Showing 3001 words to 6000 words out of 24103 words

Chapter 2 - WASU MAZAN Part 1 Complete By Ummu hibbat .pdf

27 Apr 2025

1594

har na zo wuri ya k'uremin ta
yadda idan na tara yara rabuwar zata min wahala idan bai sauya ba. Dum! Na ji zuciyata ta
buga. Karfa naje na samu wani ciki a daren yau, na furta a zuciyata. Anya ba zan koma ba
kuwa? Na tambayi kaina, ya zakiyi da tarin yawan damuwar da take zuciyar ki? Ai ko ba komai
wata k'ila ki samu nutsuwa idan Allah ya sa yayi abin kirki.
Da wanann shawarar ta karshe nayi na'am da zuciyata da kuma tuna yadda idan na koma
ba lalle na yu baccin kirki ba yadda nake jin marata kamar zata b'alle, sai kawai na hau gadon
na gyara kwanciyata na nima na juya masa baya tunda na saba. Da zan kalli bayan sa tabbas
ba zai juya ba har sai na yi bacci. Amma idan na juya baya to shi sannan zai samu damar
juyowa gareni.

Cikin wasu mintina da ba su wuce uku ba wanda nake k'ok'arin na gyara kwanciya domin
samun farin ciki, kawai na ji Awwal ya saki jiki yana wani irin mun shari kamar na bacci.
"Bantan uba! " Na furta cikin wata irin matsanan-ciyar damuwa. Anya Awwal yana da hankali
kuwa? Wallahi ba zan yadda da wannan zaluncin ba, duk da ba yau haka ta saba faruwa ba
yau kam ko ni ko shi a cikin gidannan.
"Awwal! Awwal!" Na shiga kwara masa k'ira saboda idanuna duk sun rufe yau kunyar ma babu
sauranta a cikin idanuna ko ta doke yau sai ya sama min farin ciki kamar yadda ya samawa
kansa. Tunda auren daman b'angare biyu ne ba shi daya ba.
Zabura yayi ya kalle ni yaha fad'in "Haba Samha, a cikin daren nan ai mak'ota ma za su ji ki
wallahi. Wai tukunna ma mene ne na wannan k'iran ne hakan?"
Raina ne ya kuma b'aci da jin tambayar da ya min kamar bai san laifin sa ba. "Dole ka
tambayeni tunda ka samu nutsuwa, wallahi na yi dana sanin auren ka Awwal. Kullum burinka ka
soya min zuciya da mugunta? To wallahi yau.........."
Bai bari na gama maganar ba kawai na ga ya d'auki filo ya yi falonsa. "Baka isa ba!" Na furta
ina bin bayan sa.
Sai dai kafin naje tuni ya zaburo da masifa yana fad'in "Wallahi kar ki biyoni, ni matsalata da ke
kenan! Sai kije kiyi wasu shaye-shayen ki kuma idan dare ya yi ki damu jama'a! To ki koma
kawai bana son damuwa abin da kike so ne an yi maki to kuma sai mene ne?"
Idanu na zaro kamar yana kallona duk da cewa ya juya baya ne na ce, "Ai ba ni ce na kawo
kaina ba, amma ka sani akwai gaba wallahi.
Ina gama fad'ar haka na fice a d'akinsa na koma na wa. Da kuka da addu'a da komai daren
ranar na samu nacci.
Sassafe na shiga kitchen na shirya abin karyawa yana zaune a dining na same shi yana wani
sussunkuyar da kai.
Solob'iyo kawai! Kamar wani wanda yayi abin arziki har yake jin kunyar ganina. Na fad'a cikin
zuciyata.
Ban ko zuba masa ba na zuba nawa na fara cin ka ya na, idanu ya lumshe ya jigingina da
kujerar sannan yace " Ki zubamin abinci na ci gajiya ke damuna ina son na je na kwanta."
"Dole ai ka kwana kana zikiri ai dole kaji bacci." Na ba shi amsa ina tura masa abincin da na
zuba masa gaban sa. Murmushi ya yi sannan ya bude idanun sa a kan abincin ya fara ci.
Ina gamawa na shirya na fita ban ce masa komai ba na tafiyata makarantar islamiyya.
Ina chan muna karatu ya k'irani yake sanar min idan na ta shi naje gidan hajiya an yi bak'o sai
ku dawo da yaran.
Bayan mun ta shi sai na koma gida tunda ya ce bak'o ai ba zanje gidan hakan ba. Abinci na yi
sannan na shirya cikin wani les na alfarma, jilbab na saka me girma na saka gilashi a idanuna
na fita zuwa gidan hajiya da ke anguwar samunaka.
Da sallama na shiga gidan karon farko da wani mutum na yi idanu hud'u wanda sai da
zuciyata ta tsinke da kallon da ya min. Kad'an ya hana na saki fulas d'in kayan su sube sai na ji
Amira tana fad'in oyoyo Mommy......


3
Cikin sanyin jiki kamar zan fad'i kasancewar rungumar da Amira ta yi min ba ta wasa bace, sai

na dai-dai ta tsayuwar na na ce mata, "Amira sannu muje ciki ko.
Tsabar na duburburce da kallon da yake min har na mance da wani batu wai shi gaisuwa. Don
haka na kama hannun Amira muka shiga ciki muka samu su hajiya a tsakar gida suna zaune ita
da Shaheed da Ahamd k'annen Amira, sai kuma k'anwar Awwal mai suna Salma ita ma tana
zaune. Tana ganina ta fara murmushi ta mik'e ta karbi kayan hannun nawa ta ajjiye, zama na yi gefen
hajiya ina gaida ta ta amsa min cikin farin ciki.
Salma ma ta gaida ni na amsa ina tambayar da ya bata je school ba, saboda islmiyyar mu
guda da ita sai dai tana ajin farko ne.
Hira muke da sirikata gwanin ban sha'awa saboda mace ce mai kirki ba ruwanta da wani batun
surukuntaka jina take kamar Salma.
"Ashe bak'o aka yi hajiya?"
Na furta cikin sanyin murya.
"Efa wallahi yaron k'anin babansu Awwal ne ya zo wanda suke abokaine daman."
Ta ba ni amsa.
"Ma sha Allah gaskiya ya yi zumunci sosai wallahi."
"Sosai kuwa aunty tun da ga abuja fa ya zo."
Salma ta ba ni amsa.
"Kai! Abuja? Gaskiya ya sha tafiya. "
"Ba kad'an ba kuwa wallahi.
Hira muke yi nida Hajiya da Salma har muka ji sallamar Awwal ya shigo.
Ban juya ba saboda ko ganin sa bana so a yanzu.
Har suka iso inda muke hajiya ta yi musu sannu da zuwa suka zauna kan ta kafet d'in.
" Samha ga nan bak'on na mu fa Mu'azzam."
Na ji Awwal ya furta.
D'ago da kaina na yi da niyyar na gaida shi kawai sai na ga wanda na gani mai shegen kallon
nan ne a lokacin da na shigo .
Kuma har yanzun ma ya kureni da manyan idanun sa, gaida shi na yi ya amsa yana washe
min baki.
Awwal ya ce, "Mu'azzam ka gane ta kuwa?"
"Gaskiya ban gane ta ba wallahi kasan na jima ban zo ba, Amma ko ita ce matar ta ka?"
"Au ashe ma ka gane ta ita ce aikuwa."
"Kai ma sha Allah cewa zakayi matarmu ce ai."
Harara Awwal ya watsa masa ya ce, "Da kai muka biya sadaki ne?"
"Kai Awwal ai tunda ka biya kayi mai wuyar."

Dariya dukan su su hajiya sukayi Salma ta ce, "D'an uwa bar shi duk kishine yake damun yaya
fa."
Harara Awwal ya aikamata ita ma har da jifanta da charbin hajiya ta mik'e da gudu ta shige
falom hajiya .
Ganin haka ya sa na mik'e tsam na bi bayanta saboda daman na gaji da zaman.
A can falon Hajiya muka yada zango muna ta hira nida Salma har la'asar ta yi mukayi sallah
muka shiga kitchen muka d'aura abincin dare.

Da misalin shida na yamma muka kammala girkin tuken shinkafa miyar yakuwa da kunun
gyada na Hajiya, saboda hajiya kullum dare sai ta sha kunun gyada take bacci.
Wanke komai mukayi da muka b'ata muka gyara kitchen d'in duka sannan muka sake gyara
falon muka saka turaren wuta mai d'adi sosai.
D'akin Salma muka wuce chan muka samu yaran duka sun had'e wayoyinmu suna aikin
game, wanka na yi saboda matukar nayi aikin girki bana jin dad'in jikina matukar banyi wanka
ba, ina fitowa Salma ta dube ni tace, "Aunty Samha kwad'uwa."
"To fa! Saboda kinganni ina lunk'aya a kogi?"
Na bata amsa ina dariya.
"Aa, kawai yawan wankanki ne yake ba ni mamaki. Ke fa kullum kika zo mukayi girki da ke sai
kinyi wanka a gidan nan."

"Ai Salma wanka duniya ne wallahi, kuma matukar kika yi aikin girki to kawai kiyi wanka kar ki
ce wai ai mukubur ne ko gas, a'a shi kansa wannan hayakin dake fita a cikin abincin ai duka
kamshin sa jikin ki zai turara, to kinga bai kyautu ace ke da abincin kuna kamshi guda ba.
Amma idan ki kayi wanka kika sha k'amshi to abinci daban ke ma daban."
Baki Salma ta sake ta na kallona tace, "Ai kuwa dai gaskiya ne, sai dai ba kowacce mace ce
zata iya hakan ba sai Irin ku gaskiya, ina yiwa ya ya murna ya samu mace ta gari kuma mai
addini."
Murmushi na yi da yabon da ta yi min na ce, "Kai Salma wallahi baki da dama."
"Kai aunty ina da mana tunda ga shi har abinci nake ci da ita."
Da hararar wasa na bita na saka kaya muka fita falo domin yin sallar magrib, muna zuwa muka
ga Hajiya tana kan sallaya tana lazimi ita da Amira.
Su Shaheed kuwa na san sun tafi masallaci.
Kowa sallah ya fara yi jin an gama k'iran sallar magrib d'in.
Sai bayan isha tukanna su Awwal da Mu'azzam suka shigo suka zauna da nufin cin abinci.
Nan falo muka shirya komai ni da Salma muka zubawa kowa ya fara ci.
Can sai Mu'azzam ya yi gyaran murya tare da fad'in, "Um na ce ba."
"Muna jinka." Salma ta ba shi amsa.
"Yawwa Salma wai wace ce ta yi wannan abinci mai shegen dad'i?"
Dariya Hajiya ta yi ta ce, "Allah ya sa dai Mu'azzam kana kusa da kujera."
"Gaskiya kam."
Awwal ya furta.
"Ya Mu'azzam ai matartaku ce ta girka."
Salma ta fad'a.
"Kai! Yanzu Awwal saboda rashin mutumci matar ta iya wannan girkin shine ba ka gayyace ni
da sallah ba?"
"To yanzu da gulmarka ta motsa ba gashi ka zo ba kuma ka ci."
Awwal ya ba shi amsa.
Hajiya kuwa cewa tayi ita yaronta ba gulma yazo ba zumunci ya zo. Haka dai sukayi ta raha har
muka gama.
Sai wajen tara tukunna muka fara haramar tafiya gida, Mu'azzam ya dubi ne ya ce, "Matar
gaskiya ranar da zanzo atabbatar an yi mana girki wanda ya fi wannan ma dad'i."

Kallo na kai ga Awwal na ga yadda ya had'e fuska da alamu baya son ya k'irani da wannan
sunan.
Ganin hakan da nayi ni kuwa tuni na sake fuska tare da fad'in, "Karka damu, in sha Allah duk
yadda ka ce hakan za'ayi."
Washe baki Mu'azzam ya yi ya na fad'in, "Godiya nake ginbiyarmu."
Daga haka Awwal ya sa ke b'ata fuska ya fice a gidan.
Bayan sa muka bi dukan mu har Hajiya har sai da muka shiga ya tayar da motar sannan suka
juya cikin gida.

Sassafe da gari ya waye na shirya yara da yakr monday ce suka ta fi School. Ina kwance a falo
ina hutawa sai ga shi ya shigo gidan fuska duk a chakud'e ya dube ni ya ce.........


4


"Wai ke da ga kinga maza sai kiyi ta washe baki saboda rashin hankali, har ya na ce miki matar
kina wani washe baki ko? To wallahi karki ga d'an uwa na ne duk wanda zai shiga gona ta zan
ragaraga da ke da shi d'in."
Ni maganar ta sa ma dariya ta ba ni, don haka na tik'i dariya sosai iya san raina har da
tuntsurawa sannna na dube shi ya cika ya kai iya wuya, na ce, "Ragaraga ko? Su Awwal
manyan mazaje."
Ina fad'ar haka na mik'e na yi hanyar d'akina.
Da sauri har da sassarfa yake biyoni, ni kuwa ganin haka sai na arce da gudu na shiga na
saka sakata.
"Ki bud'e mana! Ai da na koya miki hankali, ina magana kina dariya kamar kin samu sa'anki?"
Ina daga ciki na ce, "Haba mazaje kamar ka ai ba duka aka sanku da shi sai dai gwaninta da
nuna isa a inda ya da ce."
"Mazaje!!" Na furta da k'arfi tare da sake kwashewa da dariya ba wai don ina jinta ba.
Kwafa ya yi ya bar wurin ina jinsa.
Bakin gadona na koma na yi jigum ina tuna yadda Awwal ya nuna min zallar k'auna a lokacin
da yake sona, wanda hakan ne har ya sa na bijirewa zabin da na yi a farko wanda har na nuna
shi a gida.
Ba zan mance lokacin da muke 'yan mata ba, watarana mun ta shi a makaranta ni da k'awata
kulsum muna sanye cikin uniform na kayan gammande kuma a lokacin muna aji uku wato
matakin k'arshe na gamawa. Kasan cewar ana zafin rana ga shi yau mun sha duka a wurin
wani malamin mu dalilin rashin yin aikin gida da yabu, shine ya sa na ce da kulsum yau sai dai
mu ne mi mashin ya kaimu gida don ba zan iya tafiya ba, har wani jiri nake ji idan na mik'e .
Tsaye mukayi bakin hanya muna duba na mashin wanda zamu hau amma wayam ba kowa .
Kusan minti goma muna tsaye har na fara jin juya ta na d'ibata, don haka sai na jingina a jikin
wata bishiya.
Mashin muka hango yana zuwa inda muke, don haka sai muka shiga tsaida shi. Sai da ya zo
daf damu sai muka ga ashe Isa saurayina ne. Wata kunya ce ta lullub'eni ganin irin murmushin

da yake sakar min tare da kashe min ido d'aya.
"Samhata yau kuma me ya faru kuke tsaye haka anan?"
Jin na yi shuru ne ya sa Kulsum ta ce, " Isa wallahi masiyiyarka ce ta tsaida mu wai ba zata iya
tafiya ba sai a mashin."
"Fad'uwa Ta zo daidai da zama. Kinga yanzu sai ta hau na kaita na dawo kema na d'auke ki."
Isa ya furta yana me kallona.
"Cab! "Shine abin da na furta tare da fara jan k'afata domin ko giyar wake na sha ba zan tab'a
hawa bayansa ya goyani ya kaini gida ba.
Ganin haka tuni kulsum ta ce, " Ai daman na san za'ayi haka, ba za ta hau ba fa."
"Wai kina nufin Samhata ba zaki hau ba?"
Ni dai ban kula shi ba na mak'e kafad'a na yi gaba.
Lallashin duniya Isa ya yi amma sam na k'i hawa. Don haka dole ya hak'ira ya tafi ya barmu.
Daga haka ba mu kuma jiran abun hawa ba muka kama hanya har gida.
La'asar sakaliya ina yiwa mama gyaran kayan miya za ta d'aura miya sai ga yaro ya yi sallama
wai ana k'irana a waje.
Ko da jin haka tuni na san cewa Isa ne. Wani farin ciki ya mamaye min zuciya saboda ina
matuk'ar kaunar Isa a zuciyata sosai, amma duk da haka ba zan iya fita ba sai mama ta bayar
da izini Saboda ina jin kunya.
Kusan minti biyar mama ta ce, "Samha ba jiran ki ake yi ba ne?"
Ban ce komai ba na ta shi simi simi na yi falonmu na kuma gyara fuskata da hota da kwalli.
Turaren mama na fesa mai kamshi na zura hijabina na fita domin na same shi. A zauren
gidanmu na same shi tsaye har ya gaji da tsayuwa ya tsugunna. Da sallama na shigo a bakina
ya dube ni yayi mirmushi ya ce, "Wa'alaikissalam ya ke ma'abociyar k'amshi da shanya
mutane."
Murmushi na yi na sa ci kallonsa na ce, "A'a fa dai, ba shanya ba ce."
"To mene ne?"
"Ina yini, kawai mu gaisa kafin."
"Wato kina nufin a bar zancen ko?"

"Kamar haka dai."
Na ba shi amsa
"Wai Samha sai yaushe zaki daina jin kunyata ne?"
Isa ya tambaye ni. "To ai dole na ji kunyar ka." Na furta cikin shagwaba tare da turo baki gaba.
"Me sa to ?"
"Saboda kai d'in kai ne mijina, nan gaba."
"To yanzu idan munyi auren ma kunyata zaki na ji?"
"Uh uh ni dai a bar maganar kawai."
"Samha sarkin kunya, Allah dai ya sa ba zaki juya min baya ba har gaban abada, saboda
wallahi samha ina matuk'ar k'aunarki a zuciyata, Samha k'aunarki fa ta kai girma da ko cikin
dare na kan iya farkawa na saka hoton ki gaba ina kalla ina hawaye ba don komi ba sai dan
tsabar yadda zuciyata da numfashina suke fusgowa ta dalilinki. Samha ina k'aunarki k'aunar da
bazan iya yiwa wata mace a duniya ba.
Idan na rasa ki wallahi na san zayyi wuya na rayu, ke ko da na rayu ma ba lalle na yi amfani

ba. Saboda ko da yaushe lumfashima da soyayyar ki yake fita. Don Allah Samha ki kasance
tare da ni har karshen rayuwata."
Ya k'arashe maganar cikin wata irin murya wacce ban san shi da ita ba, daga inda na ke kuwa
ina iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login