Showing 15001 words to 16852 words out of 16852 words
Chapter 6 - AJALI littafin Shafiu Dauda Giwa-1.pdf
mutum wanda zai yiwa wani nasiha a
ce kana rigima kai da surukanka kana amsar
musu dukiya? Yanzu ga abin da ka jawo
mana, wannan mutunci ne?"
.
Ramammen mutumin ya girgiza kan shi
kamar uwa na wa danta fada "To ai laifin
yarinyar ne ni wannan tsinaniyar yarinyar
wallahi ta cuce ni.."
.
"Ka da ka tsinewa yata a banza domin kuwa
ba ta da laifi, kai ka jawo mana wannan
rigimar muna zaman zamanmu lafiya. Ka san
cewar A'isha ba ta kaunar yaron nan ka nace
a kan maganar nan don ka gan shi da kumbar
susa, ga shi yanzu kana jin tsoron fita waje ka
da surukinka ya harbe ka
.
Ina na taba jin irin
wannan abin tsiya ma a duniya, ni Juma."
Alhaji Dage cikin nadama ya ce.
.
"Kin ga laifina ne a banza Juma, amma a
matsayina na magidanci saboda Allah ba ni
da yanci zabarwa yata mijin da na ga ya fi
dacewa da ita? Wani zamani dai Allah ya kawo
mu inda yara ke kangarewa su fi karfin
iyayensu.
.
Mu a zamaninmu wane yaro ya isa
ya ce shi zai yiwa kansa zabi sai wanda ya ke
so, mu kuma mutane sai mu bar abu ya
lalace da kanmu, mu ce ai zamani ne, da
gangan ake kyale yara suna wannan iya
shegen da fitsarar ana kallon su."
.
"Ba haka ba ne maigida" Juma ta ce da shi
"Ko ka ki ko ka so al'amura suna canzawa,
kuma zamani ya kan zo da abubuwa iri-iri
dole kuma mutum ya bi abinda zamani ya zo
da shi matsawar bai sabawa shari'a ba. Ai ba
haramun ba ne don yaro ya zabi wanda ya ce
yana so ya aura. Kuma da ka ce a naka
zamanin ba haka ake yi ba, kai zamaninka ka
sani, ba ka damu da zamanin yayanka ba. A
zamanin naka ai bante ake daurawa ba sutura
ba, me ya sa ba za ka cigaba da daura bante a
wannan zamanin ba, tun da ka ce ba ka
amince da canjin zamani ba, sai ka koma
tafiya tsirara da bante, don kuwa shi ake
daurawa zamaninka na baya."
.
"Yanzu dai mu bar wannan maganar" ya ce da
ita abin da ya faru dai ya riga ya faru, dole ne
in sanar da jami'an tsaro su shiga cikin
maganar don a kawo karshen wannan rigima,
kafin abin ya kai mu ga kashe-kashe don na
ga alamar abin da wannan mahaukacin sojan
ke nufi kenan, in ya so daga baya sai in sayar
da gidana na sabuwar unguwa in biya shi
kudadensa, ita kuma A'isha sai a nemo ta a
bata wanda take so."
.
Juma ta dan saki ranta ta ce da shi.
"To yanzu da ka yi haka kai kanka ba ka fi jin
dadi a ranka ba? Ai wannan shi ne datattako
maigida, yanzu to ka nemi a zauna lafiya."
Kamar aikin budar idanu cikin yan tsararun
mintuna mafadanta ma'auratan biyu suka
dawo cikin raha kamar ba su ba. Shekaru
sama da talatin kenan, suna wannan halayya,
an ce a cikin minti daya sai su hautsine da
fada, kafin kiftawa da bismillah sai kuma a ga
sun dawo suna dariya.
.
To sai dai kuma a wannan karon da sun san cewar akwai wani
shu'umin saurayin da ya cika bindigarsa da
harsashi, sannan kuma ya saya musu likkafani
jana'iza da ba su sake yin wata raha ko dariya
ba.
_____________
A'isha ta dubi angonta Nazifi cikin farin ciki
sannan ta ce da shi "Nazifi 'darling' yau dai
Allah ya cika mana burinmu, mun zama mata
da miji. Duk duniya babu mai raba mu ni da
kai masoyina."
.
Nazifi ya dube ta shi ma duba na so da kauna
yana kwance a kan doguwar kujerun da ke
cikin tsararren dakin da suke ciki, ya ce.
"Ai ni A'isha ba ma abinda zan iya cewa sai
dai kawai in godewa Allah da kuma wannan
abokin nawa domin kuwa wallahi ni dai ya
gama yanto ni, ya yi min komai na alheri."
A'isha da ke zaune a kusa da shi ta ce cikin
mamaki "Wai da gaske bayan ya ba ka rabin
miliyan har kuma wannan gidan duk shi ya ba
ka, Nazifi?"
.
"To ga zahiri ma kin gani A'isha tun da har ga
shi kuma na shigo da ke kin tare a ciki, ko
kuwa ke a da kin ga na yi miki kama da
wanda zai iya mallakar wannan tsantsareren
gidan?"
.
A'isha ta yi dariya farin ciki.
"Mun gode masa wallahi. Don Allah sai
yaushe zai zo don in gan shi mu yi masa
godiya ta musamman akan wannan abin
alheri da ya yi mana?"
.
Nazifi yace da ita "An jima nan kadan za ki ji
ya zo ya kwankwasa mana kofa domin
kuwa shi ma yau ake daura aurensa da wata
yarinya a nan garin kuma mun yi da shi zai
biyo min ya dauke ni mu wuce wurin daurin
aure tare."
.
A'isha ta sake lumshe idanu cikin murna ta
ce.
"Mun gode wallahi, Allah ya bar zumunci
tsakanin mu da shi. Yaya sunan tasa amaryar
Nazifi?"
.
Nazifi yayi farat ya ce.
"Ai abin namu ni da shi ya zo daya domin
kuwa saboda tsabar shakuwa da muka yi da
shi, har ankon sunan amare muka yi, cikin sa'a
ita matar tasa sunanta A'isha."
.
Suka yi dariya, A'isha ta ce.
"Lallai abin yayi min dadi Nazifi, ka ce kun
samar min kawa kenan ni ma" Suka ci gaba
da dariya abin gwanin ban sha'awa. Suka fito
da naman kaza suka tasa a gaba, dama tun
tarewa su gidan a daren jiya Nazifi ya sawo
dakwalen kaji soyayyu har guda uku. Tun a
jiya suka cikye biyu saura ragowar daya wacce
suka baje a halin yanzu.
.
Ba abin da ya dame su, kudine dai sun samu abin kamar daga sama, dole ne su godewa
wannan abokinsu
mai farar aniya.
A daidai wannan lokaci ne Gali ya karaso
kofar gidan fuskarsa a murtuke kamar wanda
aka yiwa albishir da mutuwa. Lokaci-lokaci
yakan kai hannusa cikin aljihu ya shafi
bindigarsa. Kamar yadda ya tsara a ransa,
.
daga nan idan ya gama gaisawa da ango da
amarya, to farauta zai wuce abinsa. Ba
farautar namun daji zai fita ba, farautar
amaryarsa A'isha zai fita da kuma saurayin da
aka ce ya sace masa ita sun gudu. Kuma ya
sha alwashin muddin ya yi ido biyu da A'isha
da wannan saurayi da ya sace ta, to ba wani
bata lokaci duk aikawa da su zai yi barzahu
.
Gali ya yi murmushin mugunta sannan ya
sake mika hannu ya shafo bindigarsa wacce
ke boye a cikin aljihu. Ya daga hannu ya
kwankwasa kofar gidan a sanyaye. A'isha da
Nazifi da ke cikin gidan suna baiwa juna
naman kaza a baki, suka dubi juna cikin farin
ciki a dai dai lokacin da suka jiyo sautin
bugun kofar "Kin ji dan halak!"
.
Nazifi ya ce
"Shi ne yake kwankwasa kofa, Gali ne
abokina. Je maza ki bude masa kofa ki rako
shi, A'isha."
.
Amayar ta ce da angonta a sanyaye.
"Wata kila ma wasu miliyoyin kudin ya sake
kawo mana 'darling'."
Nazifi ya ce "Babu mamaki, A'isha ai na fada
miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke
dai je ki bude masa kofa, ki tarbo shi ya
shigo."
.
___________
YAU KAM RIGIMA ZATaYI KISA
.
Ya kuke ganin zata kaya
Ku biyoni Shuraih 99% a littafin AJALI
Nazifi ya ce "Babu mamaki, A'isha ai na fada miki abokin nan nawa yana bala'in sona, ke dai je
ki bude masa kofa, ki tarbo shi ya shigo."
.
A'isha ta mike cikin farin cikin tana rangwada ta nufi kofar gidan.
Hakika sun yi dace ita da angonta Nazifi, Allah ya hada ta da mai sonta kuma ita ma take
kaunarsa. Ya raba ta da wannan wahalallen da a da ya nace mata, A'isha ta ce a zuciyarta tana
murmushin farin ciki.
.
Ta kama kofar gidan da hannayenta biyu, ba tare da wani fargaba ko zullumi ba TA BUDE
MASA kOFAR!
****====******
Dankareren kayataccen gidan ne da ya kai matuka wajen tsaruwa. Jama'a da dama kan dakata
don yiwa kyakkyawan gidan kallon tsaf! saboda ginuwarsa.
Mutane da dama kan tuna da kayataccen gidan saurauniyar ingila
dake "BUCKINGHAM PALACE" a duk lokacin da suka dubi tsararren gidan. Wani dadin abin da
ke matukar jan hankalin jama'a ga hadadden gidan shi ne daddadan kamshin furanni dake
gewaye da gidan.
dan tsamurmurin dattijon maigadin da ke zaune akan bencin a gefen katotuwar kullalliyar kofar
gidan mai fasalin fuka-fukan dawisu, ya dan yamutsa fuska gami da gyara rikon jaridar da ke
hannusa tamkar mai tsammanin shekowar wani a guje ya wafce ta, cikin zakuwa ya soma bude
shafukan cikin ta, a shafi na biyar ya yi ido hudu da labarin da yayi matukar jan hankalinsa mai
taken KADDARA KO FANSA!
.
A hanzarce ya muskuta gami da gyara zama, kana ya sake kafa kwala- kwalan idanunsa akan
hotunan gawarwakin wasu mutane biyu mace da namiji da ke gefen rubutun, cikin zakuwa ya
soma karantawa.
.
A safiyar jiya ne yan sanda suka tsinci gawar
wani saurayi Nazifi tare da masoyiyarsa A'isha.
.
An tsinci gawarwakin ne yashe a cikin wani sabon gida bayan an harbe su da bindiga har lahira.
Tuni jami'an tsaro sun cafke wanda ake zargi da aiwatar da kisan gillar wanda ya kasance wani
matashin soja wanda shima yake kaunar budurwar, wanda kuma har an sa ranar bikin su da ita
amma kuma ita ba ta kaunarsa.
.
Mahaifin yarinyar mai suna Alhaji Dage ya yi
nadamar afkuwar mummunan al'amarin sannan kuma ya tabbatarwa da wakilinmu cewar
dukkan wannan al'amari da ya afku laifinsa ne sakamakon tilastawa diyar tasa da ya yi a kan
sai ta auri wanda ita ba shi take so ba. A karshe ya yi kira ga iyaye a kan su dinga mayar da
hankali a kan dukkan abin da `ya`yansu ke bukata matsawar dai hakan bai sabawa addini ba. .
Sannan kuma ya yi doguwar addu'a gami da bayyana matukar alhininsa ga mamatan
.
Don jin yadda zata kaya mu hadu a cigaban littafin nan mai suna A’ISHA don
jin karshen sarkakiyar sarkakakken labarin.
Na gode, naku Shafi’u Dauda Giwa.
.........................
Anan kuma ayau muka kawo karashen littafin AJALI amma da yardar Allah daga nan zuwa wani
lokaci zan saka maku cigabansa
.
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing Shuraih Usman 99%
....
JINJINA GA
Shafukan
Shuraih 99%
Zauran labarai
Home of Littatafan yaki and Hausa novels
.
Ina mika sakon gaisuwata ga ahalin kungiyar
TSANGAYAR MARUBUTA
TASKAR GIDAN LITTAFI
.....
Nine naku a kullum da ko yaushe Shuraih Usman
99%
Ku tareni a littafin A'ISHA AJALI
Marubucin littafin
Shafi'u Dauda Giwa
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da
littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com