Showing 9001 words to 12000 words out of 12157 words

Chapter 4 - TSATSUBA 2 Littafin Yaki Na Abdulaziz Madakin Gini .pdf

Yaƙi
.
.
Sai gashi nan da nan ya haɗa mashi jini da majina yana bal dashi kamar tamola, ashe duk
wannan abu dake faruwa shadila ta leko ta cikin tantin da take tana ganin abin dake faruwa
cikin tsananin fargaba da tashin hankali kwatsam sai sarki shardas ya sami nasarar saran
kafadar hailur ta hagu hailur ya kurma ihu a lokacin da jini yayi tsartuwa a kafadar tasa amma
sai yayi sauri ya rike takobin ta Sarki shardas a lokacin da shi sarki shardas ke son ya danna
takobin ta nutse a cikin kafadar koda shadila ta hango abinda ya faru ga mijinta saita kurma ihu
bata san sa adda ta fito da gudu daga cikin tantin da take boye ta rugo izuwa inda suke jiyo
ihunta da gudun tane yasa sarki shardas ya waigo yayi arba da ita koda yaga irin tsananin
kyawunta sai ya dimauce ya juya da sauri ya doke kirjin hailur da karfin gaske saboda karfin
dukan saida hailur yayi tsalle sama da baya kamar an janyeshi da majajjawa ashe bayan nasa
wani rami ne mai tsananin zurfin tsiya wanda karshensa kwazazzabo ne da magudanar ruwan
wata korama koda hailur yaji ya fada cikin wannan rami sai ya kwarara uban ihu irin na wanda
ya saddakar mutuwa zaiyi ita kuwa shadila tana ganin abinda ya faru ga mijinta sai ta sulale
kasa sumammiya.
.
Sarki shardas ya bushe da dariyar farin ciki ya ruga da baya izuwa inda shadila ke kwance ya
dauketa ya azata akan dokinsa nan take dakarunsa suka kwashe gaba dayan dukiyar wannan
ayari nasu hailur suka ingiza keyar bayin da suka kama akayi gaba ana tunkarar birnin
Romaniya. .
Ana fara tafiya sai sarki shardas ya sake rufe fuskarsa da bakin rawani kuma ya shakawa
shadila banju barcinta ya sake nauyi don haka bata farka ba har aka isa birnin romaniya da
tsakiyar dare lokacin da shadila ta farka daga barci sai ta tsinci kan wani luntsumemen gado na
alfarma a cikin wani kasaitaccen daki na sarauta cikin razana ta mike tsaye da sauri ta sauko
daga kan gadon, ta kama kallon kowacce kusurwa koda tagama ganin kayan kawar dake cikin
dakin sai tunanin mijinta da sauran jama arsu ya fado mata ta tuno da duk abinda ya faru a
sansaninsu sa adda aka kawo musu sumame na mamayar bazato nan take shadila ta dafe
kunnuwanta da hannayanta biyu ta kurma uban ihu tana mai fashewa da matsanancin kuka
faruwar hakan keda wuya sai taji an bude kofar turakar ba wani bane ya shigo cikin turakar face
sarki shardas a cikin wata irin kyakkyawar shiga ta sarakai fuskarsa cike da annnuri ya
durfafeta.
.
Koda tayi arba dashi sai ta razana ainun taja da baya tana mai nunashi da yatsa a lokacin da
hawaye ya zubo mata tace ka cuceni ka kashe mini miji kuma ka kashe dukkan mazajen
ayarinmu ina sauran yan uwana mata?
.
Me kake nufi dani ka kawoni nan ni kadai kawai ka kasheni na huta da kunci da bakincikin
rayuwa tunda ka rabani da masoyina da dukkan zuri ata koda jin wannan batu sai sarki shardas
ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dubeta yace yake wannan ma
abociyar kyawu da cikar zati kiyi sani cewa kece mafi sa a bisa dacewa da zama matar sarkin

birnin Romaniya a yanzu duk wata rayuwa da kikayi a baya ki manta da ita ki manta da komai
da kowa ki fuskanci sabuwar rayuwar da tazo miki wacce zaki tsinci kanki a cikin daular da baki
taba ji da gani ba koda jin wannan batu sai zuciyar shadila ta kama tafarfasa kamar zata kone
saboda tsananin fishi taji ta tsani sarki shardas fiye da komai a doron kasa koda idanunta suka
kai kan wata wukar dake kan wani faranti babba mai dauke da tuffa masu yawa sai tayi zumbur
ta suri wukar ta ritsa sarki shardas da ita tace kada ka kusanceni idan ka matso kusa dani zan
kasheka.
.
Sarki shardas ya bushe da mahaukaciyar dariya ya durfafeta kai tsaye ai kuwa yana kusantarta
sai ta caka maza wukar a kirji take wukar ta balle gida biyu taji kamar akan dutse ta bugata
kawai sai sarki shardas ya hankadata ta fada kan gadon dake bayanta sannan ya bita izuwa
kan gadon bai rabu da ita ba har sai da bukatarsa ta biya tana ta faman rusa ihu da kukan bakin
ciki daga wannan rana shadila ta zama matar sarki shardas da karfin tsiya ya zamana cewa
kullum a cikin daula take babu abinda takeyi da hannunta sai dai kuyangi da barori suyi mata
duk da cewar ta tsinci kanta a cikin daula irin wacce bata taba ji da gani ba sai ya zamana cewa
kullum a cikin kuka da bakinciki take musamman
idan ta tuno da tsohon masoyinta kuma sabon angonta hailur da kuma sauran danginta da zuri
arta lokacin da shadila ta matsawa sarki shardas akan sai taga inda aka kai sauran +yan
uwanta mata wadanda aka kama a matsayin bayi sai yayi mata jagora izuwa wani bangare
daban na gidan sarautar wannan ranace ta farko wacce shadila ta sami damar fita daga
bangaren da turakarta take koda taga yadda girman gidan sarautar yake da yawan dakarun
dake tsaro a ko ina sai hankalinta ya dugunzuma ainun domin take burinta na son guduwa ya
yanke, haka dai sarki
shardas yaci gaba da yiwa shadila jagora suna ta ratsawa ta cikin lunguna da sakuna har sai da
sukayi tafiya mai nisa duk inda suka ratsa sai dai kaga bayi barorim hadimai da dakaru suna
risinawa suna gaishesu har suka iso wani katon gida wanda ke cike da bayi mata.
.
Koda shadila tayi arba da yan uwanta mata yan zuri arsu suna ta yin ayyuka na bauta iri iri sai
ta ruga garesu tana mai kiran sunayansu daya bayan daya tana zubar da hawaye take suma
bayin suka rugo gareta suka rungumeta suna kuka.bayan ta dan jima a kankame dasu sai ta
janye jikinta daga cikin nasu ta juyo ta dubi sarki shardas tace ina neman alfarmar ka yanta
wadannan yan uwa nawa daga matsayin bayi masu aikin bauta zuwa ga kuyangina.
.
Koda jin wannan batu sai sarki shardas yayi shiru yana mai sunkui da kai ya dubi shadila cikin
murmushi yace yake matata kiyi sani cewa babu wani abu da zaki nema a wajena ki rasa
saboda tsananin irin son da nake yi miki don haka zanyi miki wannan alfarma bisa sharadi guda
shardin kuwa shine wadannan bayi idan suka koma can wajanki ba zasu taba fita ba daga cikin
harabar gidanki duk wacce aka kama da laifin hakan hukuncin kisane a kanta.
.
Koda jin haka sai farinciki ya lullube bayin suka fara rungume shadila sunayi mata godiya ita
kuwa shadila sai ta dubi Sarki shardas tace na amince da wannan sharadi naka nan take sarki
shardas ya sa dakarun dake kula da wadannan bayi suka kwankwance musu sarkokin dake
wuyansu da hannayensu sannan aka tafi dasu izuwa can bangaren gidan shadila a nan ne aka

basu suturu masu kyau sukaje sukayi wanka suka sanya suturu
.
Tun da aka kawo shadila wannan gidan sarauta na birnin romaniya bata taba yin farin ciki ba sai
a wannan rana da aka 'yanta wadannan bayi kuma bata taba yiwa Sarki Shardas murmushi ba
sai a yau din nan.
.
Hakika shadila ta tsani sarki shardas fiye da komai a duniya kuma inda tana da ikon kasheshi
ko guduwa daga gidan sarautar da tuni ta aikata haka dai dai da rana daya shadila bata taba
mancewa da mijinta ba Hailur kusan kullum sai tayi mafarkinshi
sau tari a mafarkin nata ana nuna mata cewar hailur yana nan a raye bai mutu ba amma idan ta
tuno da tsananin zurfin ramin da ya fada sai taga cewar mafarkin nata ba zai taba zama gaskiya
ba babban abinda take yin nadamar aikatashi shine karya sharadin da tayi a lokacin da hailur
ya gaya mata cewa komai tsanani kada ta kuskura ta fito daga cikin wannan tanti da take amma
sai ta mance da sharadin ta fito da gudu bisa dimaucewar da tayi a lokacin da taga sarki
shardas ya sareshi da takobi a kafada ta kwalla ihu ta fito da gudu ta baiyana kanta.
.
Tabbas inda bata fito ba da sai hailur ya kubuta daga sharrinsa kuma da sai sun gudu tare
lokacin da shadila ta sami wata uku a cikin gidan sarautar sarki shardas sai alamun juna biyu
suka baiyana a gareta ya zamana cewa tana fama da tashin zuciya, kumallo da zazzafi da
ciwon kai ko da sarki shardas yaga shadila bata da lafiya sai hankalinsa ya dugunzuma nan
take ya tura aka
kirawo wata likita tazo ta dubata cikin murmushi likitar ta dubi sarki shardas tayi masa bushara
cewar matarsa ta sami juna biyu
Koda jin haka sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki amma da ya tuno da wani al
amari sai hankalinsa ya dugunzuma ainun kuma ransa ya baci take zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone jikinsa ya kama kyarma bai san sa adda yasa hannu ya zabgawa shadila mari
ba, saboda karfin marin saida ta fadi kasa bakinta ya fashe jini yazubo sarki shardas ya
sunkuya ya kamo kafadunta yana mai daka mata tsawa yace wanene yayi miki ciki ban sani ba
a cikin gidan sarautata kiyi sani cewa yau shekara ashirin kenan ina neman haihuwa ban samu
ba kuma matana na aure guda goma sha shida ne a cikin gidannan bokana ya tabbatar mini da
cewar ba zan taba haihuwa.ba har sai na mallaki wata hular sihiri wacce ake kira LAMSARA.
.
Lallai wannan ciki da kike dauke dashi ba nawa bane maza ki hanzarta sanar dani maishi kona
shakeki ki mutu yanzu.
.
Koda sarki shardas yazo nan a zancensa sai shadila ta bushe da dariya al amarin da yayi
matukar baiwa sarki shardas mamaki kenan kuma jikinsa yayi sanyi ya mike tsaye yana mai
kura mata idanu, shadila ta yunkura ta mike tsaye ta dubi sarki shardas a fusace tace shin kana
tunanin ina tsoron mutuwa ne? To ka sani cewa duk wannan daula da nake ciki a wannan gidan
sarauta daidai yake da kurkuku a wajena, gaba daya rayuwar duniya ta fita daga raina tun daga
ranar da ka wargaza rayuwata ka rabani da babban masoyina hailur kuma ka tarwatsa
ayarinmu, ka sani cewa wannan hari da kuka kai mana an kashe uwata da ubana da dukkan
dangina a yanzu bani da sauran masoyi a doron kasa face masoyina hailur wanda har yanzu

xuciyata ke wasu wasin cewar yana nan a raye bai mutu ba idan har yana raye ina tabbatar
maka da cewa sai yazo har nan gidan sarautar ya daukeni mun tafi domin wannan juna biyu da
nake dauke dashi nasa Ne bana wani ba, kafin shadila ta gama rufe bakinta ya sake zabga
mata mari ta baje a kasa sumammiya nan take kuyangi suka rugo izuwa kanta suka shiga ceto
rayuwarta.
.
Koda ganin haka sai sarki shardas ya rude yayi nadamar abinda ya aikata saboda tsananin son
da yake yiwa shadila don haka bai san sa adda ya kwarara uban ihu ba har kwallar takaici ta zo
masa.
.
A fusace ya baro turakar shadila ya aika aje a kirawo masa babban bokan birnin wanda ake kira
da Barwas ibn Mus ab Lokacin da ya isa wajan boka barwas sai ya labarta masa duk abinda
yake faruwa nan take bokan yake shaida masa abubuwan
matakin da ya kamata ya dauka yake cewa akan wannan juna biyu data samu ya kasance mai
nuna mata kauna kulawa da soyayya irin wacce ma baka taba nuna mata ba ka zamo mai
tarairayarta kada ka bari koda kuda ya taba lafiyarta kuyi renon cikin tare kai da ita har izuwa sa
adda zata haihu lafiya kuma har izuwa sa adda yaron zai cika shekara bakwai a wannan lokaci
kun shaku ainun da yaron kawai saika tsiri tafiya wannan tafiya kuwa nine zanyi maka jagora a
cikinta kuma ba zamu dawo ba har sai mun sami nasarar mallakar hular lamsara ina mai
tabbatar maka da cewar da zarar mun mallaki hular lamsara tamkar mun dora duniyar nan ne
dukanta a tafin hannunka komai da kowa sai ya dawo karkashin ikonka kuma babu wani
makiyinka da zai iya samun nasara a kanka
.
Anan zan dakata haka amma kafinnan nake cewa mu kwana lafiya.

Lokacin da boka Barwas yazo nan a zancensa sai sarki shardas ya kamu da tsananin farin ciki
bai san sa adda ya rungume boka barwas ba yana mai kyalkyala dariya daga can kuma sai ya
janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna ya dubeshi yace tabbas yanzu na sami
nutsuwa da kwanciyar hankali saboda haka ka zuba idanu kawai kasha kallo zaka ga abin da
zai biyo baya, koda jin haka sai boka barwas ya kyalkyale da dariyar farin ciki yayi ta
kyakyatawa kamar ba zai daina ba daga can kuma saiya hade fuska tamkar an aiko masa da
sakon mutuwa ya dubi sarki shardas cikin alamun tsananin damuwa yace ya shugabana yaya
batun alkawarinmu idan bukata ta biya? Koda jin wannan tambaya sai sarki shardas ya bushe
da dariya yace ai alkawarina dakai dutse ne babu abinda zai kankareshi face rashin biyan
bukatata, daga wannan rana Sarki shardas ya fara aiki da shawarar boka barwas ya zamana
cewa ya karbi juna biyun shadila hannu biyu ya rinka riritata da kyautata mata fiye da kowa
.
Al'amarin da yayi matukar baiwa shadila mamaki kenan tun tana ganin abin kamar yaudara ce
taga ashe zahiri ne kuma gaskiya domin babu abinda fuskarsa da zuciyarsa ke nunawa face
tsananin soyayya da kulawa Abu dai kamar wasa a cikin wata uku kacal sai gashi shadila ta
fara sakin jiki da sarki shardas duk da cewar ta daukeshi babban makiyin da babu kamarsa a
cikin zuciyarta sai gashi ta fara rayawa a cikin zuciyarta cewar ya kamata ta danne wannan
gaba a ranta ta dauki komai a matsayin kaddarar da ta wuce nan fa zuciyarta taci gaba da raya

mata cewar ya kamata ta manta da duk rayuwarta ta baya ta fuskanci
sabuwar rayuwar da take ciki yanzu domin samun rayuwa ta gari ga abinda take dauke dashi a
cikinta kamar sarki shardas ya san abindake cikin ranta.
.
Wata rana shadila na zaune ita kadai a cikin turakarta bisa wata doguwar kujera ta alfarma irin
ta sarakai a wannan lokaci tana sanye da wata doguwar riga fara mai shara shara wacce ke
nuna tsiraicin jikinta koda ta dubi cikinta taga ya dan fara girma sai ta shiga shafa cikin tana
murmushi ba komaine ya sa ta wannan murmushi ba face tunowa da babban masoyinta wato
mahaifin abinda zata haifa nan take ta shiga tunanin irin abubuwan da suka faru a baya
tsakaninta dashi tun farkon soyayyarsu kawo izuwa sa adda su sarki shardas suka kawo harin
sumame ga sansaninsu lokacin da yake gaya mata cewar kada ta kuskura ta fito daga cikin
wannan tanti da take ciki.
.
Koda tazo dai dai inda taga sarki shardas ya sareshi da takobi sai ta kwalla uban ihu, ihun ne
sarki shardas ya jiyo a lokacin da dama ya nufo turakar tata cikin firgici da razana sarki shardas
ya rugo da gudu izuwa cikin turakarta yana shigowa sai yayi turus bisa ganin cewar babu kowa
a cikin turakar face shadila ita kadai a zaune hawaye na zuba daki daki a kan kyawawan kumatunta cikin sanyin jiki sarki shardas
yaje ya zauna akan kujerar dake fuskantar wacce shadila ke zaune ya kama hannayanta biyu
ya
rike suka kurawa juna idanu sannan ya budi baki a cikin murya mai taushi da sanyi a lokacin da
idanunsa suka ciko da kwalla wannan shine karo na farko da shadila taga kwalla a cikin idanun
sarki shardas tun da aka kawo ta gidan sarautar Sarki shardas yace ya ke matata na sani cewar
a duniya babu wani mutum wanda kika tsana kuma kika daukeshi babban makiyinki sama dani
saboda na kashe miki miji a ranar farko na amarcinku sannan na rabaki da duk zuri'arki na
kawoki kasata da karfin tsiya inda nayi miki fyade kuma na maishe dake matata ta dole har
abada babu abinda zan yi na goge wannan tabo nawa akan idanunki ko kuma na burgeki bare
harna sami gafararki ki sani cewa ni masoyinki ne na har abada duk da nasan bakya kaunata
dai dai da tsawon dakika daya ba zan taba so naga rayuwarki da ta abinda zaki haifa ta
kasance a cikin farin ciki, alfarma daya nake so na nema a wajanki ina son ki boye laifin da na
yiwa mahaifin abin dake cikinki a tsakanina dashi har izuwa kamar tsawon shekaru bakwai nan
gaba a sannan zaki iya sanar dashi komai idan yana ganin zai iya daukar fansa a kaina sai ya
dauka , kin san cewar ni ba zan taba haihuwa ba face na mallaki Hular lamsara kamar yadda
na fada miki a baya burina kawai shine na reni dan mijinki hailur a matsayin dan cikina, wannan
zai kawai mini da bakin cikin rashin samun da kuma nayi miki alkawarin cewar daga nan har
izuwa tawon shekaru bakwan ba zan taba cutar dashi ba amma fa ki sani cewar a ranar da ya
cika shekara bakwai zanyi shiri na bar kasar nan don tafiya neman hular lamsara bokana ya
tabbatar mini da cewa shima wannan da naki idan ya zama saurayi zai tafi neman hular
lamsara to a sannan ne nake son ki sanar dashi gaskiyar asalinsa da mahaifinsa domin daga
wannan rana mun zama ABOKAN GABA na sani cewa a wannan lokaci bana gida don boka
barwas ya tabbatar mini da cewar sai mun shafe shekara goma sha daya kafin mu gano inda
hular Lamsara take, kinga a wannan lokaci ban san kamannin danki ba shima bai san nawa ba
don haka ko da zamu hadu a wani wurin daban ba zamu shaida juna ba zamu iya abokai kuma

ko kuma abokan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login