Showing 12001 words to 15000 words out of 16852 words
Chapter 5 - AJALI littafin Shafiu Dauda Giwa-1.pdf
kidimawa "Duka ka bar mini Gali?
Rabin miliyan fa ka ce...?"
Gali ya daga masa girar idanunsa sannan ya
ce da shi.
.
"Eh, rabin miliyan ne Nazifi, ko sun yi maka
kadan ne in kara maka kamarsu su zama
miliyan guda?"
.
Nazifi bai gasgata kunnuwansa ba.
________
Hehe Rikici bata kisa amma da alama zata fara takan Nazifi
SOJA GALI yayi tabargaza, shin meye tunaninku alokacin daya gano budurwarsa daya rage
saura kwana biyu a daura masu aurene, Nazifi zai aura, kuma zasu zauna cikin gidansa, me zai
faru
.
GWARAMA KENAN
Its shuraih 99% ________________
BABI NA HUDU|
.
Dogon malamin wanda ke sanye da dogayen
kaya farare rike da dogon carbi a hannunsa
ya gyara zaman katon nadinsa, wanda ya
mike tsawon bayan sa ya kwanta, kamar
wutsiyar doki, ya dubi saurayin da budurwar,
wadanda ke zaune a gaban shi suna
sauraronsa kamar wadanda ke daukar darasu
ya ce dasu cikin girmamawa,
.
"Yara me yake tafe daku?"
Nazifi da A'isha suka dubi juna a sannan
lokaci guda suka yi ajiyar zuciya, domin kuwa
shi dai Nazifi tun kafin su zo wurin malamin
da ma yana shakkar da wahala idan za su yi
nasara, to amma dai a yadda ya ji ana kishin-
kishin tabbas ya ji an ce wai wannan malami
dan tsubbu ne shi ya sa ya zabi su zo wurin
sa, domin kuwa ya san cewar zai dan fi saukin
kai in dai suka nuna mishi makudan da ke
hannusu
.
Nazifi ya dan yi masa murmushi sannan ya ce da shi.
"Mhm. da ma malam wata `yar matsala ce
ke tafe da mu zuwa wurinka."
.
Malamin ya sake gyara zaman a kan tafkeken
buzu, sannan ya gyara zaman nadinsa mai
kama da mushen jimina, domin kuwa tun
zuwan wadannan yara biyu saurayi da
budurwa, ya ji kansa yana dan sarawa kamar
zai yi ciwo, domin kuwa duk ya rasa kansa
kamar ba mutane ba.
.
"Ni fa a gaskiya ban gane abin da kuke nufi
ba, ban san me yake tafe da ku ba. Ina jin da
za ku fito fili ku fada mini matsalarku da zan
fi son haka, amma kuna ta wasa da hankalina
sai ka ce wani karamin yaro."
.
Nazifi ya sunkuyar da kan shi cikin ladabi ya
ce da malamin.
"Ka yi hakuri malam lamarin ne yana da dan
wahala shi ya sa ka ji muna fargabar fada
maka."
.
Malamin ya shafi dogon gemunsa ya ce da su
"Duk da haka dai tun da kun rigaya kun zo ai
sai ku fada mini in ji domin kuwa ina da aiki
da yawa a gabana, kun ga yanzu dare ne
lokaci ne da muke aiki da rauhanai, ba
lokacin tsayawa wasa ba ne." Wannan karon
yana magana yayin da yake dan zazzare ido don
barazana.
.
Saurayin da budurwar suka sake kallon juna.
`Yar budurwar tana sanye da burmemen
hijabi, tana sauraron diramar da ake yi
tsakanin saurayinta da kuma malamin mai
kama da rauhani, domin kuwa ya mafi kama
da rauhanin fiye da mutane. Nazifi ya ce da
shi kai tsaye..
.
"Alagafarta malam ka gafarce mu, ba wani
abu ya sa muka zo wurinka ba ni da wannan
masoyiya tawa sai kawai don wata `yar
bukata wacce muke son ka share mana hawaye a
kan ta."
.
Nazifi ya dan saurara sannan ya cigaba.
"Alagafarta malam mun zo gurinka ne don
ka daura mana aure a boye, ma'ana ba ma
son kowa ya san da faruwar wannan
al'amari."
,
Dogon malamin ya zaro idanunsa cikin rudani
kana ya yi saurin dafe kan shi. A wannan karo
ji yake kamar zai rabe gida biyu domin kuwa
duk shekarun da ya dauka yana wannan
sana'a ta tsubbu ya hadu da attajirai da
talakawa, `yan kasuwa, da kuma `yan siyasa,
kai har da `yan fashi da makamai, amma ko
sau daya bai taba jin wani ya zo masa da
tatsuniya irin wannan ba, sai a wannan karon.
.
Ya gyara zamansa sannan ya muskuta baya
kamar yana tsammanin za su haushi da duka
a cikin dan tsurkun dakin nasa na ganawa da
baki.
.
"Ku gafarce ni yara a gaskiya ba ni jin zan iya
wannan aikin, ina jin sai dai ku lalubi wani
malamin amma dai ni ba na irin wannnan
aika-aikar."
.
Nazifi ya dubeshi cikin damuwa.
"Ka taimake mu malam, wannan ba wai abin
assha ba ne domin kuwa kai ma za ka samu
lada, tun da dai raya sunnar fiyayyen halitta
ce."
.
Malamin ya ce "Ba wai taimakon naku ne
bana son yi ba, to amma shi aure ba haka
nan ake yin sa kawai ba wani bincike ba,
domin kuwa ni yanzu ba zan iya sani ba ko da
aure a tsakaninku ko babu ba, tunda dai ban
taba ganinku ba. Sannan kuma ban san da
wacce manufa za ku yi auren ba."
.
Nazifi ya sake marairaicewa.
"Wallahi malam ba wata manufa, muna so ne
kawai mu yi aure, wadansu matsaloli ne suka
sa za mu yi a boye."
.
"To me ya sa ba za ku sa iyayenku a gaba su
wakilci maganar ba? Ko ba ku da iyaye ne a
nan garin?"
.
Masoyan biyu suka sake duban juna, kana
saurayin ya ce, "Muna da iyaye Malam, to
amma dai wannan wani sirri ne a tsakaninmu
da kai. Mun wakilta ka ka zama iyayenmu,
sannan kuma ka zama waliyi a tsakaninmu
duka, kuma kai ne shaida."
.
Malam ya tattara carbinsa wuri guda kamar
`ya`yan goriba sannan ya dubi masoyan biyu
ya ce da su.
"Aure irin wannan ba shi da kyau, ko kuma in
ce yana da matsala domin kuwa babu
mamaki ma kun sha nono daya."
.
Nazifi ya ce a marairace.
"Wallahi malam ba mu sha nono daya ba,
masoyiyata ce ba kanwata ba ce."
Malam ya sake hade fuska duk ya yi zufa
sharkaf ya ce da su "Kai ni fa ban taba yin
wannan aika-aikar ba, a gaskiya sai dai ku
gafarce ni ba zan aikata wannan tabargazar
ba, domin kuwa shi aure ba haka kawai
ake..."
.
Maganar ta makale a makogwaronsa, bai
samu damar karashewa ba sakamakon
abinda ya hango a hannun saurayin. Sababbin
`yan dari biyar ne dami guda suna daukar
idanu. Saurayin ya ajiye kudin a gaban
malamin sannan ya ce da shi
.
"Amincewarka muke bukata ba wa'azinka ba
Malam, domin kuwa ba haka nan za mu barka
ba. Idan ka amince ka dauki wannan duk naka
ne ladan aiki. Idan kuma ba ka amince ba shi
kenan sai mu dauke kudinmu muje gaba wani
malamin ya daura mana auren. To amma dai
me ka gani?"
.
Malamin ya sake gyara zama kamar wanda
yake zaune a kan kunama, ya sake duban
kudin a halin yanzu bayan ciwon kan da yake
ji har wani abu kuma yake ji yana tsikarar
hakarkarinsa da cikin zuciyarsa. Ya yi ajiyar
zuciya sannan ya ce da saurayin.
.
"Kada ku damu yara zan dan yi shawara. Mu
gani, ni dai a gaskiya ban taba irin wannan ba,
to amma dai tunda kun ce a taimaka muku ai
dole ne a taimaka muku din. Ina ganin ba
wata matsala ta yanka maka sadaki ka biya,
yanzu nan ma sai a daura muku auren, ku yi
tafiyarku."
.
Yana gama fada ya warce damin kudin, ya
bankada karkashin tafkeken buzunsa ya watsa
su ciki. Duk fa wa'azin da ya yi musu a baya
duk ya mance.
.
_____________________________________
Shuraih 99%
.
"Ku yi hakuri Gali, wallahi ni kaina ban ji
dadin faruwar wannan mummunan al'amari
ba. To ka san zamani ya canza. Wallahi ni
kaina ban san lokacin da yarinyar nan ta
lalace haka ba, ban taba tsammanin zata iya
guduwa ta bar gida a kan wannan maganar
ba."
.
Gali da ke sauraron Alhaji Dage ya hade
fuskar shi.
''Agaskiya Alhaji ba zan yarda da duk abinda
za ka fada mini a kan wannan al`amari ba.
Ta yaya ma za a ce in gama raba katin
gayyata, anjima nan jama`a fa za su fara
zuwa kofar gidan nan don daurin aurena da
yarinyar nan, amma ka ce da ni wai tun
daren jiya ba a san ma inda take ba
.
Dole ne a nemo mini matata, in dai ana son zaman lafiya.''
Alhaji Dage ya gyara zaman faskeken
tabaronsa, wanda ya fi fuskarsa sai ka ce
wazirin akun magana jari.
"Bai kamata a ce ka yi saurin fushi haka ba
Gali, domin kuwa wannan yarinyar dai ba za
ta bata ba a garin nan. Koda bayan an daura
auren dole ne a nemo ta, dole ne a gano
inda ta shiga."
.
"Haba Alhaji, to amma saboda Allah yaya za a
ce an daura mana aure ba amarya? Kai ma ka
san cewa wannan ba karamin tonon asiri ba
ne a gare ni. Ya kamata dai a san abinda ake
ciki kawai."
.
Siririn mutumin ya share zufa de ke kan
dokin wuyansa. "Wallah ni kaina ban san me
yake damun wannan yarinyar ba. To ka san
bai yiwuwa ka haifi yaro sannan kuma ka haifi
halinsa, wannan hali nata ni ban san inda ta
samo shi ba, domin kuwa daga ni har uwarta
duk mutanen kirki ne wallahi."
.
Gali ya harari mutumin a fakaice, a zuciyarsa
ya ce "Kana matsayin mutumin kirki amma
ka damfare ni kusan miliyan guda, don kawai
za ka ba ni 'yarka?" To amma dai a zahiri
cewa ya yi da shi, "Ni dai ka ji bayanina
Alhaji, in dai har ba a gano mini amaryata ba,
to ina jin mu duka sai kawai mu yi hakuri da
maganar. Domin kuwa jiya aka daura auren
abokina, muna so ne mu hada bukukuwanmu
rana daya da aurenmu, amma kuma ni a ce
wai ba a ga tawa amaryar ba. Wannan ai
tonon silili ne ake nema kawai a yi mini."
.
dan motsattsen mutumin ya yi ajiyar zuciya,
jikinshi ya soma kyarma domin kuwa a yadda
ya lura da kwayoyin idanun saurayin ya san
cewar abubuwan da yake fada har cikin
zuciyarsa abinda yake nufi kenan.
.
"To ni yanzu don Allah me kake son in yi
maka? Ai'sha dai ni na haife ta, kuma ta
kwashe kayanta ta gudu ta bar gidan nan, me
kake so yanzun in yi maka, tunda ka ce ba ka
yarda ba?"
.
Saurayin ya sake hade fuska sannan ya ce da
shi.
"Ai ba wani abu ba ne mai wahala, ina ganin
Alhaji, in dai ban takura maka ba, ai ina gani
ban yi laifi ba idan na ce ka shiga cikin gida ka
tattaro min kudadena da na kashe tun farkon
soyayyata da 'yarka A'isha. Domin kuwa idan
har za ka iya tunawa ka amshi manyan
kudade a wajena, kuma kai ma ka san dai ai
ba kyauta na ba ka su ba, domin kuwa inda a
ce ni talaka ne ba ni da kumbar susa, na
tabbata daidai da rana daya ba za ka taba
barina in zo kofar gidanka har in furta ina
neman 'yarka ba
.
Don haka ni ma na rika ba ka kudaden da kake bukata, na san dai ba ka mance ba da su ba."
Saurayin ya dan yi murmushin takaici sannan
ya ci gaba da shaidawa ramammen tsohon
.
"Tun fara neman auren A'isha na fara lissafin
abubuwan da nake kashewa a dalilinta, kai
hatta man da nake zubawa a motata in zo
wurinta, da kuma kudin da nake baiwa yara
su kira min ita, duk ina rubutawa. A halin
yanzu lissafi ya yi kauri, domin kuwa kullum
sai na ciro doguwar takardata ta lissafi, na yi
bitar kudaden da ke cikin akawun dina da
wurinka
.
Don haka na ba ka awowi goma ka
tattaro min kudadena. In ba haka ba, ka ji na
rantse maka da Allah, sai na dankara ma ka harsashin bindiga,
tsohon banza makwadaici kawai macuci!"
.
Gali ya bude kofar motar a fusace ya shiga ya
tashe ta. Ya juyo ya dubi motsattsen
mutumin, wanda a halin yanzu ko'ina a
jikinsa kyarma yake yi hatta fuskarsa da ke dakon faskeken tabaron
ita ma kyarma take yi, duk da uban kayan da
aka jibga mata,
.
"Kada ka damu Baba, na ga ka rude, ai kudin
ba wasu masu yawa ba ne, miliyan daya da
dubu dari bakwai da hamsin kawai, sai naira
dari uku da talatin da biyar." Ya fizgi motar ya
fice a guje daga kofar gidan
.
Motsattsen mutumin ya bi kurar motar da kallo. A daidai
lokacin ne faskeken tabaron ya kubuce daga
'yar mitsitsiyar fuskar tasa, ya fadi kasa. Tuni
har ya fara tsammanin hawan jini.
.
___________
Shuraih 99%
Iyaye ayi hattara da amsar kudi ko wani abu a hannun siriki kafin Aure
.
Duniya ta lalace da cin hanci wai har MALAMAN ADDINI suna RASHAWA
._____________
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 11
.
____________
Tsawon mintuna biyar mafadaciyar matar na
ta faman yiwa mijin nata banbami. Yana
tsaye kawai yana duban ta, sai zufa ke ta
faman kwararo masa, tana wanke masa
fuska, kamar ana yi masa sakiya
.
Ya rasa da me zai ji tsakanin masifar da kuma gargadin da surukinsa ya zo ya yi masa. Ya san
cewar
wannan saurayin dan bindiga-dadi ba hankali
ya cika ba, kamar yadda da ma ya dade yana
jin ana cewa ba duk soja ne ke da cikakken
hankali ba
.
Hakika yana iya aikata duk
abubuwan da ya fada, ga shi kuma yanzu
Juma ta tuso shi a gaba da tata masifar.
.
Duk ya rasa abinda ke masa dadi a duniya.
"Kawai aikin banza Malam, ka jawo min 'yata
kwalli kwal da nake alfahari da ita a duniya ta
tattara kayanta ta gudu, da ma haka kake so
sai ka zuba ruwa a kasa ka sha, burinka ya
cika."
.
Alhaji Dage ya yi shiru, bai ce da ita kala ba,
domin kuwa ya san cewa yanzu ba lokacin
tankawarsa ba ce, don kuwa har ga Allah
matar tasa ta tunzura. Ya san cewa idan ya
biye mata, tana iya kama shi da kokawa,
kuma ba ya kokwanto ya san cewa shi za ta
kayar
.
Shi ya sa ya rufawa kansa asiri ya rabu
da ita, in ta yi ta gaji dai ai dole ne ta bari.
Juma ta sake cewa da motsattsen mutumin
cikin kwarmato kamar za ta hadiye shi.
.
"Wai me kake nufi ne Alhaji, ba ka ce komai
ba. Ko kuwa kana nufin shi kenan, kai ka
cinyewa mutane kudi, ni kuma ka bar ni da
asarar 'yata. To ai sai ka sake tunani, don
kuwa ba kyale ka zan yi ba, duk inda 'yata ta
shiga sai ka je ka kwakulo min ita, in dai kana
son zaman lafiya a duniyar nan, to wallahi ka
nemo min A'isha domin kuwa duk kai ka
jawo mana wannan masifar."
.
Ramammen mutumin ya yi ajiyar zuciya, a
karo na farko ya ga cewar ya kamata dai ya
dan ce wani abu. Don kada ta ga ya ki tabuka
komai, ta sake haye masa yadda ta ga dama.
.
"Ba na son rashin albarka, Juma." Ya ce da
ita, "Ni kike yi wa wannan tsagerancin ko
kuwa kin fi ni son 'yar tawa ce, da kike fada
min wadannan maganganun? Ko kuwa ni ne
zance ta gudu ta bar gidan? Wannan
tsinanniyar yarinya ina amafaninta, duk ba
halinki ta kwaso ba? Ke din a da can me ye ba
ki yi ba? Ba don yanzu an mance, ba a tone-
tone, shi ne har kin samu bakin magana.
Kada in sake jin muryarki a kan maganar nan
Juma."
.
Ya zazzaro mata idanunsa da ke cikin
fasasshen tabarau, a tsammaninsa watakila ta
dan ji tsoro ta lafa. To amma kuma cikin
rashin sa'a sai ya ga ta yi shewa, sannan ta yi
tafi ji kake fas, ta ce da shi.
.
"Lallai yau da tone-tone a gidan nan. Au kai
nan har gori zaka yi min? Ka mance da
abubuwan tsiyar da ka kuntuka a baya? Haka
fa kawai nake zaman hakuri da kai.
.
Shi ne yanzu har ka samu bakin da za ka yi tonon
silili. To ai sai mu fara a ji ni da kai wa ya fi
wani mugun tabo, ba tsoron ka nake ji ba
Alhaji, mu yiyar tonon asiri."
.
Alhaji Dage yayi saurin tsayar da ita, da ya ga
ta sake hayewa.
"Duk wannan ba ta taso ba, ni dai gaya miki
na yi dama don maganar da ya dace ki rika
fada, ai ba cewa na yi za mu yi wani tone-
tone ba, don kuwa mu dai ba yara ba ne, ya
isa a ce mun mallaki hankalinmu a halin
yanzu."
.
Juma ta yi guda sannan ta ce da shi.
"Ashe ka ji tsoro mai gida. Ai na so mu
jarraba tonon silili da kai wallahi da ka ga dan
biki da cika yau a gidan nan. In ana fadin abin
kunya kai har ma ka sa baki a gidan nan. In
ba abin kunya ba mene ne amfanin karbarwa
mutane dukiya don za su auri yarka? Haka
fa ka yi ta yi wa ragowar yayan danginka da
ka rika a gidan nan. Ka aurar da yan mata
sama da biyar duk a bisa zalunci. Yanzu suna
can dakunan mazajensu suna shan wahala ana
yi musu gori da wulakanci, tunda dai ka
saida musu da mutunci. To ni ba mai yi wa
yata A'isha wannan mulkin mallakar, mu
zuba ni da kai a gidan nan tun da kai ba ka
gudun abin kunya."
.
Mutumin ya yi ajiyar zuciya, ba shi da ta cewa
domin kuwa duk abin da matar ta fada
gaskiya ne duk ya aikata. Yana jin ta ta ci gaba
da cewa da shi.
.
"Duk wanda ya sa ranshi a kwadayin abin
duniya dole ne ya ga wulakanci mai gida,
amma ina amfanin a ce a matsayinka na
babban