Showing 1 words to 3000 words out of 19493 words

Chapter 1 - A WUNI DAYA BOOK COMPLETE BY ESHAAAT.pdf

05 Jun 2025

1330

COMPLIED BY
ESHAAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE
ATU SANI KATIBU Ƙ ( BABY
MSH ) MOBILE BLOG
Home » » A YINI ƊAYA 1-2
A YINI ÆŠAYA 1-2
By babymsh 08:24 No comments
[11:20pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
💀💀 💀💀

*NWA*
NA *Princess Amrah*
Da *Rabiatu sk msh*
*~hannu biyu writers~*
Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah
mad`aukakin sarki, tsira da aminci su k`ara
tabbata ga shugaban mu annabi Muhammad
(SAW) tare da alayen sa. Kamar yanda muka
fara rubata wannan littafin, muna fatan mu
k`arisa shi cikin aminci da yardar Allah
mad`aukakin sarki, muna fatan abun da muke
son isarwa ya isa ga d`aukacin al'ummah
musulmai har ma da wanda ba musulmai ba.
Wannan labarin k`irkirarre ne k`agagge ne munyi
shi ne akan illar zuwa party, da duk wurin da
addinin musulunci yayi hani dashi, ba munyi shi
don cin zarafin wani ko wata bane, munyi ne
domin nuna illar abun.
Abstract (shimfid`a).
Labari ne mai ku`nshe da wasu bayin Allah da
suka mayar da zuwa party tamkar ruwan shan
su, sukan fita a kowane lokaci ba tare da sanin
iyayen su ba, sai dai kuma daga baya zasu
had`u da rikicin rayuwa suyi dana sani a lokacin
da bashi da amfani. Allah ya shiryar damu bisa
hanya madaidaiciya, Allah kuma ya bamu ikon

d`aukar abunda zamu karanta a ciki.
But idan kin San kina da tsoro kar ki karanta
shi. (Lol..😊)
Page 1⃣
K`arfe 8:00AM.
Kwance take kan lallausan gadon ta na royal
bed, wayar ta na jikin chaji amma still tana
latsar ta, zumbur ta mik`e cike da murna tana
fad`in "yesss! Am glad to hear that woooo"
komawa tayi ta kwanta taci gaba da charting
d`in ta.
Wani kyakkyawan yaro ne ya shigo d`akin
cikin shagwab`a yace "yaya Afnan momy is
calling youh",
Cikin haushi tace "am coming",
"Buh yaya Afnan the momy said...", katse
yaron tayi "Affan tell her that am coming now",
tafiya yayi yana waigen ko ta taho har yabar
d`akin bata tafi ba, aikin charting kawai take.
Jin shiru Afnan batazo ba yasa momy sake
tura Affan, a bakin k`ofa suka had`u tace "sai ka
tafi ai uban gulma gani a hanya".
Bakin shi tunzure ya tafi tana biye dashi a
baya.
"Afnan wai bazakije islamiya bane tun d`azu
Affan ya shirya yana jiran ki amma kin k`i
fitowa?", "momy banda lafiya fa" Afnan ta fad`a
cikin shagwab`a.
"Me ya same ki?"
"Momy mp ne fa",
"Eyyah sorie, kije ki kwanta ki huta, hope kin
sha magani"
"Yeah momy nasha"
"Ok Allah baki lafiya, Affan kaje kacewa
driver ya kai ka kawai, kace wa malamin su
Afnan wai bazata samu zuwa ba may be da
yamma idan ta samu sauk`i taxo".
Kitchen ya nufa ya d`auki launch box nashi
ya nufi mota.
Dakin ta ta koma taci gaba da charting d`in
ta. A fili tace "kawai abi a damu mutun da wata
islamiya, da yamman ma barin je ba birthday
party'n Kerry zanje".

"Arewa Stars kun jini shiru wlh momy ne ta
kira ni wai sai na tafi islamiya".
D`aya daga cikin members na group d`in
Arewa Stars tace "hhhh tou ya kika ce da ita?"
Afnan ta mayar mata da "nace mata mp
pain ke damu na".
Wani namiji ya turo da "lol...Afnan bakya ji
fa, yanzu dai ku fidda mana colour`n da zamu
saka anjima",
Sally tace "ai an riga da an fitar, ash, pink
and black ne zaa saka, har na kira wanda zai
mana decoration na sanar dashi colour d`in",
Haka dai sukaci gaba da hirarrakin su cike
da nishad`i da munanan k`udurin abubuwan da
zasu aikata a wurin birthday party`n Kerry.
A rikice ta fito daga d`akin ta dan duk a
kayan ta bata da colour d`in da zasu saka,
"Afnan lafiya?" Momy ta fad`a tana kallon ta.
"Lafiya lau momy, maganar practical
materials d`in mu ne, malamin yace daga ranar
monday za`a rufe sayar wa",
"Tou Afnan yau fa Saturday, kina tunanin idan
kinje yau zaki samu ne? Kuma ma ai naga duka
fa jiya kikace ya fad`a maku ku siya",
"Momy tun fa last week ya fad`a nice dai ban
sani ba sai jiya".
"Ok akwai kud`i hannun ki ko sai na baki?",
"Momy sai kin k`aro min dan ban san ko
nawa zan kashe ba kar suyi min short",
"Ok ki bud`e side drawer na ki d`auki yanda
zai ishe ki".
Cikin murna ta nufi d`akin, kud`i sosai ta
d`auka sannan ta fito. "Zaki iya driving ko sai
Abu ya dawo ya kaiki?",
"Zan iya momy" ta fad`a tare da d`aukan key
ta fita waje, a daidai parking space d`in babban
gidan su taje, wata benz cement colour ta bud`e
ta shiga.
Bata zarce ko ina ba sai gidan su Feenah.
Bayan ta gaishe da maman Feenah suka
shiga d`an k`aramin d`akin ta.
"Ina fatan kina sane da birthday party`n kerry
yau ne, kuma nasan baki da colour`n kayan da

za`a saka, shine nazo d`aukan ki muje na siya
miki",
"Eyyah Afnan nikam yau barin je wannan
party`n ba, wanda naje a baya ma ina rok`on
Allah ya yafe min dan zunubi ne babba muke
kwasar wa kan mu, kuma ga k`arya da muke
yiwa iyayen mu kawai dan muje wurin sab`on
Allah, gaskiya ki tafi kawai bana so".
Cikin takaici Afnan ta mik`e tsaye "haka kika
fad`a ko? Aikuwa yanzun nan zanje na sanar da
umma`n ki abubuwan da kikayi a baya, kuma
wallahi harda k`ari zan miki nasan dole zata
yarda",
Marairaicewa Feenah tayi dan tasan halin
umman ta, k`aramin aikin tane ma ta hana ta
zuwa har skul d`in ta da ko ina ma, sosai
ummanta ke tsaron ta.
Ganin Feenah tayi zurfi a tunani yasa Afnan ta
fara cewa "sai kisan abunda zaki fad`awa
umman ki dan ki kare kanki".
Cikin takaici Feenah tace "kiyi hak`uri Afnan
kar ki fad`a mata, na yarda zanje".
Murmushin mugunta Afnan tayi tace "oya lets
go".
Hijabin ta har k`asa ta sako, a d`an
madaidaicin parlor`n su suka tayar da umma`n
ta, "ummah zan raka Afnan gidan su Maryam
khalil amma bazamu dad`e ba".
"Ok a dawo lafiya, ki gaishe min da hajiya
Zainab, kiyi saurin dawowa ki tafi tahfiz k`arfe
sha biyu".
"Insha Allahu momy barin dad`e ba".
Daga nan kuma suka kama hanyar AA
BOUTIQUE don sayen k`ananan kayan da zasu
saka.
©Amrah and Rerbee'art novels
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[11:29pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*®NWA*

*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page2⃣
Nan suka hau dudduba kalar kayan da zasu
saka, Afnan ce taci karo da wata had`ad`d`iyar
top gown hot pink sai torches d`in black kad`an
kad`an, baki d`aya k`irjin rigar a bud`e yake da
wasu hudojin da aka k`awata su da zanen
manyan flowers, bayan rigar yafi gaban ta tsawo
da kad`an, hannun ta ma d`aya dogo d`aya
gajere ne, gata da shape sosai irin wadda take
fidda zahirin coca cola shape na mace, (niko
Amrah nace wannan kyan ta masu aure su same
ta, ai ranar babu oga ba zuwa office..lol).
Bayan ta tabbatar da rigar ta burge ta ne
suka hau dubama Feenat nata, "nidai Afnan pls
bana son mai tallan jikin nan, asamar min mai
rufe tsiraici",
Cikin fushi Afnan tace "wallahi duk wadda
aka samu ita zaki d`auka kuma dole ki saka ta",
Shiru Feenat tayi taci gaba da bin bayan
Afnan suna kewaye boutique d`in, da k`yar suka
samu wata gown ash da torches d`in pink, gown
ce ta mutunci mai A shape, zata iya sauka har
k`asa, tana da turtle neck da dogon hannu. Sosai
Feenat taji dad`in wannan rigar, dan tasan zata
iya sakata ba tare da taji komai ba.
Side d`in jewelries suka koma, nan naga
k`aryar fashion sark`a da `yan kunne da abun
hannu, komai na AA BOUTIQUE kyau gare shi,
nan Afnan ta zab`i wata siririyar chain mai kyau,
Feenat ma irin shi ta zab`a, kud`in suka biya
sannan suka koma mota dan nufar gida.
Cike da damuwa Feenat ta kalli Afnan tace
"yanzu Afnan wace k`arya zan ma Ummah
anjima idan zan fito?"
"Oho miki, sai kisan abunda zaki fad`a mata,
nidai k`arfe biyar na yamma zanzo d`aukar ki, ki
tabbatar kin shirya by then",
Tun daga nan kuma sukayi shiru su duka har
akazo k`ofar gidan su Feenat.
Afnan da kanta ta fitar ma Feenat da kayan
ta daga leda, cikin in ina Feenat tace "Afnan ki

tafi da kayan nan idan mun tafi can zan saka,
dan yanzu Ummah zata iya cewa in bata ta gani
kuma nasan halin ta zata iya fahimtar wani
abu",
Bata ce mata komai ba sai jinjina kanta da tayi,
daga nan taja motar ta sai gida.
*K`arfe 1:00pm*
*~Gidan su Ruky.~*
"Momy ta samu fa, yau ma akwai wani
casun",
Wadda ta kira da momy tayi mirmushi tace
"kedai Ruky bakya gajiya da casu, kullun baki
nan baki can, duk inda ake wani biki ko party
kina can ko? Yau kuma wane casu ne akeyi?"
"Momy birthday party`n Kerry ne fa za`ayi
kuma mune best friends nata, idan bamuje ba
waye zaije?"
Momy tace "ehh kuma fa gaskiyan ki, to
amma ki k`ure kwalliya dan nasan yau akwai
wankan gayu, so nake auta ta tafi kowa yin
kyau a wurin, kiyi chajin iphone d`in ki sosai
yanda zaki d`auko pictures da yawa",
Can naji wata murya zazzak`a daga bakin
k`ofa tana fad`in "haba momy, wai yaushe zaku
tuba ga Allah ne ki daina d`ora Ruk`ayya akan
wannan munanan halayen? Ku baku ma tsoron
mutuwar ku? Koda yaushe fa mutuwa zata iya
riskar ku dan ita bata alerting mutun kafin tazo",
Cikin takaici momy tace "ke Rumaysa wai ina
ruwan ki ne? Ni tunda na gane ke ba wayayyiya
bace kinga ina saka ki a irin wannan harkokin
ne? tou wallahi kul dinki, kar ki kuma jefo mana
wannan shegen bakin naki idan muna maganar
mu".
Rumaysah tayi shiru daga nan bata kuma
fad`in komai ba, sai dai kuma har a ranta tana
tir da Allawadan halin mahaifiyar ta da k`anwar
ta Rukayya, mahaifin su yana kabari amma su
suna nan basu ta yi mashi addu`ah sai munanan
d`abiu, da wannan tunanin ta shiga d`akin ta
cike da tsanar halayyar su.
Da tafiyar ta kuwa suka hau shewa da k`arfi,
momy tace "k`arfe nawa ne party`n?"

"K`arfe biyar na yamma ne momy, amma kuma
nasan ba lallai ne a fara shi a lokacin ba ana iya
akai dare",
"A ina zakuyi"
"Momy nima ban sani ba, suna so suyi suprising
namu ne, Sally ce kawai tasan inda za`ayi dan
har ma ta tura wanda zayyi mana decoration ina
tunanin ma har an gama",
"Tou yayi daidai `yata, ya maganar dressing fa?",
"Pink, black and ash ne za`ayi kuma ina dasu ai
da banda shi momy da tun d`azu na mimi
magana",
"Ok yayi daidai autah nah, Allah kaimu anjimar,
sai ki tafi da mota ta dan bana so kowa ya kara
ki a tashi dan kar a miki wulak`anci",
Tafi sukayi da junan su, Ruky tace "das my
momy, saisa nake sonki always".
©Amrah and Rerbeeart novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
YINI ÆŠAYA 3-4
By babymsh 08:26 No comments
[11:35pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
*~hannu biyu writers~*
Page3⃣
*Karfe 1:30pm*
*~Gidan su Iby.~*
"Yaya Mukhtar dan Allah zaka bani aron
motar ka anjima?",
"Me zakayi da ita?" Yayan nashi ya fad`a yana
latsar system nashi.
"Yaya zanje wani wuri ne?"
"Shi wurin baya da suna ne?"
"yana da suna yaya, ganin abokina zanje",
"Ganin abokin ka kuma shine bazaka iya d`aukar
mashin d`in ka kaje ba dole sai a mota?", yayan
nasa ya fad`a a lokacin da ya dawo da kallon shi

ga Iby.
"yaya wai me yasa kake min haka ne? Yaya na
yana da kud`i ina alfahari da hakan amma kuma
baya kyautata min, me yasa yaya bazaka so aga
k`anin ka da manyan harkoki bane wai?",
Cikin mamaki Mukhtar ya kalli Iby yace "au!
Ashe abun ma hakane, tou tunda hakane ma
bazan bayar ba, kaje ka nemi loud speaker kayi
shela akan nak`i ara maka mota ta kuma bayan
ina da motocin da yawa, sai inga idan akwai
wanda ya isa yamin wani abu",
Tashi Iby yayi yana gunguni can k`asa k`asa,
"Me kake fad`i!?" Mukhtar ya fad`a a hayak`e.
"B..b...bance komai bafa yaya" ya fad`a in
tammered.
*Karfe 2:30pm*
*~Gidan su Shareef da Shareefat.~*
Shareefat ce kwance kan doguwar kujera ta
rasa abunda yake mata dad`i dan tunanin rashin
kayan da zasu saka wurin party`n kerry, alamar
tafiya taji tayi saurin duba ko waye, ganin
Shareef ne yasata ajiye nannauyan ajiyar zuciya
tare da fad`in "Reesha dama ina jiran zuwan ka",
"Menene?" Ya fad`a yana kallon ta,
"Mubar area`n nan dan kar mamy taji mu",
Barin parlor`n sukayi suka koma can kusa da
gate d`in gidan,
"reesha dama in fad`a maka wallahi banda
kayan sakawa anjima, nasan kuma kai kana
dasu, ya za`ayi dan Allah",
Dariya yayi sosai yanayi yana nuna ta da yatsa,
sai da yayi mai isarshi lokacin har Shareefat ta
k`ule,
"Tou Reeshat ni yanzu me zan miki? Kije kiyi aro
kawai",
K`ara b`ata fuska tayi tace "ai wallahi inda akwai
inda zanyi aron da nayi, dan bazan yarda kowa
da anko ni banda shi ba",
Shareef yace "kar ki damu zan nemo miki shi
yanzu, amma fa ban iya zab`e ba zakiyi hakuri
da duk wadda na siyo miki?",
Kallon shi tayi sosai tace "kai Reesha ka tafi
dani dan Allah",

Zaro ido yayi yace "idan na fita dake yanzu
anjima idan zamu fita k`aryar me zan ma
mamy? Kedai kiyi hak`uri kawai zan duba miki
mai kyau, kuma koya take indai kalar ta hau ai
shikenan",
"Ehh haka ne kuma, Reesha, pls nidai mai kyau
nake so", da wannan maganar Shareef ya tafi,
shareefat kuma ta koma cikin gida.
Amrah and Rerbeeart sk novels
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[11:45pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
*~hannu biyu writers~*
Page4⃣
Haka dai gidajen su *Arewa stars* d`in suka
kasance, kowa ya nemi kalar kayan da da suka
zab`i sakawa a birthday party`n kerry d`aya daga
cikin members na *Arewa Stars,* murna fal a
zukatan su, sun d`au dogon lokaci suna
tsumayen wannan ranar duk da yawan party da
suke amma na kerry ya banbanta saboda asalin
ta ba tashin Nigeria bace a America ta tashi,
tasan duk wani salo na wayewa da gayu, sannan
kuma iyayen tama suna bakin k`ok`arin su ganin
sun mata duk abunda take so, yanzu ma haka
bata k`asar ta tafi Dubai inda za`a d`inka mata
rigar da zata saka yau wurin birthday party`n ta
kuma a yanzu suke sa ran isowar ta saboda
gashi rana har tayi.
*K`arfe 3:20pm* yayi daidai da dirar jirgin su
Kerry a babbar airport d`in aminu Kano dake
cikin jihar kano, jikin ta har rawa yake taga ta
fito daga jirgin dan bata san tsawon lokacin da
zasu d`auka a mota basu isa katsina ba, gashi
kuma bata son African time a harkar ta.
Da sauri ta fito daga jirgin ta fara hangen
inda zata ga Dad nata, da sa`a kuwa can ta

hange shi sanye da suit black and white yana
kalle kallen ta inda zaiga fitowar tilon `yar sa.
Da gudu ta iso gaban shi tare da hugging
nashi sosai kamar mata ta rungumi mijin ta,
"Welcome back my daughter" Dad d`in nata ya
fad`a bayan ta sake shi yana mata murmushi.
"Thank you Dad, amma ya kamata muyi sauri
Dad, kaga time is going friends d`ina har sun
fara shiri I know",
"Ok lets go dear" ya fad`a suka kama hanyar
fita.
Gaban parking area naga sun nufi wata
had`ad`d`iyar corolla s fara tas, tun daga nesa
ya latsa remote motar ta bud`e kanta, gaban
motar Kerry ta zauna bayan ta zauna ya rufe
mata k`ofar sannan shima ya shiga ya rufe tashi
k`ofar. Da k`arfi yaja motar jin autar shi tace
suyi sauri su isa katsina.
"I missed youh so much my Dad, tafiyar
kwana biyar amma ji nake kamar nayi one year
ban ganku ba",
"Muma munyi kewar ki my Kerry, musamman
ma Mum inki kamar zata min kuka wai sai ta
biki, sai da nata bata baki sannan ta hak`ura"
"Dad pls ka k`ara gudun nan bai fa ishe ni ba"
Gudun ya k`ara sosai kamar mai shirin tashi
sama, ba dan komai ba sai dan yaga ya
farantama Kerry rai.
*Karfe 4:34pm*
A wannan lokaci ne su Kerry suka iso garin
Katsina, sai a lokacin kuma ta kunna wayar ta,
nan taci karo da sak`onni sosai na *Arewa
Stars* wanda suka neme ta a waya basu same
taba, suna son jin kota dawo dan kar suita
wahalar shiri bayan kuma bata dawo ba.
Data ta kunna ta shiga watsapp,
*Arewa Stars* taci karo dashi a farko, nan taci
karo da conversations da yawa duk suna
magana ne akan jin ta shiru da akayi bayan
kuma sun gama plans d`in komai da zai wakana
a gurin.
Guntun murmushi tayi sannan ta rubuta
"Kar ku damu *Arewa Stars Allah ya min

dawowa kuci gaba da shirin ku daga inda kuka
tsaya, birthday party na dole sai anyi shi babu
gudu ba ja da baya.*
Nan suka hau replying na dad`in da sukaji,
sauka tayi daga watsapp d`in ta kira Deezee
makeover akan tana son ganin ta yanzu sannan
ta shiga wanka.
bata wani b`ata lokaci ba sai gata ta fito
daga wankan.
Trolly bag d`in da ta dawo dashi ta bud`e ta
ciro wata riga, "shantalin uwar nan kai" sis
Rabi`ah ta fad`a a lokacin data kalli rigar, ni kam
uwar gayyar kasa fad`in komai nayi saboda
tsantsar kyawun ta.
Doguwar riga ce irin mai bin jikin nan, an
tsaga gefe gefen ta, complete pink ce rigar arm
less, an k`awata ta da wasu irin manyan stones
masu walk`iya tamkar zinari, wuyan ta kuma V
neck ne inda aka zagaye shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login