Showing 1 words to 3000 words out of 12157 words
Chapter 1 - TSATSUBA 2 Littafin Yaki Na Abdulaziz Madakin Gini .pdf
TSATSUBA
BOOK 2
Part (A)
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
Lokacin da takobin Shumaira ta isa kirjin sarauniya larbisa sai ta dan soketa a kirji, tana kokarin
danna takobin a cikin kirjin nata kafin larbisa tayi kara sai shumaira taji an daka mata tsawa
daga baya bisa dole ta fasa dannan takobin izuwa cikin kirjin larbisa, ta mike tsaye daga kanta
ta waigo tayi arba da wanda yayi mata tsawar, ba wani bane face mahaifinta mafarauci imshal. .
Mafarauci Imshal ya kasance dogon mutum mai kirar sadaukai sai dai girma ya kamashi sosai
domin shekarunsa zasu kai kusan arba in gaba daya gashin kansa sajensa da gemunsa duk
farin gashine, yana rike da wata doguwar sanda a hannunsa ya rataya kwari da baka a bayansa
rigarsa, wandonsa da takalminsa dake kafarsa duk anyi sune da fatar damisa. .
Koda jaruma shumaira ta hango mahaifinta Imshal sai ta rugo izuwa gareshi ta dukar daki tana
mai nuna girmamawa a gareshi, A wannan lokaci ne sarauniya larbisa ta mike tsaye tana mai
dafe gefen kirjinta inda
shumaira ta soka mata takobi don har dan jini ya fito kawai sai sarauniya larbisa ta sunkuya
cikin biyayya ta gaisheda tsoho Imshal. Imshal ya karbi gaisuwar yana mai kare mata kallo
sama da kasa sannan ya karewa dakarunta kallo ya dubi shumaira yace akan wani dalili kike
yaki da wannan mace mai daraja? Shin bakya ganin alamar cewa mai mulki ce. .
Koda jin wannan tambaya sai shumaira ta dago kai ta dubi imshal ta ce yakai abbana kayi sani
cewa haka kawai wannan sarauniya tare da dakarunta suka shigo cikin dajin nan suka dasawa
dabbobinmu wawa, bisa wannan daliline na tarwatsa dakarun nata kuma na umarcesu da su
fice daga cikin dajin nan tun kafin fishinmu ya tabbata a kansu amma saboda naci sai wannan
sarauniya ta biyoni har cikin garken dabbobi, ni ina ganin cewa kawai ka kyaleni na gama da ita
yanzu domin da ita da yaran nata su gane cewa ruwa ba sa an kwando bane kuma bakin rijiya
ba wajan wasan yaro bane.
.
koda jin wannan batu sai tsoho imshal ya bushe da dariya sannan ya hade fuska ya dubi
shumaira yace ai ruwa baya tsami banza, shin a farkon bayaninta gareki bata gaya miki cewar
tana da wata bukata ba a wajanki?
.
Cikin alamun sanyin jiki shumaira tace ta gaya mini cewar tana da wata bukata a wajena amma
saina gaya mata cewar bata da abinda zata iya biyana da shi don haka babu abinda zan iya yi
mata koda jin wannan batu sai imshal ya gyada kai yace yarinya kinyi hanzarin yanke hukunci
shin bakya tunanin cewa bukatar da tazo mana da ita wata kila a sanadinta ne muma zamu fita
bakin cikin da ya addabemu tsawon shekaru bakwai.. Shin kin manta ne cewar na gaya miki
zamu iya nasarar samun abinda muke nema a cikin wannan shekara idan kin hadu da wadansu
bakin jarumai guda uku?
.
Koda jin wannan batu sai jikin shumaira yayi sanyi ta sunkui da kanta kas ta kasa cewa komai
daga can kuma sai ta dago kai da sauri ta dubi tsoho imshal tace amma ai wannan sarauniya
ba ta da kama ko siffa irin ta mutane ukun dakayi mini bayani imshal yace hakane amma dai ki
tsaya muji abinda ya kawota wajanmu babu mamaki a sanadin hakan a samu dacewa cikin
nutsuwa tsoho Imshal ya dubi sarauniya Larbisa yace yake wannan sarauniya ma abociya
kyawu da karjini wace bukata ce dake tasa har kikayi tattaki kikazo har wannan daji namu?
.
Kafin larbisa ta budi baki tace wani abu sai tsoho Imshal ya kara tarar numfashinta yace amma
kafin kice komai ya kamata ku fara yiwa raunikan jikinku magani yana gama fadin hakan sai ya
bude wata jaka dake rataye a bayansa ya dauko wani farin magani me maiko da kauri kamar
daskararren nonon shanu ya mikawa yarsa shumaira yace ungo ki shafa a rauninki kuma ki
shafawa bakuwar tamu cikin alamun damuwa shumaira ta karbi maganin ta fara shafawa kanta
sannan taje ta zauna a gaban larbisa ta kama shafa mata fuskarta a daure babu annuri, su
kuwa su sadauki Humaisu sai hankalinsu ya kwanta sukayi murna da ganin yadda tsoho Imshal
ya karbesu hannu biyu, bayan shumaira ta gama sawa larbisa magani a rauninta sai tsoho
Imshal ya dubi larbisa yace yake wannan sarauniya kiyi sani cewa ni yanzu na karbeku keda
jama arki a matsayin bakina saboda haka yanzu zan kaiku zuwa gidana domin ku huta in yaso
bayan kun nutsu saimu zauna mu tattauna mu dake idan har zamu iya taimakon juna zamu iya
yarda da buqatarki, idan kuma ke
kadaice zaki amfana damu to sai dai muyi miki fatan samun nasara ki kara gaba, koda jin
wannan batu sai farin ciki ya lullube sarauniya larbisa, ta dubi Tsoho Imshal cikin murmushi tace
nayi farin ciki da wannan tayi da ka bani ya kai Abul Shumaira kuma zuciyata ta bani cewa nima
zan iya baku taimako bisa taku bukatar. .
Tsoho Imshal yayi murmushi yace sai an gwada Sannan ake sanin na kwarai yana gama fadin
hakan sai ya kama hannun shumaira suka nufi bayan wani katon dutse yana mai yafito su
larbisaa, Da hannu cikin hanzari larbisa taje ta kama dokinta ta hau tabi su.
.
Tsoho Huzallatul marwas ne ya fara bin bayanta sannan sadauki Humaisu da sauran Dakaru.
Ana zagayawa bayan wannan katon dutse sai kowa ya cika da mamaki bisa ganin wani
dankareren gida wanda aka ginashi da duwatsun wuta Gidan katone kuma anyi masa fasali na
gidan sarauta dauke da bangare bangare, banbancinsu da gidan sarauta kawai shine babu
bayi, dakaru da kuyangi mutum daya kacal suka gani a cikin wannan gida kuma ba wani bane
face larisa mahaifiyar Jaruma shumaira
lokacin da larisa ta hango mijinta imshal da yarta shumaira tare da bakin mutane sai tsoro ya
baibayeta domin wannan shine karon farko a iya zamansu a cikin wannan daji da ta ga sun zo
mata da mutane har gida don haka bata yarda ta bude kofar gidan ba sun shigo har sai da suka
matso kusa taga cewar babu wata alamar damuwa akan fuskar mijinta da 'yarta Ita kanta larisa
shekarunta sun kai hamsin da biyu koda uku amma saboda tsananin kyawun jikin da Allah ya
bata mutum ba zai taba zaton ta kai hakan ba.
.
Da isowarsu tsoho Imshal ga larisa sai ya gabatar da sarauniya Larbisa a gareta sannan ya
gaya mata cewa ita da jama arta bakine masu mahimmanci, cikin farin ciki larisa ta karbi
sarauniya larbisa tana maiyi mata barka da zuwa, nan take aka kaisu sadauki Humaisu izuwa
wani bangare daban na gidan ita kuma larbisa sai tabi jaruma shumaira izuwa dakinta. .
Cikin hanzari shumaira ta dafa ruwan dumi ta kaiwa larbisa kewaye ta shiga wanka kafin larbisa
ta fito daga wankan tuni shumaira ta shirya musu abinci. Larbisa na fitowa daga wankan sai
itama shumaira ta shiga wankan sai da ta fito daga wankan sannan suka zauna tare bisa wasu
kujeru dake karkashin wani tebur suka fara cin abincin, tsawon yan dakiku da fara cin abincin
dayansu baice uffab ba.
.
Abinda ya daurewa shumaira kai shine ganin yadda larbisa ta saki jiki take ta cin abincin Alhalin
ba abinci ne mai dadi ba irin nasu na sarakai Abincine irin wanda kowane talaka zai iya ci
musamman mazauna daji cikin matukar mamaki shumaira ta dubi sarauniya larbisa tace yake
wannan sarauniya menene dalilin da yasa kika saki jiki kike ta cin irin wannan abinci namu na
talakawa alhalin nasan a guzurinki akwai irin naki abincin da kika taho dashi?
.
Koda jin wannan tambaya sai sarauniya tayi murmushi tace ai dokar bakunta itace yin koyi da
irin mutanen da ka riska, ni kaina nayi mamakin yadda akayi naji ina matukar jin dadin wannan
abinci naku amma fa babu abinda ya bani mamaki a yanzu sama dake, koda jin haka sai
shumaira ta dago kai da sauri ta dubi larbisa cikin mamaki tace ke kuma me nayi wanda ya baki
mamaki? Larbisa ta ajiye cokalin da take cin abinci gami da yin ajiyar numfashi sannan tace
gani nayi da farko baki karbeni da wata daraja ba har ma yakata kikayi kikauda batun matsayina
na sarauta yanzu kuma sai gashi kina yin biyayya da hidima a gareni.
.
Yayin da shumaira taji wannan batu sai tayi murmushi tace ai nima nayi amfani da maganar
manya da suke cewa idan babba ya rike girmansa dole ne karami yayi masa biyayya. Lokacin
da kika shigo cikin wannan daji namu ke da jama arki baki hanasu kokarin yi mana sata ba
dalilin da ya sa na ki karbar bakuncinki kenan tun da farko amma yanzu dana gane cewar wata
kila kina da mahimmanci ga rayuwata shi yasa nake yi miki ladabi da biyayya larbisa ta bushe
da dariya sannan tace ai kowane mutum yana da rana komai kaskancinsa shin zaki iya gaya
mini babban burinku na duniya keda mahaifinki wanda har kuke tunanin zan iya taimaka muku a
kansa?
.
Sa adda shumaira taji wannan tambaya sai tayi murmushi tace me kikeci
na baka na zuba ehm wato ( what are you eating na baka is falling down )
zakiji amsar wannan tambaya taki idan mukayi zama na musamman mu dake kuma a sannan
ne muma zamuji taku bukatar a wajanmu, kodajin
wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace tabbas zancenki dutse ne, haka dai
shumaira da larbisa suka ci gaba da hira har suka gama cin abincin kuma dare ya raba sannan
suka kwanta sukayi barci, .
.
Kamar yadda aka karrama sarauniya larbisa hakama aka karrama sadauki humaisu da dukkan
dakarunsa suka ci suka sha sukayi hani'an kuma suka kwanta a masauki mai kyau, Al amarin
da yayi matukar daure musu kai kenan suka cika da tsananin mamakin yadda wadannan
mafarauta suka tara arziki mai yawa haka.
+++±+++++++
Kashe gari da safe bayan sarauniya larbisa ta yi wanka ta kimtsa sai ta ga shumaira bata kawo
musu abincin kalaci ba kawai ta zauna tana jiranta ta gama kimtsawa tana gama kimtsawa
kuwa sai shumaira ta mike tsaye ta dubeta tace iyayena suna jiranmu acan turakarsu domin
muyi mude baki tare dasu kuma mu sami damar tattaunawa akan abubuwan da muka sa a
gaba koda jin haka sai sarauniya larbisa ta mike da sauri cikin murna ta bi shumaira a baya
suka fice daga cikin dakin suka nufi hanyar da zata kaisu bangaren da iyayen shumaira suke,
sai da sukayi yar tafiya mai dan tsawo kadan sannan suka iso wani babban falo mai dauke da
Wani faffadan tebu A karkashin teburin kujerune guda biyar
tsoho Imshal tare da matarsa larisa na zaune akan kujeru biyu ga abinci nan wajen kala uku
akan teburin dake gabansu, da isowar shumaira da larbisa sai tsoho imshal da larisa suka mike
tsaye suna musu girmama sarauniya larbisa gami dayi mata barka da isowa nan take larbisa da
shumaira suka janyo kujeru daga cikin karkashin teburin suka zauna aka fara cin abincin. .
Tsawon yan dakiku da fara cin abincin dayansu baice uffan ba daga can sai tsoho Imshal yayi
gyaran murya yace yake wannan sarauniya mai daraja yanzu saiki gaya mana abin da ya
kawoki garemu kafin muma mu
gaya miki bukatar da muke da ita a wajanki.
.
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi sannan tayi gyaran murya tace ba
wani abu bane ya sa na baro kasata ba mulkina da jama ata face don na riski kogon Kitabul
sihir inda littafin TSATSUBA yake, littafin da shine kadai zai cika mini babban burina na duniya
na samun damar yin aure gami da samun magaji kuma na mallaki komai da kowa dake cikin
wannan duniya ba zan iya isa inda kogin yake ba face na ratsa ta cikin dazuzzuka guda uku;
.
Daji na farko shine ake kira da Shajarul Shaljuma wanda ke dauke da mugayen dabbobi da
mugayen tsuntsaye. Bokaye sun tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki wanda zai iya
wucewa dani ta cikin wannan daji a raye face wannan ya taku shumaira daga nan ne zamu
wuce izuwa dajin Ujurul Majnun bisa jagorancin Jaruma Larifat, daji na uku kuwa wanda ake
kira darul maut zamu shigeshine bisa jagorancin jaruma Lubaina muna wuce wadannan
dazuzzuka sai kuma mu tunkari dajin da kogon Kitabil sihir yake shi kuwa kogon babu mai iya yi
mana jagora izuwa cikinsa face jarumi Ruhaisu dan sarki Zaiyanu na birnin kufa. A cikin kogon
kitabul sihir ne zan iya dauko littafin TSATSUBA domin na lalata duk sihirin tsafin dake cikinsa
don na sami damar yin aure na sami da ko yar da zata gajeni idan ban lalata sihirin dake cikin
wannan littafi ba na tsatsuba har abada burina ba zai cikaba.
.
Koda sarauniya larbisa tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal ya tuntsire da dariya Al amarin da
ya baiwa larbisa dasu shumaira mamaki kenan daga can kuma sai Tsoho Imshal ya murtuke
fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla har
hawaye ya zubo masa..
.
Nan fa sarauniya Larbisa ta kara cika da tsananin mamaki ta dubi tsoho Imshal tace yakai Abul
Shumaira ina dalilin yin dariyarka gami da zubar hawayenka a bisa
abinda kaji na fada??...
.
Ni nima zan dakata ana sai Allah Ya kaimu gobe inda za mu ji abin da tsoho Imshal sai fada a
huta lafiya.
TSATSUBA
BOOK 2
Part (B)
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Yayinda tsoho Imshal yaji wannan tambaya sai yayi Ajiyar numfashi ya dubi sarauniya larbisa
cikin nutsuwa yace yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa ba wani abu bane ya
sakikaga na bushe da dariya ba sai saboda nasan cewa kin daukowa kanki gagarumin aikin da
sai kinyi nadamar yinsa domin aikine wanda babu tabbacin samun nasara a kansa, sannan
kuma zaki iya shan bakar wahala da bata da misali kuma dake da duk abikan tafiyar taku zaku
iya rasa rayuwarku ko lafiyarku. Ke a takaice dai fiye da shekaru dari baya ba a taɓa samun
mahalukin da ya ratsa ta cikin wadannan dazuzzuka guda uku har ya isa kogin sihir a raye
ba don haka ni yanzu ina kallonki ne a matsayin wacce ta gaji da rayuwar duniya take neman
mutuwa ruwa a jallo! Ko kuma ince wacce ta sami tabin hankali !!
.
Dalilin da yasa kikaga ina zubar da hawaye kuwa shine biwa wannan TAFARKI da kike son bine
na rasa iyayena da kakannina domin suma sun bar gida sun tafi izuwa kogon kitabul sihir domin
magance wata matsala data addabi gaba daya zuri armu tsawon shekaru masu yawa amma
dayansu bai dawo a raye ba, wannan matsala kuwa ba komai bace face wani sihiri wanda wani
abokin gabarmu ya yiwa kakanninmu, shi dai wannan abokin gaba namu mafarauci ne kuma
takadarin boka ne tunda akayi GASAR FARAUTA a birninmu kakanmu ya lashe gasar sai
wannan
boka yayi masa sihiri ya kasa ci gaba da zama a cikin gari shi da iyalinsa yaji kamar ana
konashi da wuta. Matansa da 'ya'yansa da jikokinsa ma haka suka rinkaji ya zamana cewa ba
shiri suka hada nasu 'i' nasu suka koma cikin daji da zama bisa dole kakan namu ya hakura da
sarautar sarkin daji da aka bashi ya daina zuwa fada gaba dayan zuri armu sai suka tsani cikin
gari daga wannan rana kawo iyanzu babu sauran mutum daya daga cikin zuri armu wanda ke
rayuwa a cikin daji duk mun watsu a cikin dazuzzuka har yau har gobe ni din nan da matata da
yata shumaira da kike ganinmu bamu taba shiga cikin gari ba mu tsaya tsawon rabin sa a sai
dai muyi siyayya a kasuwa mu fito babu irin kokarin da bamu yi ba wajan neman yadda zamu
karya wannan sihiri amma abu ya gagara kafin mahaifina ya rasu ya shaida mini cewa ba zamu
taba iya samun nasarar karya wannan sihiri ba face mun bude littafin TSATSUBA mun karanta
wata kalmar tsafi guda daya wadda ke shafin tsakiya, yake wannan sarauniya mai daraja kiyi
sani cewa bukatarki kusan iri daya ce da tamu amma ni ba zan iya barin yata shumaira tayi
wannan tafiya ba tunda ita kadai gareni a wannan duniya kinga nidai tsufa ya riskeni mahaifiyar
tama gata nan ta fara manyanta , yau idan babu ita shikenan zuri armu gaba daya ta shude
kenan tunda mu ne kadai mukayi saura kafin tsoho Imshal ya gama rufe bakinsa sai jaruma
shumaira ta mike zumbur ta durkusa bisa guiwoyinta a gabansa ta rike hannayansa biyu a
lokacin da hawaye ya zumo mata tace ya kai abbana kayi sani cewa ko ka barni ko ka hanani
yin wannan tafiya watarana sai mutuwa ta daukeni shin ka manta cewar ka gaya mini cewa
dukkan mai nema yana tare da samu lallai ina son na karya wannan asiri wanda ya gagari
iyayenmu da kakanninmu domin na barwa birninmu abin tarihin da baza a taba mancewa dashi
ba ka tuna cewa har yanzu sarautar sarkin daji tana hannun zuri ar babban makiyinmu boka
zarratu tunda mu mun kasa zama a cikin gari lallai ta kowanne hali saina kwato mana yancinmu
na dawo mana da sarautarmu mun koma mun zauna a cikin wannan gidan sarauta namu na
sarkin daji wanda kai kanka rabonka da shi tun kana jariri ina mai rokonka daka bani wannan
dama ayi wannan tafiya dani da izinin iyayenka dake kwance cikin kabari saina sami nasara na
kwato mana yancinmu.
.
koda jaruma shumaira tazo nan a zancenta sai tsoho Imshal da matarsa larisa suka kamu da
tsananin tausayinta suka rungumeta sunamasu fashewa da kuka itama saita tayasu kukan.
.
Al amarin da ya karya zuciyar sarauniya larbisa kenan a karon farko a rayuwarta taji tausayin
wani ya kamata har itama idanunta suka ciko da kwalla kuma ba komai bane ya janyo hakan ba
face ganin matsalar ta