Showing 9001 words to 12000 words out of 19493 words
Chapter 4 - A WUNI DAYA BOOK COMPLETE BY ESHAAAT.pdf
kuma
zaki iya magana tou ki fad'a min, wannan ishara
ce ga wasu mutanen masu hali irin namu, zan so
naji komenene saboda gaba".
Wata irin k'ara ta saki da k'arfi wadda ta
k'ara gigita Feenat, hatta da ruwan dam d'in sai
da ya canja launi, itatuwan gurin kuwa ganyen
su suka ringa cirewa da kansu suna fad'uwa
k'asa, jijjiga kanta ta hau yi baki na rawa tana
k'ok'arin yin magana amma ta kasa,
Da k'yar ta iya bud'e baki zatayi magana
kenan sai ga wani irin ruwa yana fita daga bakin
ta, wannan ruwan da yake fita shi ya hana ta
fad'in komai amma da alama tana son yin
maganar babu hali ne,
Hanya ta nuna ma feenat da hannun ta da
alama tana nufin ta tafi ne, amma Feenat tak'i
tafiya sai kad'a mata kai take tana hawaye,
"Bazan iya tafiya in bar 'yan uwana anan ba,
bazan tafi ba har sai kin fad'a min abunda muka
miki",
Itama kan taci gaba da kad'a mata tana
yunk'urin magana ta kasa,
Dogon tunani Feenat ta tafi a wani lokaci tun
kafin ta shiga group d'in *AREWA STARS,*
Wata rana suna zaune da Ummah tana mata
karatu, bayan sun gama ne take bata k'issoshi
ciki har da na aljanu a ciki, anan ne ummah ta
shaida mata da cewa duk ranar da taji zahirin
muryar aljani tou sai ta kurumce, haka kuma duk
ranar da kikaga aljani da idon ki sai kin makance
ko kuma ki haukace",
Saurin zabura tayi tare da fad'in "bama sai
kinyi magana ba amma ki sani nayi nadama,
nayi nadamar sanin *AREWA STARS* ina mai
baki hak'uri idan akwai abunda muka miki
wanda ba daidai ba, zan tafi gida zan shaidama
iyayen mu dan suzo su tafi da gawarwakin
wanda suka mutu, wanda sukaji rauni kuma a
kaisu asibiti" tana kaiwa nan ta kama hanyar
tafiya k'afarta babu takalmi kanta ko d'ankwali
babu.
Tayi tafiya mai nisa kafin ta isa bakin titi,
mutane ne sosai wurin tamkar da rana ne
saboda wani mai sai da shayi daya tada gen,
daga gefen shi kuma wani mai tsire ne shima da
tashi tawagar, ganin haka yasa feenat tayi
hamdala tare da k'arisowa inda suke.
Suna ganin ta kuwa suka hau daddarewa, su
a tunanin su mahaukaciya ce, sallamah tama
sauran da basu gudu ba amma suka k'i amsa
mata,
"Dan Allah ku taimake ni wallahi ni ba
mahaukaciya bace ina buk'atar taimakon ku ne",
Da sauri wani yace "dama kin tab'a jin inda
mahaukaci yacewa kansa mahaukaci ne? Ki
gafara ki bamu wuri dallah can kn kore mana
mutane daga majalisa",
Kuka ta b'arke dashi sosai tare da tafiya a
ranta tana tunani "banga laifin ku ba saboda
nayi kama da mahaukatan, duk abunda muka
shuka shine muke girbewa, ya Allah mun azabtu
hakanan, Allah ka sassauta min".
Wata mota ta gani irin babbar nan (j5) an
sako dabbobi a ciki, hannu tasa ta tsaida ita ta
tsaya, driver'n ne ya lek'o ta window saboda ta
gefen shi take yace "malama lafiya?",
"Lafiya k'alau malan, dan Allah idan cikin katsina
kayi ina neman taimako ne ka taimaka ka tafi
dani ka sauke ni ko bakin roundabout d'in farko
ne"
Mamaki k'arara a fuskar shi yace "ke amma
kin raina min hankali, a cikin tsohon daren nan
zakice na taimake ki, wata k'ila ma ke aljana ce,
ke ban yarda dake bama inga k'afarki" ya fad'a
yana nuna k'afar da yatsa.
"Wallahi malan kaga k'afa ta ni mutun ce" ta
fad'a tare da nuna mashi k'afar tana kuka.
"Katsina zanje, amma kinga motar duk dabbobi
ne daga kasuwar Mai_adua nake nayi dare, sai
idan kin yarda zaki shiga cikin su to",
Da sauri tace "wallahi na amince",
Bud'e mata yayi ta shige cikin su tsamo tsamo,
sauk'in ta d'aya ma dare ne akwai duhu duk
sunyi bacci. A cikin kashi da fitsarin su ta
kwanta tana sauke ajiyar xuciya.
Amrah and Rerbeeart sk novels,
Admns
ONLINE HAUSA READERSí ½í³š
[8:29pm, 27/09/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: í ½í²€
*A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣4⃣
Nan da nan kuwa suka isa katsina, cike da
tausayi yace mata "baiwar Allah!"
Amma ina, tayi nisa da baccin ta,
Sake kiranta yayi "ki tashi mun iso katsina ki
fad'a min wace unguwa zan kaiki?" Nan ma
shiru.
Parking yayi da motar ya fito ya zagayo ta
bayan inda take kwance cikin dabbobin ya
bubbuga ta a hankali ta bud'e idon ta da suka
kumbure sosai,
"Nace mun iso katsina ina zan kaiki?",
Tunani ta farayi inda zata je, nan ta yanke
shawarar kawai ta fara zuwa gida wurin
Ummanta,
Har ta bud'e baki zata fad'i haka kuma ta
tuna da Ummah zata iya yi mata komai idan
taje, ta fara zuwa ko gidan su Afnan ne yanda
koda sunje gida daga baya baxata mata komai
ba a gaban iyayen AFnan,
"Goruba road zanje wurin kalamu waheed
shopping mall",
Fita yayi ya koma gaban motar yaja ta sai
goruba road.
*K'arfe 12:30am.*
A daidai k'ofar gidan su Afnan aka dire
Feenat, a hargitse tama mai motar godiya tare
da shigewa gidan duk ta daburce,
Kai tsaye cikin gidan ta dosa, securites d'in
suka nemi hana ta shiga d'aya daga cikin su ne
yace "k'awar Afnan ce fa, kuma kun san ana
case na b'atar su Afnan, ku barta ta shiga wata
k'ila tana da masaniya ma".
"Shiga" ogan nasu yace mata, da sauri kuwa
ta shiga jiki sai rawa yake mata, tashin hankali
k'arara a fuskar ta.
Sallamah tayi murya na rawa ta shiga cikin
parlor'n,
Hankalin tane ya dad'a tashi yanda taga
manyan mutane zazzaune sunyi tagumi har da
masu yin kuka, daga gefe kuwa Ummah ce da
momy suna ta faman kuka babu mai rarrashin
wani,
Daga can k'arshen kujerun kuma mami
(maman Ruky) ce tayi tagumi ta zurfafa a
tunani.
Sai da tayi sallamah har sau uku amma babu
wanda yaji ta saboda duniyar tunanin da suka
lula,
Ata hud'un ce duka suka amsa mata a tare,
Kasantuwar duka mazan basu san ta ba yasa
suka bita da kallo dan yanda take a rikice kamar
mahaukaciya.
Da sauri Ummah ta d'ago kanta daga kukan
da take, cikin hanzari ta isa inda Feenat take ta
rungume ta da k'arfi tana sauke ajiyar zuciya,
Wani sabon kukan taci gaba dayi tana mai
tausayin ummanta, lokaci d'aya tabi ta xube
kamar ba ita ba.
Momy ma tasowa tayi da k'yar ta iya fad'in
"Safeenah! Ina kika baro min Afnan? ina fatan
kuna tare da ita",
Sakin ummah tayi ta koma ta rungume Momy
tana ta faman ajiyar xuciya ta kasa fad'in komai,
Dady jin haka yasa ya tabbatar da itace
k'awar Afnan, mik'ewa yayi ya isa inda take tare
da fad'in "Safeenah kiyi hak'uri ki daina kukan
nan ki mana bayanin inda yaran nan suke"
Nan ma shiru tayi dan bata san ta inda zata
fara ba,
Alhaji Abdallah yace "ki taimaka mana kiyi
shiru kiyi bayanin inda suke, idan basa raye ne
ko gawar su muna da buk'atar gani dan mu
sallace su"
Da sauri Alhaji Ma'aruf yace "haba Alhaji
Abdallah! Ya zaka ringa fad'in haka? Insha
Allahu yaran mu basu rasu ba, suna lafiya aduk
inda suke".
Ummah ta share hawayen ta tace "Safeenah
ki kwantar da hankalin ki ki mana bayani kinji?",
Mami ce ta taso daga kan kujerar da take
tace "duk wannan bashi zaisa tayi bayani ba,
idan kun kula ai a rikice take, ya kamata a bata
lokaci ta samu tayi wanka taci abinci ko zata
samu natsuwa",
Momy tace "hakane kam, muje kiyi wanka
idan ana binki bashin salloli ma sai kiyi".
D'akin Afnan momy ta kaita, da k'yar ta iya
yin wanka tayi alwala, koda ta fito har momy ta
fiddo mata wata doguwar riga ta Afnan, cif ta
mata a jiki kuwa sannan ta kama yin sallar isha
dan itace kawai a kanta,
Da gamawar ta tayi shafa'i da wutri, ta rok'i
Allah gafara sosai sannan ta fita parlor da
hijabin a jikin ta.
Ta samu iyayen sun kasa zaune sun kasa
tsaye, kowa yana tunanin inda yaron shi yake,
Da fitowar ta duk suka mik'e idon kowa a
kanta, kowa cike da son jin inda yaron shi yake.
Zama tayi akan carpet d'in dake tsakiyar
parlor'n, wani sabon kuka taji amma a haka ta
daure ta fara fad'in
"Da farko ina mai neman gafarar ku a bisa
k'arya da muka maku baki d'ayan mu, birthday'n
k'awar mu Kerry ne yau sai sa muka shirya
maku k'arairayi domin mu samu kubar mu mu
fita,
Sai gashi Allah ya gwada mana iyakar shi, ya
nuna mana mummunan aikin da muka aikata
tun a duniya duk da yake wannan bashi ne na
farko ba".
Cike da k'osawa Alhaji Abdallah yace "go to
the staright point, ina yaran suke yanzu!?"
Cikn rawar murya tace "suna *Ajiwa dam,*
but am sorry to say, duk basa cikin hayyacin su,
tayi kaca kaca dasu dan bana sa ran akwai
rayayyu a cikin su" tana kaiwa nan tayi shiru
sanadiyyar salatin da suka d'auka duka d'akin.
Alhaji Ma'aruf ne yayi k'arfin halin cewa
"wacece ita!? Wacece ta mana kaca kaca da
yara? Wallahi sai nayi ajalinta matuk'ar ta kashe
min yara, yara na 'yan biyu su kenan na mallaka
fa, wallahi sai ta raina kanta, zata san ta tab'a
iyalin Alhaji Ma'aruf Sale, ku tashi mu tafi wurin
ta ni zan maku maganin koma wacece ita, ko
ubanwa ya haife ta a fad'in k'asar nan sai ta
raina kanta" yana kaiwa nan ya fice sauran ma
suka mara masa baya,
Ganin za'a tafi abar su yasa Ummah da
Feenat ma suka bi bayan su.
Amrah and Rerbeeart sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERSí ½í³š
YINI ÆŠAYA 15
By babymsh 08:33 No comments
í ½í²€ *A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣5⃣
*NOTE:-* *kuyi hak'uri na rashin jin mu kwana
biyu, hakan ya faru ne na rashin isasshen time,
tests nake sosai ga kuma exam muna facing, am
in need of your prayers fans, love youh all.*
**************
A mota d'aya suka d'unguma suka tafi, sai
momy, ummah, mami da kuma Feenat driver ya
tafi dasu,
Sosai suke gudu nan da nan sai gasu a Ajiwa,
a bakin dam d'in sukaje tare da barin fitilun
gurin a kunne saboda duhun dake akwai.
Sosai suka razana ganin yaran su a babbaje
k'asa kamar marasa gata,
Wasun su kuka kawai suke dan babu alamar
rai a tare dasu musamman ma wanda suka
hango can gefen ruwa babu k'afa d'aya.
Feenat kuwa jikin ta sai rawa yake dan kar
wannan halittar ta dawo dan tana matuk'ar
tsoron ta, ta k'ank'ame ummanta sosai tana
kuka tana k'ara tuno da yanda aka ringa illata
mata abokai.
Alhaji Ma'aruf yaci gaba da dube duben inda
zai hango yaran shi, daga can nesa ya hangi
Reeshat k'ank'ame da MD duk kansu babu
alamar numfashi, wata irin k'ara ya saki cike da
tashin hankali, da k'arfi yace "idan ba tsoro ba ki
fito mana! Wallahi sai na kashe ki in har yara na
suka mutu, ki bayyana kanki inji wanene ubanki
a k'asar nan!" Yana kaiwa nan yaci gaba da
kukan shi kamar k'aramin yaro.
Su kuwa sauran suka hau bincikar yaran su,
Nan da nan kowa ya gano yaron shi amma fa
duk kanwar ja ce saboda babu alamar rayuwa a
tare dasu.
Sauran da babu iyayen su kuwa nan aka
barsu babu galihu,
A hankali suka fara jin wata k'ara mai had'e
da guguwa tana dosowa inda suke,
Sosai hankulan su suka tashi musamman
yanda sukaji k'arar tana k'ara tinkaro su, ga
wani irin haske daya bayyana a wurin,
Cike da tashin hankali suke kallon al'amarin,
Feenat kuka sosai take tace "ummah gata
nan, ta dawo zata kashe ni, dan Allah kice mata
tayi hak'uri ta koma"
Ummah ta rungume ta tace "ki kwantar da
hankalin ki, insha Allahu babu abunda zata miki,
kici gaba da addu'ah kawai kar ki daina, kar
kuma tsoro ya hana ki yi kinji?",
Kai kawai ta gyad'a mata idon ta kyam akan
guguwar dake nan dunk'ulewa wuri d'aya.
Dady ya rungume momy yana fad'in "mun
shiga uku! Ga Afnan bata numfashi kuma ga
wannan al'amarin, mu gudu kawai mu kai 'yar
mu asibiti dan tabbatar da ko tana da rai",
Cikin tashin hankali momy tace "insha Allahu
ma tana raye, Alhaji ban san ya zanyi ba idan na
rasa Afnan, itace 'yar budurwar da nake tak'ama
da ita gashi mahaifata ta lalace" ta k'ara
fashewa da kuka.
Dady yace "ki daina kukan nan kina k'ara
tayar min da hankali ne, mu tafi abun mu kawai
tunda dama da mota ta muka zo",
Daidai sunbi hanya zasu tafi kenan wannan
guguwar ta tare su, da k'arfi iska ya ringa dawo
dasu cikin mutane, duk k'ok'arin da suke na
tafiya amma dawo dasu iskan yakeyi, ga Afnan
dauk'e a hannun Dady, momy kuma ta rik'e shi
tam saboda tsabar tsoro, tunda uwar data haife
ta bata tab'a shiga tashin hankali irin wannan
ba,
Dole basu dan yanda zasuyi suka tsaya cikin
mutanen, shi kanshi Dady'n k'arfin hali ne kawai
ya hana shi yin kuka,
Dan kuwa Alhaji Bashir yanayin daya ga
Nuratun shi ciki dole shima ya shiga tashin
hankalin, kuka yake sosai kamar k'aramin yaro,
ga wata irin k'ara data sa babu mai jin wani
idan yayi magana.
A hankali guguwar ta dunk'ule wuri d'aya
inda ta koma wasu irin k'anana k'ananan halittu
bak'ak'e wulik, exact abunda ya faru a baya
yanxu ma shine, haka suka ringa cin junan su
har suka zama babbar halitta guda d'aya.
Feenat na gani ta tabbatar da wannan
halittar ce, nan da nan hankalin ta ya k'ara tashi
tana k'ara tuno baya, "tou wai ma me ya dawo
dani bayan ta sallame ni? Babu fa wanda yace
mu bisu mune kawai mukayi niyya" maganar
data ringayi a ranta kenan.
Da k'arfi halittar tayi wata irin k'ara wadda
sai da komai na wurin ya jijjiga, mutanen wurin
kuwa wasu suka ringayin sama da k'asa, basu
samu daidaituwa ba har sai da ta tsaya da
wannan k'arar ta fuskance su baki d'aya tana
k'ok'arin yin magana.
Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERSí ½í³š
By babymsh 08:34 No comments
[4:45pm, 2/10/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜:
í ½í²€ *A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣6⃣
Da sauri Ummah ta k'ara matsawa inda take
tace "dan Allah kar kiyi magana",
Duka hankulan su suka dawo kan Ummah
suna mamakin dalilin da yasa ta hana halittar
yin magana,
A tsorace Feenat tace "nasan dalilin hana ta
magana Ummah, amma kuma ya zama dole tayi
magana domin sanin musabbabin abubuwan
data mana".
Duk kanin su kallon Ummah da Feenat suke,
babu wanda ya iya yin magana saboda yanda
suke cike da tsoro, tun da suke a rayuwa basu
tab'a ganin halitta mai girman ta ba, ko a
frictions films basu tab'a gani ba, amma sai
gasu yau a gaban ta bayan ta illata masu yara.
Ummah ta juyo gare su tace "tabbas idan
muka bari ta mana magana duk kan mu muna
cikin hatsari, duk da bani da tabbas amma
wannan aljana ce, ta b'oye halittar ta ne saboda
matuk'ar muka ga zahirin ta tou no more us, da
zarar muka bari tayi magana har mukaji muryar
ta komai zai iya samun mu, saboda jin zahirin
muryar ta zai iya saka mu kurumce ko ma mu
haukace baki d'aya, ina mai bada shawara da
indai magana kuke son yi da ita tou mu rok'e ta
ta shiga jikin d'aya daga cikin mu sai ta mana
bayanin komai".
Kallon Ummah suke sosai saboda furucin ta,
Alhaji Ma'aruf daya gama tsurewa yace "indai
har sai ta shiga jiki na tou sai dai ta tafi bamu
son jin bayanin kuma mun yafe mata",
Dady ma bayan ya ajiye Afnan yace "ai
wallahi na yafe, mu dai dan Allah kiyi hak'uri ki
tafi kawai, ki bar mu mu koma gidajen mu dare
nayi sannan kuma bamu san ya lafiyar yaran mu
ba", bayan ya miyar da kallon sa ga halittar.
Momy ta d'aga kai alamar maganar da Dady
yayi gaskiya ne.
Alhaji Abdallah yace "bai kamata mu tafi haka
kawai ba, mu dai daure ta shiga jikin wanin mu,
kunga tanan ma zamu iya samu ta warkar mana
da yaran mu data illata",
Mami cikin kuka tace "kayya! Babu maganar
warkarwa a halin yanzu, kaga fa yanda tamin da
yarinya, Ruky na ta baro gida lafiya lau amma
yanzu jita fa, *Allah ya wadaren zuwa party ma
baki d'ayan shi"* ta k'ara fashewa da kuka.
Ummah ta sauke ajiyar zuciya tace "ni
nasan bazata iya shiga jiki na ba, amma barin
gani", ta koma close to halittan babu alamar
tsoro a tare da ita.
Sunkuyawa tayi har k'asa tace "idan zaki iya
shiga jiki na ki shiga, ki shige ni dan ki masu
bayanin komai".
Wata irin k'ara ta kuma saki bakin ta a
bud'e kamar zata had'iye Ummah, hakan bai sa
Ummah taji tsoro ta matsa ba, sai ma cewa da
tayi "ke nake jira".
Kai tahau girgizawa har a lokacin bata rufe
bakin ba, wannan blue hawayen sukaci gaba da
kwaranya daga idon ta, a hankali ta soma ja da
baya kanta sunkuye k'asa tana girgixa kanta.
Mik'ewa Ummah tayi tsaye tace "kun gani!
Na fad'a maku bazata tab'a iya shiga jiki na ba,
abunda yasa kukaga nace ta shiga d'in nasan
wasun ku zasuce k'arya nake kawia dai ina
tsoro ne, tou kun gani da idon ku, bazata tab'a
koda shafa na ba, haka kuma ina da tabbacin
baxata iya shigar Feenat ba, saisa ma kuka ga
ita kad'ai ta koma gida ba tare da ta mata wani
abu ba".
Kai sukaci gaba da jinjinawa alamar sun
gamsu da duk kalaman Ummah,
Dady yace "tou yanzu miye mafita? Nidai a
zahirin gaskiya ina tsoron ta shige ni dan kar
tak'i fita, tou wai ma baiwar Allah me yasa ta
kasa shiga jikin ki da 'yar ki mu kuma kike
tunanin zata iya shigar mu?".
Ummah ta ce "ba