Showing 18001 words to 19493 words out of 19493 words

Chapter 7 - A WUNI DAYA BOOK COMPLETE BY ESHAAAT.pdf

05 Jun 2025

1327

wurin ummanah,
tsananin tsoron ummah da nake yasa na bata
hak'uri banda yanda zanyi dole sai da na bisu,
wannan shine asalin k'ungiyar *AREWA STARS"*
Ta k'arisa maganar tana kuka sosai cike da
nadama.
*Amrah nd Rerbeeart sk novels*
[1:06pm, 20/10/2016] AmrahPinkydurling:
*A YINI 'DAYA*
� �

*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 36-40
Duka iyayen sunyi shiru sun ma rasa abunda
zasu fad'a, yaran kuwa in banda kuka babu
abun da suke yi ga azabar ciwo da ta addabe
su, ga DJ da MC ance baza'a iya raba su ba
dole sai d'aya ya rasa rayuwar sa.
MD ma shike nan ya rasa k'afar sa d'aya ya
zama gurgu.
_(Allah sarki! Haka rayuwar take, ba'a gama
halittar d'an adam ba har sai lokacin daya
kwanta damar sa, wallahi wannan rayuwar abun
tsoro ce, yanzu zaka ganka da lafiya kuma
yanxu xaka iya rasa ta, yanxu kike da k'afa
yanzu Allah yana iya yin yanda yaso da k'afar,
haka kuma zaki ganki lafiya lau da idon ki Allah
zai iya sawa ki rasa idon a lokaci d'aya, wallahi
ko wannan ya ishe mu ishara akan muji tsoron

Allah, mutuwa bata alerting idan zataxo, wallahi
wannan labarin dana rubuta kusan abubuwan da
suke faruwa kenan da gaske, muna fita daga
gidaje ama iyaye k'aryar xa'aje wani wuri amma
inda za'aje d'in daban yake, shin bamu gudun
Allah ya zare mana rayuwar mu a inda mukaje
d'in? Kar ku manta cewa manzon tsira Allah ya
k'ara masa aminci yace "za'a tada mumini akan
abunda ya mutu yana aikatawa" shin zamuso a
tashe mu muna aikata alfasha? Duk abunda
muke aikatawa fa Allah yana ganin mu, idan a
tunanin mu ai mun ma iyayen mu k'arya bazasu
tab'a gane wa ba tou ko mun manta cewa akwai
RAQIB DA ATIB? wanda ranar k'iyama zasu
bada shaidar abunda duk muka aikata, mun
manta cewa k'afafuwan mu zasu bada labarin
inda muka taka mukaje dasu? Mun manta cewa
hannuwan mu zasu bada labarin abun da muka
tab'a dasu? Mun manta da cewa bakin mu zai
bada labarin abunda aka fad'i dashi ko akayi
dashi? Mun manta da cewa ido zai bada labarin
abun da aka kalla dashi? Mun manta da cewa
ba'ayiwa Allah dabarah, baki d'aya rayuwar
yanzu tarbiyyar yaran mu ta tab'arb'are, na
kirkin mu k'alilan ne, wallahi muji tsoron Allah,
mu dage yiwa kan mu da iyalan mu adduo'i'n
shiriya, wallahi zaman kabari kanshi abun tsoro
ne, zaman kad'aici kenan, barin ace tsayuwar
k'iyama, ranar da wayon ka da dabarar ka bazai
amfane ka da komai ba, ranar da uwa da uba ba
tamu suke ba kowa ta kan sa yake, Ya Allah
kasa mu cika da imani, Allah ka shiryar mana da
duk wanda suka b'ata)._
Da kuka da komai Dad da Mom suna ji suna
gani aka d'auki Kerry bayan an d'ad'd'aure ta
aka nufi psychiatric (asibitin mahaukata) da ita.
```Bayan wata daya.```
Duk wata k'asa da suke tunanin idan sun kai
Kerry zata samu lafiya sunje amma abun babu
sauk'i, kud'i kawai suke kashewa amma abu
yaci turah, daga k'arshe dai haka suka hak'ura
suka dawo da ita Nigeria a asibitin mahaukata
saboda xama da ita bazai tab'a yiwuwa ba, duka

take sosai ga surutai marasa ma'ana da take yi
tana fad'in "ai duk laifin ku ne, kune baku bani
tarbiyyar kirki ba, inda kun kula dani da tarbiyyar
kirki ai da komai bai same ni ba" sai kuma ta
fashe da kuka, hakan yasa kawai suka hak'ura
suka miyar da ita asibitin.
Su kuwa su Afnan abu babu sauk'i, ciwon ana
magani amma kamar bayi ake ba, kulkun k'ara
rub'ewa yake yana wari, Momy tace ta fiddo miji
a mata aure amma duk a samarin ta wanda
tama magana a waya da murna zasu amince,
amma da zarar sunxo sukaga yanda take ga wari
tana yi sai su tafi bazata sake ganin su ba,
kullun cikin damuwa take.
Samir kuwa ya warke sosai dan shi kad'ai ne
ma ya warke, amma abun haushi da takaici
shine bashi da mazakunta, bazai tab'a auruwa
ba har abada, in ma yayi auren babu macen da
zata iya zama dashi.
*Amrah nd Rerbee'art sk no

MSH ) MOBILE BLOG
Home 禄 禄 A YINI 茒AYA 41
A YINI 茒AYA 41
By babymsh 09:24 No comments
馃拃 *A YINI 'DAYA* 馃拃
馃懝馃拃 馃拃馃懝
馃懞
*庐NWA*
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 36
*```KARSHE```*
馃挀馃挀馃挀
haka dai rayuwar taci gaba da tab'arb'are masu,
raunukan su sai k'ara rub'ewa suke abun
k'yama da tausayi, Ummy banda wari babu
abunda takeyi, ko Mamin ta ta daina shiga
d'akin da take, in ma abinci zata kai mata sai
dai ta ajiye daga bakin k'ofa ta rarraho ta
d'auka.
Afnan kuwa Momy ta aika da hoton ta
masallatai ayi tallar ta, nan da nan kuwa aka

fara rububin ta, amma da mamaki duk wanda
yazo yaga fuskar ta da yanda take sai ya tafiyar
sa.
Kamar kullum Momy ce zaune ta buga
tagumi ta tsurawa Afnan ido tana kallon ta cike
da tausayi, sallamah akayi Momy tayi saurin
amsawa tana kallon mai shigowa, Dady ne ta
gani hannun shi rik'e da Affan sanye da Uniforms
alamar daga makaranta ya d'auko shi,
"Oyoyo momy na" ya fad'a tare da isowa
wurin Momy.
"Sannu da dawowa Alhaji" ta fad'a bayan ta
rungume Affan a cinyar ta tana cire masa safar
k'afa.
"Momy wai yaushe Yaya Afnan zata warke
ne?",
D'an murmushin yak'e ta mashi kafin tace
"insha Allahu zata samu lafiya yaro na, ka ringa
saka ta a addu'ah kaji?",
Kai ya d'aga cike da tausayin 'yar uwar sa.
"Assalamu alaikum" akayi sallamah,
Dady ya amsa da "wa alaikumussalam, Mati
ya akayi ne?",
"Yallab'ai kayi bak'o",
"Bak'o? Waye ne?",
"Wani gurgu ne yallab'ai, yace ayi masa
sallamah da kai",
"Gurgu? To kace ina zuwa".
Kallon shi ya miyar ga Momy yace "Maman
Afnan barin fita inga mai nema na".
Bayan ya fita ya samu wani gurgu ne ya
mik'a masa hannu suka gaisa,
"Bawan Allah meke tafe da kai?" Dady ya
fad'a yana kallon gurgun mai ido d'aya.
"Sunana Sani, dama yallab'ai naga wani hoto
ne a masallacin da nake aiki, so ina da ra'ayin
auren yarinyar indai babu damuwa"
Shiru Dady yayi ya k'are masa kallo sosai
sannan yace "ehh to! Nidai a wuri na babu
damuwa, amma ka shigo mu shiga ciki idan
yarinyar taji tana son ka sai ayi binciken komai
sannan a d'aura aure".
Murmushi yayi sannan yabi bayan Dady daya

fara shigewa cikin gida.
Bayan sun shiga ciki ya gaishe da Momy
cikin girmamawa itama ta amsa masa da sakin
fuska.
Dady yayi ma Momy bayanin abunda yake
tafe dashi kai tsaye momy ta goyi bayan abun,
Afnan ma dake kwance take ta amince dashi
duk da yanda yake d'in.
*****
Shirye shirye sosai suka kankama na bikin Sani
gurgu da Afnan, duk da ba wani abu za'ayi ba
walima ce kawai za'ayi.
Ranar jumu'ah aka d'aura auren su amarya ta
tare a babban gidan ta da Dady'n ta ya mallaka
mata ita da mijin ta.
Feenat kuwa taci gaba da zuwa makarantar
ta har sun fara zana jarabawar k'arshe ta
sakandire.
Kerry kuma har yanzu abun shiru babu
sauk'i, gashi kuma sun k'i zuwa wurin malamai
duk da shawarar hakan da ake basu.
*AREWA STARS* dai a haka suka k'are da
tab'arb'ararriyar rayuwa, wannan ishara ce ga
masu hali irin nasu, masu yawan zuwa party ba
tare da iyayen su sun sani ba, ina fatan wannan
gajeren labarin zai zama fad'akarwa ga
al'ummah musulmai har ma da wanda ba
musulman ba.
ALHAMDULILLAH!!!
Duk abunda yayi farko zayyi k'arshe, muna
godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya
bamu ikon kammala wannan labarin namu,
kurakuran dake cikin labarin Allah ya yafe
mana,inda muka yi daidai kuma Allah ya bamu
ladar.
Muna godiya ga masoyan mu da suka bibiyi
labarin har ya kaiga k'arshe irin su:-
```Rukayya Auwal,```
```Faty KK```
```Husnah Ibrahim,```
```Aysha Khalil,```
```Amman Suraj```
Da da da da, lissafo ku ba abune mai sauk'i ba,

sai dai muce muna k'aunar ku akoda yaushe,
kuci gaba da kasancewa damu a littattafan mu
na gaba.
Jinjina, fatan alkhairi, godiya su tabbata ga
K'ungiya mai albarka *```NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION```* Allah ya bar zumunci ya k'ara
had'a kawunan mu amin.
```ZARAH~B~B``` *godiya da jinjina mai tarin
yawa a gare ki, kin nuna mana soyayya kuma
kina kan nuna mana ita, Allah yabar mu tare ya
k'ara miki baseerah.*
All groups members and admins na group d'in
da muke muna gaishe ku, tsayawa lissafo ku ba
abune mai sauk'i ba, sai dai mu maku godiya da
bibiyar labarinmu da kukayi.
'Yan uwan mu writers muna godiya a gare ku,
Allah ya raba mu da sharrin mahassada da
mak'iya.
Amrah and Rabi'atu sk novels group mun gaishe
ku da babbar murya, Allah ya barmu tare ameen.
Kuci gaba da kasnacewa dani Amrah a cikin
novel d'ina mai suna *UMMU HAYDAR* idan na
kammala exam insha Allahu.
Amratu A Mashi an

5
6
7

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login