na fidda kunya na tambaye shi
sunansa ya ce da ni Awwal. Abu guda da Awwal ya furta a gare ni shi ne ya yi silar watsewar
tarayya ta da shi. Muna tsaye muna hira kamar kullum ni da shi ya du be ni ya ce, "Samha,
yaude ya kamata na bud'e miki sirrin zuciyata ki sani tunda dai na ga kin gaza fahimta."
Ban kawo komai ba a zuciyata na ce, "Yaya Awwal ina jinka."
Murmusawa ya yi ya kalle ni ya gyara zama ya ce, "Wato Samha ranar da na fara ganin ki na
tausaya miki sosai fiye da yadda zaki tsammata. Zuciyata ta yaba da ke sosai da jin cewa na
samu matar aure, sai dai bayanin da k'awarki kaltum ta yi min a asibiti shi ne ya dakatar dani da
abin da ya ke zuciyata. Amma zuwa yanzu ya kamata ki san cewa Wallahi ina matuk'ar kaunar
ki sosai a zuciyata. "
Tun da ya fara magana nake jin sa, yana kawo k'arshen zancen na sa na ji zuciyata tana min
wani irin d'aci. "Awwal ka yi hakuri zuciyata ta Isa ce shi kad'ai, yadda ya mutu ya barni ina jin
cewa ba zan wani jima ba ni ma zan bi shi." Ina gama fad'ar haka na mik'e na shiga gida. Wasa
gaske tsawon mako biyu dukkan sanda ya aiko yaro bana fita har mama ta fahimci da matsala
ta zaunar da ni ta tambaye ni ba'asi. A maimakon na ba ta amsa kawai sai na saka mata kuka,
ba ta hanani ba sai da na yi don kaina na gama sannan ta ce dani tana ji na.
Kwashe dukkan abin da ya faru na yi na sanar mata har k'aryar da muka yi ni da Kaltum
ranar da Isa ya rasu. Mama ta yi min fad'a sosai kan hakan sannan ta nuna min cewa matukar
Awwal ya na da halin kirki na daure na amshi ta yinsa, wata kila Allah ya d'auke Isa ne saboda
rabon Awwal ce ni. Da to na amsa mata na koma d'akina ina ta zubar hawaye.
Wata biyu masu zuwa aka saka ranar bikin yayyuna. Na yi murna sosai kuma na yi kuka
kasancewar da Isa yana raye da yanzu har da bikin mu.
Dai-dai lokacin kuma mukayi walimar gama makarantar secondry school d'inmu. Munyi murna
sosai ka sancewar muna daga cikin d'alibai masu hazaka da malamai suka yaba mana. Kuma
muna daga cikin k'ungiyar MSS har ma ina a matsayin mataimakiyar Amira.
Lokacin auren su Aunty dija ya na ta gabatowa ana ta shirin biki, haka kuma daga bangaren
Awwal ya na ta nacin zuwa. Ganin bai samu had'in kai a wurina ba sai ya koma ya aika manyan
sa wurin baba a kan aba shi damar zuwa wurina. Lokacin da na ji haka na yi dariya sosai domin
abin da ya kamata ya yi tun a farko ne bayyi ba sai yanzu. Haka Babanmu ya ba shi dama tilas
idan yazo sai na fita na saurare shi har ya yi nasara na amshi soyayyar sa. Ko da ya samu haka
tuni Babanmu ya ce matukar yana cikin shiri zai iya ba shi ni nan da sati takwas. Tuni Awwal ya
amsa da babu wata matsala, don haka shirin biki sai ya zama na mu uku ake yi. Daga nawa
sashen ba zan iya cewa ina farin ciki ba, kuma ba zan iya cewa ina bak'in ciki ba. Saboda a
yanzu ina jin Awwal a zuciyata sosai. Sai dai duk da haka idan na tuna Isa sai na ji sam bana da
muradin rayuwa da kowanne d'a na miji.
Haka su aunty suka yi ta yi min fad'a da kuma nuna min mahimmancin auren Awwal domin
tunanin si zayyi wuya na samu me min irin wannan son. Tun da sun ga yadda ya na ce min duk
da irin k'orar da na yi masa.
Wasa gaske har ranar aure ta zo, akayi duk wata hidima da ake yi a wurin aure aka kaimu
gidajen mu. Abu mafi farin ciki iyayen mu da d'anginmu ba su da ra'ayin durawa amare
magunguna na mata idan za'a kai mace gidan miji. Iya wuya kawai akwai wani had'i da innarmu
ta yi mana ana gobe za'a kaimu ta bawa kowa ta ce take ya shanye ya bata kwanon. Tun a daren farko na fuskanci Awwal yana da matsala, domin daren farko na kowacce
amarya da ango dare ne da ake sa ran farin ciki zai mamaya, domin dare ne na d'okin ango
kuma na fargaba a wurin amarya. Tabbas na ga d'okin har ma da zalama a wurin Awwal, se de
cikin wasu mintuna da badu wuce shida ba Awwal har ya gama cin amarcin sa ya baje yana
bacci. Na yi mamaki matuk'a da jin yadda aje ruruta daren domin anawa b'angaren banji wata
hangurb'ar damuwa ba. Hasalima zan iya cewa Awwal ba lalle ne idan ya cimma hak'arsa ba,
tun da na san cikakkiyar budurwa na ke.
Wasa farin girki! Dare na biyu Awwal bai ma san da ni ba. Sai da muka d'auki tsawon kwana
goma kafin Awwal ya kuma waiwaya ta, ranar sai da....Yi kuka da idanuna, saboda tamkar a
jefaka a lilo za'ayi maka linji ka rufe idanu da niyyar jin dad'i kawai sai ka jika an gwara kanka da
bangon da ke gefen lilon kuma an barka ba me lallashi bare kuma baka hakuri . Na yi kukan zahiri har ma da kukan zuci. Amma kuma da matukar kunya na ce da Awwal ga
matsala.
Bank'ado da kofar da ya yi shi ne ya saitani na dawo tsaf daga tunanin shekarun da suka
shud'e. Fuska ba annuri na yi maza na mike na zuba masa abinci na wuce d'akina.
Wase gari tare muka fita amma kowa da motarsa, makarantar islamiyya na ya da zango.
Bayan karatun safe mun fira karyawa Adama ta bude mana jaka da tulin maganin mata har
ma da maza. Kun san mata da kayan mata kowa sai ta fara jida har da masu d'aukar yajin
maza. Ganin haka sai na ce da Adama ta had'amin kowanne guda bibbibu da na mazan da
matan zan kai unguwar mu akwai me son siya. Farin ciki sosai adama ta yi ta had'amin ta bani
na karb'a cikin zuciyats cike da farin ciki yau na samu makamin da zanyi nasara akan Awwal.
Sai dai ashe da sauran rina a kaba............
9
Ina ta farin ciki a cikin zuciyata yau ni ma zanyi bacci me d'adin gaske. Domin na gama yanke
hukuncin na samu maganin matsalata. Gida na koma daga makaranta na fara shirya mana abin
da zamu ci. Kamar kullum dai zuwa k'arfe biyun rana na kammala komai. Yara suna gidan
Hajiya Bonbino yau bai dawo da wuri ba. Ina tsaka da kallon tv ina sauraren wa'azi tukunna na ji
zuwan sa a mota. Ban yi wani yunk'uri ba har ya iso bakin k'ofar falon. Ko da ya shigo daga inda
na ke na yi masa sannu da zuwa gudun kar na yi wani abu ya ga ina rawar kai ne. "Yawwa." Ya
ce da ni sannan na ta shi na amshi jakar sa na bi shi har d'akin na sa. Ko da muka shiga gefen
hado na zauna na ce, "Wanka ko abinci wanne za ka fara?" Tare da turo baki gaba wai ni adole
irin matar love d'innan. Jim kafin ya ce, "Wanka zan yi." Da to na ba shi amsa na wuce toilet na
sa na na had'a masa ruwan wanka na fito. Ina fitowa na koma bakin gadon tare da fari da idanu
na ce, "Masoyi, na had'a ruwan wanka sai gare ka."
Yi yayi kamar bai ji me na ce ba, sai kuma ya ce, "To ai sai ki je falo ki jirani zan cire kaya ne na
saka jallabiya.". Murmushi na yi, idan da sabo na saba sa wannan kam. Don haka ban tanka ba
na fice a bina a zuciyata kuwa na ce, " Hummm! Zamu had'e ne anjima za ka gane da wa kake
magana." Ban go na kaiwa harbin iska cike da farin ciki na wuce kitchen. Abincin sa na bud'e na d'auko
wannan maganin da aka ce na maza ne na barbad'a masa shi sosai ta yadda zai buge shi
yadda ya kamata. Ko da na je na ajjiye ina jiran fitowar sa amma shiru. Sai da na fidda rai da
fitowar sa sannan ya fito ya zauna na zuba masa ina yi ina satar kallon sa ina murmushi. Baki
ya bud'e tare da bismillah ya fara a fawa cikin sa, har ya gama ba muyi magana da juna ba ni
dai kawai na matsu na ga sakamako. Sauri na yi na shiga daga ciki na kuma gyara jikina da
turaruka masu k'amshi saboda tsaro domin ban san ya abin zai kasan ce ba. Yanzu ne ko sai
zuwa dare. Abu kamar wasa dai har yamma ba wani alamu a wurin Awwal na canji. Sai jikina ya
yi sanyi duka ina kuma