Showing 33001 words to 36000 words out of 62795 words
Chapter 12 - Auren Huce Haushi Book 3 Complete By arewahausanovels.com.ng.pdf
gama gyaran falukan na shigo da abincin da Baba Haruna ya
kawo".
" OK babu damuwa ke kinci abincin?"
"Eh nayi mana tunda da safe nida security din kofa haka Ammi tace na ringa yi tunda na iya
sosai race Amman ke Aunty zilai ce zatana yi miki".
Ok. Ga saura can na Wanda aka kawo din ki diba sauran ki fitar musu dashi, yanzu zoki tayani
dauka muje can babban parlour Abbana ne yazo ganina".
" to Aunty muje" zahra ta dauka itama ta dauka suka nufi can parlourn.
"Haba uwata danmi kika wahalar da kanki haka?"..
Binta ce ta tsuguna tana gaishe Abban sannan ta gaishe da sauran ta koma dauko sauran.
" Abba abinda kakeso fa nayi maka tunda na duba naga da fresh milk ta shanu".
Ya Abdul Hakeem ne yace "to kaji Abba Biryqni rice tayi maka kaga kuwa tayi abinda bazakaqi
ci ba, kinyi masa mutumin?".
Kaita gyada Masa.
Table mat Binta ta shimfida guda biyu daya Abba dayan su ya Abdul Hakeem.
Saida ta zubawa Abbanta komai sannan ta zuba musu ba karya ta tabbata rainon Ammah
abinci tayi dadi iya dadi ga gas meat din Abba shima yayi dan kin cin pepper soup din sukayi sai
nasan sukaci Mahmud bai wani ci abin kirki ba tunda basu Dade da yin breakfast ba kawai da
dan kada taki ci ne ba dadi.
Suna gamawa zayyan ya Karaso da Hajiya inna afujajan dan cewa ba lafiya ba tunda jiya suka
bar gidan kuma Yau a tura daukota.
Saida ta shiga ne kuma ta samu Salama tunda taga zahra lfy sai hira sukeyi da jama'a.
Zahra ce ta tashi tana fadin "sannu da zuwa Hajiya daga ina haka?".
" O'o daga gida mana mijinki ya tura a daukoni babu shiri wallahi nayi zaton wani danyan aikin
yayi yake nemana"
Rufe ido sameer yayi tana ayyana "wlh duk jirgi daya ya kwasosu ba saiti kina sisin kwabo".
Sameer din ne ya tashi ya nufi Inda suke dan kada ta kira musu ruwa da bakinsu da babu saiti.
" Sannu da zuwa Hajiya ki karaso baki garemu saiku gaisa ko".
"To muje din ai hakan zumunci ne".
Saida ta shigo sosai taga Alhaji Jafar sai kuma ta fara fadin "ikon Allah yo ai nasan wannan
Alhajin ba kai bane ka sauko dani daga kan dutsen Arfa dana hau bara waccen lokacin dasu
Mustapha suka bace min?".
Dariya Abba yayi saboda ya tuno drama da suka sha a lokacin.
" nine mana Hajiya Ashe bazaki manta in ba".."
"Kai Haba shege ke mance Alheri ai nayi takaicin rashin tambayarka kai na Ina ne lokacin yo a
gigice nake daka rakani gurin ma'aikatan sokoto kuma nayi gaba naga na gida a she da sauran
haduwa kaima sana'ar ce ta hadaku da wannan miskilin?".
" Dan Allah ki zauna Ku gaisa sai ayi miki bayaninsa".
Sameer ya fada.
"Kai tafi can lokacin daya taimaka min kuna can kuma taku sabgar ba sai daga baya kika sani
ba, shiya yasa bara nace bana zuwa ina jimamin rashin dan tagwaye tunda shine me biya min
nida 'yan uwana muje,gara muje umara tunda Allah ya fito min dashi".
" Dan Allah ki zauna ku gaisa tukunna sai ayi labarin" su dai dariya kawai sukeyi tsohuwar
warka ce bazake ce itace mahaifiayar milliners ba kuma kakar billionaire it's very simple and
funny.
Alhaji Jafar ne yace "rabu dasu Hajiya sannu da zuwa ya akaji da jama'a?".
"Alhamdulillahi Yaya bayan rqbuwa kuma Ashe addu'ata ta karbu ai a gurin d'awafin bankwana
saida nace Allah ya had'a fuskokin mu ko a daras salam ne Ashe a nan ma zamu hadu".
Zarha ce ta matso suka gaisa da Hajiyar wannan sauran suka gaishe ta.
" kai kuma haka ake sai kayi min aike haka wuta wuta duk a tada hankalina".
"Kiyi hakuri to daman kiranki nayi ki tayani rokon Abban zahra akan marar lafiyar da kukaje
dubawa da Hajiyar maru itace za'a fitar zuwa Egypt to har an gama komai kawai visa ake jira
sai yace a'a a bari shine nake son a bashi hakuri ya bari mu ida ladarmu, ayi hakuri Abba ba
qararka na kawo ba". " wai kana nufin shine baban zahara'u taka?".
Kai ya gyada mata "Ikon Allah kace ta gida ce ka auro yo ai ni tun ranar daya taimaka min ya
zama Dana,kuje kuci gaba da aikin ladarku ni nayi izini ai Dana ne ake yiwa wasu ma bare shi
ai kujerun makka na wajena duka a kaisu Azare badan babu ba a'a kyauta ce a bawa hadimai
da dangi da makota kafin nazo naga guri duk da daman nayi niyyar zuwa naga masu karancin
nan da suka bawa dan tagwaye mata irin wannan ga jijyarsa da kukayi bamu da abinda zamu
Baku sai dai Allah ya biyaku da mafificin alkhairinsa".
" Allahumma Amin Hajiya nagode kwarai da gaske yanda kikace haka za'ayi".
Sameer ne yadan risina tana da sadda kai "to min gode Abba kenan basai kun tafi da ita ba ayi
hakuri jibi ne zamu wuce sai kuma idan wani ze bimu daga baya Amma nida yayar Hajiyar
zamu wuce in sha Allah"..
" kai kuje kuyi shirin Ku a banza ma dawa ake yiwa ruwa bare kuma a karkara"..
"To mun gode Allah yaja kwana".
Hira ce ta balle tsaanin Abba da Hajiyar duk yanda yaso ya yakice hirar yabar gidan taki saida
suka fita sallah ne yace a fada mata zeyi mata zuwa na musamman ya bada dubu Dari uku a
bata,ko zahra basuyi sallama ba sai ta waya ya kirata ya fada mata dalilinsa.
Sai dare aka mayar da Hajiya inna wuni tayi tana fadin " haba shi yasa naji kin kwanta min
zahra'u Ashe da walakin goro a miya,kin taso gidan masu nagarta da saninin ya kamata".
****
Tunda Mahmud ya fita maida Hajiya bai shigo ba sai gurin Tara tunda har lokacin ya rike su
sails bai bari sun koma Azare ba.
Tana shafa' da wuturi ya shigo da alama a gajiye yake sosai,wanka ya fada bai jima ba ya fito
lokacin tana ninke hijabin ta fito daga gurin sallar.
Hannunsa ya bude mata ta taho a hankali ta fada kirjinsa yayi mata murfi da hannuwansa,ajiyar
zuciya ta sauke jin sanyin ruwan yana ratsata.
Shirya ki rakani unguwa duk da a gajiye nake Amma gara muje kawai gobe in sha Allah babu
inda zan fita so nake na zauna dake na fada miki waye ni,da dalilin daya fitar dani daga gida da
duk komai nawa tunda naga alamar ko zamu shekara Dari ba tambayata zakiyi ba".
Lif tayi tana jin dadin sanyin jikinsa.
"Preciousss"..
Ya kira sunanta yana dan yawo da hannunsa a jikinta.
" Na'am meu amorrr..."
"Fada min ina kike son muyi honeymoon din mu kinga ummee tabamu ticket na qasashe uku".
Dan Jim tayi kafin tace "nafi son Qasashen middle East gaskiya bana son European countries
idan so samu ne mu fara da Saudi Arabia muje Ku ziyarki Qabarin Annabin Rahama muje muyi
umara kuma kaga saimu tafi da Hajiya inna ko tunda naji tana fadin zataje".
" Tab Allah ya kiyaye na tafi da ita yanzu Ashe ba angwancewar zanyi ba ai ruwa zata hana
guru ko tace dakinku daya tasani a bakin duniya idan na hana kada ma kice mata ga India
samu kiyi shiru da bakinki idan ba so kike na Dawo nayi dan wuya ba maimakon aga nayi free
lamura sun karbeni". Sunne kai tayi a kirjinsa "kai meu Amor kaida Hajiya fa bata baci ka manta lokacin da kace idan
mun hadu zaka kai mata qarata akan abincin?".
Lakuce mata dan bakjnta yayi " ke bakya mantuwa ne Wai?"
"Eh da sauki ai unguwarma na fasa gaskiya ka manta duk ranar dana rakaka unguwa bama
dawowa lafiya, haka kawai kaje ka hadani da abinda tafi su bar-bar tunda naga baka da ragi
idan ta had'oka da mutane kaje ka Dawo kawai bana zuwa bansan ina zamu ba yauma ace ga
mace an kawo maka naje na mutu a banza gara kaje kai kadai".
" kai!kai!kai! Ashe ni tsihon mai laifi ne ni wlh ni nama manta anyi wannan abun kice dole su
little su taho gida tunda har kina kewarsu".
"A'a wallahi bana son ko ganinsu mutuwa ce kawai banyi ba a ranar, shi yasa nake ganin
mutuncin zayyan shi yayi min alfarma aka dauke min su fa".
" kinsan Allah a ranar hankalina fa yana kanki dan abinda nayi niyyar yi din ma ji nayi bazan iya
ba idan na tuna kina cikin wani yanayi kinsan daga ranar zayyan ya Kara samun wata daraja ta
musamman a gurina? Kulawa fa da tausayi duka ya muna miki "
"Wai dan Allah me kayo a cikin gidan nan nifa har yanzu ban samu nutsuwa ba".
Tsinin hancinsa ya fara gogawa a kan nata hancinsa yana dan hura mata iskar hancinsa cikin
nata.
" kizo muje ki rakani mana a can zakiji wannan amsar taki"
Dan rausayar da kanta tayi "gaskiya Ina shakkar binka tunda idan idonka ya rufe ba sauki kaje
ka kaini inda Zan kwana Ina kuka ba Mai lallashina tunda idan kana fushi ba ruwanka Dani".
"Kai ai da Kennan Banda yanzu yaushe zanyi fushi ai nine a kwana da din ba bansa yanda
abun yake bane kinsan ni kifin rjiya ne a wanna fannin.
*_AUREN HUCE HAUSH_*
AISHAT ISAH NUSAH
Maman Fateemah
Bismillahir Rahamanir Rahim.
Allah ka jikan iyayen mu kayi gafara da jinkai a garesu tare da sauran Alhummar musulmi da
suka rigamu gidan gaskiya.
Ina gaishe da dukkan masoyana na kiss Dana nesa Allah yabar kauna da zumunci, nagode
kwarai.
Gaisuwa ta musamman ga
1.Ramatu sunusu Ummi ( Mrs.Sani shehu kazaure )
2. Fauziyya lawal Ammanj sokoto.
3.Hajiya Zainab Bashir Aliyu ( Mrs Muhammad manga Taraba state.
Ina godiya Allah yabar zumunci da kauna.
__Page 90.
____cikin abinda bai wuce minti goma ba Mahmud ya gama nasa shirin cikin suit Navy blue
Goirgio Armani sai eyeglass daya saka mai azabar kyau yana daura agogo pateks a wrist
dinsa, wani iri fitinannen kyau yayi mata ta kasa dauke idonta daga Kansa harya karaso inda
take tsaye yana sakar mata da tsadadden murmushinsa mai shagaltar da ita, rumgumota yayi
yana fadin
"Yaya dai 'yan mata? ko kin kyasa dan malam ne irin wannan kallon haka? Ko dai mu fasa fitar
ne dan kina Neman hanani nutsuwa fa, wannan eyes din suna dauke da wani sirrin dake hanani
nutsuwa matukar suna kallona,kina tuna abinda ya faru a soron gidan baba malam ranar da Mai
mamana Mai sunan Ammi Bata da lafuya?Wlh bansan fa yanda akayi na jiki cikin jikina ba,
kinsan abinda kuwa hakan ya jawo min a ranar?nayi Dana sani yafi sau shurin masaki precious,
kinsan abinda ya daure min kai dake?".
Kai kawai ta iya girgiza masa.
" Da kika kasa ko daga ido ki kalleni ko naji mari kamar yards nayi tsammani, amma sai naji
shiru kinyi lif kina dibar ni'ima ko?".
Sinne kanta tayi ji tayi kamar yanzu abin yake faruwa.
"Dan Allah abar zance nan bakaji abinda bature yace ba? Fast is fast present is continue".
"OK to shikenan ya wuce princess,zo muje".
Shi yake driving din motar su zayyan na biye dasu a hankali suke tafiya yana nuna Mata
mahimman wurare a cikin garin bata San ina zasu ba saida taga signed board na Usman dan
fodio teaching hospital.
Kenan gurin mama sukazo, to meya had'a tambayarta da zuwa gurinta ko kuma daga nan zasu
wuce wani gurin ne.
A parking space suka tarar da Sameer, batayi mamakin ganinsa ba dan suna tafiya taji suna
magana badai tasan koda waye ba.
Daga dan nesa da inda sukayi parking su zayyan suka Parker.
Shida sameer suna gaba zahra na bayansu bar suka shiga Aminity word na Bangaren retainer
ship.
Dan knocking sameer yayi a kofar room four Aunty ladi ce ta bude kofar ganin sameer yasa ta
matsaya tunda daga hanya tunda tun zuwanta shi yaketa fadi tashi da kai komo abisa 'yar
uwarta, shiya turo mace ta zauna da Mama dazu lokacin da yasa a kaita immigration office.
Hanya ta bashi tana fadin "yallabai sannu da zuwa".
Kamar zatayi Kai kasa, Sam hankalinta Bai Kai Kan su Zahra ba, zaman glass dinsa Mahmud
gyara sannan ya riko hannun Zahra suka shiga dakin.
Mamar na Zaune an jingina Mata pillow tana Shan wani Abu a cikin cup,tana kurba kafin ta Kai
ga hadiyewa su Zahra suka shigo sunyi wata irin dacewa ta ban mamaki kana ganinsu kasan
wasu irin couple ne da a cikin dubu da wuya a samu Kashi goma irinsu, basuyi aune ba suka
tsinkayo tarin kwarewar ruwa ya sarke Mama babu k'ak'k'autawa Nan da Nan idanunta suka
firfito abinka da Mai idanu a warwaje da sauri Aunty laran ta natsa kusa da ita ta karbe kofin
tana fadin "sannu Rabi'a kibi a hankali tunda an samu tarin ya lafa".
Da kyar ya lafa Mata tana ta faman haki.
Daki ne madaidaici Wanda ya hada ababen more rayuwa sosai tamkar gida.
Duk yanda Zahra taso Mahmud ya saki hanunta yayi biris da ita.
"Sannu Mama ya jikin naki?"
Cikin raunin murya ta amsa da gani tana Jin jiki, "yauwa Zahra na gode kwarai da gaske kuyi
min godiya gurin mijinki na gode Allah ya saka da Alkhari".
"Amin" Zahra dasu Sameer suka amsa shi Dan gogan ko tari Bai kubce masa ba tunda ya shigo
sai wani kallo yake bin mamar dashi, ji yayi ya Fadi nauyi yayi faduwar sanho a rairaiyi, shi ashe
ganin tsoro yake Mata a Dan ganin da yayi mata, sai yaji duk abinda yayi niyyar ya sauke mata
yaji baze iya ba ya barta da wannan kaddarar ciwon data sameta kawai ta isheta musiba. Tun ganin da Mama tayi musu Bata Kara dogo da kanta ta kallesu ba Dan wani irin kunya da
nauyi ne suka rufeta yau ga Zahra a gabanta tare da Wanda suka dauka kaskantacce marar
galihu a baya Wanda aka dunga fad'a musu da wani haske a tare dashi da yafi na sauran
manemanta na baya amma tayi biris da maganar, gata gasu cikin wani irin yanayin da yafi duk
wani tunaninta da hangenta.
Sai da ya bushi iska sannan yasa hannunsa na hagu ya zare glass din dake idonsa ya yiwa
Mama kallon Kai tsaya cikin muryar data saka zuciyarta kadawa ya furta.
"Hajiya Rabi'aaaa..!!!".
Ba ita daya ambaci sunanta ba su Zahra ma Saida sukaji tasu zuciyar ta kada, Dan Zahra zata
iya rantsewa da girman Allah Bata tab'a Jin muryarsa da gautsi irin haka ba.
"Ga Zahra nan ki dubeta ki K'ara kinso ki daqile Mata rayuwa ki Hana ta Kai inda ubangiji ya
nufa taje kinyi ta kulle-kulle ki dan kada ta cimma rabonta na rayuwa da Allah ya hukunta a
kanta, kin manta tun mutum na cikin mahaifiyarsa yake rubuta duk al'amuransa na duniya daga
arzikinsa ajalinsa Dan wuta ko Dan Aljanna, an riga an rubuta alkalamin ya karya tawadar ta
bushe, alkawarin Allah gaskiya ne baya tashi,gata Nan KAINUWA ce dashen Allah. Kuma duk
kullin da kikeyi Allah ya nuna Miki iyakarki naso da lafiyarki da sai kinyi Dana sanin zuwa garin
Nan to Amma sai gashi Abu kadan ya Hana zuciyarsa ta zauna lafiya tana neman bugawa a
banza, abinda Kika so ya Sami Zahra sai gashi tun ba'aje ko Ina ba ya Sami yarinyarki, kinso
Zahra ta lalace sai Kuma ta Zama Dan tsiron da Allah keso ko babu ruwa Saiya rayu,an Bata
Almajiri marar galihu Maimakon tausayawa maraicinta a'a sai Kika gano tunda da Dan rufin asiri
ba yanda Kika zata ba kina.cewa sai dai kyau ya qare a banza inda sai dai a kare a yawon
kakksbar raba, duk da haka sai Kika dauri aniyar wargaza Mata rayuwar Aure saboda naki
yaran Basu samu kamar nata almajirin ba, kin manta ayar da Allah subahanahu wata'ala yace
cewa wamakaru "wamakarallah wallahi khairul makirin" Bari na maido Miki da abubuwan da
kikayi ta fafutukar su zamar Miki tsanin daze ruguza duniyar gidan aurenta naji garin yayi min
zafi na manta da ita har abada sai dai Wanda suka hada su gaji su kwance auren ko?" Ya jefa
Mata tambayar duk jikinta rawa dake ga gumi ya tsatstsafo Mata a goshi har diga yake, duk
tsiyar da kuke k'ullawa Asabe yarinyarki ta fada min komai har garuwan da Kike aikenta neman
tsubbace tsubbacen ku, kinci daraja Daya wadda tasa na kyaleki na Kuma kyale 'yan koren
naki, shi yasa na raba yarinyar taki da garin Dan matukar tana kusa zanyi Mata abinda asirin ki
ze tonu abinda bazan so ace iyalin Abba itace ja Baga a cikin tafiyar, ko Mai gadin gidansa
bazan iya keta masa rigar mutunci ba bare matar da yake aure ance ko a lahira wani Yana cin
arzikin wani, Wallahil Azim da sai kunyi Dana sanin Baku santa ba a rayuwarku,Kinga zaman
lafiya a kiyaye shigia eighteen dinta Amma duk Wanda ya kuskura ya k'ara gigin saka kansa a
cikin lamarinta tofa maganar ba irin wannan za'ayi ba, zakuje asibiti na dauki nauyinki da duk
Wanda yake tare dake a tafiyar saboda kinzo rako min princess ne ciwon ya tashi tunda dama
da akwai shi,to gara ki Fara sheda wutsiyar ragumi tayi nesa da kasa, idan kin raba kanki da
ciwon hassada idan Allah ya taimakeki ki samu waraka idan Kuma Yana Nan tofa Saida ya
zamar Miki sanadin komawa ga Allah tunda ita dai wannan dai da aka dunga kokarin daqileta
kada ta Kai inda ubangiji ya nufa tifa tayi Miki tazarar da za'a iya cewa tamkar tsakanin sama ne
da kasa".
Wayarsa ya mikawa Sameer.
'Kira zayyan ka fada Masa ya shigo da sakon Nan".
Glass dinsa ya mayar a idonsa.
Tunda ya Fara zazzaga maganganunsa wuta da daukewa duk wani mahaluki dake cikin dakin
Dan wannan dabi'ar ba kowa ne yasan Yana da ita