Showing 57001 words to 60000 words out of 62795 words
Chapter 20 - Auren Huce Haushi Book 3 Complete By arewahausanovels.com.ng.pdf
gabatar da zainab gurin Mahmud suka gaisa tace Mata maigidanta ne, ta gabatarwa da
Mahmud zainab kawarta tun suna secondary Nan suka koma gefe Hirar yaushe gabo ta balle
anan zainab ke fada Mata itama tayi aure shekara Daya da rabi kenan harta haihu Dan ba rai
sai yanzu take da wani cikin sun shagala da Hira sukaji magana daga bayansu ana fad'in.
"My beauty wato Hira Kika samu Kika manta Dani ko?".
"Wayyo my love wallahi na gamu da friend dina ce, rabon damu hadu tun secondary kaga kuwa
ai mun gaisa mu tuna baya ko?".
Haka Nan Zahra taji kamar tasan muryar dake magana a bayanta.
"Zahra ga my love Mubeen ku gaisa".
Dan juyowa tayi tana fadin.
"Barka da yamma".
Ido cikin Ido sukayi dashi Amma saita dake tayi kamar Nan duniya Bata tab'a ganin Mai Kama
dashi bama, Amma shi saida ya Dan so ya rude Dan da kyar ya iya fad'in "lafiya kalau".
Zainab Zahra ta kallo tana fad'in "sai munyi way kenan? Bari na wuce sai anjima ku gaida gida".
Ta juya ta koma gurin da Mahmud din yake Zaune Yana faman daddanna wayar hannunsa, da
kallo Muneeb din ya bita sai kuma idonsa ya sauka akan Mahmud. Da sauri ya nufi inda yake
zaune yana karasowa ya Fara fad'in .
"Wa nake gani kamar Mahmud Dange a gurin Nan?".
"Nine Mana muneeb sale,daman talaka na ganinku?".
"Tuba nake yallabai wane ni ai ku ganinku sai Mai sa'ar gaske Nima tsintuwa nayi Allah ya
tsaga da rabona a yau, Daman kana kasar nan watannin baya akace min kana uk can ka koma
da zama".
"A'a gani kuma a Nigeria,kawai dai nayi tafiya ne wadda na jima shine ake cewa nabar k'asar'.
Zahra dai Batasan inda suka San juna ba Amma da gani sun yiwa juna farin sani.
Zahra Bata San Abinda Mahmud ya bawa Muneeb ba taji dai Yana godiya kamar ba gobe Saida
suka tafi Mahmud ya kalli Zahra.
"Gafa ex-boy friend dinki Wanda ze min shigar sauri".
"Daman kasan shi ne? Naga the way yanda kuke magana da sanayya sosai a tsakani".
"Zomu tafi wannan Kuma sirrine".
Sai dare suka karaso gida saboda go slown garin, sati daya sukayi a Lagos suka dawo sokoto,
sun dasa wata irin soyyaya Mai tarihi a Lagos Dan ba karya sun gane juna yanda ya kamata, da
gani kasan suna cikin ganiyar kuruciyarsu ga wadatar arziki sai abun yayi musu wani irin kyawu
na ban mamaki, satinsu Daya da dawowa Ammah tazo sokoto, ai tun daga gate din gidan Alhaji
Muhammad Dange Ammah ta Fara tasbihi ga Allah s. w. a Dan ko makaho ya shafa yasan da
abun Wai an Rana nik'a da Akuya.
Ammi ta yiwa Ammah tarba ta girmamawa kamar ta goya Ammah sun Dade suna Hira tamkar
Aminai Ammi tayi godiyar karamcin kyautar 'ya sumutum da akayiwa Mahmud ba tare da
la'akari ko shi waye ba, an Kai Ammah gidan Hajiya Inna sun gaisa sun aje Mata tata tsarabar
da sakon Abba Daya bada a kawo Mata, ai Ammah Bata k'ara tsinkewa da Lamarin ba Saida ta
shiga gidan Zahra tasbihi kawai take ga Allah Dan wani garin yafi gaban kunu, Ashe Bataga
komai ba Saida idanunta suka nuna mata.
Tana kasa suna Hira da Mahmud suka shigo tun kafin su taso magaji ya Kira shi ya fada Masa
gasu nan tare da Ammah Amma tace kada a fadawa zahra bazata kwantar da hankalinta ba
idan tasan zasu shigo gari, ya dai ce Mata ayi special girki zasuyi Baki,suna zune aka Danna
door bell baiyi amfani da remote control ba yace ta tashi ta bude, ba musu ta tashi tana tafiyarta
kamar tana tsoron taka kasa ta bude kofar, ai ita dai Zahra Batasan lokacin da tayi wani uban
tsalle ba ta fada jikin Ammah sai kuka tana fadin.
"Yanzu a kasa fada min gakunan a hanyar zuwa, wallahi magaji mun Bata da kai na fasa rik'on
wallahi tunda kaci amanata".
"A'a ki tuhumi Ammarki da mijinki sune Basu fada Miki ba,Ni Dan Rakiya da sai yanda akayi
Dani".
Har suka shigo zahra na jikin Ammah tare suka zauna kamar zata shige cikinta sai dariya
magaji yake musu Dan itama Ammar idanunta kamar ruwan hawayen ne, sun gaisa da
Mahmud sosai sannan Zahra ta Kira Aunty zilai a waya tace tazo ga Ammah, sai gata da gani
harda gudu ta hado, dan Sai daga bayanta sannan Binta ta shigo, murna kamar me sai dariya
take yi Mahmud fita yayi magaji ya bishi tunda ya cika cikinsa a gidan Ammi.
Bayan fitar Mahmud Zahra ta tashi ita Aunty zalai suka shiga fito da kayan abinci dasu drinks
tamkar mutum goma ne zasuci sai da Ammar ta tsawatar musu tana fadin.
"Ke Zahra duk waye kuke kawowa wannan abincin haka? Nifa na koshi naci na surukarki mace
Mai kirki ga nagarta".
Zilai ce ta karbe zancen "wallahi kuwa Ammah kirkinta ya Isa gashi kamar ta goya uwar dakina
Dan so da kauna wallahi Ammah ranar Nan Ina mofin a wancen parlourn naji Yana fadin
"wallahi Ammi Ina son Zahra ki tayini sonta". Bansan dai Abinda ta fada masa ba naji dai Yana
jera Mata godiya". Babu laifi Ammar taci abincin,Saida ta Gama suka haura sama tayi sallah, ta shishshiga ko Ina
ta gani tana godewa Allah Daya bawa marainiyar ta gidan da ko cikin mafarki Basu tab'a zato
ba.
A Nan zahra ta zazzagewa Ammah yanda Mahmud yaje asibiti yayiwa Mama tatas, abun ya
bawa Ammah mamaki kenan shi harya gano abunda ta kasa ganewa shekara da shekaru,
sannan Ammah ta fada Mata Mahmud ne yasa aka dawo da Salma daga Jos da duk abinda ya
faru har tarewar Hameeda wancen satin, duk sai tausayinsu ya Kama Zahra ganin ita 'yar riko
ma Abba ya zage dantse yayi abun azo a gani na shidimar daurin Aure to bare Kuma na 'yayan
cikinsa wadanda daga su ba saura 'ya mace a gidan Kuma Amma ace abun yazo haka a
hagunce babu Dadi duk da ance yayi musu komai Amma dai ba haka akaso ba. Sai karfe hudu da minti goma su Mahmud da magaji suka shigo gidan, a gurguje saboda lokaci
jirgin hudu da rabi zasu bi zuwa Bauchi.
Mahmud da kansa ya Kai Ammah airport tare da zahra sukaje lokacin da zasu shiga jirgi rike
Ammah Zahra tayi tana kuka da kyar Ammah ta lallabata ta wuce lokacin da zata shige ta juyo
sai taga Mahmud ya rungumeta da gani lallashinta yake yi.
Bayan sati Daya visa dinsu ta fito inda zasu Fara shiga India gurin Baba malam tunda an
sallamesu suna gidan Mahmud din, tare suka juya da Aunty Aishat saboda hutun su Abulkhairi
ya kusa karewa.
Tun daga airport kowa yayi nasa gurin ita Aishat Ya Abbas yazo suka wuce, su Kuma Mr
salahuddeen yazo ya daukesu.
Sun samu jikin Baba malam yayi sauki sosai Dan Yana tafiya da kafafunsa sai Dan abunda
baza'a rasa ba Kuma sunce sai a hankali komai ze zama normal, murna da farin ciki ba magana
kamar malam ya hadiyesu Dan farin ciki Dan yanda ya gansu yasan suna cikin nutsuwa da
kwanciyar hankali. Da dare ne Mahmud suka zauna da Malam ya warware masa zare da abawar Abinda ya faru
dashi Wanda ya sabbaba fitowarsa daga gida, sannan ya juya ya kalli Habib da yake Zaune
Yana saurarensu.
"Habib".
Mahmud ya kirawo sunansa.
"Na'am" ya amsa.
"Wadannan shugunan na kayan motoci Daman da sunanka nayi komai ai ka sani lokacin har
kana korafin ya za'ayi haka nace ka barshi duk Daya ne, anyi hakan?".
Kaiya gyada kafin yace "Tabbas anyi haka".
"To Alhamdulillahi, Daman nayi ne da sunanka lokacin bani da bakin fadar hakan shine dalilin,
sai Kuma shagunan da aka zuba Atamfofi da su laces da materials Dana kayan Yara, ina ga
shida ne ko?".
"Eh haka suke".
"Ok.to na Ammah ne Kai na wakilta kaje ka kaimata takardun shugunan da duka lissafin daka
turo min ka mayar dasu cikin Account dinta, Sai Kuma sauran kantin Nan guda hudu na
shaddoji da sauran kayqn maza da sabuwar plazar Nan Mai sunnan malam wadda aka bude a
katagum road duka na malam ne, gidan kusa da Malam sani Mai wankin hula duk da dai
bakasan anyi gininba to na Ashiru mai shayi ne, Shima yayi abin a yaba Masa ya bani shayi ba
adadi nayi nayi ya karbi kudin yace a'a Kuma na fadawa Sameer a bashi jarin sana'a bayan
shayi badan ya manyanta ba da Kano Zan kawa shi kamfani to nauyin iyali sunndanne shi, ka
karbi takardun gidan suna hannun Bilyaminu sai kaba Baba malam ya bashi ayi min godiya
kafin na shigo garin".
Tunda Mahmud ya fara bayani malam ke jinjina Kai yasan za'ayi haka Dan yayi istihara yafi sau
shurin masaki Amma babu canji wata irin daukaka yake gani tare da yaron.
"Allah yayi maka Albarka ya shiga cikin dukkan lamuranka yanda ka kyautatawa bayin Allah
Ubangiji ya kyautata lamuranka na duniya da lahira yayi maka tukuici da gidan Aljanna ya baka
zuri'a dayyiba ya Kare gabanka da bayanka ya Kara arziki Mai Albarka, lallai Ubangiyi maji
rokon bawayinsa ne nayi Addu'a tun Ina da kuruciyata Ashe sai girma ya kamani Allah ze
tabbatar Mana da abun, sannu mahmudu kaji mun gode! Mun gode!! Ubangiji yayi jagora". Saiya sadda kansa kasa sai Jin shashshekar kukansa sukaji.
Nan da Nan Mahmud ya rude Yana tambayarsa menene? Sai da yayi Mai isarsa sannan ya
shafe hawayen.
"Mahmudu wani Alherin sai kayi hawaye, wallahi yafi gaban dariya me Zan cewa Ubangiji
banda nayi ta tahamidi ga sarki rabbil Izzati. Alhamdulillah!. Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi,!!!
Alakulli halin.
Fitowa su Mahmud sukayi Nan compound din gidan shida Habib, suna Ida fitowa Shima Habib
ya Fara nasa matse hawayen Yana fadin "wallahi bani da bakin yi maka godiya kayin min gata
na gidan duniyar Nan kayi min Abinda bani da halin yinsa akan yayan mahaifita Allah yayi maka
sakayya da Aljanna madaukakiya". Kafadarsa Mahmud ya Dan doka kadan.
"My man kana bada maza fa gurin yawan kuka nan ai namijin duniya baya kuka duk wuya duk
dadi, haba! Be strong Mana Dole ka baro gida ka shiga duniya kaga yanda maza ke yin
kwakawrmaya, Zan fadawa Baba malam dole a cikin uku ka zabi Daya ko Nan India ko Dubai
ko Kuma China,amma saina hadoka da Ubaidat yanda aikin ze tafi yanda nake son ganinka,
zamanta kusa da Kai ze Kara maka support ba kadan ba, tunda Nima ban samu nutsuwa ba
Saida kuka bani Kanwar ku, Zan fadawa malam ayi maganar biki a kusan Nan ku tattraro ku
taho".
Ya fada Yana Masa murmushi, Shima Habib murmushin yayi kafin yace.
"Ai Ubaidat an kasani ta samu Mai kudi a Itas gadau Amma mazaunin Abuja har anyi biki wata
Daya Daya wuce tayo min text Wai nayi hakuri a gidansu ne aka takura Mata, to nima lokacin
lna cikin tawa damuwar ta lalurar Baba malam wallahil Azim ban ji komai ba fatan Alkhairi nayi
Mata kawai Kuma Daman a yanda take bijiro min da bukatu na kudi banga alamar zamu dai
daita ba da farko ba haka take ba sai daga baya na fuskanci ta fiye rokon kudi Kuma duk mace
Mai wannan d'abi'ar sai wadda Allah ya tsare Dan an Bata da yawan 'ya'ya Mata masu irin
d'abi'ar".
Jinjina Kai Mahmud yake kafi ya nisa yace.
"Allah ya kyauta, wato tsakanin hakuri da rashinsa tak'in kadan ne da tayi hakuri babu Abinda
zata nema ta rasa da izinin Allah, ka tuna wata magana daka tab'a fada a dakinta mu na Azare?
Lokacin da kace min muma ai ba haka Allah ze barmu ba".
Dariya Habib yayi ya tuna lokacin da aka bawa Mahmud Auren Zahra ne ya Fadi haka.
"Kada ka damu kaje ka nemi suhailat kanwata ce na kori Mai zuwa gurinta sauran masu neman
izini ma na fadawa uncle Mustapha ya fada musu anyi Mata miji Daya nemi sanin waye mijin na
nuna masa hotonka da irin karamcin da kayi min, take ya nuna goyon baya Shima na saka ya
kirata ya fada Mata ya nuna Mata hotonka yace taje tayi tunani idan kayi Mata tana sonka ze
kirata bayan kwana biyu, to Alhamdulillahi tayi shiru ta sadda Kai lokacin daya Kara tambayar
ta, hakan ya nuna ta amince, to Daman da da maganar Ubaidat din biyu zan maka Rana Daya
kaima ga hoton suhailat Nan idan tayi maka idan Kuma batayi ba Dan Allah kada kayi min Kara
ka fada min gaskiya idan ka rufe min saimun tsaya gaban Allah da kai".
Ya fada Yana mikewa tsaye Yana Danna wayarsa yayi gaba Saida ya danyi nisa ya juyo ya kalli
Habib Daya rasa bakin magana.
"Ka duba WhatsApp Dinka na turo maka pictures dinta". Ya wuce ciki..
Habib jikinsa har tsuma yake ya bude Whatsapp din ai Bai San lokacin daya Mike tsaye ba
Yana tsarkake sunan Ubangiyi buwayi gagara misali, yarinya ya gani danya sharab Mai wani irin
kwantaccen kyau da gani gayu yaci gidansu a gurin tayi wani smile Daya kusa ya saka shi
zaucewa, shi kadai Fadi yake. "Yessss... Yessss... Tayi"..
Take a Nan yayi sujudush shukur Dan yasa Rahamar Allah ta bashi wannan yarinya ba Wai
iyawasa ba, ya Kara jinjina girman Qudurar Allah wato idan aka hada wani connection din sai
dai bawa ya zuba Ido yayi kallo, a watannin baya da za'a ce Masa za'a baka aure a Family din
DANGE dake sokoto ze rantse harda girman Allah hakan bazata tab'a faruwa ba Dan ba'a hada
kankana da guna.
Komawa yayi ya zauna Yana Kara duba hotunan sai yaga ai Wanda ya Fara dubawa ma Bai
Kai sauran kyau ba sai lokacin yaga number wayar ta daga kasa da Dan bayani a kasan
number.
"Ga number ta Nan ka kirata sauran aikin Kuma naka ne tunda Nima Ni nayi nawa aikin. Ina
Maka fatan dacewa kamar yanda Nima AUREN HUCE HAUSHI da akayi Mana ya huce Mana
namu haushin Dana iyayen mu.
Dariya Habib yayi ya Dan kwantar da kansa jikin kujerar da yake a Kai ya zubawa fuskarta
Idanu Yana tasbihi ga sarkin da yake amsa Addu'oin bayinsa, yayi Addu'a iya Addu'a akan
neman zabin Allah akan mace ta gari.
****Washe gari su Baba malam dasu Abubakar suka wuce Nigeria, su Mahmud Kuma suka nufi
Dubai, a hotel dinsa na gudun hijira suka sauka tunda Shima permanent room ya kama, a
MJ.moritte Marquis hotel din, Zahra ta Kara tabbatar da Mahmud bana Wasa bane ganin irin
wannan hotel din Daya Kama permanent daki a cikinsa zamansa yake Kuma ana biyan kudin
daki duk wata tunda booking din monthly akayi shi.
Sun huta iya hutawa sunyi honey moon yanda ya kamata zahra taga gata iya gata taga soyyaya
kamar ya hadiyeta sunyi wani irin mahaukacin kyau bare Zahra tamkar ka taba ta jini ya fito tayi
Shar da ita ko uhum tace Saiya ce menene a Nan watan Ramadan Mai Albarka ya samesu,
dole ya rage Zama har hakan ya tayarwa da zahra hankali Dan baya dawowa sai gaf da Kiran
sallar magariba har dai ta gaji tayi masa magana yace Mata aiki ne yayi yawa yanzu, ranar da
suka Kai Azumi na bakwai Yana Zaune a office Yana karatun Alqur'ani Kiran Sister twins dinsa
ya shigo, bayan sun gaisa ne take tambayarsa " Waime yasa baka son Zama a gurin Zahra ne?
kullum idan na kirata sai tace min baka Nan".
Dan murmushi yayi yasan juya abin Aishat tayi Amma ba haka abun yake ba kararsa kawai ta
Kai gurinta, ita Kuma sai tayi Masa Education.
Ba wani rufa-rufa ya bude Mata aiki tunda ba kunyarta yakeji ba.
"Kina jina idan na zauna a gurinta wallahi matsala za'a samu dan azumi dai karya shi za'ayi
bako tantama saboda wata irin fitina takeji da ita kwanan Nan wallahi wani lokacin sai munyi
wanka muke sallar insha'i da asham to gane min idan Ina zama gurinta sai mun shekara muna
kaffara wallahi".
Tunda ya Fara Kora Mata bayani Aishat ke kunshe dariyarta.
"Ok na gane Zan Mata bayani, Amma Anya Bata da ciki kuwa? Kuje a bincika ana samun irin
haka ga wasu matan idan suna da shigar sabon ciki".
"Kai Anya bana tunanin hakan ba kune kuka dunga zabga Mata hade hadenku ba gashi Nan ya
mayar da ita fitinanniya, ga azumi Kuma".
Dariyar ce ta kwace Mata Saida tayi Mai isarta sannan tace "nidai ba ruwana gyaran jiki kawai
nasa akayi Mata"
"Kuka sani dai babu Mai sakani kaffara Ina zaman zamana" dif ya katse kiran, Yana Jin dariyar
Aishat din.
A ranar Bai shiga ba Saida yayi har asham sannan ya shiga ya sameta a kwance a parlour a
kasan Kan carpet sai juyi take da sauri ya karasa Yana tambayar ta menene?
Mararta ta nuna masa. "Bari muje Asibiti".
Kai ta girgiza masa alamar a'a yanda yaga eyes dinta yasan da magana cak ya dauketa yayi
bedroom da ita.
Karfe Tara na dare suna gaban doctor Mahmud ne ya fada Masa bukatarsu ta binciken madam
saboda tayi fama da matsalar fibroid, Bai fito yace Yana zargin ko ciki ne.
Tashin farko ana Dora abun scanning saiga ciki kwance a mahaifarta, kusan wata biyu kuma
lafiyayyan cikin da babu tantama, tun a gadon scanning din ya rungumeta Yana godiya ga Allah
da yayi musu wannan kyautar da kudi ko mulki basa badawa. Aishat ya Kira yayi Mata Albishir
din cikin, yana fadar Ashe da gaske ne Abinda ta fada, kenan ba kowa ke kwanciya ciwo ba
yayin laukayin ciki? Dariya kawai tayi masa, duk murna ta cikata tana son ta fesawa Ammi
labari.
A ranar zahra taga kulawa ta musamman Dan biye Mata yayi ganin da gaske baby dinsa ne ya
canzata.
Zahra taga soyyaya gurin Ammi Dan cewa tayi ya dawo Mata da ita Nigeria tunda Daman tayi
fama da lalura a mahaifa kada cikin ta samu wata matsala tunda lokacin da zahra ta fadawa
Mahmud baya zamqn gida mummy Bada'a Aishat ta Kira ta fadawa itace tace ta tambaye Shi
dalilin hakan