Showing 6001 words to 9000 words out of 16852 words
Chapter 3 - AJALI littafin Shafiu Dauda Giwa-1.pdf
ganin farko da suka yi wa saurayin ya shigo unguwarsu, duk da yake a cikin mota yake, ta
gilashi suke hango shi, a matsayin suna kwararrun zauna gari-banza, sannan kuma masana
akan ilimin sa-ido, sun fahimci cewar wannan saurayi duk inda ya fito ba mutumin kirki ba ne .
Akwai wani mutum da ya taba cewa ma da ganin saurayin ya san cewar dan fashi da makami
ne, shi yasa da zarar ya shigo unguwar suke hade masa fuska, kamar sun ga mutuwa.
.
Saurayin bai taba kula ta tasu ba, don kuwa ya
san cewar wata rana ma ba za su sake ganinsa ba, neman aure ya jawo mishi shigowa wannan
unguwar mai cike `yan sa-ido, dazarar an yi aure kuma ta kare
.
Saurayin ya yi murmushi da ya tuno cewa nan da kwanaki hudu za a daura auren sa da A'isha
rabin
ransa, Aisharsa da ya mace a kan kauna tsawon lokaci.
.
Ko da ya tsallaka titi sai ya shiga layin gidan
su masoyiyarsa A'isha wacce yake ta faman
ambatar sunanta sai kace mai bitar darasi. Ya
ci gaba da murmushinsa sannan ya daki
sintiyarin motar cikin farin ciki,
.
hakika komai yana da iyaka, ya ce a zuciyarsa. Ya dauki dogon lokaci yana nunawa A'isha
soyayya, amma ta ki ta gane kullum sai dai kawai shi yake kidansa sannan kuma yake rawarsa,
amma ita ba ma ta tasa ta ke ba. To amma
dai yanzu ai wulakanci ya kare tunda dai ta
kusa zama matarsa, ko da a ce ba ta
kaunarsa, ai ya zame mata dole ne ta zauna
da shi tunda dai ya saye iyayenta.
.
Saurayin ya ci gaba da murmushinsa na
samun nasara, ya ce a zuciyarsa, "Hakika kudi
suna da matukar amfani a rayuwa," domin ya
san cewar da bai mallake su ba to da shi da
A'isha kyakkyawa sai dai hange daga nesa. Da
yawa daga cikin abokansa sun sha damun shi
da surutai a kan wannan soyayya da ya ke yi
wa A'isha domin kuwa ta sha ta kwabsa shi ko
a gaban wanene ko da kuwa yana tare da
abokansa ne
.
Akwai wani lokaci da wani abokinsa ya ce da shi.
"Don Allah Gali ka rabu da yarinyar nan tun
da dai ba ta kaunar ka, wai kai ina ma ka
taba jin inda aka yi soyayyar dole ne? Ya
kamata ka canza sheka haka nan, domin kuwa
akwai `yan mata kyawawa a garin nan, ba
A'isha ba ce kadai kyakkyawa"
Gali ya yi murmushin ya ce da shi
.
"Abokina kada ka ga laifina don na likewa
yarinyar nan, wani lokaci ni kaina nakan yi
kokarin ganin cewar na cire son ta a zuciyata,
don in huta wa rayuwata domin kuwa A'isha ta
zame mini kamar maruru ko sartse a cikin
zuciya, ba na minti daya a duniya ban yi
tunaninta ba sannna kuma ba na iya daina
son ta a zuciya ta."
.
Tun daga wannan rana mafi yawa daga cikin
abokan Gali suka shafa masa lafiya, wadansu
kuma suka ma bata da shi domin kuwa su a
ganinsu ya ba da sojoji, ba haka aka san
zuciyar soja ba. To amma kuma abin da ba su
sani ba game da lamarin soyayya shi ne, ta
kansa mutum ya makance ya dukufa akan
son wani abu, wanda sauran jama'a ko da
kudi aka hada su ba za su so wannan abu ba,
.
domin kuwa idan ba haka ba, babu abinda zai
sa babban ba'askare a cikin sojoji, wanda ya
shiga har kasashen turai, amma ya dishe da
kaunar wata yarinya `yar cikin gida ba kirar
waje ba, har kuma ta zo tana wulakanta shi,
lallai abin dai kam akwai takaici.
.
Gali ya yi ajiyar zuciya da ya tuno walhalun
da ya sha a baya na kaunar wannan yarinya
A'isha, ya ce a bayyane cikin rada-rada.
"Kin ba ni wahala A'isha amma ba komai na
kusa ramawa"
A daidai wannan lokaci ne ya karaso kofar
gidan, ya yi fakin din dunkulalliyar motarsa
mai tudun baya, ya fito yana sanye da
dogayen kayan shudiyar shadda, dinkin ta-
zarce, dogo ne kakkaura baki, yadda yake
haka zuciyarsa take bakikkirin domin kuwa
da ran mutum da na kiyashi duk daya suke a
wurinsa.
.
Shekarunsa za su kai talatin da biyar koma fiye a duniya. Ya shiga zagayen gidan
kai tsaye, ya tsaya a cikin harabar inda shuke-
shuken alfarmar suke. Bai dade ba a wurin
wata karamar yarinya ta shigo cikin gidan, ya
tsayar da ita, ya ce da ita.
.
"Kice wa Ai'isha Gali yana jiran ta a waje"
Ba a jima ba yarinyar ta fito ta ce da shi.
"Ta ce tana zuwa"
Ya zaro wazobiya sabuwa fil ya mikawa
yarinyar. Ta amsa cikin doki ta fice a guje.
.
Gali ya yi ajiyar zuciya ya fara nazarin
harabar gidan. dawisu da agwagin ruwa da
suka fi komai ba shi sha'awa suna ta yawace-
yawace, da kuma koke-koke abinsu. Ya yi
mamakin yadda mahaifin A'isha rabin ransa
ke matukar kulawa da wadannan halittu. Ba a
jima ba A'isha ta fito. Tun daga nesa ta
murtuke fuskarta da ta hango Gali tsaye
kamar gunki
.
Ta ce a ranta "Wannan
wahalallen banzan kuma yaushe ya dawo?" Ta
karaso wurin da yake ta tsaya, ko sallama ba
ta yi masa ba, ballantana kuma ta dube shi,
to amma shi da yake ya saba da wannan
dabi'a tata, bai damu ba sai kawai ya fara
aikinsa na surutu.
.
"Ai'sha ya kamata yau dai rana daya ki saki
fuskarki a gareni, domin kuwa ni da ke mun
zama daya, kin ga fa yau saura kwanaki hudu
kenan a daura mana aure
.
Bai kamata a ce mu yi aure kuma ya kasance ba wata kwakkwarar jituwa a tsakaninmu ba.
A'isha
ya kamata ki hakura haka nan, bakin alkalami
ya riga ya bushe."
.
Ta juyo cikin izgili ta dube shi a yatsine ta ce
da shi.
"Kai da wacce kuma za a daura muku aure?"
Gali ya dube ta cikin kaduwa.
.
Ku jira part 7
_________
Yan mata kudaina wulakanta samari
Domin kuwa zai iya yiwuwa su zaku Aura
Izan ya kasance Saurayin da ki ka wulakanta wajen neman aurenki ya zama mijinki sannan ki
ka kamu da ciwon sonsa a yayin da shi kuma ya fara Rama wulakancin da ki ka masa
.
Mutane masu tsananin fushi, masu rike abu a zuciya, basa taba manta wulakanci
.
Wani mawaki yace = in aka furta so gareka sai kai na'am a zuciya karka zagi Kauna,
= Masoyi yana da rana
= Masoyi yana da Rana
.
Sai mun hadu gobe
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 7
.
"Kai da wacce kuma za a daura muku aure?"
Gali ya dube ta cikin kaduwa.
.
"A'ah! ni da ke mana A'isha, ko ba ki gane ni ba ne? Ni ne Gali masoyinki."
.
A'isha ta yi murmushi, amma ko da ganin
murmushin ka san cewar a boye a bayan sa
akwai abubuwa marasa dadin ji bila'adadin.
.
"Wani lokacin ka kan ba ni mamaki Gal wai
kai don Allah wanne irin mutum ne a duniyar
nan? Ba tun yau ba na nuna maka a zahiri, na
furta maka baki da baki ba na sonka, ba zan
taba sonka ba kuma, to amma kai ka like
mini. Yanzu kai saboda Allah har sha'awa
kake yi ka auri matar da ba ta kaunarka a
duniya?"
.
Saurayin ya yi ajiyar zuciya ya ce da ita cikin
damuwa "A'isha kin dade kina wulakanta ni a
lokacin da ni kuma nake ganiyar nuna miki
tsantsar soyayya tagari. To amma kuma ke
mene ne dalilin da za ki ce ba kya kauna ta?
.
Dole ne ma ki so ni A'isha, don kuwa babu
dalilin da zaki ki so na. Me kike bukata ki
mallaka a duniya wanda ba ni da shi? Ke
kanki kin san cewar ina da abinda za ki so ni a
duniya.."
.
Aisha ta tsayar da shi ta hanyar jifan shi da
wani busashshen murmushi "Lallai ba ka da
hankali Gali kuma ba ka san soyayya ba,
tunda har ka iya bude baki ka ce wai kana da
abin da zan so ka da shi dole
.
Na san cewar ba wani abu kake takama da shi ba face dukiyarka, to bari in fada maka ni ba
dukiyarka ba ce a gaba na? Kai a haukanka shi
kenan don kana da kudi dole ne mace ta
soka wannan ba gaskiya ba ne ka sake
tunani, domin kuwa kai ka mallaki kudi
amma kuma ni ba na sonka. Ka ga kenan
ashe ko wannan ma ya ishe ka darasi, don ka
fahimci cewar kudi ba sa iya sayen soyayya."
.
Gali ya dubi `yar budurwar cikin harzuka,
tunda suke ba ta taba kule shi irin wannan
karon ba. Ya ce da ita a fusace "To ya isa
hakan nan mu bar wannan zancen, yanzu
mene ne shirye-shiryenki game da auren
mu? Na san dai ba za ki rasa bukatar wani
abu ba."
.
Tace da shi "Ina bukatar abubuwa da dama
amma kuma ba wurinka ba. Ina da bukatar
ne a wajen mijina da zan aura, ko ba ka san
cewar wani zan aura ba ne Gali?"
.
Ya dube ta a tsorace "Wai me kike nufi ne?
A'isha ni fa ban gane ba, duk kin ruda ni
wallahi."
.
Ta ci gaba da murmushinta sannan ta ce da
shi.
"Abin da nake nufi shi ne saura kwanaki hudu
a daura aurena da wani saurayi da nake
kauna a zuciyata, amma ba kai ba."
.
Gali ya ce da ita cikin rudani.
"To ai ni ma saura kwanaki hudu kenan
mahaifinki ya daura aurenki da ni, kuma har
ma na fara raba katin gaiyata, A'isha."
.
"Wannan matsalarka ce Gali, ni dai
kasancewar ban taba cewa in kaunarka ba
kuma ban taba amsar komai naka ba don
haka idan an daura aure sai a kai maka wata
amayar amma ba dai ni ba."
.
Tana gama furta kalaman sai ta juya ta shige
gida tan kunkunai hade da yin tsaki. Saurayin
ya bi ta da kallo har ta bace, maganganunta
na ta faman amsa kuwa da kururuwa a
kwakwalwarsa. Tuni har ya fara lissafo
mutanen da ke bukatar a sai musu likkafani a
cikin jerin wadanda zai aika barzahu, indai
har ba a kai masa amaryarsa daki nan da
kwanaki hudu masu zuwa ba
_____________
BABI NA UKU
.
Ba kasafai Nazifi yake barcin rana ba, domin
kuwa ko ba inda yake da bukatar zuwa, da
wahala ka same shi a kwance da rana tsaka
kai ko rashin lafiya yake yi bai cika kwanciya a
daki da rana ba,
.
bar shi dai ya fito kofar gida ya zauna a dakali ya karanta mujallun fina-
finai ko kuma littafan soyayya. To amma
kuma sabanin wannan halayya tasa da aka san
shi da ita shekara da shekaru, kwanaki biyu
kenan Nazifi yana wuni a gida a kwance, ko
lekowa waje ba ya yi
.
Mahaifiyarsa Tabawa ta yi iyakar kokarinta
don ya fada mata dalilin canjin wannan
halayya tasa amma kuma abin ya faskara, ya
ki ya fada mata, sannan kuma babban abin da
ya fi ba ta mamaki shi ne wai a cewarsa
lafiyarsa kalau, ba inda ke yi masa ciwo. A
cikin kwanakin biyun nan ko wurin sana'arsa
ta kafinta bai leka ba,
.
wanda abu ne mai wahala ko ma kuwa menene dalilin a ce
Nazifi ya ketare rana daya bai je wurin
wannan sana'a tasa ba.
To amma kuma abinda ya tsorata Tabawa shi
ne, wani lokacin idan yana kwance yana barci
idan ta leka dakinsa
,
sai taji yana ta sambatu a cikin barci, yana fadar sunan wata yarinya
wai ita A'isha. Sannan kuma wani lokaci sai ta
same shi yana ta murmushi
.
Ko da Tabawa ta lura da wannna bakon al'amari da ya sami danta Nazifi sai ta ce da shi a
fusace a wuni na biyu
.
"Haba ai ni dama na san a rina ai ga irin ta
nan kullum kwanan duniya yaron nan sai na
yi fama da kai ka rika shan maganin miyagu
da kuma na mutanen boye, amma taurin kan
tsiyarku na `yan zamani ya hana ka Nazifi, ga
shi nan ai ka yi gamo da aljana za ta sabautar
da kai a banza."
.
Tun daga wannan lokaci Tabawa ta fara
shirye-shiryen kaiwa bokanyarta ziyara,
domin kuwa ta san cewar wannan aljana da ta
cafi danta guda daya da take alfahari da shi a
duniya, duk tsiyar aljanar in dai har ta kai ta
wajen kwararriyar bokanyarta Iya mai
dogari, to ko ba ta shirya ba sai ta fice daga
jikin danta Nazifi
.
To amma kuma shi Nazifi ya san cewar ko sarakan bori na duniya ne suka taru a kan shi ba za
su iya maganin
wannan matsala tashi ba, domin kuwa duk
kwarewarsu akan wannnan sana'a ba za su iya
mallaka masa masoyiyarsa da ya kamu da
ciwon so ba, wacce saura kwanaki biyu kacal a
daura aurenta da wani saurayin can daban
....
CIWON SO kenan
___________
MASOYA AKIYAYE
Izan zaka so mutum to ka soshi daidai wa daida
Haka nan yan mata kada ku dauki son duniya ku daurawa saurayi/budurwa, daga karshe kuma
ku rasasu, rayuwarku ta fada cikin garari
.
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 8
.
Kamar kullum a cikin kwanaki biyu yana
kwance sai mahaifiyarsa ta shigo cikin dakin.
Ya yi tsammanin zancen neman maganin ta
zo yi masa, to amma sabanin haka sai ta ce
da shi.
.
"Wata yarinya ce wai ta zo tana son ganin ka,
shi ne na ce bari in zo in sanar da kai."
.
Nazifi ya mike zumbur cikin mamaki, domin
kuwa inda haka nan ne banza sai a wuni ana
fama da shi ba zai tashi ba, kai a cikin
kwanaki biyun nan har lokacin sallah sai ya zo
ya wuce yana kwance ba zai yi ba.
.
Amma yanzu daga jin an ce wata ta zo nemansa, duk da dai bai san ko wace ce ba, amma a
can
cikin zuciyarsa sai ya ji ya dokanta da ya fita
din.
.
Ya tashi da sauri kamar ba shi ne ke wuni
a nannade a gado ba, kamar wanda ake yiwa
karin ruwa. Lallai dai sha'anin yaran zamani
sai dai a bar su, Tabawa ta fada a zuciyarta,
ita ma ta fice daga dakin.
.
Fitar sa ke da wuya ya cikaro da ita a tsakar
gida tana sanye da atamfa shudiya da kuma
dan fingilin gyale. Hakika zatonsa ya zama
gaskiya domin kuwa wacce yake tsammani ce
ya gani. Suka yiwa juna murmushi, Nazifi ne
ya fara yi mata magana.
.
"A'isha da ma ashe ke ce...?"
Ta jefe shi da murmushin Allah kashe ni don
dadi, sannan ta ce da shi.
"Kai da wa kake tsammani?"
"Ban yi tsammanin ki ba, domin kuwa na
dauka cewar tuni kin mance da ni A'isha."
Ta sake jifan shi da wani murmushi.
.
"In ban da abinka Nazifi ka taba ganin inda
mace ta mance da mijinta? Ko ba ka san
cewar ni a matsayin mijina nake daukarka ba,
ko ka mance da alkawarin da na daukar maka
ne in dai ina da miji a duniya ai kai ne
Nazifi."
.
Ya lumshe idanu don farin ciki, a zuciyarsa ya
ce Allah ya sa haka ya zama gaskiya A'ishata,
sannan ya ce da ita.
.
"Zo mu shiga daga ciki A'isha nan ba wurin da
za mu tattauna matsalolinmu ba ne."
Suka shiga cikin dakinsa, rufin kwano doron
zabuwa amma kuma babu silin babu komai a
ciki idan aka tsame dan tsurkun gadonsa na
katako mai kama da makara da kuma wata
kujera daya ita ma ta katako mai kafa uku da
rabi. A'isha ta yi wa kujerar kallon nutsuwa
kafin ta sami mazauni a kanta, domin kuwa
tunda suka shigo cikin dakin ta dubi
rubabbiyar kujerar ta fara zullumin cewar da
wahala kujerar ta iya daukar nauyin mutum
dukansa
.
To amma kuma cikin sa'a sai kuma
ta dauke ta gaba daya, duk da yake dai takan
nemi ta turgude a dalilin nakasar da ta yi na
gutsurewar rabin kafa guda. Nazifi ya fada
kan gadon katako
. Da farko A'isha ta yi tsammanin gadon zai baje a kasa, to amma
abin mamaki sai ta ga shi ma gadon taurin rai
gare shi irin kujerar, bai yi komai ba sai dai
burari da raki domin kuwa ko'ina a jikinsa ihu
yake yi da zarar an motsa.
.
Saurayin da budurwar suka kalli juna cikin
nutsuwa, Nazifi ya fara magana "A'isha ina
fatan ba ki samu wata babbar matsala ba a
wurin mahaifinki, domin kuwa ransa ya baci
sosai a dalilin ganina da ya yi tare dake."
.
Ta ce da shi "Kai zan yiwa wannan tambayar
ka riga ni Nazifi, domin kuwa tun rabuwarmu
nake faman zullumin ina fatan bai doke ka ba
Nazifi."
Ya yi ajiyar zuciya.
.
"Bai doke ni ba amma kuma gara ma a ce
duka na ya yi da abin da ya sanar da ni. Ya
gargade ni kada in sake kusantar inda kike
A'isha. Wannan kalami da ya yi ya sosa
zuciyata, a dalilin haka ne na sami kaina a
cikin wani hali mawuyaci. Tun wannan lokaci
ban sake fita ko waje ba kullum ina nan a
daki ina jimamin rabuwata da ke domin ni
ban ma yi tsammanin zan sake ganin ki ba
har abada, A'isha."
.
Ta yi murmushin karfin hali.
"Duk wannan bai kamata a ce sun sa ka
tsorata ba, domin ni kaina ya sha yi mini
wannan barazanar, don haka ka kwantar da
hankalinka Nazifi, aski ya riga ya zo gaban
goshi."
.
Ya dube ta cikin rashin