Showing 12001 words to 15000 words out of 19493 words
Chapter 5 - A WUNI DAYA BOOK COMPLETE BY ESHAAAT.pdf
wai ina da tabbacin zata
iya shigar ku bane, ina dai tunanin zata iya d'in
ne, akwai wasu abubuwan wanda muka rik'a
nida Safeenah wanda ina da tabbacin babu wani
abun cutarwa da xai iya cutar damu har sai idan
Allah yayi nufin sa akan mu".
*Amrah nd Rerbee'art sk novelsí ½í³š*
[4:54pm, 2/10/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜:
í ½í²€ *A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣7⃣
Dady yace "menene wannan abun da kuka rik'a
baiwar Allah?"
Ummah tace ba wani abune mai wahala ba,
wasu kalmomi ne wanda baku kad'ai ba hatta da
*Amrah and Rabiatu sk Fans* idan suka rik'e su
zasu kub'uta daga duk wani aljani namiji ko
mace, kai baki d'ayar al-umman musulmai ma
nake maka magana. Kalmomin sune:-
*LA-ILAHA ILLA-LLAHU WAHDAHU LAA
SHARIKALAHU LAHUL-MULKU WA LAHUL-
HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KAD'IR*
so d'ari ko wace safiya, sai kuma *A'UDHU BI
KALIMATULLAHI TAAMMAAT MIN SHARRI MA
KHALAK* itama sau d'ari a yini, sai *AYATUL
KURSIYYU, BISMILLAHILLADHI LA YA DHIRRU
MA'ASMIHI SHAI'UN FIL-ARDI WALA FISSAMA'I
WAHUWAS-SAMI'UL ALEEM, U'IDHI KUMA BI
KALIMATULLAHI TAAMMAAT WAMIN KULLI
SHAID'ANIN WA HAAMMAT WA MIN KULLU
AININ-LAAMAT, FALAQ, NAS DA IKHLAS K'AFA
UKU UKU* a kowace safiya, idan mutun yana da
yara ma yana masu tou insha Allahu babu
abunda zai same sa, hatta da sihiri ko kambun
baka yana da wuya ya kama mutun matuk'ar ya
rik'i wannan adhkar d'in, sune na rik'a kuma
koda wace safiya sai munyi su tare da Safeenah
inayi tana amsawa kafin ta fita ko ina, kuma
kuma inda zaku rik'e su am sure babu abunda
zai iya cutar daku".
Dady yace "tabbas wannan wani babban
makami ne kuka rik'a, kuma muma insha Allahu
daka yanzu mun rik'e su kenan", (ina fatan
masu karatu ma zasu rik'e su saboda suna da
muhimmanci a rayuwar mu, musamman ma a
wannan lokacin da kana baccin ka wasu na
maka nasari, Allah yasa mu dace ameen).
Ummah tace "tou yanzu ya kukace? A barta
ta tafi ko kuwa akwai wanda zai bari ta shiga
jikin sa? Nasan dole tana da maganganu a bakin
ta, sannan zamuyi da wajewa in har ta shiga
jikin mutun zata fita, idan ba haka ba kuma
komai na mata ita taja, ina da babban malamin
da zai iya salwantar da rayuwar ta, malam
Mu'awuya *(na cikin JINNUL_ ASHIQ)* Zai iya
da ita, barin ma nasan bazatayi haka ba".
Alhaji Abdallah yace "babu komai ni ta shiga
jiki na, a adhkar d'in da baiwar Allah'n nan ta
bamu na rik'e su sosai, kuma nasan koda ta
zauna a jikina baxata dawwama ba saboda zan
kasance mai yawan yin su insha Allahu".
Dad'i sukaji su duka, Ummah da Alhaji
Abdallah suka k'ara matsawa kusa da wannan
halittar tace "ga wanda zaki shiga nan, amma
ina fatan bazaki cutar dashi ba" kai kawai ta
d'aga masu tare da b'acewa b'at daga wurin.
Su duka sai da suka tsorata, har umman ma
yanzu ta tsorata,
Bayan 'yan seconds Alhaji abdallah ya fasa
wata irin k'ara da k'arfi kamar ba mutun yayi ta
ba, nan ya hau jijjikar jikin sa hawaye na fita
daga idon sa.
Sun dad'e a haka babu wanda ya iya furta
komai kafin ya bud'e baki yace "yaran ku sun
illata min duka iyali na (family na), tun daga
mamana, babana, yarana uku da miji na, wasu
sun mutu a dalilin haihaye su da suka ringayi,
babana ya tsufa sosai da mamana, hakan yasa
basu da wani k'arfi sosai abu kad'an yana iya
yaji masu ciwo, sun mutu baki d'ayan su, sai
yaro na d'aya jinjirin da na haifa yau kwana biyu
shima ya mutu, miji na da sauran yara na biyu
sun ji ciwo sosai. Bayan nan kuma a inda na
zauna ina karb'ar gaisuwar mutane ma basu
barni ba, sai da suka k'ara kashe min wasu
mutanen wasu kuma suka gudu, taya kuke
tunanin zan k'yale su? Ni ba muguwa bace
saboda bani da ra'ayin shiga bil-adama, Feenat
kuwa tafi k'arfi na, a lokacin dana d'auke ta da
nufin yi mata wani abu kawai na kasa, kuma ma
inda ace na mata wani abun da na cuce tane
saboda babu abunda tamin, gefen su take tana
dana sanin xuwa wurin da tayi, hakan yasa na
bata izinin ta tafi gida, tun kafin ta tafi ta
buk'aci na mata bayanin dalilin da yasa na masu
haka amma na kasa saboda bana son taji murya
na a zahiri, yaran ku kuma babu wanda na kashe
sai dai duk sun raunana sosai, zasu farfad'o
koba yanxu ba, ku kwashe su ku tafi dasu
sannan ku masu gargad'in kar su sake zuwa
wurin *party,* koda wani sukaji xaije tou su hane
sa da xuwa, ni abun da na masu mai sauk'i ne,
na tabbatar da inda wasu ne a cikin jinnu har
kashe su zasu iya yi, gashi kuma duk cikin su
babu mai neman kariya daga Allah".
*Amrah and Rerbee'art sk novelsí ½í³š*
[5:03pm, 2/10/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜:
í ½í²€ *A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣8⃣
Tayi shiru kafin taci gaba da "akwai abubuwa da
dama da mu jinnu bama son su, matuk'ar bil-
adama suka rik'e su tou komai muguntar aljani
bazai iya ma mutun komai ba, kamar abubuwan
da matar nan ta lissafa maku, bayan su kuma
akwai yawan amfani da man hulba, bamu son
warin shi sosai, sannan kuma akwai miski,
shima idan bil-adama yana amfani dashi babu
abunda jinnu zasu iya masa, yin addu'ah kafin
shiga ban d'aki yana makantar mana da
idanuwa, akwai su dai da dama wanda idan na
tsaya lissafo su zaku iya kwana anan. Kai kuma
bawan Allah" tayi nuni da inda Alhaji ma'aruf
yake da yatsa tace "ka kiyaye ni! Zan maimata
maka cewa ni ba muguwa bace, inda ace ni
muguwa ce da ko gawar yaranka bazaka tayar
anan ba, kana tak'ama da kud'i kud'in banza
gareka! Sai kuje yanzu kud'in ka su warkar
maka dasu ai, na haukatar da uwar birthday d'in
saboda itace silar komai, sannan kuma ita da
saurayin tane suka kashe min iyaye, saurayin
nata ma na haukatar dashi, tunda iyayen su
masu kud'i ne sai su neman masu magani, bana
buk'atar ku sake nema na saboda na gama
daku" tana kaiwa nan Alhaji Abdallah yayi
atishawa da k'arfi had'e da yin hamma.
Koda na duba naga duk jikin su a sanyaye
yake har dai Alhaji Ma'aruf da hawaye ke
kwaranya daka idon sa, fatan shi dai Allah yasa
yaran sa zasu mik'e da k'afafun su.
Dady da momy dai kuka ne kawai aikin su,
sun tasa Afnan gaba da har yanzu bata da
alamar tashi, baccin ta fad'a masu cewa bata
kashe su ba da sunce Afnan bata da rai.
Bayanin komai suka ma Alhaji Abdallah, wurin
'yar sa ya koma ya d'aura ta akan cinyar sa
yana fad'in "why Ihsan? Mesa kika zab'i wannan
rayuwar? Mesa kika d'aukarwa kanki wata
tarbiyyar da ban sanki da ita ba? Gashi yanzu
kin jawa kanki, ga yanda Allah ya maku, wannan
ishara ce ga duk masu hali irin naku, musamman
matasan yanzu da suka miyar da *party* tamkar
ruwan shan su, suma iyayen su k'arya a kowane
lokaci kawai dan su tafi *party,* ga yanda tayi
dasu *A YINI D'AYA* ta gama da rayuwar su"
yaci gaba da kuka sosai yana jijjiga ta.
Haka Dady ma ya ringa jijjigar Afnan wai a
nufin shi ko zata farka amma babu ko alama,
Momy da kuka ya gama cin k'arfin ta tace
"Afnan ki rasa irin k'aryar da zaki mana sai ta
mutuwa? Ki danganta mahaifin k'awarki da
rasuwa? Kenan dama ciwon k'arya kike min a
lokacin da nace miki ki tafi islamiya? K'arya kike
min da kikace zakije school d'in ku siyen kayan
practical? Fita *party* kawai kuke zuwa Afnan?
Haka kike so yaran ki su miki Afnan? Na gama
yarda dake har abada, na gama yarda da duk
abunda zaki fad'a min, ina fatan Allah ya gwada
min ranar da kema 'yar ki zata miki haka, bana
fatan Affan yayi koyi da mugun halink..." Bata
k'arisa maganar ba sanadiyyar toshe mata baki
da Ummah tayi tana fad'in "kar ki mata baki
Hajiya, kefa uwa ce kuma duk bakin da kuka
mata zai iya binta, dan Allah kar b'acin rai yasa
ki fad'in munanan kalmai akan 'yarki da kika
haifa".
Cikin kuka Momy tace "dole ne yasa ni
fad'in haka, Afnan taci amana ta taci amanar
mahaifin ta, ni a kowane lokaci ina tink'aho da
ina bama 'yata tarbiyya mai kyau, ina alfahari da
yanda nake basu tarbiyya ita da k'anin ta, ashe
duk a banza, tana jefar dasu ne a cikin gida kafin
ta fita, aikuwa kinma kanki, 'yar secondary
School d'in da kike shekarar k'arshen ma bazaki
k'arisa taba aure zan miki, mu koma gida
wallahi sai kin fitar da miji, idan ma baki dashi
zan kai hoton ki masallaci mai so yazo zan basa
sadakar ki"
A hankali Afnan ta fara bud'e idon ta, tana
d'ora shi akan Momy da sauri ta rufe tana
rewinding d'in abubuwan da suka faru tun daga
k'aryar da tayi kafin ta baro gida, casun da
sukayi da kuma yanda wannan halittar ta ringa
yi dasu, wasu zafafan hawaye suka ringa
kwaranya daga idon ta, "tou me ya kawo su
Momy nan? Ya akayi suka san muna nan? Me
ma ya same ni naji jiki na duk babu dad'i?"
Maganar xuci ce tayi amma bata san ta fito
zahiri ba.
*Amrah and Rerbee'art sk novelsí ½í³š*
YA 19-25
A YINI ÆŠAYA 19-25
By babymsh 08:35 No comments
[10:42am, 13/10/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: í ½í²€
*A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 19-22
"Lokacin tonuwar asirin ku ne yayi" momy ta
fad'a tare da watsa mata wani mugun kallo.
Duka wurin shiru kake ji babu mai magana in
banda sautin kukan Afnan dake tashi,
Da k'yar ta iya furta "momy sharrin shaid'an
ne dan Allah kiyi..." Bata gama maganar ba
sanadiyyar tsawa da ta yi mata da k'arfi dolen
ta tayi shiru.
Nan iyayen suka hau harhad'a su wuri d'aya
suna k'ara tausaya masu musamman ma Md da
cinyar shi ta fita daga gangar jikin sa baki d'aya
duk jini ya gama b'ata shi.
Alhaji Ma'aruf ne yayi waya a asibiti yace a
kawo masu mota, ya kwatanta masu inda suke
sannan ya kashe wayar yaci gaba da kukan shi,
babban tashin hankalin shi bai wuce yanda yaga
jikin Reesha duk ya zagwanye ba, babu fata
kwatakwata a jikin kamar ya k'one, ga kanshi
babu ko alamar gashi yayi fari fat. Reeshat ma
can jikin k'arfen shiga ruwan ya gano ta jikin ta
duk ya fashe har a lokacin jini bai daina zuba ba,
kuka kawai yake yi kamar k'aramin yaro.
Ba'a wani jima ba sai ga Ambulance taxo,
take a ka fara saka su a cikin motar baki d'ayan
su sannan aka tayar suka tafi, suma iyayen bin
bayan su sukayi a motocin da suka xo ciki. Nan
da nan sai gasu bakin Federal medical center,
ciki suka shige basu zarce ko ina ba sai accident
and emergency.
********
An dudduba su sosai dan manyan likitoci aka
kira dan su duba su amma babu nasarah,
Duk wanda ya kamata ama d'inki anyi amma
wurin baya d'inkuwa, da zarar an d'inke sai ya
dare, su kansu likitocin abun ya d'aure masu
kai.
Md kuwa duk iya k'ok'arin su sunyi amma
abu yaci tura, sun samu sun tsayar da jinin dake
fita daga jikin shi amma cinyar baxata tab'a
komawa a jikin sa ba, shikenan ya zama gurgu.
Nuratu, Shamow da Sally kuwa in banda wari
babu abun da sukeyi, idan aka fasa maruran jikin
su sai wani ruwa mai yauk'i ya ringa fitowa, sai
kuma marurun ya koma yanda yake. Sosai suka
tsorata da wannan al'amarin, ga wasun su har
yanxu basu farfad'o ba amma kuma suna jin
alamar suna numfashi kad'an kad'an.
Samir kuwa nashi yafi na kowa illah shikenan
yanxu ta raba shi da mazakuntar sa, babu shi
babu aure, haka likitocin suka ringa fita dan
basu da yanda zasuyi masu.
Da sauri Dady ya tari wani likita yace "Dr. Ya
ake ciki? Ina fatan an samu nasarah"
Kai kawai ya kad'a masa yace "sai dai mu jira
zuwa safe in sha Allahu zasu farfad'o, wasu sun
farfad'o a cikin su wasu kuma shiru ne, mun
samu anyi d'inki amma ya ringa daddarewa,
Alhaji akwai al'ajabi a wannan abun, mesa d'inki
zaina warwarewa idan anyi shi?",
Dady yace "shikrnan Dr. Mun gode sosai sai
goben".
Momy kuwa ta koma gida saboda har
asubah ta kusa gashi kuma Affan shi kad'ai ne a
gida. Ummah da Feenat ma sun koma gida da
nufin sai da safe zasu dawo.
*Gidan su Kerry*
*4:56am*
Har a lokacin iyayen Kerry sun kasa bacci,
babban tashin hankalin ma yanda suke ta neman
number d'inta amma yak'i shiga, daga farko
tana ta ringing ne ba'a d'auka ba, daga baya
kuma sai ma suka daina samun ta kwata kwata.
Mom d'in ta banda kuka babu abunda take yi,
shima Dad d'in k'arfin hali ne kawai baya so
matar shi taga yayi kuka hankalin ta zai k'ara
tashi,
Ko sanda suke America Kerry bata tab'a
kwana wani wuri ba, duk inda taje komai dare
bata kwana acan sai ta dawo gida, kuma idan
taga alamar xatayi dare sosai ma tana kiran su
ta shaida masu zatayi dare sosai dan kar
hankalin su ya tashi, wannan dalilin ne yasa
suka k'ara rikicewa ganin har asubah ta gabato
amma babu ita.
K'arfe shida na safe iyayen suka tattaru a
asibitin, wanda suka farfad'o d'in su suka bayar
da adress d'in sauran ciki kuwa har da na Kerry,
Dady, Alhaji Ma'aruf da Alhaji Abdallah suka
ringa bin addresses d'in suna sanar wa iyayen
yaran, a rikice suka ringa tafiya asibitin suma.
Gidan su Kerry ne k'arshe saboda shine wajen
gari, horn Dady yayi sai ga mai gadi ya bud'e
masu gate suka shiga daga ciki, umurni suka
masa da ya shiga yayo sallama da mai gidan.
Koda ya shiga ya samu Mom kwance a cinyar
Dad kamar zautacciya sai sumbatu take tana
kiran Kerry,
Cikin girmamawa yace "Oga kayi bak'i",
Da sauri Mom ta tashi daga jikin shi tana
share hawayen ta,
"Je kace gashi nan zuwa"
Tafiya yayi inda Mom kuma ta mik'e tace "mu
tafi tare, may be ko maganar Kerry ne".
Fita sukayi hannun ta rik'e dana Dad saboda
wani jiri jiri da take gani kamar zata fad'i tsabar
kukan da tasha.
Hannu Dad ya mimmik'a masu suka
gaggaisa,
"Ince dai ko lafiya" Dad ya fad'a yana kallon
Alhaji Ma'aruf.
"Ehh tou, lafiya ba lafiya ba, wata magana
ce muke tafe da ita" Alhaji Ma'aruf ya fad'a.
"Duk kan mu sai dai mu taru muyi hak'uri mu
mik'awa Allah al'amarin sa.." Dady bai gama
maganar ba Mom tayi saurin katse sa da cewa
"kar dai kace min 'yata Kareemah wani abu ya
same ta" cike da firgici idon ta kan Dady.
"Duka yaran mu da suka je wurin Party'n ne
suka had'u da wahalar rayuwa, sun tab'o ma
kansu *JINNU* ne, so kun san su kuma basa
yafiya sai sun d'auki fansa, indai aka tab'a su,
yanzu dai maganar da nake maku suna asibiti su
duka yaran, wasu sun farfad'o wasu kuma har
yanzu shiru ne, shine muka karb'o address na
wanda basu tashin ba dan mu sanar dasu
saboda mun san hankalin iyayen su ba a kwance
yake ba, yara tun jiya sun bar gidajen su amma
shiru basu dawo ba dole hankali zai tashi".
Tuni wani kukan ya kufce ma Mom, da k'yar
ta iya furta "ai dama na fad'a maka haka, ni
nasan kerry ba lafiya ba, bata tab'a zuwa wani
wuri ta kwana ba" taci gaba da kuka jikin ta sai
rawa yake. (Inda zaku san akwai k'arancin ilimin
addini har yanzu fa daga Dad har Mom d'in
babu wanda ya ambaci sunan Allah).
Tasu motar suka shiga suma take suka
rankaya sai FMC. Nidai Amrah biye nake dasu
dan ganin yanda iyayen kerry zasuyi idan suka
samu labarin 'yar su ta haukace, gasu da jahilci
kuma jahilin mutun bai iya d'aukar k'addara ba.
Muje zuwa dai.
*Amrah nd Rerbee'art sk novelsí ½í³š*
[10:54am, 13/10/2016] Amrahí ½í²“Pinkyí ½í²“durlingí ½í¸˜: í ½í²€
*A YINI 'DAYA* í ½í²€
í ½í²€ í ½í²€
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 23-25
D'aya bayan d'aya suka ringa farkawa duk
kansu da hawaye bushe a fuskokin su ga wani
irin rad'ad'in ciwo dake damun su.
A daidai isowar su Dad d'akin ne yayi daidai
da farkawar Kerry,
Da k'arfi ta fasa wani irin ihu wanda sai da
duka d'akin ya amsa, take kuma ta k'yalk'yale
da dariya tana kallon su.
Gadon da take kai ta fara lilawa da k'arfi
kamar zata karya shi, zanin dake shimfid'e jiki
ma ta cire ta nannad'e shi ta jefa shi sai kan
Mom d'in ta da k'arfi.
Kayan jikin ta kuwa tuni ta fara k'ok'arin cire
rigar amma saboda yanda ta kama ta sosai yasa
ta kasa cirewa, ganin ta kasa cirewa yasa ta
fashe da kuka wanda babu ko alamar hawaye,
can kuma ta k'ara fashewa da dariya
mahaukaciya dai sak.
Hankalin Mom da Dad ya k'ara tashi sosai
ganin abunda ke faruwa, da an ganta an san
bata da hankali, gashin kanta duk tayi tuzu tuzu
dashi lokaci d'aya kamannin ta suka soma
sauyawa,
Da sauri Mom ta fara k'ok'arin nufar inda take
amma ta bud'e baki tace "idan kikaxo min nan
sai na kashe ki, ni ban sanku ba" ta b'ata fuska
kamar da gaske bata san sun ba.
Duka hankali ya koma kan su, ganin yarinya
mai gata wurin iyaye ga abun da ya same ta
yasa Afnan fashewa da wani irin kuka mai tsuma
zukata.
Ana cikin haka ne sai ga wani likita ya shigo,
Cike da damuwa yace "ina iyayen yaran nan
da suka had'e wuri d'aya?"(Mc da Dj),
Da sauri suka ce "gamu",
"Tou gaskiya munyi bakin k'ok'arin mu dan
ganin mun raba su amma abun yaci tira, mafita
d'aya ce nake tunanin in har akayi tou za'a
samu solution d'in abun",
Da