Showing 3001 words to 6000 words out of 12157 words
Chapter 2 - TSATSUBA 2 Littafin Yaki Na Abdulaziz Madakin Gini .pdf
tazo iri daya da tasu.
.
Saida tsoho Imshal da larisa suka dan jima a kankame da shumaira sannan imshan ya janye
jikinsa daga cikin na shumaira ya dubeta cikin Alamun tsananin damuwa yace yake yata hakika
kinzo mini da babban Al amari wanda ya dugunzuma hankalina kuma wanda a halin yanzu ba
zan iya yanke hukunci ba a kansa lallai ina bukatar ki bani lokaci daga nan zuwa gobe muyi
tunani da nazari akan al amarin nida mahaifiyarki koda jin wannan batu sai hankalin sarauniya
larbisa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe domin ta fara tunanin cewa tsoho Imshal ba zai
yarda da wannan tafiya ba don haka duk shirinta ya rushe.
.
Nan dai shumaira ta mike tsaye ta kama hannun sarauniya larbisa ta jata suka fice daga cikin
falon duk su biyun jikinsu a sanyaye, lokacin da dare ya sakeyi sai shumaira da sarauniya
larbisa suka kasa barci saboda zulumi da fargabar sakamakon shawarar da iyayen shumaira
zasu yanke akan wannan tafiya suna cikin wannan hali ne shumaira ta mike zaune daga kan
gadonta ta dubi larbisa tace ranki ya dade ni fa tunda ina cikin zulumin abinda zai biyo baya ba
zan iya barci ba, ina mai tabbatar miki da cewar rayuwata gaba daya yanzu babu wani abu da
ya shiga raina sama da yin wannan tafiya koda kuwa ina da yakinin zan mutu nafi son na mutu
jaruma akan na mutu raguwa a cikin rashin yanke wannan bakin ciki na zuri armu saboda haka
yanzu zanje na gana da mahaifina domin naji hukuncin da ya yanke koda gama fadin hakan sai
shumaira ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin ita kuwa sarauniya larbisa saita bita da kallo
kawai cikin alamun tsananin damuwa, jikinta na tsuma zuciyarta na dukan uku uku tana
fargabar abinda zaije ya dawo lokacin da shumaira ta isa falon mahaifinta saita iske
mahaifiyarta zaune akan kujera tayi tagumi kanta a sunkuye tana zubar da hawaye shi kuwa
tsoho Imshal yana tsaye yana kai kawo duk su biyun fuskokinsu na nuna alamun tsananin
damuwa da fargaba.
.
Koda shumaira taga iyayenta a cikin wannan hali sai hankalinta ya dugunzuma ainun taji kamar
ba zata iya tunkararsu da maganar ba tunda su ma suna cikin irin halin da take ciki kawai sai
shumaira ta juya da nufin ta koma izuwa dakinta.take tsoho Imshal ya kira sunanta shumaira ,
kada ki koma kizo mu tattauna wata muhimmiyar magana koda shumaira ta juyo tana mai amsa
kiransa saita ga fuskar tsoho Imshal ta juye izuwa murmushi da annuri cikin mamaki shumaira
ta tunkari mahaifin nata ta iso daf dashi yadda har suna iya jin numfashin juna tsoho Imshal ya
dafa kafadar shumaira yace, yake yata ki kwantar da hankalinki kiyi sani cewa ba zan iya
hanaki yin wannan tafiya ba saboda ganin muhimmancinta.
.
Amma akwai sharadi guda daya da zamuyi dake wannan sharadi kuwa shine ba zamu yarda
kiyi wannan tafiya ke kadai ba sai tare damu koda jin wannan sharadi sai idanun shumaira suka
zazzaro hankalinta ya dugunzuma ainun ta dubeshi tace haba yakai Abbana tayaya zanyi
wannan tafiya tare daku alhalin girma ya kamaku baku da karfin jiki gami da jarumtaka irin tawa
koda jin wannan batu sai tsoho Imshal ya sake yin
murmushi a karo na biyu yace Ashe kin manta da cewar nine na koya miki yadda ake farauta a
cikin daji da yadda ake yin yaki a cikin dandazon mayaka??
.
To kiyi sani cewa ko giwa ta fadi tafi gaban a dasa mata wawa malami har abada malami ne
akan dalibansa ina mai tabbatar miki da cewa ni da mahaifiyarki zamu baku gagarumar
gudumawa a cikin wannan tafiya yadda zaku sha dumbin mamaki saboda haka ki koma dakinki
ki gayawa sarauniya larbisa cewar ku fara shirin wannan tafiya tun a daren yau amma ina son
ta turo mini babban abokin tafiyarta tsoho Huzallatul marwas yanzu take kuma ta gaya masa
cewa ya taho tare da jakar sihirinsa shumaira ta juyo jikinta a sanyaye ta koma izuwa can
turakarta zuciyarta cike da zulumi. Fargaba da tsananin damuwa lokacin da shumaira ta isar da
wannan sakon mahaifinta izuwa ga sarauniya larbisa ta firgita kuma ta kamu da tsananin
mamakin yadda akayi tsoho Imshal ya san da batun jakarsa ta sihiri alhalin bata gabatar dashi
ba a wajansam nan take larbisa ta gano cewar lallai shi ma tsoho Imshal ya cika boka masanin
abinda ke boye ba tare da boye komai ba sarauniya ta tashi ta tafi izuwa masaukinsu tsoho
huzallatul marwas ta jashi izuwa gefe daya ta sanar dashi sakon tsoho Imshan, koda jin hakan
sai huzallatul marwas ya bushe da dariya.
.
Al amarin da ya baiwa larbisa mamaki kenan kuma ranta ya baci ta dubeshi a fusace tace
menene kuma abin dariya a cikin wannan Al amari??
.
Huzallatul marwas ya numfasa yace hakika mahaifim shumaira ya cika hatsabibin boka domin
ban taba zaton zai gano da batuna ba a cikin wannan tawaga taki bare ma har ya san da batun
jakar sihirinsa babu komai ki kwantar da hankalinki yanzu jamuje na riskeshi domin naji dalilin
da yasa ya bukaci ganina, koda gama fadin hakan sai tsoho huzallatul marwas ya yunkura da
nufin ya juya ya nufi hanyar da zata kaishi inda turakar tsoho Imshal yake. Tsulum sai suka ga
aljani subauratu ya baiyana a sama daf da fuskarsa yana mai kyalkyala dariya lokaci guda
kuma sai ya hade fuskarsa ya risina ga huzallatul marwas yace ya shugabana kayi sani cewa
zuwanka kai kadai izuwa ga tsoho Imshal yana da hadari don haka duk yadda za ayi ka tafi tare
da sarauniyarka komai rintsi da tsanani kada ka yadda kayi wata magana dashi sai sarauniya
na kusa tana sauraronka, kafin tsoho Huzallatul marwas ya budi baki ya tambayi subauratu
dalilin da yasa ya bashi wannan shawara tuni subauratu ya bace bat, sai jin motsinsa yayi a
cikin jakarsa ta sihiri Huzallatul marwas ya dubi larbisa yace ranki ya dade menene abinyi?
.
Larbisa tayi murmushi tace yadda Aljani subauratu ya fada haka za ayi, nan take suka
dunguma su biyun suka koma can turakar tsoho Imshal inda suka iskeshi tare da yarsa
shumaira da matarsa larisa a zaune koda Isham yaga larbisa ta biyo tsoho huzallatul marwas
sun dawo tare sai ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dubi larbisa
yace ai sai ku bamu wuri don ina son na gana da huzallatul marwasu koda jin haka sai
huzallatul marwas ya matso gaban Isham ya mika masa hannu suka gaisa sannan yace yana
daga cikin sharaddan tafiyarmu nida sarauniya cewar komai tare da ita zanyi, ba zan boye mata
komai ba koda jin wannan batu sai jikin tsoho Isham yayi sanyi kawai sai ya kyalkyale da dariya
ya rungume huzallatul marwas yana mai cewa lale marhaban da babban aboki ma abocin
hikima da hangen nesa shi kenan kuje ku kwanta domin ku dan rintsa kafin gari ya waye mu
kama hanya dajin haka sai larbisa da tsoho Huzallatul marwas marwas suka dubi junansu suka
yi murmushi nan take suka yiwa su tsoho isham sallama suka juya suka fice daga cikin falon,
fitarsu keda wuya sai jaruma shumaira ta dubi isham fuskarta cike da alamun tsananin damuwa
tace ya kai abbana yanzu ta yaya kenan zamu san shafin da ya kamata mu karanta a cikin
littafin tsatsuba domin kawai da wannan matsala tamu tunda gashi sarauniya larbisa taki yarda
ta barka ka kebe da tsoho huzallatul marwas bare har kuyi wannan yarjejeniya damu ka tsara?
.
Koda jin wannan batu sai tsoho isham ya bushe da dariya yace ai maso abinka ya fika dabara
kuma masu iya magana sunce samu yafi iyawam idan har muka mallaki littafin tsatsuba a
hannunmu munyi mai wuyar da sannu zamu gano duk wani sirri dake cikinsa da jin wannan
batu sai hankalin jaruma shumaira ya kwanta zuciyarta ta cika makil da farin ciki amma da ta
tuno irin mugun hadarin dake cikin tafiyar da zasuyi kuma gashi tare da iyayen nata za ayi
wannan tafiya sai hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abinda yake yi mata dadi haka dai ta
yiwa iyayen nata sallama cikin sanyin jiki ta tafi izuwa turakarta kashegari kuwa tun kafin Alfijir
ya keto kowa ya gama shirin tafiya nan take aka hau dawakai aka kama hanya aka nausa cikin
daji tsoho huzallatul marwas, sarauniya larbisa da sadauki humaisu ne akan gaba jaruma
shumaira da iyayenta kuwa sune a karshe domin dakarun larbisa ma suna gabanta bayan an
shafe sa a guda ana tafiya sai tsoho huzallatul marwas ya dubi sarauniya larbisa a lokacin da
suke tafiya kafada da kafada bisa dawakansu yace ya shugabata kiyi sani cewa ruwa baya
tsami banza lallai akwai wata hujja mai karfi wacce tasa iyayen shumaira suka siyar da
rayuwarsu wajen biyomu a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske. Yayinda sarauniya larbisa taji
wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai zamu gani tunda dai sannu sannu
bata hana zuwa sai dai a dade ba a jeba
.
Kamar yadda sannu sannu ba zata hana AlQuyraemey xan ci gaba da rubuta muku wannan
littafi saidai a jima ba ajeba..A nan nake cewa sai Allah ya kaimu Gobe dominmjin Yadda zata
kaya a cikin wannan Littafi Na tsatsuba
TSATSUBA
BOOK 2C
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Yayin da sarauniya larbisa taji wannan batu sai tayi murmushi tace koma menene a ransu ai
zamu gani tunda dai sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba, Tsoho Huzallatul
marwas ya gyada kai yace tabbas zancenki Dutse ne Larbisa tace wai shin yanzu ina Muka
dosa ne? .
Huzallatul marwas yayi murmushi yace in banda abinki ya zaki tambayi kaza hanyar rafi, ni
kaina ina bin jagorancin jaka ne, duk inda naga ta nuna nan nake bi damu. Amma ai idan baki
manta ba zamuje neman jaruma larifat ne wacce zata yi mana jagora a cikin daji na biyu wanda
shine dajin Ujurul majnun ki kwantar da hankalinki don nasan cewar ba zamu dauki wani dogon
lokaci ba muna tafiyar zamu riske ta bisa taimakon wannan jakar sihiri nawa.
.
Koda jin haka sai Larbisa tayi shiru bata kara cewa komai ba haka dai aka ci gaba da wannan
tafiya ba dare ba rana babu abinda yake sawa a tsaya ko a yada zango face gajiya ko yunwa
da kishirwa, har tsawon kwana uku sannan suka iso wani babban birni mai kyau gaske wanda
aka kawatashi da gine gine masu kyau da kawa ita kanta sarauniya larbisa sai da wannan birni
ya birgeta ta raina kyawun nata birnin harma tana cewa a cikin ranta lallai duniya da fadi
hakama abin cikinta a iya tunanin sarauniya larbisa ba za a taba samun birnin da
yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya da yafi nata girma da kawatuwa ba a duniya amma sai
gashi tun kafin ma tafiya tayi nisa ta fara ganin cewar ba haka
bane.
.
Tun daga nesa da masu gadin kofar birnin suka hango tawagar sarauniya larbisa sukaga
alamar cewar manyan mutane ne masu daraja sai suka bude musu kofada sauri har daya daga
cikinsu yayi musu jagora izuwa fadar birnin tun akan hanya kafin a isa fadar sai jaruma
shumaira ta matso kusa da larbisa ta dubeta tace to wai shin mu yanzu menene yashigo damu
cikin wannan gari alhalin mun zo ne neman jaruma larift kuma ga yadda aka bayar da labarinta
ba zata yi rayuwa ba a cikin gari sai dai a daji?
.
Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa tayi murmushi tace ai da dan gari akanci gari, yanzu
idan muka ce zamu tafi neman jaruma larifat bamu san a cikin dajin da take ba amma da zarar
mun shiga cikin birnin zamu sami labarin inda take wata kilama mu sami karin haske akan
yadda zamu tunkareta ba tare da mun fuskanci wata matsala ba. koda shumaira taji wannan
batu sai tayi ajiyar zuciya tayi shiru bata kara cewa komai ba... .
Fada ce kasaitacciya abar kwatance domin lokacin da aka shigo dasu sarauniya Larbisa cikin
fadar sai gaba dayansu suka kama kalle kalle suka zama kamar yan kauye saboda ganin irin
kyan fadar da kawatuwarta.
.
A wannan lokaci ne larbisa ta dada tabbatar da cewar gaba da gabanta Aljani ya taka wuta Ita
dai a iya saninta a can nahiyoyin dake bangarenta babu wata kasa mai girma da karfin Arziki
kamar kasarta don haka sai ta fara tunanin cewa a duniyar ma gaba daya ba a taba samun
kamarta ba amma a yanzu da ta tsinci kanta a cikin wannan birni da wannan bakuwar fada sai
ta karyata kanta, wani kyakkyawan saurayi ne na kwatance bisa karagar mulkin wannan fada
ya yi babbar shiga ta alfarma irin wacce attajiran sarakai da suka gawurta ne kadai ke iya yinta
domin tufafin dake jikinsa darajarsu takai jarin wani mashahurin attajirin, hatta takalminsa da
kwagirin dake hannunsa na lu'u lu'u ne a yatsun hannayensa na hagu da dama akwai zobuna
guda shida kuma duk na zinare ne masu tsadar gaske, shi kansa rawanin dake kansa da
falmaran din dake jikinsa da zaren zinare a aka dinkasu.
.
Koda jaruma shumaira da sarauniya larbisa sukayi Arba da wannan sarki sai kyawunsa da
kwarjininsa ya dimautasu sukaji nan take sun kamu da tsananin sonsa. Hakika babu wata 'ya
mace da zata ga wannan sarki bataji ta kamu da tsananin sonsa ba, saboda baiwar da allah
yayi masa ta kyau da arziki, gashi idan yayi ado sai kaga tamkar dawisu ne koda shigowar su
sarauniya larbisa cikin fadar sai sarkin ya dubesu sau daya ya kau da fuska kuma babu annuri
akan fuskar tasa, Al amarin da ya dugunzuma hankalinsu kenan domin a tunaninsu kyawunsu
kadai zai iya sawa sarkin yayi marhaban dasu bare kuma ga matsayi na sarautar larbisa, cikin
sanyin jiki suka karasa kusa da karagar mulkin sukayi cirki cirko caraf sai tsoho isham ya zube
kasa gaban sarki ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da sarauniya larbisa da jaruma
shumaira ya kara da cewa yakai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa ba wani abu bane ya
kawomu birninka ba face neman jaruma Larifat ma abociyar basira da hangen nesa saboda
muna son tayi mana rakiya izuwa dajin ujurul majnun domin biyan
wata muhimmiyar bukata ta sarauniya Larbisa.
.
Koda jin wannan batu sai sarkin ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ta mulki. Fuskarsa
cike da annuri ya kama kafadun tsoho Isham ya tashe shi tsaye
ya jashi har kan karagarsa suka Zauna tare, su sarauniya larbisa ma sai yasa aka basu kujeru
na alfarma suka zauna sannan aka kawo musu abinci da abin sha na alfarma suka kama kimtsa
cikinsu suna masu murna da mamakin yadda akayi nan da nan ra'ayin sarkin ya sauya bisa jin
abindake tafe dasu sai da kowa ya gama kimtsawa ya sami natsuwa sosai, sannan kyakkyawan
sarkin ya dubi tsoho isham yace yakai wannan dattijo kayi sani cewa yau shekara bakwai kenan
ina fama da tsananin so da begen wannan jaruma larifat amma ko sau daya bata taba kallona
ba tayi mini murmushi bare ta karbi tayin soyayyata sai dana kwanta rashin lafiya sau bakwai
sakamakon ciwon sonta da ya kayar dani amma bata taba zuwa ta dubani ba ni da ita bata taba
yi mini magana ba kuma bata taba amsa gaiyatata ba izuwa wannan gidan sarauta ba.
.
Lokacin da na dameta da aika manzanni da kyaututtuka iri iri na duniya sai ta tattaro duk abinda
nake bata na tsawon shekaru bakwan ta dawo mini dasu gami da wasika.
.
A cikin wasikar ne ta shaida mini cewa na daina bata lokaci na da tunanina a kanta domin ta
daukarwa kanta alkawari cewar ba zata taba yin aure ba ko soyayya har sai tayi gagarumin abin
gwanintar da wani bai taba yi ba a duniya lokacin da naji wannan batu sai na kamu da tsananin
bakin ciki kuma na fashe da kuka na takaici domin banga ranar da larifat zata cika wannan buri
ba daga wannan rana ne nima na yi alkawarin na daina cin abinci mai dadi na daina kwanciya a
wuri mai kyau kuma na daina murmushi da sukuni har izuwa karshen rayuwata face a ranar da
naji cewar ta sami damar da zata cika burinta.
.
A tsawon shekaru bakwai da suka gabata wannan dama bata samu ba sai yanzu naji kunzo
mini da wannan batun na zuwa kogon Kitabul sihir inda littafin tsatsuba yake sai naji a jikina
cewar lokacin samun yardar larifat yayi a gareni
domin a yanzu ne zata iya yin jarumtakar da har abada ba za a mance da ita ba a duniya, ko
shakka babu na san cewa larifat zata karbi wannan tayi naku domin bata tsoro ko shakkar wani
abu mai rai akan biyan bukatarta, babu wani abu wanda zaku iya biyanta da shi domin ta wuce
daku ta cikin dajin ujurul majnun face kwadayin cika na ta burin ba wani abu da yake burge
jaruma larifat a cikin wannan duniya, saboda ta rasa iyayanta yan uwanta da dukkan danginta
bisa wannan daliline ta kebe kanta daga cikin mutane ta koma cikin daji da zama inda ta zabi ta
karasa sauran rayuwarta gaba daya yanzu dai a gajiye kuke, don haka zan sa a kaiku masauki
ku huta washe gari da safe ni da kaina zanyi muku jagora izuwa dajin Da jaruma larifat take
domin ku gana da ita, ku sanar da ita bukatar dakuka zo da ita a gareta. Amma ina neman wata
alfarma guda daya a wajanku? Alfarmar kuwa itace ina son nima nayi muku rakiya a cikin
wannan tafiya domin idan kuka tafi kuka barni fargaba tunani da begen halin da larifat ke ciki zai
iya jefani cikin wani mugun hali.
.
Koda sarki AYUBUL HASNU yazo nan a zancensa sai kowa ya cika da mamaki musamman
sarauniya larbisa da shumaira. Sarauniya larbisa ta dubi sarki Ayubul hasnu cikin mamaki tace
yakai wannan