Showing 9001 words to 12000 words out of 16852 words

Chapter 4 - AJALI littafin Shafiu Dauda Giwa-1.pdf

fahimta, "Kamar yaya
ban gane ba?"
Ta sake yin murmushin. "Abin da nake nufi
shine wahalar mu ta zo karshe in dai ka
shirya, kuma da gaske kana kauna ta har cikin
zuciyarka kamar yadda ni ma nake kaunarka"
Ta dan saurara sannan ta ce da shi a sanyaye.
''Nazifi ka shirya gobe mu je a daura mana
aure.''
.
Saurayin ya ji gabanshi ya fadi ras da kalaman
suka dira a cikin dodon kunnen shi a bazata,
kadan ya rage ya fado kasa don tsananin
razana.
.
''A`isha aure fa kika ce?''
Ta dube shi har cikin idanunsa ta ce da shi.
''Aure mana Nazifi ko ba ka shirya ba ne,
dama yaudarata kawai kake son yi ban sani

ba."
.
Saurayin ya dubi kwayoyin idanin `yar
budurwar da ke zaune akan kujera ta sa shi a
gaba, ya tabbatar lafiyar ta kalau ba tabin
hankali ta samu ba, ya ce da ita cikin mamaki.
.
"A'isha kin taba ganin inda saurayi da
budurwa kawai suka ware kansu suka aurar
da kansu ba wasu shaidu ko waliyyai, sannan
kuma ya za a yi a ce gobe-gobe ba wani
shirye-shiryen komai."
.
`Yar budurwar ta ce da shi "Ni ba cewa na yi
ka sayo min akwatuna ba, sadaki kawai nake
so a wurinka, shi ma don ya zama dole ne, da
ba zan bukaci komai a wurin ka ba kuma shi
din ma sai abinda ka kawo ka ba ni. Malamin
da zai daura mana aure da shaidu, kai ko ma
mene ne ake bukata ba za mu sha wahalar
samu ba.
.
Wannan alhakin ka ne ka nemo mana malami wanda zai daura mana aure
cikin sirri daga mu sai mu sai shi. Daga nan
kuma sai ka samar mana wurin zama na sirri
.
Duk wadannan abubuwan ne da ya kamata a
ce ka shirya su a gobe domin kuwa idan abin
ya wuce gobe, to mun rasa juna kenan har a
bada."
.
Shiru bai ce da ita komai ba domin kuwa
maganganun da take fada duk sun gama sa
shi tsurewa. Zuwa can sai ya ce da ita cikin in-
ina "To ai ni a gaskiya A'isha wallahi abin ne
ya zo mini duk a kurarren lokaci, kuma bayan
haka kin dai gani da idanunki wallahi ba wani
wadata ne da ni ba kuma ba wata
kwakkwarar sana'a nake yi ba. sannan...."
,
Ta katse shi cikin damuwa.
.
"Duk da haka dai na tabbatar a matsayinka na

namiji indai har ka yi niyya duk wadannan
abubuwan ba za su gagare ka ba, in dai har
kana sona da gaske to bai ma kamata ka tsaya
ka kawo mini wadanan matsalolin ba,
kasancewar dai ko rance ka nema a wurin
abokan sana'arka ba za ka rasa samu ba. Ba
wasu kudin ba ne masu yawa za ka tanada ba
Nazifi, sadaki kawai fa na ce ina bukata, daga
nan kuma sai 'yan kudin da za a baiwa
limamin da zai daura auren, don mu rufe
bakinsa kada ya tona mana asiri. Haba Nazifi
ka yi tunani fa ka gani, akwai wanda ya kashe
miliyoyin kudi a kaina, amma na ce ba na
kaunar shi sai kai Nazifi, amma kuma kana
nema ka ba ni kunya, ka kware mini baya."
.
Ya yi saurin cewa da ita "Ba haka ba ne
A'isha, ke kina ganin kamar ba na son
al'amarin ne, wallahi ina so. To amma
matsalolin da ke tattare da al'amarin nake
hangowa. Idan fa muka yi auren nan a boye,
muka nemi wurin zama dole ne a yi bincike
don a gano inda kike a garin nan, kuma abin
duniya ba ya boyuwa, dole ne asirin mu ya
tonu wata rana, don aure ba abin wasa ba
ne."
.
"To sai me don an gane daga baya in dai mun
yi auren? Ai shi kenan, ka san dai duk duniyar
nan idan an taru ba mai raba mu, tunda
muna son juna. Kuma wai kai tsoron me ma
kake ji? Sai ka ce ba namiji ba. Rigima wa ta
kashe a duniya? Mu yi auren nan shi ne mai
wahala, komai zai biyo baya ya ma biyo. Ni fa
mace ce Nazifi amma har in ce na ji na gani a
kan soyayyar mu, amma kai kana namiji ka
tsaya kana fargaba. Ni wallahi ka fara ba ni
kunya Nazifi."
.
Ta kura mishi idanu a yayin da ya yi shiru
yana mis-mis da baki, yana kokarin fitar da
tunani daya tsakanin amincewa da kuma
sabanin haka, daga nan sai ta cigaba da ta ga

bai ce komai ba.
.
"Idan kuma kana ganin ba zai yiwu ba, shi
kenan ba matsala sai in tashi in yi tafiyata, ka
nuna mini kenan da ma ba kauna ta kake yi
ba, sai in je in rungumi kaddara in auri
wancan saurayin da ba na kauna a zuciyata,
wanda shi kuma yake sona kamar ya hadiye
ni. Ba komai Nazifi, dama an ce son maso
wani koshin wahala."Ta mike daga kan musakar kujerar da niyyar
ficewa. Nazifi ya yi farat ya ce da ita, bakin sa
na rawa.
.
"Ki gafarce ni A'isha, abin bai kai mu ga haka
ba. In dai don wannan maganar ce kina
bukatar komawa ki zauna, na amince zan yi
duk abin da kika ce da ni. Ni dai a halin yanzu
ko sisi ba ni da shi a aljihuna, to amma kuma
tunda kin ce da ni rigima ba ta kashe uban
kowa, to ni ma zan jarraba yin ta, don na san
ba za ta kashe ni ba. Domin kuwa ba karamar
rigima ba ce mutum ya tunkari aure awoyi
ashirin da hudu masu zuwa sannan ya nemi
gidan haya, da kuma kudaden limamin daurin
aure duk kwana daya kacal, amma kuma bai
tanadi ko ahu a aljihunsa ba, ke ma kin san
wannan katuwar rigima ce, A'isha."
.
___________
Tab malam Nazifi kwarankwasa maganarka dutse ce,
Don da rigima na kisa, da wannan typing din bai zo gareku ba sakamakon rigimar dana jajibo
ma kaina shekaran jiya, sai de dakyar na sha yayin da fuskata ta suntuma suntum, idanuwa na
sukai luhu luhu, sakamakon dukan da na ci wajen .........
Kaga su o'o da o'o an kasa kunne don jin tsurku to na fasa bada labarin, its shuraih 99%
.
Part 9 is loading
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 9
.

Washegarin ranar tun da sassafe misalin
karfe bakwai, Nazifi ya fara zirga-zirga a cikin
garin yana fafutukar nemo rancen isasssun
kudin da zai rike
,
kafin nan da wadansu awoyi
in dare ya yi, domin kuwa a yadda suka rabu
da 'yar budurwar ta ce da daddare za ta zo ta
same shi su wuce wurin daurin aure.
.
To amma kuma tun a jiya din bayan sun rabu
yake ta faman cuku-cukun inda zai sami kudin
da yake bukata, amma kuma shi dai a iyaka
kokarin sa bai san inda zai samo wadannan
kudi ba.
.
Sannan kuma bugu da kari ba shi da wata
tsohuwar ajiya ko kuma wadansu kadarori
ballantana ya daga su ya makar don ya sami
kudaden da yake bukata. Ya san cewa in dai
ba tsohon kekensa ba to da wahala ya sami
wani abu da zai sayar, wanda kudinsa za su
kai dubu daya, ko suturunsa ya daga ya sayar
ya san cewar ba za su samar masa kudin ba.
.
Don haka ya kasance cikin rashin kwanciyar
hankali ko wani barcin kirki bai yi ba.
Duk mutanen da Nazifi yake tsammanin zai
sami kudi a wurinsu, da kuma abokansa duk
ya bi su daya bayan daya amma kuma Allah
bai sa ya dace ba
.
Da rana ta take misalin karfe sha biyu sai Nazifi ya zauna a makarin
wata kwalbti dake bakin titi, yana tunanin
inda zai sake dosa kuma gashi lokaci
kara kurewa yake yi.
.
Nazifi yayi ajiyar zuciya, sannan ya mayar da hankalin shi kan motocin
da ke wucewa ta gabashi ya yiwa kansa
murmushi, da ya yi tunanin cewar wai saura
bai fi awoyi takwas masu zuwa ba ya zama
ango, amma kuma babu ko ahu a aljihunsa,
.

gashi kuma wata azababbiyar yunwa ma yake
ji, ko abin da zai sa a cikin shi bai mallaka ba
amma kuma wai a yau ne zai tare da sabuwar
amarya, wacce wani ya kashewa kusan
miliyan guda don a mallake ta, lallai wannan
shi ne daukar dala ba gammo.
.
To wai shin me zai sa ma in dami kaina ne?
Nazifi ya tambayi kanshi lallai fa bai kamata
ba ma ya tsaya yana damun kanshi, domin
kuwa ita ta ce ta ji ta gani, ko ba shi da ko
sisi, ya san cewar za ta san inda za ta samo
masa kudaden tun da dai ta riga ta mutu akan
kaunarsa.
.
Ya sake yiwa kansa murmushi
sannan ya ce a bayyane.
"Kada ka damu Nazifi, ko baka da ko sisi yau
sai ka zama ango a duniyar nan, kuma sai ka
tare a dakin kyakkyawar amarya, wacce
farashinta ya zo daidai da naira miliyan..."
.
Bai gama tunanin ba ya ji dirar zukekiyar
motar a gabanshi, ya dawo hayyacinsa cikin
kaduwa a lokacin har gilashin motar ya sauka
kasa
,
suka dubi juna shi da dogon saurayin
dake cikin motar, shi kadai sanye da bakar
kwat, yana murmushi. Da farko Nazifi bai
gane shi ba, domin kuwa rabon da a ce sun
hadu da wannan saurayi tun a makarantar
sakandire, inda suka gama tare, to amma a
halin yanzu ya kara girma da kiba da ba don
tun a wancan lokaci sun shaku ba, to har ga
Allah da Nazifi bai gane babban abokinsa Gali
ba.
.
"Nazifi me kake yi a nan zaune, lafiya"
Nazifi ya mike ya dafa tagar motar ya ce
dashi cikin mamaki "Gali ashe dama kana
duniyar nan"
Saurayin ya yi dariya.

.
"Ina nan a raye Nazifi, ina nan a garin
wallahi"
Samarin biyu suka gaisa cikin farin ciki nan
suka tuna da tsohuwar abotarsu tun suna
makaranta.
.
"Wallahi Gali na cire tsammanin za mu sake
haduwa, domin kuwa tun shekara da shekaru
na neme ka har na gaji." Amma kuwa har
yanzu tunanin awoyin da suka rage ta zo ta
same shi ne zuciyarsa.
Gali ya ce da Nazifi ya bude bangaren mai
zaman banza ya zauna suka sake gaisawa da
Gali babban aminisa. Gali ya ce da shi.
.
"Na san cewar dole ne ka yi mamakin
bacewar da na yi shekara da shekaru Nazifi,
ba na kasar ne domin kuwa tun bayan gama
makaranta ni ban ci gaba da karatu ba, sai na
shiga aikin soja, aka turani kudancin kasar
nan, daga baya kuma da za a je sasanta
rigimar kasar Saliyo aka diba har da ni.
.
Tun wancan tsawon lokacin muna can sai bara aka dawo da mu, shi ne na dawo gida a halin
yanzu don in yi aure, domin kuwa wallahi
abokina mun sami alheri sosai a dalilin
wannan yaki da muka je."
.
Nazifi ya ce da shi cikin yake-yake, dariya-
dariya.
"Ai na ga alama wallahi mutumina ka sami
hutu, mu muna nan har yanzu a rabe muna
ta `yan buge-buge, amma ba wani canzawa
kullum muna guri guda."
.
"Tun bayan gama makarantarmu me ka yi
Nazifi?"
Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce da shi.
.
"Ba na aikin komai Gali, kawai dai ina dan
taba sana'ar kafinta wacce nake dan samun na
batarwa a cikinta"

.
Gali ya dan nuna damuwarsa a fuska sannan
ya ce da shi.
.
"Rayuwa kenan Nazifi sai hakuri, ka san
cewar kowa rabon shi yake samu a duniya
mutum bai wuce rabon shi Nazifi."
.
Nazifi ya yi murmushi a zuciyarsa yace "Ni
kuwa na san haka tunda gashi ba ni da ko ahu
amma zan auri kyakkyawa wacce wani
miloniyan ke burin ya aura a duniya."
.
"Yanzu zaman me kake yi a nan kai kadai
cikin rana, Nazifi?"
Ya sake yin ajiyar zuciya,
"Wallahi wannan zaman da ka ga na yi Gali
ina cikin wata katuwar matsala ce wacce ta fi
karfina."
.
Gali ya yi masa murmushi ya ce da shi.
"Ni kuwa ban yi tsammani cewar a wannan
halin da nake ciki har akwai wanda zai ce ya fi
ni shiga matsala ba, matsalarka ba ta kai ko
rabin wacce nake ciki ba"
.
Nazifi ya ce dashi.
"Haka dai ka ce Gali amma da a ce za ka ji
matsalata, kai da kanka za ka san cewar ta fi taka matsalar" fada min matsalar taka na ji ni
kuma zan fada maka tawa matsalar." Nazifi ya kurawa gilashin
motar idanu ko kiftawa ba ya yi sannan ya ce
da abokin nasa
.
"A halin yanzun da ka ganni a nan Gali, yau
ne za a daura aure na kuma a yau ne zan
nemi gidan da za mu zauna ni da amarya,
amma kuma ko sisin kwabo ba ni da shi a
aljihuna
.
Ka san cewar ina cikin matsala maigirma, Gali"
Gali ya tuntsire da dariya.
.
"To kai Nazifi ya aka yi ka daukowa kanka

wannan rigimar, ka san cewa ba ka da ko sisi?
sai ka ce za ka auro `yar tsana ba mutum
ba?"
.
Nazifi ya dube shi sosai ya ce.
"Wallahi rigima ce kawai Gali, bari ka ji yadda
abin ya faru. Tun farko yarinyar ce ta like
mini na rasa yadda zan yi da ita shi ne ta ba
ni zabi ko dai in nemo kudi a daura auren a
yau din nan ko kuma mu yi hannun riga
ma'ana mu rabu , to ni kuma ina bala'in son
yarinyar nan Gali, kullum tana raina, shi ne
na yi mata karya zan nemi kudin amma har
yanzu da ka same ni a nan ko kwabo bai zo
hannuna ba, kuma anjima za a daura
aurenda daddare"
.
Gali ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce.
"Eh, to kai ma kana cikin matsala Nazifi, to
amma kuma dai har yanzu ina jin matsalata
ta fi taka domin kuwa ni ma gobe ne za a
daura aurena da wata yarinya, na kashe kudi
sun kusa miliyan daya a kan wannan yarinya,
.
to amma kuma ba ta kauna ta ko nan da can.
Ko jiya da na je wurinta da zage-zage muka
rabu amma kuma gobe ne za a daura mana
aure domin kuwa tuni har na gama rarraba
katin gayyata, Nazifi."
.
Nazifi ya ce da shi "Ina ban da abinka Gali me
ya ja maka yin wannan tabargaza? Yaya za a yi
bayan kasancewar yarinyar ba ta kaunar ka
amma kuma ka kashe mata wadannan uban
kudade sai ka ce za ka auri `yar zinariya, ba
wacce take da jini irinka ba?"
.
"Wallahi Nazifi ni ma dai rigima ce kawai ta
sa ni yin wannan aika-aikar domin kuwa irin
ciwon son yarinyar nan da nake shi ya sa na
turawa iyayenta wadannan makudan kudade,
domin kuwa na san cewar duk tsiyarsu dai ko
ba sa so dole ne su ba ni yarinyar, tunda dai

ba za su iya biyana kudin da na kashe ba."
.
Abokan biyu suka tuntsire da dariya a lokaci
guda hade da tafa hannuwa. Nazifi ya ce da
abokin nasa.
.
"Kai rigima dai ba ta karewa a wannan
duniyar Gali, in kana duniya ka ga tsiya iri-iri,
wato in da za ka san cewar ni dan tsiya ne,
bani da kirki abokina, wani miloniya ne fa ke
son yarinyar nan tawa amma kada ka ga
yadda take kwabsa shi
.
An ce wai da motoci yake zuwa wurin ta zuka-zuka, amma kuma na kwace mishi ita."
Suka sake fashewa da dariya Gali ya ce
.
"Ai ni har yanzu ban ma gano nawa abokin
karawar ba, wallahi na rasa dan iska da ke
hurewa tawa budurwar kunne a garin nan. To
amma ina nan ina zuba idanu sai na gano dan
banza."
.
Ya rage fara'a sannan ya ce da abokin nasa.
"Ka san abin da zan yi masa kuwa Nazifi?"
Nazifi ya girgiza kai cikin rashin fahimta. Gali
ya dan yi busasshen murmushin mugunta
sannan ya ce da shi.
.
"Harbe shi zan yi da `yar kaunar bindigata."
Suka sake yin dariya a lokaci guda, amma
shi Nazifi yake-yake yi ba dariya ba, domin
kuwa bai taba tsammanin irin wannan tunani
na kashe mutum a zuciyar abokin nasa ba.
.
To amma kuma abin da bai sani ba, shi ne
abokin nasa yafi jin tausayin kashe kiyashi
fiye da kashe mutum. Gali ya tattara
hankalinshi wuri guda sannan ya ce da Nazifi.
.
"Kada ka damu Nazifi zan magance maka
matsalarka gaba dayanta, daga nan kuma sai
mu dawo ni ma ka taya ni don mu magance
tawa matsalar.

.
Yanzu dai da farko zan ba ka gida da zaka zauna kai da amaryarka domin
kuwa ina da sababbin gidaje har guda uku a
garin nan duk gaba daya na ginasu, sannan
kuma zan ba ka isassun kudin da za ka yi
hidimar komai da komai na wannan aure."
.
Nazifi ya ji numfashinsa ya dauke, don
tsananin murna, "Na gode sosai Gali, wallahi
ka yi bala'in `yanto ni mutumina"
.
Gali ya jawo wata bakar jaka da ke bayan
motar, ya dorata a kan cinyar Nazifi, sannan
ya danna wani kwado murfin jakar ya bude.
Nazifi ya some a zaune, jakar dankare take
da 'yan dari biyar-biyar sabbi fil da su, suna
ta daukar idanu. Gali ya dafa kafadarsa cikin
tsokana sannan yace da shi.
.
"Kai banza na ga duk ka bi ka wani rude sai ka
ce ka ga wasu kudin arziki Ka da ka damu Nazifi ba su da yawa rabin
miliyan ne, da ma yanzu na je banki na amso
su, Allah ya sa rabonka ne, ka je ka yi
hidimar aurenka da su."
.
Nazifi ya dubi abokin nasa a rude ya ce da shi
cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login