Showing 6001 words to 9000 words out of 19493 words

Chapter 3 - A WUNI DAYA BOOK COMPLETE BY ESHAAAT.pdf

05 Jun 2025

1329


muje zuwa dai inji ni Amrah.
Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[8:14pm, 21/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘:
💀 *A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣0⃣
Bari mu koma b'angaren gidajen su.
*Karfe 10:30pm*
*~Gidan su Feenat.~*

Ummah ce zaune tayi tagumi baki d'ayan
hankalin ta a tashe yake, ita dai tasan a duk
inda Feenat take ya kamata by now ta dawo
gida, "to ko dai jikin maman Afnan d'in ne ya
rikice?" Ta fad'a a ranta,
"To inko hakane ai ya kamata Safeena ta kira ni
a waya ta sanar dani in ma acan zata kwana,
amma gashi har dare yayi babu ita babu kiranta
kuma",
Wayar ta ciro nan ta hau neman lambar Feenat
tana ta ringing amma bata d'aga ba, a hankali ta
soma jiyo k'arar ta daga d'akin Feenat alamar
can ta barta, "to kenan anan ta bar ta kome?",
D'an guntun tsaki tayi tare da komawa ta
kishingid'a ko zataji zuwan Feenat dan har a
lokacim bata rufe gida ba.
Jin shiru har sha d'aya ta kusa yasa tace
"bari dai in tashi in tafi gidan su Afnan d'in sai a
fad'a min asibitin da maman take, wata k'ila dai
babu lafiya",
Hijabin ta ta zira a hargitse ta rufe gidan da
makulli ta fita. Da sa'a kuwa tana zuwa bakin
titi ta samu napep babu kowa, bata koyi ciniki ba
ta hau ta kwatanta inda zai kaita.
*Karfe 10:49pm*
*~Gidan su Afnan.~*
Momy ce zaune ta rungume Affan dake ta
bacci abin sa hankali kwance, ita kuwa tv kawai
ta tsura ma ido tana kallon NTA wai a nufin ta
ko za'a fad'i cewa wani jirgi yayi had'ari amma
har yanzu babu, canjawa tayi ta kai AIT amma
nan ma babu, tab'e bakin ta tayi tace "wata
k'ila har an gwada ban gani ba, Allah dai yayi
ma duk musulman cikin jirgin rasuwa, wanda
suke raye kuma Allah ya basu lafiya, nayi zaune
har Alhaji ya kwanta ya barni da wannan
rigimammen",
D'aukar Affan tayi ta d'ora a kafad'ar ta
sannan ta kashe kallon,
Daidai zata kashe wutar parlor'n ne yayi daidai
da shigowar Umman Feenat.
Cikn mamaki Ummah ta gaishe da momy,
momy ma amsawa tayi da mamaki dan sam

bata wayi Ummah ba,
"Ina zuwa dan Allah" momy ta fad'a tare da
nufar d'akin Affan ta kwantar dashi sannan ta
dawo.
Zama tayi tace "baiwar Allah lafiya dai a cikin
wannan daren?",
Ajiyar zuciya ummah ta sauke sannan tace "to
ko dai ba inda nake son zuwan bane nazo? Ni
inda zanje fa mai gidan bata da lafiya tana
asibiti, kuma tun a waje mai gadi yace min wai
me nan gidan lafiyar ta lau",
Momy tace "Allah sarki! Gaskiya ba nan
bane sai dai ko makwaftan mu, ya sunan mai
gidan da kike neman?",
"Ban san sunan su ba gaskiya, sai dai nasan
sunan 'yar Afnan Abbas tana da k'ane kuma
Affan, maman ta bata da lafiya ne 'yata ta tafi
ganin ta, amma gashi har yanxu bata koma gida
ba shine nake son jin ko lafiya?, amma babu
komai nagode barin ci gaba da bincike ko Allah
zaisa in dace", ta fad'i hakan ne tare da mik'ewa
tsaye tana neman fita.
Cikin mamaki Momy ke kallon Ummah, baki a
sake da 'kyar ta iya furta "b..b..b..baiwar Allah
ai nan ne gidan su Afnan Abbas, kuma nice
mahaifiyar Afnan, sai dai kuma ni lafiya ta k'alau
babu abunda ya same ni",
Da sauri Ummah ta dawo ta zauna tana
kallon momy, "kina nufin 'Yata Safeenah Al-
hassan ba nan tazo ba kenan?",
"Gaskiya ba nan tazo ba, k'ila dai wani wurin
zataje shine ta miki k'aryan zatazo gani na",
"Hajiya dan Allah ki kira min Afnan in tambaye
ta ko tana da masaniyar inda Safeenah ta tafi"
ummah ta fad'a tashin hankali k'arara a fuskar
ta,
momy cike da tausayin Ummah tace "sai
yanzu na gane ki ashe kece maman Feenat, kin
san kolacin da muka had'u last speech and
prizes given d'in su ban kalle ki sosai bane,
wallahi Afnan bata nan taje gidan rasuwa ne",
Ummah tayi salati ta rufe idon ta tana
matsar hawaye, "to ina Safeenah taje? yaushe

Safeenah ta koyi wannan halin? Kenan k'arya
tamin? Allah yasa dai ba maza tabi ba suka
sace min ita" wasu zafafan hawaye sukaci gaba
da bin ta.
Momy kuwa a ranta cewa take "kai! Allah ya
shiryi yaran yanzu, k'ila ma yawon iskancin ta
xata tafi shine ta ma uwarta k'aryar banda
lafiya, kuma ta rasa wanda zata ce baida lafiya
sai ni",
Dady'n Afnan ne ya fito yana fad'in "maman
Afnan lafiya kuwa?", yana fad'in haka yana
kallon Ummah cike da mamakin yanda tazo
gidan su cikin wannan daren dan shi tsoro ma ta
bashi.
Momy bata bashi amsa ba sakamakon
sallamar da sukaji, maigadi ne ya shigo yana
fad'in "yallab'ai wani bawan Allah ne yaxo, da
ganin shi dai babban mutum ne yace wai sunan
shi Alhaji Abdallah, wai baban Ihsan ne k'awar
Afnan, wai yana son ganin ka",
Dady yace "Alhaji Abdallan da akace yayi
hatsarin jirgi ya rasu!? Kace masa ya shigo".
Tir k'ashi! Kallon sis R. Nayi cike da k'aguwa da
shigowar Alhaji Abdallah, muje zuwa dai sis R.
Ta fad'a, sai kuma gobe zakuji posting d'in mu
insha Allah.
Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
YINI ÆŠAYA 11-12
By babymsh 08:31 No comments
[11:36pm, 23/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣1⃣
Ba'a jima ba kuwa sai ga maigadi tafe Alhaji
Abdallah a bayan shi,
A kid'ime Dady ya mik'a mashi hannu suka
gaisa tare da cewa "bismillah ga wurin zama",

Alhaji Abdallah ya zauna sannan yace "nazo
ne dama inji ko lafiya tun da yamma Ihsan ta
baro gida tace nan zata zo wai Afnan bata da
lafiya, kuma gashi har yanzu bata koma gida ba"
Ido bud'e momy ta kalle shi cike da mamaki
tace "Alhaji ai muma nan tun yamma Afnan
tabar gidan nan wai kayi accident da jirgin sama
ka rasu",
Salati Alhaji Abdallah yayi a bayyane yana
mamaki, a ranshi yace "kenan Ihsan bata zo nan
ba?",
Momy tace "innalillahi wa inna ilaihi rajiun!
k'arya Afnan tamin kenan dama ba can zataje
ba?",
Ummah dai na tsaye cikin tashin hankali
tana sauraren su, sun jima d'akin babu wanda
ya kuma cewa wani abu kowa da abunda yake
sak'awa a ransa, sai daga baya ummah tace "in
kuwa hakane tou duk inda yaran nan suke suna
tare, babu mamakin ko wani wurin sukaje shine
suka tsara mana k'arairayi mu kuma muka
yarda, Allah dai yasa lafiya suke".
Dady yace "wannan hakane baiwar Allah! Tou
ina yaran nan sukaje ne?",
Alhaji Abdallah yace "nima tunanin da nake
kenan, wai yara k'anana har sun san su had'a
mana k'arya idan zasu tafi, kuma ni wallahi
bana kullen Ihsan sosai, inda ma ace ina mata
tsanani ne da sai ince banga laifin ta ba".
Dady cikin tashin hankali yace "barin tafi
Office yanzu nasan Sajent Musa yau night gare
shi, inspector Bala ma kamar night ne saboda
sanda na baro office lokacin yaje, barin hanzarta
in tafi",
Alhaji Abdallah yace "na manta ashe tare
nake da DSP, ai da sauk'i ma kenan, sai mu tafi
tare".
Wayar Dady ce ta d'auki k'ara, dubawar da
zayyi yaga Inspector Ashir ne, d'aga kiran yayi
tare da fad'in "akwai magama inspector, gani
nan zuwa Station d'in yanzu",
"Yallab'ai nan ma dai akwai matsala, mutun
biyu sukazo wai suna so a masu cigiyar yaran

su sun fita tun yamma basu dawo ba, d'ayan ma
wai twins ne yaran", inspector'n ya fad'a cike da
girmamawa.
Dady ya kalli Alhaji Abdallah sannan yaci
gaba da fad"in "same case da zai kawo ni
station d'in, ka jira ni yanzu zan taho" yana
kaiwa nan ya kashe wayar tare da d'aukar key'n
mota ya fita, Alhaji abdallah ma ya mara masa
baya.
Basu jima a hanya ba suka isa station d'in,
cikin hanzari Dady ya nufi office d'in Inspector
Ashir ya samu mutun biyu dattijai zauna sai
raba ido suke kamar sunyi k'arya an turke su
(lol..).
Bayan inspector Ashir ya saaraa ma Dady
sannan yace "yallab'ai kamar yanda na fad'a
maka to ga mutanen nan, amma dai kaji daga
bakin su",
D'aya daga cikin su yace "sunana Alhaji
Ma'aruf, yara na 'yan biyu Shareef da Shareefat
ne suka bat'a",
Cikin mamaki Dady yace "b'ata? Garin ya
hakan ta faru?"
Alhaji Ma'aruf yace "d'azu ne da yamma
lokacin da bana nan Shareef yaje wurin Mamin
su yace wai zasu je wata gaisuwar rasuwa
baban classmate d'in su ya rasu, to da naji su
shiru shine na gano inda sukace sunje d'in da
k'yar da wahala ma na gane gidan, naje sun
shaida min su babu wanda ya rasu a gidan su,
suma 'Yar su ta fita tun yamma bata dawo ba,
duk gidajen dangi da nake tunanin yaran nan
zasuje naje amma ban same su ba, ga lambobin
wayar su bata shiga, hankali na ya tashi sosai
shine nazo nan ko da wani abu da za'a iya yi
min".
nannauyan ajiyar zuciya Dady ya sauke,
gaban shi ya k'ara fad'uwa yayin da bugun
xuciyar shi yake tafiya da sauri sauri, ya jima a
haka kafin yace "to kai fa bawan Allah me ya
faru?"
D'ayan mutumin yace "nifa tawa 'yar gidan
mahaifiya ta tace min zataje ta duba ta wai ta

dad'e bata je ba, nikau har da dad'i naji ta kula
min da uwa, jn ta shiru har dare yayi bata dawo
ba yasa na kira ta amma tak'i shiga, na kira
mahaifiya ta tace min ai Nuratu bataje inda take
ba, hankali na ya tashi sosai, nayi iya bincike na
amma ban same ta ba, shine na yanke hukuncin
zuwa nan nasan insha Allahu zakuyi bakin
k'ok'arin ku".
Alhaji Abdallah in banda kallon su babu abun
da yake yi, to wai miye dalilin da yasa yara
matasa suka b'ata a lokaci d'aya? Kuma same
case ne kowa k'arya yayi kafin yabar gida?
Tambayar da yakewa kansa kenan wadda yasan
bata da amsa har sai lokacin da aka gano yaran.
Dady ya gyara murya yace "abunda ya kawo
ku nima shine muhimmin abunda ya fito dani a
wannan lokacin nida bawan Allah'n nan.." nan
ya basu labarin duk abunda ya sani har Ummah
dake gidan su akan b'atar 'yar ta itama.
Alhaji Ma'aruf yace "tabbas yaran nan aduk
inda suke suna tare, baza'a tab'a kiran wannan
da coincidence ba saboda abu ne wanda yake a
bayyane, fatan mu dai Allah yasa a duk inda
suke suna lafiya",
Alhaji Bashir (Baban Nuratu) yace "ai sai asan
abunyi ba wai mu tsaya anan muna magana ba,
ko gidajen radio ne sai mu fara xuwa kafin gari
ya waye asan abunyi".
Da wannan maganar suka rantaya su duka
hud'un a cikin motar Dady, basu zarce ko ina ba
sai VISION FM, nan suka bada sanarwar b'atan
yara matasa wanda dukan su babu wanda ya
wuce shekaru 16-17 ba.
Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚
[11:43pm, 23/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*

Page1⃣2⃣
K'arfe 11:05pm
*~AJIWA DAM~*
Wani irin haske ne mai had'e da guguwa mai
k'arfi ya haskaka wurin,
Feenat dake gefe makure har ta sik'e da
kuka tana ganin hasken ta saki ajiyar zuciya dan
wani sanyi sanyi taji a ranta, d'aga kanta da
zatayi taga yanda akayi kaca kaca da *AREWA
STARS* kamar wasu dabbobi,
Can kuma hasken ya canja launi izuwa red
colour,
Md da Reeshat dake gefen ruwa suna kallon
ikon Allah bayan hasken ya b'ullo sukaji alamar
motsi ata inda suke, cike da tashin hankali
Reeshat ta k'adaddabe Md gabanta sai dukan
uku uku yake, bata ankara ba taji anja gashin ta
dataima mayen gyara sama ana ta wulu wulu
dashi, sosai take jin zafi dan dama a ranar tayi
sabuwar relaxer, sai da tayi sama sosai da ita
sannan ta jefar a bakin wani k'arfe da akebi ta
jikin shi idan za'a shiga ruwa, take ta sume
bayan ta sai zubar da jini yake.
Md ma ta up side down ta d'auke shi da
k'arfi ta jefar a jikin Reeshat, shima sumewar
yayi inda k'afar shi d'aya ta cire tun daga cinyar
shi sai zubar jini take, cinyar daban ta fad'a a
cikin ruwa sai sauran gangar jikin ne a jikin
Reeshat.
Nuratu, Shamow da Sady sun dunk'ule junan
su suna kallon yanda wannan halittar take wuji
wuji da Md da Reeshat saboda har a lokacin
wannan jan hasken bai mutu ba, hankalin su
tashe dan sun san dole suma sai anzo kansu,
babu mai iya yiwa d'an uwan sa magana a cikin
su sai faman rawar lab'b'a suke, ga wata irin
zufa na keto masu duk da sanyi sanyin ruwan
Dam d'in dake akwai amma bai hana masu jin
zafi ba.
A hankali wani irin ruwa ya ringa saukowa a
daidai inda suke, ruwa ne bak'i k'irin tamkar
ruwan kwata ga wari da yake yi,
Da mamaki a duk inda ya d'iga na jikin su sai

yayi wani irin bororo kamar masu gyambo, haka
yaita sauka a jikin su har saida yayi masu kaca
kaca da jiki kamar wanda suka k'ok'k'one,
A had'e ta jefo masu wani d'an k'aramin dutse
wanda baki d'ayan su ya had'a ya sumar dasu a
lokaci d'aya basu kuma sanin kome yake wakana
ba.
Dariya ta kuma fashewa da ita da k'arfin
gaske har sai da itacen wurin suka ringa girgiza
da kansu, k'yallayen da akayi decoration dasu
kuwa da kansu suka ringa yayyagewa, speakers
da generator kuwa rugurgujewa suka ringayi
kamar yanda ake rugurguza dunk'ulallen gishiri
ko maggi,
Ta dad'e tana dariyar kafin ta d'aure fuska
wasu irin blue ruwa suka ringa kwaranya daga
idanuwan ta wanda da alama ruwan hawaye ne,
Girgiza kanta tayi taci gaba da waigawa
gabas da yamma bata ga kowa ba, ta diba kudu
inda taci karo da Samir wanda ya gama
kid'imewa amma shi a zaton shi ya tsira saboda
a wani lungu ne ya lab'e inda matuk'ar baka san
yana wurin ba to bazaka ganshi ba, amma da
mamaki wannan halittar ta zira dogon hannun ta
ta cafko shi a tafin hannun ta, bakn ta takai a
cikn wandon shi sai ga kayan marmarin sa
(lol..) a bakin ta had'e da jini sai zirara yake,
Tofar dashi tayi sannan ta jefar da Samir
wanda a lokacin har ya sume tsabar azaba da
tayi masa yawa.
K'arfe 11:30pm
*~kerry~*
tayi tafiya mai nisa har sai da ta sik'e da
tafiyar ta nemi wuri ta zauna sai haki take,
hankalin ta tashe sai nishin gajiya take,
A hankali ta fara jin hayaniya a kunnen ta
wadda ta k'ara tsorata ta, k'ara kasa kunnenta
tayi taji k'arar tana k'ara yawaita,
"Oh Dad help me!" Kawai take fad'a,
Da k'arfi halittar ta jawo ta da hannu ta rik'e
ta da tafin hannun ta, wata shu'umar dariya tayi
wadda ita kad'ai tasan ma'anar ta sannan ta
busa ma Kerry iska da bakin ta adaidai kanta

sannan ta jefar da ita, take Kerry ta sume
itama.
bakin Dam d'in ta koma ta kalli Arewa nan
taga Feenat takure sai rawar jiki take,
Hannun ta tasa ta jawo ta ta rik'e ta, a
hankali Feenat ta fara furta *"AU'DHU BI
KALIMATULLAHI TAAMMAAT MIN SHARRI MA
KHALAKA, BISMILLAHILLADHI LA YADHURRU
MA'ASMIHI SHAI'UN FIL ARDI WALA FISSAMA'I
WAHUWAS SAMI'UL ALEEM"*
Amrah and Rerbee'art sk novels,
Admins
YINI ÆŠAYA 13-14
By babymsh 08:32 No comments
[8:20pm, 27/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀
*A YINI 'DAYA* 💀
�💀 💀�

*®NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣3⃣
Wata irin k'ara ta saki da k'arfin gaske tare da
yin wulli da Feenat can nesa da ita,
Wannan blue hawayen ne yaci gaba da
kwaranya daga idonta, tsantsar damuwa ce
k'arara a yamutsatssiyar fuskar ta,
A razane ta koma inda ta jefar da Feenat ta
sake d'aukar ta ta matse ta tam a hannun ta,
tsananin girmanta yasa kamar bata rik'e komai a
hannun ta ba,
Sosai Feenat ke kuka, a wannan karen ma
sai ta kasa yin ko addu'ar ma, a nan ne ta
samu damar dunk'ule ta wuri d'aya ta nad'e ta
kamar gammon kifi, ta d'aga ta zata jefa a cikin
ruwa saboda yanda ta b'ata mata rai, duk cikin
su babu wanda yayi k'ok'arin hana ta abunda
take yi sai Feenat, hakan yasa kawai ta yanke
hukuncin ta jefar da ita a cikin ruwa yanda tasan
babu ita babu fita saboda girman ruwan bama
za'a gane akwai mutun a ciki ba,
Daidai ta d'aga ta zata jefar kenan Feenat ta
sake bud'e baki tace

*"LA HAULA WALA K'UWWATA ILLAA BILLAH,
U'I'DHU KUMAA BI KALIMATULLAHI TAAMMAAT
WA MIN KULLI SHAID'AANIN WA HAAMMAAT
WA MIN KULLI AININ LAAMMAAT,
ASTAGHFIRULLAHI WA ATUBU ILAIK, YA ALLAH
NASANI NI MAI LAIFI CE, INA NEMAN GAFARAR
KA YA ALLAH, ALLAH KAI KAD'AI KAKE DA IKON
TSERATAR DANI DAGA WANNAN AL'AMARIN,
ALLAH NA ROK'E KA DA SUNAYEN KA
TSARKAKAKKU, KA CECE NI DAGA K'ANGIN DA
NAKE CIKI",*
Tana kaiwa nan tayi shiru sai wasu zafafan
hawaye dake fita daga idon ta, kawai ta barma
Allah al'amarinta ne dan tasan shine kawai zai
iya fitar da ita, bata da k'arfi ko wata dabara sai
Allah.
Da mamaki sai ga wannan halittar ta ajiye
Feenat k'asa a hankali tana sauke ajiyar xuciya,
Sumbatar ta tayi a goshi wanda yayi daidai
da saukar hawayen ta akan fuskar Feenat,
Da sauri Feenat ta d'ago kanta ta kalle ta
tace "yake wannan halitta, nasani mu masu laifi
ne ga Allah kuma laifin da muka aikata ne yake
bibiyar mu, ina so ki bud'e bakin ki ki fad'a min
abunda muka miki saboda mu rok'i gafarar ki"
jiki na rawa tayi maganar bayan ta sunkuyar da
kanta k'asa saboda halittar fuskar tama kanta
abun tsoro ce, just imagine halittu da yawa su
dunk'ule su zama guda d'aya, ya girmanta zai
kasance?
Kanta ta gyad'a alamar baxata fad'i komai
ba, Feenat tace "dan Allah idan kina jina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login