Showing 45001 words to 48000 words out of 62795 words
Chapter 16 - Auren Huce Haushi Book 3 Complete By arewahausanovels.com.ng.pdf
ta fizgoni gaba daya na fada saman kanta kafin
nayi wani yunguri Dan tunda na shigo na shaki warin Nan na kara rasa kuzarina, naji an kwalla
ihun kuka a saman kaina, abinda yayi saving din kenan daga rikon da Safna tayi min, da sauri
na mirgina na tashi, sai lokacin na Farga da suturar dake jikinta, wata rigar barci ce marar
Albarka duk breast dinta a waje. Ga hawaye bibiyu na bin fuskarta gashin kanta Mai Kama da
hatsin bara ta barbaza shi.
Aunty Sameera na gani ta Dora hannu a ka sai kuruwa take yi, da gudu Safna ta tashi tana
wani gunjin kuka tana fadin , wayyo Allah Aunty ki taimaka mini wallahi ba laifina bane barazana
yake mini Koda yaushe ya lalata min rayuwata batun yau ba Aunty na shiga uku waye ze
aureni a haka. Cikin kuka itama aunty ta Fara fadin wallahi Mahmud kaci Amanarmu Dan kana da dukiyar da
bazamu iya ja da Kai ko mahaifinka ba shine zaka ringa ketawa yarinya haddi, haba Ashe shi
yasa taketa rama a tsaye,wallahi banyi zatonka a haka ba, aiko kana bin Mata Ina ga ka
d'agawa yarinyar Nan kafa marainiyar Allah, Kuma inda mutumci ai zaman kanwarka take Dan
haka wallahi dole ka aureta tunda Kai ka Fara saninta 'ya mace bazan yarda ba da wannan cin
mutuncin da tozarci.
Tunda na samu kaina jikina keta faman tsuma ga wani uban jibi Daya rufeni duk kuwa da sanyin
A/Cn da yake ratsa dakin, ni dai banga shigowa ko motsin uncle saminu ba sai ganinsa nayi a
gabana jikinsa na tsuma baiyi wata -wata ba ya shareni da mari Yana fadin munafuki maci
Amana,to yanzu ina masu cewa karya ake maka? Sai suzo suga ta'asar da kake aikatawa da
idanunsu tunda suna ganin qazafi akeyi maka, Daman nasan idan zabuwa na yawo kere na
yawo wata Rana zasu hadu, nasan za'a rina munafiki wallahi kaji kunya, Zina a cikin gidan
ubanka wannan masifa har Ina Allah ya Kara Basu ne da Aure -Aure ba,kadan ma suka Fara
gani.
Hannun Safna Aunty Sameera ta Kama tana sharbar kuka suka fice daga dakin, saida suka
wuce uncle saminu yayi wata dariya Yana fadin. Yaro baisan huta ba in Bai taka ba, ba dai kace
bazaka auri Asma'u ba kadan ma kenan sokoto Nan sai tafi karfin zamanka mu zuba kasa Ido
wallahi saika Zama mujiya cikin tsintsaye duk kuwa da arzikin da kake yiwa mutane d'agawa
dashi dariyar ya qarayi ya Sara ya fice daga dakin. Aunty Sameera na fita part din Ammi ta nufa
ta shiga Danna bell ba k'ak'k'autawa Batool ce ta bude tunda itace ke kasa tana zuba Kayan
dana kowa a fridge.
Da sauri ta bude Jin kukan dake tashi daga wajen, dai dai da shigowar Ammi cikin parlourn
tunda itama taji Karan door bell din da akeyi ba sassuci.
Da sauri Ammi ta karasa shigowa tana tambayar Aunty Sameera me yake fatuwa? Cikin kuka
riris Aunty Sameera ta bude bakinta da kyar ta Fara fadin . Ammin Batool Mahmud ya lalatawa
Safna rayuwa wallahi a gado na samesu shida ita tana ta rusa kuka da magiyar ya barta Amma
abun yaci turn Ashe Daman haka yake Mata ta kasa fada sai Rama take a tsaye na shiga uku
Yaya zanyi da wannan abun kunyar? Kasa ko motsi Ammi tayi haka batool ita abun Daya fi
daure Mata Kai duka yaushe hakan ta faru kamar a cikin Shirin film to da yaushe ya shigo gidan
da har wannan dogon labarin ze wakana har haka, Amma saboda tarbiyyar da akayi Mata yasa
Bata tofa ba ta zubawa sarautar Allah Ido Amma ta yiwa abun question mark.
Innailaihi wa innailaihi raji'un, abinda Ammi ta dinga maimaitawa kenan ta kasa furta ko kalma
Daya tamkar an saka padlock an rufa bakin da zatayi wani sharshi.
Uncle Saminu ne suka shigo shi da Abbie sai Momin Kano wadda ranar girkinta ne Dan a can
part dinsa na bangarenta ya iske shi shine ta biyo su ganin hankalinsu a tashe.
Da ganin yanda Abbie ya shigo hankalinsa ba a karamin tashe yake ba Fadi yake Ina safnar
take maza a Kira doctor innailaihi wa innailaihi ilaihi raji'un , wannan wace irin musibace ta shigo
gidana?.Dan cikina ya aikata irin wannan rashin Albarka a cikin gidana, Ina Mahmud din take?
Ita Ammi rasa abin cewa tayi ji tayi kamar an Dora Mata bulo inci Tara a kanta ga kirjinta yayi
Mata nauyi, sahal ne ya nufi kofar fita da sauri saboda gaba daya suka fito Jin kuka a part dinsu
Suma abin ya Basu mamaki Dan a gaban Sajjad na wuce Yana waya, Amma a cikin abinda Bai
wuce mintina goma ba wannan kurar ta tashi, tun daga parlour har bedroom suna bude Amma
bana ciki dole Sajjad ya koma ya fadawa Abbie bana nan, abunda ya Kara tada kura kenan
uncle saminu ne yayi tsagal ya Fara fadin to Daman ta Ina ze tsaya yanda yayi wannan abun
kunyar Zina har cikin gida duk wadda ake a waje Bata wadatar ba sai an yiwa yaran cikin gida
fyade.
Nan da Nan Abbie ya Kara tunzira ya shiga fada sunce yayi fadan da Basu tab'a gani yayi ba
Fadi yake wallahi babu shi babu ni ya cireni daga cikin y
'ya'yansa tunda na fita zakka naje ya sallamani gani ga duniyar Nan idan giyar kudi ke rudata
Ina Dan k'aruna yake.
Jin furucin Abbie yasa uncle saminu tarar numfashinsa Yana fadin idan ya tafi ai yaci bulus a
Nemo shi yazo ya aureta dole, idan aka barta a haka ai an zalunceta gaskiya saboda an fita
gata, ai tun faruwar wancan abun nace maka ga Asma'u Nan na bashi Amma lokacin saika
nuna ba haka ba in da anyi Masa Auren Aida hakan Bata faru ba, da ba'ayi maka halin Dan
akuya a gida ba, idan kayi sake sai an Fara shigo da shegu ma cikin gidan Nan.
A cikin hasala momin Kano tacewa uncle saminu haba wace irin magana kake fada haka Bai
Dace ba Dan zumunka meze Hana abi abun a hankali ita safnar yarinya ce karama da za'ayi ta
babatu tayiwa mutane bayanin abinda ya faru Mana. Dan me za'ayi ta dorawa mutum Daya laifi
ita meya kaita part dinsu a irin wannan lokacin ayeh?. Cikin tashin hankali uncle saminun ya taso Mata kamar ze daketa Yana fadin.
To kice da hadin bakinki yake ketawa yaran mutane haddi kenan, Dan munafurci bazaki Bari ayi
Masa hukunci ba tunda Yana kawo Miki abin duniya idan ya lalace Baki da asara Dan kishiya ne
ko?.
Momi Bata barin ta kwana ta zaburo zata gaggaya Masa magana Abbie yayi Mata Karan tsaye,
kofar fita ya nuna Mata alamar ta fice, zata bude baki tayi magana Ammi ta girgiza alamar tayi
shiru kawai.
Ammin ma juyawa tayi zata bar gurin cikin kaushin murya wadda tunda suke Bai tabayi Mata
magana da makamanciyarta ba.
Ki fad'awa danki duk inda ya shiga ya fito yazo Ina nemansa idan Kuma ba haka ba wallahi da
kaina Zan Mika case din Nan human right kinji na rantse.
Yanda Bata tofa ba lokacin da suke babatun yanzun ma wucewa kawai tayi tana jiyo yanda
Abbie din ke kwantarwa da Aunty Sameera murya Yana Bata hakuri ita Kuma tana daga murya,
Batool ma barin gurin tayi.
Hummm previous Ashe kuka Rahama ne bansan haka ba sai a ranar, Dan naso ace Zan iya
yinsa konaji sassuci Amma Ina Idanuna sun soye babu alamar hawaye sai zafin zuciya kawai
nakeyi.
Tunda suka fice daga dakin Nima na zura jallabiya na dauki key nayi waje tunda na fita na rasa
Ina Zan nufa nayi ta yawo a cikin gari har sha biyu da kusan minti arba'in da biyar, Dana gaji da
yawo na shiga wata primary na yiwa Mai gadin gurin bayani Ina son na yada zango ni matafiyi
ne, wallahi haka na kwana ko gyangyadi Bai kamani ba, ban taba tunanin haka akeji idan an
yiwa mutum k'azafi ba sai da yazo kaina, ban taba tunanin Alkhairi Yana Zama mugunta ba sai
a kaina da Safna ban taba hasasota a haka ba ko cikin mafarki, shi yasa hausawa ke fadin idan
kaga mutum a Rana barshi a ranarsa da hikimar da tasa aka aje shi a ranar.
Bayan nayi sallar Asuba gida na nufo ban shiga gurin Ammi ba part din mu na nufa Ina zuwa
dakin naji wani irin tashin hankali kamar lokacin abin yake faruwa, a parlour na zauna Ina
sakawa da kwancewa na rasa tudun dafawa, wurin bakwai da rabi naji ana tab'a kofa ban
motsa ba ban Kuma bada izinin shigowa ba, Faruq ne shida saif kanin Ya Abbas ne suka shigo
Ina Zaune Ina dafe da goshina kaina na matukar Sara min, daga kallon farko da nayi musu ban
sake daga idona na kallesu ba.
Cikin nuna damuwa Faruq ya tambayeni Wai meya faru ne jiya shi Yana barci baisan wainar da
aka Toya ba, Saida Asuba sahal ke fada Masa abinda ya faru, ta tafasa ban iya tofawa ba Dan
bakin cikin dake ci min zuciya haka ya hakura ya tashi amsa Daya na bashi nace masa babu
mutumin da ze iya yi Mana shari'a da duk Mai hannu a cikin Lamarin sai Allah. Wurin goma Kiran Abbie ya riskeni banyi kasa a gwiwa ba na nufi part dinsa, Ina zuwa na samu
Abbie ne da 'yan uwansa sai Safna da Aunty Sameera.
Ina shigowa Safna ta fara share hawaye, Abbie na fara gaishewa Wanda Ni dai da kunnena
banji ya amsa ba, sai su Uncle Mustapha nayi musu gaisuwar Jimla.
Kamar jira ake Ina Zama aka Fara surfa min fada babu ji babu gani, Auncle Mustapha ne kawai
ke supporting dina Yana fadin kowa ya lafa a tambayi ba'asin meya faru ne Amma babu Wanda
ya saurare shi, duk yanda yaso ayi adalci a cikin Lamarin abin ya gagara, Dan har gaban Abbie
mukaje zanyi Masa bayani Amma ya tashi ya bar gurin abinda ke daure min Kai yanda uncle
saminu ya Zama shike bada Umarnin abinda za'ayi Dan yace aure nida Safna babu fashi haka
aka tashi baran baran da uncle Mustapha inda ringa fada Yana fadin an fada musu mutane
jahilai ne a tsaya ayi abinda ya kamata Mana sai a dauki son Rai a Dora ga gaskiya Amma ana
neman taketa da gangan Dan wata manufa ta daban, a gaba uncle Mustapha ya sakani mukaji
wurin Ammi Abu mafi bani tsoro Kinsan kallona Ammi batayi ba duk yanda uncle yayi Mata
bayanin irin nasa hasashena wallahi Sam ta nuna Bata bukatar jin komai daga bakina haka
muka fito Ina rangaji ga Abu goma da ashirin ya tare min inda nake tunanina Zan samu tallafi da
tausaywa sai Kuma na Sami aka sin haka, Bari nayi Miki taku ta Mata a lokacin fa kakana Alhaji
sa'id ya rasu, nasan da Yana Nan abun baze Kai haka ba.
Kiran sallar da aka kwalla shi ya tsayar da Mahmud da dogon labarin da yake bawa zahra,
kallon fuskarta yayi sai ganin hawaye yayi suna bin kuncinta Bai hanata ba ya dai gyara Mata
kwanciya a cikin jikinsa duk da lokacin sallah yayi.
AUREN HUCE HAUSHI.
Maman Fateemah.
09061432339
Or
08055362975
Page 94.
_______ "Pls previous ki daina kukan Mana, abun Nan fa wani past event ne ya Riga ya wuce
kawai dai Ina fada Miki irin Qalubalen Dana fuskanta ne a rayuwa da Kuma irin yanda na koyi
iya mu'amala da jama'a Kinsan masu iya magana na cewa na daka baiyi kallon waje ba, to
Nima hakan ce ta kasance dani da ba'a Sami wannan matsalar ba da wata kila harna koma ga
Allah bazan San wasu abubuwan ba na yanda wasu suke rayuwa, previous na koyi darasin
rayuwa yanda bakina baze iya misalta Miki ba, tashi muyi haramar sallah idan Allah ya kaimu
wani Daren saina karasa Miki sauran labarin dan nasan daga safe har zuwa dare babu lokacin
Zama kinsan Hausawa sai a slow su da gidan Amarya".
Ya fada Yana dariya itama duk da zuciyarta babu Dadi Saida taurmusa.
Tare sukayi wanka ya wuce sallah itama ta Fara nafila kafin a tayar.
Har gari yayi haske Bai shigo ba itama azkar tayi da karatun Qur'an, tana kokarin cire abayar da
tayi sallah ya shigo, a hankali ya tako har inda take tsaye Yana zuwa ya Ida cire Mata Yana
Fadin. "Meya hanaki barci? dubi idanunki barci ne fal a cikinsu da gani".
Dan narke fuska tayi tana Masa wani kallo, dan smile yayi Wanda yake karawa kyakykyawar
fuskarsa kyau.
"Yaya ko da labari? Nasan jirana akeyi ko kuma gaisawa zamuyi ne?".
Kafada ta make irin yanda Yara masu kiwa sukeyi idan suna hannun iyayensu.
"Nifa Karatu nayi fa shi yasa ban kwanta ba gara na rabauta da Alkhairin dake cikin safiyar".
"Gaskiya ne sayyada". Ya fada Yana dariya, itama murmushi tayi, sunyi barci har kusan Sha
biyu sannan suka tashi wanka suka shiga tare sun Jima sannan suka fito suka shirya ita cikin
rigar material data Sha beads work shi Kuma cikin shada geezner boda style sai baza
kanshinsu suke yi. Lokacin da suka sauko su Aunty zilai suna kitchen ita da binta suna girkin
rana, fitowa sukayi suka gaisa sannan suka koma bakin aikinsu, bayan sun Gama break din ne
suka dawo second parlour inda Mahmud ya dauki remote control ya canza Tasha daga
Tauraruwa zuwa sport news inda ake highlight na kwallayen da akayi. Kasa hakuri Zahra tayi ta
jefa Masa tambayar da take ci Mata tuwo a kwarya. "Meu Amor Wai Dan Allah me kikeji idan kana kallon Ball din Nan?".
Dan kwantar da kansa yayi a gefen kafadarta Yana shaqar kamshinta Wanda yake sakar Masa
da kasala.
"Yanda kukeji idan Kuma kallon series ko Kuna karanta novels Dan nasan daidaikun mata ne
basa wannan sana'ar, Dan Batool har kwace wayarta na Sha yi lokacin tana secondary, to
muma haka muke Jin Ball a cikin ran mu".
Jin jina Kai Zahra tayi tana farin "Na gane yanzu kam, ai karatun novel duniya ne Dan Idan book
ya dauko Dadi wallahi bana kaunar abinda ze tasheni daga karatun".
Wata sinsina ya yiwa wuyanta tare da hura Mata iska ba kunne, hade jikinta tayi tana nuna
Masa bangaren kitchen da Hannu.
Ido Daya ya kashe Mata. To Nima hakan nake Jin kwatankwacinsa akan Ball din".
Sun jima a gurin suna Hira har aka Gama labaran Ball din. Baki ne suka Fara zuwa danginsu na
Dangen shuni Mama Bilkisu ce tazo Bata k'asar akayi bikin nasa, da gani sunyi saboda dashi
sosai har yaranta, mace 'yar gayu ta ajin karshe ga sakin fuska Dan kamar ta goya Zahra sai
fadin Masha Allah takeyi Nan da Nan aka cika gabansu da Kayan tarbar Baki Dan Aunty zilai
expert ce a wanna fannin.
A cikin hirar da sukeyi ne Zahra ta gane suna k'asar Canada Latin America ita da yaranta inda
mijinta yake ambassadorn Nigeria, Mahmud Bai samu fita ba sai lokacin sallar Azzuhar sannan
ya samu ya shiga gari can family house nasu, Nan suka yini da Mama Bilkisu mace ce wadda
tasan kanta Dan Mahmud na fita bayan sunyi sallah sunyi lunch taja zahra bedroom dinsu na
kasa ta zaunar da ita ta ringa koya Mata dabarun yanda zata rike mijinta ita wani abun idan ta
fada sai kunya ta rufe zahrar ita kuwa babu ruwanta sai dai tace ki dai Kade kunne ki kwashe a
gaba ze amfane ki, sai kusan magariba suka tafi Zahra ta saka Aunty zilai ta hada musu Kayan
biki masu yawa sannan ta bawa 'yan matanta designers din turarika da Dubai abaya tunda
kamar gorinsu akayi a gurin kayansu, da kyar Mama Bilkisu ta yarda suka karbi Kayan Dan fur
cewa tayi sunyi yawa sai an rage Saida Aunty zilai ta saka Baki ta barsu suka karba.
A nan falon sukaci gaba da Zama suna hira sai lokacin magariba su Aunty zilai suka wuce part
din su ita Kuma Zahra ta koma sama, har akayi insha'i Mahmud Bai shigo ba, Zahra na Zaune
ta tsula gayunta cikin English wears maroon Mai duhu tayi rolling da farin veil touching din dake
jikin coat din sama ta saka maroon din lipstick a Dan bakinta Sai tayi wanu irin kyau kamar ka
dauke ba b'oye tana fesa turare wayarta ta dauki kida Mai dadi da sauri ta nufi wayar Kiran na
magaji ne, tunda ringtone dinsa shima daban.
Sallama tayi Masa Bai Sami damar Amsa sallamar ba ya Fara fadin.
"Allah ya sauwak'e wallahi idan mutum neman taimakon emergency yake a gurinki Allah Saiya
mutu, bakiga missed calls dina ba sun kai dari ina ga, tunda zafin abun nake nemanki Amma ba
amsa na Kira oga yace min tun Rana baya gida haba ki daina nesa da waya ai abokiyar Hira ce
ko Dan kina tare da Aunty zilai ai kin Gama samun abokiyar hira". Katse Masa zubar da yake tayi.
"Haba Dan Allah ayi mutum idan ya Fara magana ba comma ba Full stop. Ka fito a mutum sak
ka fada min abinda zaka fada ba kayi ta Jan dogon labari ba".
"To yau dai ana idar da sallar la'sar Abba ya rangada daurin Auren Salma da Hameeda Dan
yanzu haka Salma har sun dira a Miya, can Aka kaita wani tsohon saurayinta ne Ma'aikacin
Nefa da yake yawan zuwa gaida Abba kusan duk sati duk da basa tare da ita shine yazo jiya
suna bin gidaje raba bill din wuta, Abban yayi Masa tayin Auren salmar Amma fa Saida ya fada
Masa gaskiya idan ze iya yace babu komai Yana so a haka. Yaje ya fad'awa magabatansa,
daman an fadawa gidansu mai son Hameeda suzo da sadaki shine ya daura musu Auren yau
yace a tafi da Salma gobe kayanta zasu biyota, taimakon da Allah yayi Mata Abba ya Basu gida
a can Miya din tunda yana da gidajen haya a garin kuma kwanaki akayi modernizing dinsu. Ita
Hameeda ce