Showing 39001 words to 42000 words out of 62795 words
Chapter 14 - Auren Huce Haushi Book 3 Complete By arewahausanovels.com.ng.pdf
duk da itace karama a cikin matan da aka Auro. Lokacin da cikin yakai wata Tara iyayenta sunso ta koma gida kontagora ta haihu Amma sa'id
ya shafawa idnunsa toka ya Hana yace sai dai a turo wadda zata zauna da ita Sai hakan akayi,
cikin Rahama ta Ubangiji kafin a kaiga turo kowa cikin Daren wata litinin nakuda ta kamata kafin
ya kaiga fad'awa kowa Allah ya sauketa lafiya ta haifi yaronta namiji murna ba magana murna
gurin sa'id Kamar me haka mahaifinsa da sauran dangi wadanda suke kaunarsa,'yan uwan
Hadiza sunzo ranar suna yaron yaci suna Muhammad Auwal sai ake ce Masa mahummad
kawai.
Tun daga Nan haihuwa ta budewa Hadiza ta haifi Maimunatu sai Mustapha, Saminu, tana
goyon saminu ne Allah ya yiwa mahaifinsu sa'id Alhaji Jibrin rasuwa sa'id.yayi kuka Kamar ba
gobe Amma dole aka dangana, bayan anyi arba"in akayi rabon gado kowa aka bashi nasa
rabon sa'id yaso su hada kasuwanci da 'yan uwansa Amma sai mahaifiyarsu tayi tsalle ta dire
tace cutarsu zeyi tunda yafisu sanin Kan kasuwa kowa yaje ya juya nasa tunda kowa Yana da
nasa nasibin, dole ya hakura sai Kuma zaman lafiya yayi kaura daga cikin family din Koda
yaushe cikin tashin hankali ake ga an tsangwani yaran Hadiza saboda duk cikinsu babu masu
nagartar 'ya'yan ta kyawawane sosai, ganin zumunci Yana neman ya lalace yasa kanin
mahaifiyar sa'id dake sokoto ma'ikacin gidan ruwa ne har yakai matsayin baturen ruwa na jaha
gaba Daya yace ya taso daga dangen ya dawo sokoto hakan akayi sa'id ya bada kudi aka saya
Masa gida Mai kyau da tsari tunda lokacin harkar petrol ta bude sosai harya mallaki gidajen Mai
kusan uku a cikin kwaryar sokoto.
Bai fadawa kowa halin da ake ciki ba sai ranar da zasu bar garin, ba wani damuwa 'yan uwan
suka nuna ba ya tattaro Kan iyalinsa suka dawo sokoto, anan yaransu sukaci gaba da zuwa
makaranta, bayan an yaye saminu aka haifi Aliyu sai Kuma haihuwar ta tsaya, kafin shekara
biyar arzikin sa'id ya habaka sosai Dan Nan da Nan sunansa yayi fice a sokoto ga taimako har
'yan uwansa Bai ragesu ba duk da kowa da nasa rufin asirin, makarantar sojoji aka Kai
Muhammad tunda Daman shine ra'ayinsa da taimakon kawun mahaifinsa Allah yasa aka samu
a kaduna, Maimunatu Nan kwatarkwashi aka kaita boarding itama sannu a hankali rayuwa na
juyawa har Muhammad ya Gama makarantar sojoji lokaci tuni Maimunatu ta Gama secondary
dinta ta shiga poly har da maganar Aurenta a gida, shi Kuma Muhammad ya tafi wata
makarantar ta sojojin a Jos.
Su Mustapha da saminu da Auta Aliyu kowa Yana nasa karatun.
Lokacin da akayi bikin Maimunatu Muhammad baya Nan ya tafi wani course America, a can
Allah ya hada shi da Mr Johnson baturen ingila kuma masanin sirrin kasuwanci sun hadu dashi
ne ta dalilin kanwarsa wadda suke course din tare Anita sunyi sabo sosai da ita tana da kirki
yawanci tana tambayar Muhammad abinda ya shige Mata duhu, ta dalilin Mr Johnson
Muhammad ya Fara business da kudin da suke samu tunda basu zauna a banza ba idan suka
Gama bunda zasuyi suna fita suyi aiki Wanda ake biyan mutum par hours.
Da taimakon Mr Johnson din Muhammad ya Fara turowa Dan uwansa Mustapha Kaya idan yayi
order sai ya turo Nigeria Kuma cikin Rahama ta Ubangiji Kayan masu da an kawo sai masu sari
su sayen ga mahaifinsu ma Yana Kara koyawa Mustapha dabarun kasuwa kafin wani lokacin
jarin yayi karfi na ban mamaki abinda yaso ya kawo sabani Kennan tsakanin saminu da
Mustapha Dan karara saminu ke nuna Jin zafinsa akan zabar Mustapha da Muhammad yayi ya
Dora akan kasuwarsa, Saida Hajiya inna sunan da wani yaron makotansu ya saka mata tayi
Jan Ido da fada na tashin hankali sannan abun ya lafa, Dan yanda saminu ke nunawa 'yan
uwansa tamkar 'yan uba.
Haka akayi ta juyawa har lokacin dasu Muhammad suka dawo lokacin tuni Maimunatu ta haihu
yaronta Tahir har Yana yawonsa ko ina, Basu Dade da dawowa ba akayi masa posting Calabar
cross river State da matsayi Mai girma, abinda ya tilasta ya tashi neman Aure kenan tunda
Daman akwai wata yarinya 'yar makotansu da suke soyaya da ita Ammaratu yaso ta sosai sai
dai lokacin da yake kokarin tafiya course dinsa mahaifinta yayi maganar Aure sai aka fada
Masa ga inda zaya shi Kuma yace yarinyarsa ta Isa munzalin Aure, abinda ya Hana Auren
kenan a wancen lokacin, akayi Mata auren da wani, abun bai kai ko Ina ba ya lalace Wai mijin
yace Bata da lafiya dole aka raba Auren, to dawowar Muhammad suka Kara hadewa duk da Da
farko Hajiya Inna taso ta Hana Amma Alhaji sa'id ya nuna Mata tayi hakuri ba'asan abinda Allah
ya hukunta a tsakaninsu ba, idan da Rai a gaba Saiya auri budurwar, ba'a dauki lokaci ba aka
Sha bikin Muhammad da Ammaratu suka tattara suka wuce calabar, yayi mamaki yanda ya
tarar da ita budurwa tunda yasan tayi Aure sai lokaci ta bashi labarin ai Bata tab'a yarda da
mijin ba shine yace baze iya ba Bata da lafiya.
Cikin ikon Allah wata buyi da aurensu ciki ya bullo a jikin Ammaratu zokiga murna gurin
Muhammad, namiji ta Haifa yaci sunnan Abdullahi, sai Ramlatu sai Habiba, Ibrahim tana
goyonsa suka dawo kaduna lokacin Yana da mukamin canal, daga gefe Kuma kasuwanci yayi
wani irin karfi. A kaduna Allah ya hada Abbie da momin Kano 'yar sarautar Kano ce, hutu taje gurin yayanta
Allah ya hada su babu Bata lokaci iyaye suka shiga Hajiya Ammaratu tayi tashin hankali Kamar
ba gobe dalilin da yasa ta koma sokoto da Zama kenan.
Amarya ta Fara tarewa a sokoto kafin su wuce kaduna, itama da Albarkar haihuwa tazo ta haifi
ummu Salma da Jamila, tana goyon Jamila wani aiki ya taso na kasa da kasa lokacin yaki ya
barke da 'yan tawayen MALI Abbie ne ya jagoranci tawagar sojojin Nigeria zuwa malin.
Sun dauki wata da watanni suna fafata yaki da 'yan tawayen kafin a karya lagonsu duk da
tallafin da suke samu na makamai daga wasu kasashen duniya, ana murna anci galaba sai
Kuma suka bulla wani bangare ba na yankin Agadas ta jamhuriyar Niger Daman Suma ana
fama da 'yan tawayen Abzinawa. Dole aka nemi Karin sojoji daga kasashen ecowas aka kara turawa arewacin Niger din, a
lokacin ne Abbie ya koma Niger aka Kai wani can MALI din.
Cikin ikon Allah suka dakile 'yan tawayen, wata rana suka fita zasuje wani kauyen buzaye
sayen Kayan dafa shayi, suna cikin tafiya Hilux dinsu ta samu matsala gashi babu gari a kusa
sun fito sunyi cirko-cirko sun rasa abun yi gashi babu order order a tare dasu, sunan a tsaye
suka ringa jiyo qugin injin mota ba'a Dade ba motar ta nufosu su Abbie suka Zama cikin Shirin
Kota kwana tunda guri ne da babu tsaro ganin sojoji yasa masu motar suka rage gudun
motarsu maza ne guda biyu a gaba da alamar uba da d'a ne sai Mata biyu a baya babbar mace
sai yarinya budurwa Mai wani irin kyau Mai fisgar hankali a kusa da ita, suna tsaywa Abbie ya
karasa ya gaishe da Babban mutumin, sannan suka gaisa da Dan nasa anan yake tambayar
meya faru da motar? Bayani yayi masa na Suma Basu San abinda yake faruwa ba kawai sun
fito ne zasu shiga kauyen dake gabansu sayen Kayan shayi shine motar ta samu matsala. Dansa Daya Kira ishai ya umarta daya fita su daura igiyar jan mota su fitar dasu daga wannan
gurin Mai hadari.
Gurin window din da Hajiyar ke Zaune Abbie ya Dan leka ya gaishe da Hajiyar ya dago idonsa
ze juya caraf suka sarke Dana yarinyar dake kusa da ita, da sauri ta juyar da fuskarta Dan ji tayi
zuciyar ta kamar zata fito Dan dokawar da takeyi. Ba zato taji mahaifiayarta na fadin "wani irin
sakarcine haka zainab kina ganin yaro yazo ya gaishe mu ke ki kasa gaishe shi?" Shi dai gaba yayi Bai tsaya yaji me zata fada ba Dan kusan Abu iri Daya sukaji lokacin da suka
hada a idon.
Basu tsaya a kauyen ba dole suke wuce cikin birni inda a Nan ne za'ayi musu gyaran,Abu
kamar Wasa aiki ya Zama Babba dole sukayi waye can camp dinsu kada hankali ya tashi. A
gidansa na wannan garin inda ya kasance mahaifarsa Alhaji Haroon ya sauke su da abinci da
gurin kwana Mai Rai da lafiya, lokacin Yana ambassadorn Niger a k'asar Rasha sunzo hutun
karshen shekara ne suka baro Yamai suka shigo gaishe da dangi Allah ya hadasu, sunga
karamci da kyautatawa mutane ne masu karki kamar me, Ishaq a gurinsa ya zauna suna ta Hira
a Nan yasa su 'yan Nigeria ne, zainab da wata yarinya suka shigo musu da kayyayakin abinci,
tunda ta shigo Abbie keta binta da kallo ita Kuma taqi yarda ta dago saboda taji yanda idanunsa
suka yawo a jikinta, serving dinsu zata Fara Abbie yace ta Bari suje kawai saboda yaga yanda
abokanen tafiyarsa biyun suke kallonta duk sai yaji ya damu,washe gari ma su suka kawo musu
break fast sai kusan goma na Rana sannan masu gyaran suka kawo motar har gida,sunyiwa
Alhaji Haroon godiya sosai Dan hanawa yayi su biya ko sisi na gyara sannan yasa akayi musu
fulltank na petrol a motar.
Har ciki suka shiga suka gaishe da Hajiyar sun taso zasu tafi Hajjar ta Kira zainab tace tazo suyi
sallama Kamar zata fasa kuka ta fito tana sadda Kai kasa da gaske mutumin Nan dodonta ne,
daga gefe ta Dan tsuguna tana gaishe su.
Ya ishai ne ya dubeta Yana fadin kunyarwa takeji da take sadda Kai kasa kamar tana gaban
sirikinta.
A haka su Abbie suka fice a waje sukayi musanyar number da Ishaq sannan ya karbi ta Alhaji
Haroon Wanda suke Kira Abu.
Har suka koma sansaninsu Abbie na makale da tunanin zainab haka yayi ta fama da ita a cikin
zuciyarsa har tsawon kwana uku Amma Kullum sai sunyi waya da Ishaq da Alhaji Haroon
Ambassador a ranar cikon na hudu ne ya kasa daurewa ya dauko mota da ordily dinsa Daya
suka biyo Sahara zuwa cikin gari. Sam Alhajin Haroon baiyi mamakin ganin Muhammad ba Dan yasa da walakin goro Miya yanda
yake kiransa da yanda yake tambayar su zainab yasa da wata a kasa, Yana zuwa baiya
kwauron Baki ba ya fito da bukatarsa ta son Auren zainab inda Kuma ya fad'awa Abu shi Mai
iyali ne har buyi a fada Mata idan ta amince zata iya aurensa a haka, Basu bar garinba Saida
magana Mai karfi Dan ana tambayar zainab din ta rufe fuska, dariya Hajja tayi tasan za'a rina ita
tun ranar da suka hadu a Sahara tasan akwai abinda Allah ya hada Dan taga yanda
kowannensu ya nuna da suka had a Ido to abinne na zamani baka zakewa.
Cikin Kankanin lokaci sukayi wata irin shakuwa ta ban mamaki tamkar sun shekara suna
soyayya sai yaji tamkar Bai tab'a son wata 'ya mace ba a rayuwarsa Dan yanda yake Jin zainab
daban ne da yanda yaji a matansa na baya, kafin wani lokaci zainab sunyi sabo da Hajiya Inna
ta waya Kuma kusan kowa a cikin family yasan Muhammad Dange zeyi Aure a Niger Dan tuni
manya sun shiga maganar babu Bata lokaci akayi biki Daman ta hada karatunta tun shekarar
data wuce, Shima suka dawo gida tunda an samu kwanciyar hankali a yankin da ake fama da
tarzomar.
A lokacin ne Abbie ya Gama katafaren gidansa da Kuma wadan da ya ginawa 'yan uwansa duk
da kowa ya Kama kasa a lokacin Amma samun ba Daya bane, da yawa Yan uwan Babansu
Wanda suke uba Daya sun dawo sokoto kowa Kuma Allah ya saka Masa Albarka a cikin
nemansa sai dai sa'id da yaransa sun Zama zakarun gwajin dafi a cikin Families din Dan babu
Hadi ko alama tazarar da nisa tamkar Dangote a cikin zuri'ar Alasawan koki ta Kano haka
misalin yake a zuri'ar DANGE da iyalan Alhaji sa'id din.
A lokacin Abbie ya dawo gida sokoto da aiki shine musabbabin da momin Kano ta dawo
sokoton itama duk abin Jin dadin rayuwa an tanada a gidansa Nan Dan ko daga waje kalli gidan
ka Kara kallon komai na furnitures ya zuba Amma dole yasa aka cire wasu Dan iyayen zainab
sunce sai sun Mata nasu jeren an kawo Kaya na garari Wanda suka tada hankalin kishiyoyinta
da farko ce musu akayi irin 'ya'yan buzayen Nan ne masu yawo suna neman sadaka ya gani a
sansaninsu 'yan gudun hijira,Amma ganinta da 'yan uwan ta da irin dukiyar da aka Zubar sai
Kuma jiki yayi sanyi Baki ya mutu tanadin wulakancin da akayi tanadi za'ayi ya kau.
Zamane aka Zubar na kishin mimmuge ba fada a zahiri Amma akwai 'yar kasa daga gurin
babbar gidan wanda da wuya mutum ya gane lokaci daya, gashi Hajiya Inna da Alhaji sun dauki
son duniya sun dorawa zainab, Shima Mai gidan wanda take Kira da general yake Mata wani
mahaukacin so Wanda baya iya boyewa a gaban kowa gashi tayiwa sauran zarra a gurin komai
na auratayya sai abun ya Zama biyu.
Ba laifi sunyi amarci sosai Dan Saida ta dauki kusan wata shida suna cin amarci sannan ciki ya
bullo Mai wata irin fitinar son kasancewa da miji dole tasa ya dauketa ya tafi da ita wani course
da zaya a South Africa abinda yaso ya tada hankali a gidan sai da yayi Jan Ido da kurarin duk
wadda bazata zauna ba kofa a bude take sannan aka Samu zaman lafiya. Ya fada Yana Dan Jan tsinin hancin Zahra "kinji yanda Muke muna ciki dan haka dole ki shirya
tunda ba rago Kika aura ba tin a ciki ya Sami energy kinsan duk Inna tawa ta bani labarin nan?".
Rike Baki Zahra tayi "har wannan Kuma?." "A'a ba direct ta fada min ba fa cewa tayi Wai cikin
rashin hakuri ya sakata, Saida na tambayi Hajiyar makwarari ta fada min kinsanta ita handsfree
ce"..
Kina ji Saida sukayi wata uku suka dawo lokacin cikin watansa shida kuma tun a can a asibitin
da take zuwa ante-natal clinic suka fada Mata twins ne mace da namiji Amma Tayi shiru ko Mai
abun Bata fad'awa ba saboda abune cikin duhu kada ta fada yazo Kuma a samu akasin hakan,
lokacin da suka dawo suka samu momin Kano ma tana fama da nata laulayin ciki wata ukau a
watan da suka wuce ta Sami nata itama.
A Nan sokoton ma sun fada mata, da watan haihuwa ya Kama Hajiya Inna da kanta tazo ta
saka zainab gaba lokacin baya Nan yaje wani aiki Lagos ai kuwa kwana biya da daukarta cikin
dare nakuda ta tashi suka garzaya asibiti a cikin ikon Allah kafin asuba ta haifi yaranta biyu
murna gurin Hajiya Inna Kamar ba'a tab'a haihuwa a gidanta ba, kafin gari yayi haske suka
koma gida kafin wani lokaci gida ya cika da jama'a bare da abun shima uban gayyar yasha
mamaki da Inna tace masa Yara biyu ne Sam cikin beyi wani girman azo a gani ba.
Ranar suna anyi hidima 'yan Niger sunzo tamkar a Niger mai jegon take yaran sunci sunan
Aishat da Mahmud, sun Sami Alheri Kamar me Hajiya Inna ta Hana su Hajja zuwaira su tafi da
zainab gida dole suka hakura suka tafi ita Kuma taci gaba da wanka a gidan innar har tsawon
wata biyu,Saida Alhajin ya gaji yace Mata Wai bazaki mayar Masa da matarsa ba sai hakurinsa
ya Kare kice yayi rashin kunya, ke ba bahaushiya bace ko wannan cika daren da yakeyi a gidan
nan Bai isheki ki gane matarsa yake So ki bashi ba,dubi fa tamkar baya da wasu matan.
Inna Bata jaba tayi Mata abinda ya kamata ta mayar da ita.
Ranar data koma suka Bata girkinta Amma Saida Inna ta karo Mata da yarinya bayan masu
aikinta.
Kafin wani lokaci yaran sunyi bulbul sunyi kyau Kamar ba twins ba, suna wata hudu momin
Kano ta haifi Faruq .
Haka haihuwa ta budewa Ammi tayi gambon 'yan biyu Khadija Mai suna Inna ana ce Mata Nur
wadda ke Aure a Germany wadda kukayi waya jiya tana kukan ba'a fada Mata ba Dan tana da
tsohon ciki.
Sai Baool da suhailat kin sansu sai su Jamal da Auwam suna london secondary.
Mu dawo baya lokaci da za'a yaye mu Hajja ta dauke mu duka badan Inna taso ba ta hakura,
da kyar Aishat tayi sati hudu aka dawo da ita saboda kuka takin cin abinci Kuma, Ni kuma naci
gaba da Zama a can har na Kai minzalin sakawa a makaranta Abbie yaso na dawo Amma
Alhaji Haroon ya Hana yace in dai makaranta ce za'a sakani wadda suke yin turancin ingila
hakan Kuma akayi ban baro Niger ba Saida Zan tafi junior secondary school inda aka kaimu
Nigerian Turkish a Abuja nida Aisha da Faruq.
A can na hadu da Sameer ajinmu Daya da farko fada mukayi dashi sai Kuma rashin lafiya ta
kamani shi da Faruq sukayi jiyyata a sickbay, tun daga lokacin Kuma muka dinke dashi,sai
lokacin muka Kara shakuwa da Faruq mutane suyi ta mamaki idan Yana ce min yaya Mahmud
sabida suna ganin ya fini garin jiki ma. Har muka Gama secondary muna tare da Sameer, lokacin da muka dawo gida gaba daya mun
Gama makaranta lokacin muka Sami Abbie ya Kara Aure ya cike ta hudu, mace ce wayayya
Aunty Sameera 'yar Minna ce Niger state bazawara ce da yaranta biyu na mijin baya Wanda ya
rasu, sai kanwarta Sakina wadda ake Kira da Safna, lokacin bazata fi shekara Sha uku ba haka
yarinya ce Mai saurin sabo Dan bamu fi sati biyu da dawowa ba muka shaku da ita sosai
tamkar mun shekara Bata jin nauyin fada min komai saima Ina kwabarta gata da son kashe kudi
Nan da Nan zata rokeni kudi, banajin komai saboda kirki Aunty Sameera Amma Ina ganin
bekenta gurin tarbiyya gaskiya saboda ita'yar social life