Showing 3001 words to 6000 words out of 16852 words

Chapter 2 - AJALI littafin Shafiu Dauda Giwa-1.pdf

gadonta, ta kurawa bangon dakin
idanu, ko kiftawa ba ta yi. To amma a zahiri

ba bangon dakin take nazari ba, hankalinta da
kuma wani tunaninta kai gaba dayan zuciyarta
ma ba ta kan komai sai a kan wannan dan
saurayin da suka hadu a wurin fatin kawarta a
daren jiya
.
Tun rabuwarsu bayan ta dawo gida, ta yanke shawarar ko dafa ta za a yi a tukunya ba za ta
taba yarda a yi wannan aure nata da wannan saurayi mai suna Gali ba.
.
Domin kuwa har ga Allah matsa mata ake yi, amma ba ta kaunar sa ko miskala zarratin, to
amma a yanzu tunda dai har Allah ya hada ta
da Nazifi, to ta kwana gidan sauki.
.
A'isha ta dade da sanin wannan al'ada ta
mahaifinta, domin kuwa ba akana ta ya fara yiwa
`ya`yansa auren dole da, attajirai masu
hannu da shuni ba. Duk yayyenta da aka aurar
su kimanin biyar duk auran dole akayi musu,
to amma ita lallai akwai alamar daga kanta
za`ayita ta kare,
.
domin kuwa komai tsiya baza ta bada goyon baya ba, duk da yake kuwa ta san mahaifinta ya
ciwa saurayin makudan kudi, duk kuwa da cewa saurayin
nata Gali soja ne, da shi aka je kasar Saliyo.
.
Ita kanta wannan dukiyar da yake facaka ita, a
dalilin wannan yaki ya same ta, domin kuwa
an ce gwamnati ta basu miliyoyin kudi,
wadansu kuma suna cewa daga can kasar ya
samo wannan dukiya. To amma dai koma
mene ne sanin kowa ne cewar saurayin ya
samu kudi,
,
wadanda kuma ba su yi masa amfani wajen mallakar masa zuciyar `yar budurwa A`isha ba,
domin kuwa ko da wurinta ya zo sai dai ya kari surutunsa shi kadai, amma ba za ta ce masa ci
kanka ba
.
To amma kuma duk da wannan durama da suke
yi wai a zahiri saura kwanaki kalilan a daura
musu aurensu. A`isha ta share hawayen da ke gangarowa
daga cikin idanunta, sannan ta yunkura
gwuiwoyinta babu karfi
.

Ta sauka daga kan gadon, domin kuwa ta san cewar a kowane
lokaci bayan yanzu, Nazifi zai iya zuwa ya
same ta a cikin wannan hali. Don haka gara ta
gaggauta ta kimtsa kafin ya zo. Nan da nan ta
nufi bandaki,
.
ta yi wanka ta fito fes kamar babu wani abu da yake damun ta. Ta fiddo kayan kwalliyarta ta
soma caba ado. Har kawo wannan lokaci zuciyarta ba ta daina tunanin masoyinta Nazifi ba.
.
Ta yi tunanin cewar duk don saboda ta ce tana kaunarsa aka lallasa
mata shegen duka, ta yi wa kanta murmushi
sannan ta ce a bayyane. "Ka da ki damu A`isha ba ki fadi kasa ba, in
dai don soyayya za a yi miki wannan uban
duka na kawo wuka. Ba ki fadi a banza ba
A'isha, 'yar autar mata, soyayya ai ta fi gaban
wasa."
.

Ta kammala shiryawa, ta dubi madubi, ta gamsu da abinda ta gani. Ta yi wa kanta murmushi
domin kuwa ta san cewar wannan kwalliyar za ta biya kudin sabulu, tunda dai masoyinta na
gaskiya ne zai ga kwalliyar.
.
Dadai a ce wannan wahalallen ne zai zo, to ba za
ta tsaya bata lokacin inganta wata kwalliya ba. Domin kuwa ita da a ce ma akwai abinda za
ta shafa, ko ta sanya a jiki, ya gani ya daina
kaunar ta, to da tuni ma ta aikata sun rabu, don ta hutawa rayuwarta da wannan naci nasa.
.
Haryanzu dai kuna tare da Shuraih 99% cikin littafin AJALI na shafi'u dauda giwa
Muje zuwa
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 4
.
Tunda take ba ta taba ganin mutum da
shegen nacin tsiya irin wannan saurayi da aka
sa ranar bikinta da shi ba
.
Babu irin cin mutuncin da ba ta yi masa ba, amma kullum yana nan like da ita don tsabar
masifar naci.
.

Don ma ta yi sa'a ne a halin yanzu ba ya nan,ya yi tafiya kafin ranar daurin aure ta zo Amma ba
don haka ba da tuni har ya zo ya dame ta da surutun tsiya.
.
Tunanin A'isha ya yanke a yayin data ji sallamar wani karamin yaro, ta amsa sallamar yayin da
yaron ya turo kofar dakin ya shigo
.
"Wani mutum ne ya ce in kira masa ke, yana can waje."
A'isha ta ji gabanta ya fadi, ta ce da yaron.
"Bai fada maka sunansa ba?"
Yaron ya dan yi jim, sannan ya ce da ita.
"Ya fada min, ya ce in fada maki Nazifi ne ke
son ganin ki."
A'isha ta rike numfashinta, ta yi murmushi
sannan ta ce da yaron. "Don Allah ka je ka ce
da shi ga ni nan zuwa yanzun nan."
"To." Yaron ya fada cikin ladabi, ya fita. Ficewarsa ke da wuya ta bazama zuwa inda kayan
sawanta suke, ta zabo wani uban leshi mai ruwan hoda, ta fara hanzarin sanyawa.
.
Duk Allah-Allah take yi ta je ta same shi, domin kuwa da tunaninsa ta kwana a zuciyarta
.
To sai dai kuma abinda 'yar budurwar ba ta sani ba shi ne ba ita kadai ce ke murna da zuwan
saurayin ba, bayan ita hatta mahaifinta ma shi ma yana matukar murna da ganin saurayin,
domin kuwa ya yi bakam a daki,
.
duk ya kosa su yi magana da sabon saurayin ya shaida masa kaulinsa na zunzurutun kudi naira
miliyan daya, idan yana son a aurar masa da kyakkyawar A'isha.
.
BABI NA BIYU
Ta fito daga cikin gida fuskarta wasai, sai
sheki take yi, tana murmushin farin ciki. Kai
da gani ka san cewar a boye, a bayan wannan
kyakkyawar fuskar tata, akwai wani
muhimmin albishir, wanda ga dukkan alamu
kuma idan har ta furta shi daga bakinta,
.
To dole ne ma ya dadada wa wanda take shaidawa, tabbas zai dadada zuciyarsa. A'isha
ta tsaya wuri guda, tana waige-waigen inda ya
tsaya a cikin harabar gidan, wadda ke cike da
shuke-shuke na alfarma da kuma tsirarun
dawisu dake zirga-zirga nan da can
$
jikinsu sai kyalkyali yake yi, a cikin dan abinda ya yi saura na hasken ranar da ke kokarin isa ga
mafadarta.

Duk da karayar arzikin da mahaifinta ya yi,
da ganin dankareren gidansa, ka san cewar a
wani zamani da ya wuce an yi tabara da naira.
.
Ba kasafai za ka samu wani mahaluki a harabar gidan ba, kullum wurin yana nan tsit kamar
makabarta. Wani lokacin kuma idan Alhaji Dage ya bushi iska, yakan fito da
kujera wajen harabar ya zauna ya yi ta
karanta jarida. Mafi yawan lokuta samarin
unguwar suna bakin ciki da wannan al'ada
tasa, ta zama a waje, domin yana matukar
takura masu wajen ganawa da 'yar
kyakkyawar yarinya A'isha.
.
Bayan A'isha ta gama waigen kowanne
bangare na harabar, sai ta hango Nazifi a can
rakabe a jikin wata bishiyar dorawar turawa
da ke kusa da babbar kofar shigowa cikin
gidan. Yana tsaye a jikin bishiyar, ya jingine
akwalar kekensa a gefe guda. Hannayensa a
harde a kan kirjinsa, ya sako wani farin yadi
boyel, wanda ya dan fara zazzagawa
.
A'isha ta isa gare shi tana murmushi. Tun daga nesa da ya hango ta shi ma yake murmushi, har
ta
kawo inda yake.
"Wallahi har na cire tsammanin zuwanka,
Nazifi."
.
Soyayya da dadi jama'a
Saide daga karshe.......
Its shuraih 99%
AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 5
.
"Wallahi har na cire tsammanin zuwanka,
Nazifi."
Ya ci gaba da murmushi, ya ce da ita.
"Haba A'isha, ai ke ma kin san cewar tunda
dai har na daukar maki alkawarin cewar zan

zo, ai ba zan karya ba."
.
Suka sake yi wa juna wadansu sabbin
murmushi.
"Gaskiya na ji dadi wallahi Nazifi, ka san
yadda soyayyar ta koma yanzu. Wani lokacin
sai ka ga an kulla alkawura sama da dari,
amma da wahala ka ga an cika ko da goma ne
a cikin darin. Kai dai ka san cewar da a ce
yadda ake kulla alkawarin soyayya a duniyar
nan, haka ake cikawa, to da yanzu babu
sauran wani mutum wanda ba shi da
masoyinsa."
.
Nazifi ya yi dariya.
"Duk da haka dai A'isha, ai dole ne a samu
nagari, kin san ba zai yiwu a ce duk an zama
daya ba, duk da lalacewar da soyayya ta yi za
a samu mutane nagari da ke cika
alkawarinsu."
"To za ki fara ke ma ko...?"
Ta yi dariya.
"Ba haka ba ne, wannan ai gaskiya ce Nazifi,
domin kuwa ba wani zolaya don ka fadi
halayen masoyinka nagari."
.
Suka sake tuntsirewa da dariya a lokaci guda.
Nazifi ya fara cewa bayan sun gama dariyar.
"A'isha akwai abun da ke tattare da zuciyata, wanda
duk na kosa da ma in zo in amayar maki da
shi. Wallahi A'isha jiya ban yi wani barcin
kirki ba, domin kuwa ina komawa gida,
tunaninki ya dabaibaye mini zuciya, sannan
kuma ko da na samu damar yin barcin,
mafarkinki ne ya buwayi kyakkyawan barcin
nawa. Don haka nake so idan ba za ki damu
ba, ina son mu yi maganar aure in dai har da
gaske ne kina so na."
.
A'isha ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce da
Nazifi, "Na ji duk bayaninka Nazifi kuma na
matukar farin ciki, to amma ina son ka yarda
har zuciyarka. Nazifi wallahi ni ma duk

duniyar nan babu wanda nake so sai kai. To
amma da akwai wata 'yar matsala guda daya
da ke tattare da ni. Ina son idan na fada maka
kada ka karaya, domin kuwa wannan matsala
ba za ta hana mu gudanar da soyayyarmu ba.
Ta dan saurara sannan ta ce da shi.
.
"Nazifi saura kwana takwas kenan a daura aurena."
Saurayin ya rike numfashinsa cikin kaduwa,
sannan ya dafe kirjinsa, "Aurenki!! A'isha...ban fahimce ki ba."
.
Ta girgiza kanta "kwarai kuwa aurena Nazifi.
To amma ina son ka sha kuruminka, domin
kuwa ni da ma ba na son saurayin da za a
daura mana aure da shi, kawai mahaifina ne
ya takura min a kan al'amarin. To amma a
halin yanzu, tunda har Allah ya hada
soyayyarmu da kai, wannan zancen aure babu
shi, ya lalace, in Allah ya so kai ne mijina
Nazifi."
.
Nazifi ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce da ita.
"To amma kuma iyayenki kuma fa A'isha,
kina jin za su amince?"
"Sun riga sun san komai Nazifi, domin kuwa
na fadawa mahaifiyata gaskiyar abinda ke
zuciyata, to amma ban samu goyon baya ba.
Domin kuwa a dalilin na ce ina kaunar ka
Nazifi sai da ta lakada min dukan tsaiya, da
kyar mahaifina ya yi mata magana ta rabu da
ni."
.
Suka kurawa juna idanu cikin jimami. Nazifi
ya ce "To amma kuma A'isha kina jin
al'amarin nan zai yiwu? Tun yanzun fa kenan
har kin fara fuskantar matsaloli, to ina kuma
a ce tafiya ta yi nisa a tsakanina da ke?"
"Me zai hana al'amarin yiwuwa Nazifi?" A'isha
ta ce da shi.
.
"Ni dai na daukar maka alkawari, duk rigimar
da za a yi ba zan amince a daura mini aure da
wannan wahalallen ba, don haka na riga na

gama tunanin komai a halin yanzu, kai kawai
nake jira, don in ji ta bakinka. In kana jin za
ka iya jurewa, kamar yadda ni ma zan jure,
komai wahala mu rike juna."
.
Nazifi ya sake yin doguwar ajiyar zuciya,
sannna ya ce da ita, "Kada ki damu A'isha, na
daukar maki alkawari, komai wahala ni ma
ina nan tare da ke, sai dai mutuwa za raba
mu."
.
A daidai wannan lokacin ne da suke ta
wannan doguwar hirar tasu ta masoya, kamar
an jeho shi, sai Alhaji Dage ya fito daga cikin
gida. Tun dazu yake zaman jira, yana
tsammanin jin sautin dankareriyar mota ta yi
fakin a kofar gidan, domin kuwa shi har
yanzu tsammani yake yi, sabon saurayin da
A'isha ta ce ta sake, wani hamshakin attajiri
ne wanda ya rude ta da zunzurutun kudi.
Fitowarsa ke da wuya, ya kai ganinsa inda
A'isha ke tsaye tare da saurayin a gindin
bishiyar. Alhaji Dage ya yi raunanannen
murmushi da ya hango wanda ke tare da ita,
domin kuwa ya dauka cewar masinjan
masoyin 'yar tasa ne, ya zo fadawa 'yarsa
A'isha cewar Alhajin ba zai samu zuwa ba.
.
Alhaji Dage ya nufi inda suke a tsaye. Ya
hango tsohuwar akwalar keken saurayin a
jingine da bishiyar, kamar dokin kara, nan da
nan sai ya ji tausayin saurayin ya kama shi,
domin kuwa yana matukar takaicin yadda
attajirai da manyan ma'aikata ba sa kulawa
da masinjojinsu, haka dai ya iske su suna
cikin hirar
.
Nazifi ya rage tsawo ya gaishe da
Alhaji Dage. Ya amsa cikin fara'a-fara'a akaici-takaici, kana ya ce da saurayin.
"Allah sarki! Kai ya turo kenan, bai samu
zuwa ba. In ka je ka ce da shi na yi zaman
jiransa, domin ina son mu yi wata 'yar
ganawa da shi a kan lamarin 'yata A'isha da ya

ce yana so"
.
dan saurayin da 'yar budurwar suka kalli juna
cikin tsananin mamaki. Ba su san me siririn
mutumin yake nufi ba, to amma shi bai
damu ba, sai ma ya ci gaba da zancensa kai-
tsaye.
"Idan ka gama fada mata sakon da ya aiko ka,
don Allah ka yi saurin janye akwalar keken ka
tafi malam, domin ina jin tsoron kada ka
tsorata mini agwagi da dawisu da wannan
tsohon keken mai shegen rakin tsiya."
A'isha ta dubi mahaifinta cikin damuwa, ta ce
da shi cike da kaduwa.
.
"Baba shi ne, ba aiko shi aka yi ba."
"Ban fahimta ba, shi ne wa?" Ya zazzaro
kwala-kwalan idanunsa da ke boye a cikin
kwafcecen-tabaron.
.
A'isha ta ce da shi cikin ladabi.
"Baba shi ne ai saurayin da nake so dama, shi
ne masoyin nawa." Tuni jikinta ya soma
kyarmar kaduwa.
.
Alhaji Dage ya kai hannu cikin razana, ya
ciccibo katon tabaronsa kaya guda, ya rike a
hannusa, ya kalli saurayin sama da kasa
sannan ya ce a sanyaye.
.
"Lallai A'isha tubarkalla na ga saurayin, ya
sunanka malam?" Nazifi ya sunkuyar da kansa
kasa, domin kuwa ya tabbatar akwai matsala
babba da ke shirin faruwa. To amma dai duk
da haka, sai ya kokarta ya bude baki ya baiwa
mutumin amsa.
"Sunana Nazifi" Alhaji Dage ya dubi A'isha ya
daka mata tsawa.
"Shige cikin gida kafin in zo in same ki `yar
banzar yarinya kawai"
.
A'isha ta juya cikin tsananin karaya, ta nufi
cikin gidan. lokaci-lokaci ta kan waigo don

ganin abin da zai wakana ga masoyinta. Nan
da nan ta soma addu'ar Allah ya sa dai kada
mafadacin baban nata ya buge shi, domin
kuwa ta san shi wajen saurin hannu.
.
Wannan na daga cikin abin da ya sa shi yin kaurin
suna a unguwar, domin kuwa ya sha marin
samarin da ke zuwa wurin `ya`yansa,
musamman ma idan a kasa mutum ya zo ba
a mota ba
.
Shigewar A'isha ke da wuya, sai ya tattara
hankalinsa gaba daya ya ce da dan saurayi
Nazifi.
"Ina son in yi maka gargadi na farko, kuma na
karshe, wannan yarinya `yata ce, ni na haife
ta, kuma saura kwana takwas kenan a daura
aurenta, ka rufawa kanka asiri ka fita daga
cikin harkokinta, domin kuwa A'isha a halin
yanzu ko kai aka sayar ba za ka biya abinda za
kai aurenta ba. Domin kuwa na san dai ba za
ka kai naira miliyan guda ba, don haka kar ka
jawo wa kanka bala'i dan saurayi."
.
Nazifi ya girgiza kai cikin gamsuwa bayan da
ya ji mafadacin mutumin ya kai aya. Ya jawo
akwalar kekensa cikin hanzari domin kuwa in
ma tsautsayi ya ratsa ya ga alamar cewar jiki
zai yi tsami, to ba zai bar akwalar keken a
wurin ba, wacce ita kadai ya mallaka a duniya
.
Malam Nazifi abun tausayi
Talakan masoyi ya hadu da ma kwadaicin siriki
Its shuraih 99%AJALI
Na Shafi'u Dauda Giwa
Typing by Shuraih Usman
Post by shuraih 99%
@shuraih 99%
Page 6
.
Nazifi ya girgiza kai cikin gamsuwa bayan da
ya ji mafadacin mutumin ya kai aya. Ya jawo
akwalar kekensa cikin hanzari domin kuwa in

ma tsautsayi ya ratsa ya ga alamar cewar jiki
zai yi tsami, to ba zai bar akwalar keken a
wurin ba, wacce ita kadai ya mallaka, a duniya.
.
Alhaji Dage ya sake cewa da shi a fusace,kafin ya tafi.
"Ka rike a zuciyarka dan saurayi ba na magana biyu, haduwar mu da kai ta biyu babu dadin
gani. Idan na sake ganin ko da inuwarka a nan gidan,kai ko sawunka na gani wallahi sai na aika
polisteshan, an kulle min kai, shege beran masallaci."
________________________________
Wata dankareriyar mota mai tudun baya, ta garzayo a guje kamar kibiya, tana sheki a cikin
hasken kwaleliyar ranar wacce ke ta faman gasa naman bil'adam. Jama'ar da ke zazzaune a
bakin titin, suka bi motar da kallo, domin kuwa lokaci-lokaci sukan ga motar ta shigo cikin
unguwar tasu, to amma kuma har yanzu babu wanda ya san takamaiman abin da ke kawo
motar a kai- akai ba
.
Kamar kullum sai motar ta rage gudu sannan ta fara sigina, cikin abin da bai fi dakika biyar
ba,har ta tsallako titi.
.
Saurayin da ke tuka motar ya daga musu hannu, wannan al'adarsa ce koda yaushe, da ma ya
kan dago musu hannu in ya same su a zazzaune. Yawanci idan haka ta faru, su mutanen ba sa
wani kula shi, ko a yanzun ma da ya dago hannu da kyar aka sami mutane uku da suka kula da
shi, su ma kuma ba hannu suka daga masa ba, kai kawai suka gyada masa kamar kadangaru. .
Me yiwuwa idan aka tona zuciyar mutanen unguwar watakila suna da gaskiya, domin kuwa tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login