Showing 48001 words to 51000 words out of 62795 words
Chapter 17 - Auren Huce Haushi Book 3 Complete By arewahausanovels.com.ng.pdf
aka bashi hakuri zuwa wani satin ta tare tunda mijin baya Nan Yana kaduna gurin
aiki, to kinji fa abinda Zan fesa Miki kike min surutu, yanzu haka Ammah dasu Aunty Hassana
da Hajiya Turan gidan maji dadi suna can, ki Bari kawai saina shigo da labari wallahi buhu-buhu
Zan shigo in zazzage Miki su ai anyi dai abun kunya wallahi Ashe duk lullubin biri aje yiwa
mutane ai Ni Ya Mahmud ya Gama min komai kindsan bibiyar Salma yasa akeyi Masa Ina gida
jiya ya kirani yace min sunyi magana da Abba Zan raka bilyan gidan malam Jos, Ashe asibitin
da aka kwantar da Salma ya tura ya daukota Ni Kuma da nasan gari nayi masa jagora wallahi
sanda ya kirani ya bani address din asibitin Nasha mamakin me zamuyo wannan asibitin
ke........"
Wayar taji an zare daga kunnenta da sauri ta juya Dan kamshinsa ya fada Mata shine Amma
koda Wasa bataji sanda ya shigo ba.
Wayar ya duba yaga magaji ne kunnensa ya Kai wayar Yana fadin "ka Adana sauran
bayaninka zuwa safe".
Ai kafin ya Gama fada Magani ya kashe Kiran Yana rike bakin Al'ajabin Zahra Daman Yana Nan
ya zage yana ta an tayo magana. Wayar ya aje yadan matsa baya Yana Kare Mata kallon ta
burge shi matuk'a Dan ji yayi kamar ya sakata gaba yayi ta kallo, hannuwa ya bude Mata
alamar ta shigo ya rungumeta, sun Jima a tsaye Saida yaji kamar kafafuwansa Bazasu iya
daukarsa ba sannan ya Dan zameta suka zauna a gefen gadon, da kyar ya tashi ya shiga
wanka Bai wani Dade ba ya fito ya saka Riga armless da wandonta three quater na Adidas dai
tunda sune best kamfaninsa gurin sport wears, tana makake a jikinsa suka fito parlourn farko na
sama In da aka aje musu dinner dinsu, sakwara ce da miyar Agushi sai black tea Mai Kayan
hadin star anise a ciki, Saida sukaci abincin sannan suka dawo cikin parlour na biyu suka zauna
duk ya kanainaye ta ya hanata sakat, nema yake ya ruda Mata lissafi ita Kuma Alla Alla take
dare yayi ya karasa Mata labarinsa.
Saida ya mila ya mile Dan kansa ya Dan ragewa kansa zafi sannan ya fara fadin "Bari muci
gaba ko" Kai ta gyada Masa Dan ita kam ba baka sai kunne.
"Wato precious Naga gararin rayuwa kowa fa juya min baya yayi babu Mai saurarena sai uncle
Mustapha da Batool kawai, abin baqin cikin Wai a tsaya nayi bayani ma abun ya faskara ta ko
Ina babu sauki a haka Muka kwana uku idan Kika ganni lokacin Zaki tausaya min a lokacin
dukiya ta dai batayi min amfanin ba tunda Bata Hana an wulakqanta ba, a ranar na hudun na
tsunci maganar Wai a ranar za'a daura mini Aure da Safna abunda ya yamutsa min lissafi
kenan cikin tashin hankali na shiga wurin Ammi wallahi precious Ina shiga Ammi ta Mike tabar
parlourn da sauri nabi bayanta Ina hadata da Allah akan ta tsaya taji gaskiyar abinda ya faru
Amma kinsan me tace min?
Wai fa cewa tayi inje inyi abinda nake so tunda karana yakai tsaiko gani ga rayuwar Nan tunda
fasadi na zaba duniya tafi Dan bagaruwa jima, wallahi a lokacin ji nayi kamar na mutu na huta
nakeji,ga wani irin Abu da nake jinsa a jikina, precious wallahi Addu'oin da nake na azkar
lokacin da kyar nake yinsu,Dana fito mabera na nufa naje yau dai na fada mata halin Dana
tsinci kaina a ciki tunda nasan Bata San wainar da ake toyawa ba, Amma kinsan abun mamakin
da tashin hankali itama sammankal duk abun iri Daya ya Zama Bata saurareni ba karshe ma
maganganu ta yarfa min masu zafi ga shi Daman wani Abu na min sukuwar sallah a cikin kaina,
Nan da Nan naji wani bacin Raina ya qaru ban baro gidan ba Saida naci alwashin saina Bata
mamaki kuma kozan mutu saina nemoki duk inda kike a duniya Kuma a dakinta a gadonta Zan
Fara saninki 'ya mace, kadafa kice Wai bani da masaniyar inda kike hummmm a'a ana bibiyar
min ke ciki da waje, kinga lokacin Dana fito daga parlourn Hajiya Inna ko takalmi kafata babu
banbi takan motar Dana shigo ba na Fara tafiya a kasa wani Abu Daya bani mamaki a lokacin
precious wallahi Ina ganin kamar mutane basa ganina tunda konaje kusa da mutane bana ganin
alamar sun San da mutum a kusa dasu gani ba boyayyan mutum ba, haka na dosa wata irin
tafiya tamkar kad'ani akeyi kuma tafiyar wata iri ce Mai cin dogon zango a cikin lokaci k'alilan a
cikin abinda Bai wuce minti arba'in ba ni dai sai ganina nayi a talatar mafara na fuskanci mutane
suna ganina a lokacin Tunda Ina wuce Ina Jin ana fadar bawan Allah ko daga Ina? haka na
dinga tafiya wlh ko gajiya banayi Dana baro cikin gari naji kamar Ina Jin barci na kwanta a wurin
wata bishiya, to Ni dai daga lokacin bansan kuma Yaya akayi ba ni dai nasan na farka na ganni
a asibiti ta tare da Abubakar wlh nayi zaton ko sokoto na dawo sai Kuma Naga bakin fuska su
Malam Abu mafi daure Kai ganin Abbanku da nayi sai Lamarin yafi karfin Dan karamin tunanina
na wancen lokacin Dan nasan wannan abun wani connection ne daga Allah Daya hadani dasu
yasan abinda nake rokonsa dare da Rana, precious nayi dawafi a dakin Allah na Kai mutane
suyi min Addu'a akan wani Abu da nake nema duk a kanki Dan Ubangijina kadai yasan yanda
ya jarabci wannan zuciyar da soyayarki tun Baki San meye soyayyar bs, Kinsan Kuma shi maji
rokon bayinsa ne Kuma mafi tausayin masu tausayi mafi jinqan masu jinkai Naga Ijaba, bana
inkari da lamarinsa Amma na Kara samun yakin Dan Rahamarsa ce ta lullubeni ya kawo Habib
ya ganni a wancen lokacin, ga wata sabuwa Ina Jin maganar mutane Amma Ni Kuma bana iya
magana, lokacin na shiga tashin hankali ba kadan ba Dan ji nayi na koma mutummutumi, asibiti
sunyi iya abinda zasu iya suka sallameni Baba malam da Abban ki su suka dunga Fadi tashi
akan lafiyata Dan abun babu dadin ji na shiga wata irin rayuwa lokacin na Kara gane
mahimmancin lafiya da tasirin Addu'a, su Habib su sukayi jiyyata a dakin soro na gidan malam
har Allah ya bani lafiya, lokacin ne Abubakar ya fada min ai aikin da yake komai na tafiya dai
dai, dan dai lokacin kina syprus to Nima ganin nesa tazo kusa saina nemi gurin Zama naje
Bauchi nayi duk abinda ya kamata akan layikan waya da dasu system da credit card na bank da
duk abinda ya kamata banyi kasa a gwiwa ba na Kira Sameer da Bilyaminu muka zauna dasu a
dakin Dana Kama a hotel, Abu na farko Dana Fara shine kad'a musu warning akan inda nake
kada naji kada na gani duk da Sameer ya fada min hankali fa ya tashi na barina gida gashi
uncle saminu ya assasa daura min Aure da Safna, banji komai ba nasan suda ganina ba Nan
kusa ba ko zan waiwayesu ba lokacin ba, aiki na bawa Sameer na Nemo ma'aikatan wata ngo's
suzo mu zauna Ina son muyi aiki dasu a zahiri Amma ba sune zasu ringa harkar kudi ba, kinsan
k'asar mu indai Zaki bada budi to kome kike nema kin samu Nan da Nan suka shigo muka Fara
aiki Ni Ina gefe Sameer ne oga, ba Saina Baki labari ba Kinga yanda makarantar Baba malam
ta Zama, ke kuma a can syprus din bamu barki sakaka ba sai Dana tura Omer ya shiga jikinki a
can ya Zama idanuna ya Kuma yi Miki tayin soyayya sai akayi Dace kince Masa a'a sai dai kuna
mutuncin da ta Kai ko siyyaya kikayi shi yake biya koba haka bane? Kuma 'yan Nigeria sai ake
Baku wasu kudin scholarship daga wata kungiya MMD anyi haka? Ke naki yana ninka na
sauran kunyi bincike kun rasa gano meyasa hakan yake faruwa haka ne? Kai kawai Zahra ta
gyada Masa Dan ya kasheta da mamakinsa, cheeks dinta ya shafa a hankali Yana Mata smile
har dimful dinsa ya Dan lotsa kadan Kinsan Allah da ban Aureki ba ina ga hummm.... Allah dai
ya kyauta da dai Kam.. za'a Sami matsala Dan inaga maza biyu Zaki aura Dan Ni dai bazan
hakura ba to sai Ubangijin Daya dasa soyayarki a zuciyar ya ta kaita al'amuran, Kinsan Muneeb
Dan yayar mummy Badi"a ne?".
Wani kallon warrr tayi Masa na nuna mamaki, ban gane ba kasan shi kenan?.
Bar wannan maganar ta wuce sirrina ne bazakiji yanda aka haihu a ragaya ba, Sameer ne ya
Zama Dan leken asirina duk yanda kaso aji wani Abu Sameer yaki fadin komai shima nunawa
yake Yana zuwa ne Koda hasken da ake samu a Kan tafiyar tawa, Kuma duk abinda nake yiwa
Hajiya Inna nace ya Dora Dan a Dan tsakanin jininta Saida yayi mahaukacin Hawa har Egypt
sukaje da Uncle Mustapha da Mama mainuna surukar Aishat Ina da masaniyar komai Dan hatta
bill dinsu na Asibitin Ina daga can nayi komai abinda ya darsa zargin Sameer yasan inda nake
a zuciyar uncle Mustapha.
Sameer ne ya kawo min labarin Ashe lokacin Dana bar gida Batool rikicewa tayi a gidan ta
Hana kowa zaman lafiya ta Fadi duk abinda ya faru a Ranar da lokacin Dana kawo musu Kaya
da lokacin da aka Fara fitinar sai lokacin Sajjad ma yayi bayanin shima abinda ya sani, Kuma
aka shiga bincike har gurin securities Suma maganar iri Daya ce data batool sai lokacin mutane
suka Fara dawowa cikin hayyacinsu aka shiga tuhumar Safna da tambayoyi na hankali Wanda
ya kamata ace tun Ina Nan akayi su, inda ta kafe kaida fata ita maganarta babu canji, Kamar
batool ta hakura Ashe gidan uncle Mustapha yaje ta nemi ya shige Mata gaba tana son aiwatar
da wani aiki, baiki ba yace ta fada masa menene? A nutse tayi Masa bayanin kamfanin waya na
MTN da AIRTEL ze rakata zata bada aiki duk da zata iya amfani da sunan family din ko ID card
dinta na dalibar koyon aikin shari'a Amma tafi son suje da Babba yanda za'ayi Mata aikin a Kan
Kari.
Ba qaramin mamaki uncle Mustaphan yayi ba lokacin da sukaje kamfanin Dan lambobin wayar
Sameera da Safna da uncle saminu da wata wadda baisan Kota waye ba ta bada tace
wadannan takeso a bibiyar Mata tun daga Kira chart , messages dinsu duka daga Nan zuwa
wata Daya haka sukaje Airtel ma ta bada suka caji nasu suma, shi dai uncle Mustapha Dan
kallo ya Zama sai lokacin yayi nadamar Hana ma'asuma yin karatun law gasu Nan ridi-ridi babu
Wanda yayi irin wannan tunanin sai 'yar cikinsu wadda take dibace ma a fagen karatun Amma
harta iya irin wannan nazarin da aiki da hankali Wanda suka kasa su.
Cikin ikon Allah komai ya kammala suka Kira uncle Mustapha suka fada masa shi Kuma ya Kira
Ammi yace ta turo Masa batool, tare sukaje kamfaninin kusan babu banbanci a aikin nasu sai
ma na Daya kamfanin Daya Dara Daya fito da hujjojin zahiri Alfarma suka nema a Basu
ma'ikacin da zeyi aikin Ranar da suke son abun ya kasance to kinsan dai yanayin Qasar indai
zaka bude bakin aljihu yanzu ne zakaga biyan bukata, suna fitowa uncle Mustapha ya cewa
Batool to ita nata aikin ya kare tabar sauran a gurinsa yashi Mata Albarka kamar me,ita fa
batool ko Ammi Bata fadawa komai ba duk Fadi tashin da takeyi saboda haushin kowa tajeji
gidan. Kwana biyu da zuwansu kamfanin taji ana maganar Abbie na Kiran meeting na duka family a
Babban hall din Nan da kukayi walima.
Mutane sun amsa Kiran kamar ba gobe Dan sun San da walakin goro a Miya, Uncle Mustapha
ne yayi Addu'a da jawabin maraba ga jama'a sannan yace wani Abu yakeso kowa ya maida
hankali ya saurara yaji sai mu yiwa kanmu adalci a ciki game da maganar Mahmud da yarinyar
Nan safna, Jin haka yasa su Aunty Sameera da uncle saminu zasu tada Zaune tsaye, Abbie ne
ya taka musu birki yace ko shi baisan menene ba tosu meye zesa su tada hayaniya Kan
abinda bakasan menene asasinsa ba, dole suka hakura Amma zuciyar Safna kamar ta fito Dan
mugun bugawar da tajeyi.
*_AUREN HUCE HAUSHI_*
AISHAT ISAH MUSAH.
(Maman Fateemah).
09061432330
Or
08055362975
Page 95.
______Ba'a dauki dogon lokaci ba ma'akacin kamfanin wayar ya hada komai ya saka
microphone yanda na nesa zasuji magana, cikin abinda Bai wuce minti biyu ba maganar Aunty
Sameera ta karade gurin ita ta Kira uncle saminu ta nemi ganinsa a lokacin take tamyarsa yaje
gurin data fada masa a Nan ya fada Mata yaje har ya bada turare Wanda safnar zata shafa taje
gurina idan na shaqa ban Isa nayi Mata musun duk abinda ta buqata Koda kuwa kwanciya da
ita ne, shine suka hada tazo da system tayi min wannan shishshigewar Dana kasa hanata a
Ranar da uncle saminu ya samemu Ni da ita da yamma Wanda yaso tun a Ranar ya hada min
gwarama sai Kuma Allah ya Kare abun ya shashance, sai kuma sauran maganganu Wanda
Basu shafeni ba, haka aka dunga sauraren yanda suka ringa kulla makirci kala-kala ita da uncle
din har turo min Safna daki, Ashe duk setup ne.
Sai Kuma wayata da Safna a mabanbantan lokuta babu komai sai gaisawa da zumunci da
Kuma requesting na kudi da dai sauransu sai Kuma wayar Safna da number din da Batool ta
bada,a Nan kowa ya shiga shock Dan abin ba tsabta Dan duk abinda sukayi tun daga chart
dinsu har Kira da voice note har video call ba'a rage komai ba Abu mafi tada hankali a cikin
wayoyinsu sunyi maganar zubar da ciki ya Kai sau biyu, da irin yanda suke shirya haduwa a
lokutan da take zuwa makaranta, a lokacin ne aka gane Ashe duk lokacin da tace ta tafi Niger
state saurayin nata take bi har outside country suke fita, ta Nan aka gane tana amfani da
layukan waya hudu da wayar ta yanda idan ta fita makaranta take rufe wayar tace saboda suna
lectures ne.
Daga karshe aka dawo kansu uncle inda aka dunga sauraren makirci abun dai babu Dadin ji,
har na karshen nan Wanda suka hada karfi sukaje har okene gurin wani matsafi suka karbo
abinda aka turara min a daki da wasu tsubbace_tsubbacen da akayi Dan kowa yayi min naqi,
duk ta waya suke shirya komai Dan a zahiri bazaka tab'a cewa da wata alaqa irin haka a
tsakaninsu ba, a Ranar da abun ya faru sun jima suna waya da hada yanda abun ze kasance
Dan turaren maganin da aka saka Aunty Sameera ce ta shiga da kanta tayi lokacin yaran sun
fice sallah sannan Safna da uncle saminu suka shigo dakin lokacin da uncle din yayi waya da
security din gidan Hajiya Inna yace Masa mun fito da zayyan, shine fa suka shirya min wannan
makircin Wanda kowa ya kasa gane meye gaskiyar Al'amarin sai batool da Allah ya tsareta ita
da uncle Mustapha, tunda aka Fara wannan fallasar su Safna da Sameerar ke zufa Shima
uncle sadda Kai kasa yayi, mutane kuwa Nan da Nan guri ya kaure da hayaniya masu Ala tsine
nayi masu sharben hawaye nayi masu Ala wadarai nayi, cikin borin kunya Aunty Sameera ta
tashi tana zazzaga masifa da hawayenta bibiyu tana fadin wallahi shirya wannan abun akayi ita
ba ita bace wadda take magana inpersonate ne akayi Mata bazata yarda ba sai tayi shari'a da
masu kamfanin wayar, uncle Mustapha ne yayi Mata zabu -zabu akan idan Bata yiwa mutane
shiru ba ze saka a tafi da ita a sakaya masa ita ta jira ai da saura.
Computer aka hada wadda akayi connecting da CCTV tiryan-tiryan aka Fara nuna duk abinda
ya faru a part din su Mahmud a Ranar tun daga safe har dare,duk shige da ficen kowa gashi
Nan kowa ya gani har abinda ba'a fada ba a wayar Saida aka gani in da uncle saminun ya fasa
interlock din kofar shiga part din mu ya binne wani Abu da turaren da akayi da shiga cikin dakin
da wayar da yayi lokacin da Mahmud ya taho da shigarsu dakin har da Wasan banza da sukayi
kafin suji shigowar su Mahmud, sai lokacin akaga Ashe uncle bayan curtains ya shige ita Kuma
ta tsaya gefen da kofa zata karareta idan ya bude kofar, duk abinda ya faru kowa yaga zahiri
Nan da Nan hankalinsu ya Kara tashi Dan An yanka ta tashi abinda hankali da tunaninsu Bai
tab'a kawo musu ba kenan, Abbie ne ya taso idanunsa sunyi jajur sai huci yake Yana fadin
Sameera tazo su fice Masa daga gida ya saketa saki uku minti biyar ya Bata idan suka wuce
haka sai sunga kaskancin da Basu tab'a tunanin ana yinsa ba, Nan Sameerar ta Fadi tana
birgima tana tuma da fadin ta shiga uku wallahi saminu ne ya sakata yace Dan mu mallake
dukiyarsa idan mukayi haka Dole sai yanda mukayi dashi da kowa ma Tunda babu Wanda ze
iya bude Baki yace Mana ba haka za'ayi ba.
Kan uncle saminu Abbie ya juya ya nuna Masa hanya Yana fadin ya fita kada ya Kara ganinsa a
gidansa yaje yaji da kunyar tonon sililin da akayi masa, Safna kuwa a Nan da sume Saida aka
yayyafa Mata ruwa ta farfado tana sambatun ita babu Mai rabata Dani Tunda an daura Aure
take Abbie ya rattaba saki ga safna a madadina Tunda Daman bansan da masaniyar Auren ba. Hajiya Turai ce matar Autan su Alhaji sa'id tasa aka fita da Safna da Aunty Sameera.
Saida aka wuce dasu sannan Ammi ta tashi wadda tun lokacin da aka Fara bayanin take
hamdala ga Ubangiji Daya wanke Mata yaro daga zargin Zina Daya karade a cikin family.
A hankali ta ratso mutane ta fito tsakiya ta Fara fadin ta godewa Allah ko