Showing 6001 words to 9000 words out of 12157 words
Chapter 3 - TSATSUBA 2 Littafin Yaki Na Abdulaziz Madakin Gini .pdf
sarki mai daraja kayi duba izuwa wannan daula da kake ciki ka dubi girman
kasarka da tarin arzikin dake cikinta ka sani cewa akwai mata da yawa masu kyau a sassan
duniya wadanda zaka iya mallakarsu da karfin dukiyarka da mulkinka saboda me yanzu zaka
siyar da rayuwarka don baiwarka?
.
Lokacin da sarki ayubul hasnu yaji wannan tambaya daga bakin sarauniya larbisa sai ya bushe
da dariya kamar ba zai daina ba daga bisani kuma sai ya hade fuska tamkar an aiko masa da
sakon mutuwa nan fa fadar tayi tsit kamar babu mai rai a cikinta kawai sai aka ga idanun sarki
ayubul hasnu sun ciko da kwallah har hawaye ya zubo masa, sarki ayubul hasnu ya dubi
sarauniya larbisa cikin nutsuwa yace yake sarauniya larbisa kiyi sani cewa a duniya babu wani
abu wanda yafi soyayya karfi da hadari masoya da yawa sun rasa rayuwarsu akan tafarkin
mallakar masoyansu ba komai ne ya janyo hakan ba face duk rayuwar da babu masoyi dai dai
take da zama a cikin kurkukun daurin rai da rai kisan sani cewa ke da jaruma shumaira duk kun
kasance kyawawan matan da babu kamarsu a duk cikin fadin kasata da nahiyarmu amma kuma
baku kama farcen kafar jaruma larifat ba a fagen kyau kunga kenan a yanzu babu wata ya
mace da zata iya maye gurbin larifat a wajena banda fagen kyau a bangaren jarumta kuwa ina
mai tabbatar muku da cewa in daku biyun nan zaku hada karfinku ku yaketa ba zaku taba
samun galaba a kanta ba koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da jaruma shumaira suka
bushe da dariya domin su a ganinsu ma tatsuniya ce abinda sarki Ayubul hasnu yake fadi
shumaira ta dubeshi tace aiko yarima RUHAISU dan sarki ZAIYANU na birnin kufa wanda
masana da masu bincike suka tabbatar da cewar babu mai karfin damtsensa da sa arsa idan
muka hada karfi nida larbisa sai mun gama dashi bare wata jaruma larifat wacce ta kasance 'ya
mace kamarmu yayinda sarki Ayubul hasnu yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ai shi
kenan inda babu kasa nan ake gardama Kokowa, ni dai shawarata guda daya ce a gareku duk
abinda zakuyi kyi shi da cikakkiyar hujja domin banson ku yi irin kuskuren da SADAUKI
HULKAS MAI HULAR LAMSARA YAYI. Koda jin wannan batu sai sarauniya larbisa da jaruma
shumaira suka dubi junansu cikin mamaki larbisa ta juyo ta dubi sarki Ayubul hasnu tace
wanene kuma sadauki Hulkas mai hular lamsara?
.
Koda jin wannan tambaya sai sarki Ayubu hasnu yayi ajiyar zuciya gami da sauke dogon
numfashi sannan yace labari ne mai tsawon gaske sai dai nayi iya kokarina na gani ko zan iya
gajarce muku shi...
.
SADAUKI HULKAS YANA DAGA CIKIN MANYAN JARUMAN DUNIYA GUDA UKU wadanda
akayi musu lakabi da MAZAN JIYA jarumai ne wadanda ba a taba yin kamarsu ba kuma ba za
ayi ba a yanzu da nan gaba domin sun bar abin tarihin da ba za a taba mancewa dasu ba sai
dai kash! Duk su ukun rayuwarsu ta salwanta ne a tafarkin soyayya. Yanzu dai saiku saurara da
kyau kuji wannan labari domin akwai dumbin darasi a cikinsa, nan take sarki AYUBUL HASNU
ya shiga basu labari kamar haka......
.
Hm yanzu ne zamu shiga cikin labarin gadan gadan a yayinda zakuji Labarin sadaukin sadaukai
Hulkas mai hular lamsara kuma daya daga cikin jaruman duniya Mazan jiya saboda haka sai ku
gyara zamanku Amma fa sai gobe idan Allah mai kowa da komai ya kaimu.
TSATSUBA
BOOK 2
PART (D)
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan Yaƙi
.
Nan take sarki Ayubul Hasnu ya shiga basu labari kamar haka ”kimanin shekaru Ashirin da
hudu da suka shude a birnin Romaniya anyi wani azzalumin sarki mai suna SHARDAS IBN
KAUMIL sarki shardas ya kasance gawurtaccen jarumin sadauki mai tarwatsa maza a filin daga
yana da tsananin karfin damtse na Allah ya isa don ance ko giwa ya yiwa naushi daya saita fadi
kasa kisan kai kwace da cin zali kuwa bai maidasu komai ba. .
A cikin wata daya yakan shirya dakarun sumame su kai mamayar bazato izuwa ga ayarin fatake
ko izuwa ga manyan garuruwan da suke da karfin arziki cikin bad da kama su kwato bayi da
dukiya da mata ba tare da an shaida ko su waye ba, a bisa wannan halaiya ne ya addabi gaba
dayan kasashen dake nahiyar gaba daya kuma gashi an kasa gano mutanen dake yin wannan
barna, babu irin matakin da sarakuna basu dauka ba kuma babu irin binciken da bokaye basuyi
ba don gano rundunar dakarun dake wannan mummunar barna amma abu ya gagara babban
abin bakin cikin ma shine sarki shardas ya tara dukiya mai tsananin yawan da jikokinsa ma da
tattabakunnansa ma ba zasu iya cinyeta ba amma duk da haka bai daina yin wannan fashi da
kwace ba.
.
Masana da masu bincike na wannan zamani sun tabbatar da cewar duk duniya babu wani sarki
da ya kai sarki shardas tarin dukiya kuma babu wani gidan sarautar da yakai nashi girma da
kawatuwa, duk bayin da ya kamo da mata ana boye sune a gidajen gonarsa da wani bangaren
daban na gidan sarautar inda har abada ba za a sake ganinsu ba bare ma wani ya shaida
dayansu asirinsa ya tonu a gane cewa shine dan fashin da ya addabi Mutane a nahiyar.
.
Tunda yake kamo Bayi da mata ba ataba samun wanda ya taba guduwa ba daga cikinsu ya
tsira da rayuwarsa face sarki shardas yasa anbi bayansa an kasheshi saboda tsananin tsoron
da ake yiwa dakarun sarki shardas ne yasa aka musu lakabi da suna DAKARUN AJALI.
.
Wata rana sarki shardas tare dakarunsa kimanin mutum dubu uku sun fito mamayar bazato
izuwa wani babban kauye da ke gefen wata makociyar kasa da ake kira salmas sai suka kai
hari izuwa ga ayarin wadansu matafiya masu yawan gaske wadanda suka yada zango a gefen
kauyennwanda ake kira Malgur. .
Su dai wadannan matafiya suna da tarin shanu tumaki da raguna masu yawan gaske kuma
Allah ya albarkacesu da kyawawan mata ababan kwatance ga kuma tarin zuri'a.
.
Al amarin ya faru ne da yammaci sakaliya daf da faduwar rana shugaban wannan ayari saurayi
ne ma aboci kyau kwarjini da jarumtaka ana kiransa da suna Hailur, a wannan rana ne hailur
yayi aurensa na farko a duniya kuma matar da ya aura budurwace yar shekara goma sha
takwas a duniya wacce babu mai kyawunta a duk cikin zuri ar ayarin gaba daya. .
A wannan lokaci wannan ayari sun shagala a cikin bikin auren hailu ana ta kade kade da raye
raye saboda murna kowa da kowa ya zage yana ta rawa maza da mata yara da manya gaba
daya dakarun ayarin dake tabbatar da tsaro sun ajiye makamansu sun shiga cikin taron 'yan
rawa suna cashewa kwatsam ba zato ba tsammani sai gani akayi dakarun Ajali sun bullo daga
kowace kusurwa gabas da yamma kudu da arewa bisa dawakai aguje kuma sun zare makamai
suna ihu da kururuwa nan fa taron biki ya watse mata, yara da tsofaffi suka kama ihu da
guje.guje suna neman maboya, a dai dai wannan lokaci ango Hailur na tare da amaryarsa
shadila a cikin tantinsa suna more amarcinsu kwatsam sai suka jiyo iface iface da guje gujen
jama arsu a rude ango Hailur da amarya shadila suka mike tsaye zumbur daga kan shimfidarsu
suka suri suturarsu suka sanya hailur yayi waje ya dauko takobinsa da garkuwarsa ya dubi
shadila yace komai wuya komai rintsi kada ki fito daga cikin wannan tanti indai kika kiyaye
wannan umarni nawa ni dake duk zamu tsira daga sharrin wadannan yan harin bazati kada ki
kuskura kiyi ihu ko maganar da wani zai jiyoki shadila ta kada kai cikin alamun tsananin
damuwa tace lallai zan kiyaye wannan umarni naka nan take hailur ya sumbaci goshin shadila
sannan ya juya zai fice daga cikin tantin sai tayi wuf ta ruko hannunsa ta rungume shi tana mai
fashewa da kuka ba komai ne ya sa tayi hakan ba face taji a jikinta cewar abune mawuyaci su
sake ganin juna, ba komai ne ya tabbatar mata da hakan ba face ta dan leka wajan tantin daga
tsananin yawan dakarun sumamen da suka kawo musu hari tasan cewa tabbas an shammaci
nasu dakarun ba zasu iya kare kansu ba.
.
Cikin hanzari hailur ya janye jikinsa daga cikin nata ya sake dubanta cikin yanayi mai nuna
yarda dakai yace ki barni kamar yadda kika saba ni nasan dabarar da zanyi na kubutar da
rayuwarki da tawa, shin kin manta ne da cewar irin wannan ta taba faruwa shekaru uku baya sa
adda wata rundunar yan fashi suka ritsamu a daji mu biyu rak nidake muna kiwo? .
Ko dajin wannan batu sai Shadila ta gyada kai cikin murmushin karfin hali tace haba ya
masoyina ai ba zan taba mancewa da wannan gagarumar jarumtaka da kayi ba, koda jin haka
sai fuskar hailur ta fadada da murmushi yace to wannan karon ma abinda zai faru kenan baya
ga wannan ina mai yi miki wani babban albishir cikin matukar mamaki da zakuwa shadila ta
zaro idanu tace wane irin albishir kuma zakayi mini yanzu?
.
Hailur yace boka zaifur ya gaya mini cewa a ranar farko dana sadu dake juna biyu zai shiga don
haka yanzu ina mai tabbatar miki da cewa kina dauke da cikin dana kona mutu a wannan yaki
bani da nadama ko takaici na san cewa na bar wanda zai kula dake.
.
Yayinda shadila taji wannan batu sai hawaye ya zubo mata tace lallai ina son ta kowanne hali
ka rayu a wannan yaki kuma mu tsira tare domin babu abinda na tsana a wannan duniya sama
da dana ya taso maraya. hailur yayi murmushi yace nayi miki alkawari cewar danki ba zai taso a
maraicin rashin uba ba yana gama fadin hakan sai ya juya da sauri ya fice da gudu daga cikin
tantin. Ai kuwa yana fitowa yaga yadda ake ragargazar jama arsu ana saransu da sukarsu suna
ihu jini na tsartuwa fallatsi da malala suna zama gawa sai ya fusata ainun ya kwarara uban ihu
ya zare takobinsa daga cikin kufenta ya afkawa dakarun sumamen ya hausu da sara da suka
ya zame musu guguwar annoba a wannan lokaci hankalin sarki shardas yana kan bayi mata da
ake ta kamawa da kuma dukiyar da ake diba amma ko da yaji ihun dakarunsa ya yawaita a
wani bangare daban sai ya juyo da sauri izuwa wajan take ya hango jarumi Hailur yanata
ragargazar dakarunsa duk inda hailur yasa gabansa sai dai kaga maza na Zubewa kasa tamkar
ana sassabe a gona Al amarin da yayi matukar baiwa sarki shardas mamaki kenan dimin tunda
yake fita sumame da yaki bai taba ganin jarumi mai irin zafin naman hailur ba gami da
tsagwaron jarumtakarsa duk da cewar a wannan lokaci dakarun sarki shardas sun kashe kaso
takwas daga cikin kaso goma na jama ar jarumi hailur sai da ran sarki shardas ya baci ainun
zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone cikin tsananin fishi sarki shardas ya takarkare ya
kwarara wani uban ihu wanda ya firgita komai da kowa dake cikin dajin aka daina yakin aka
tsaya cak tamkar babu abu mai rai a wajen a lokacin da amon ihun sarki shardas ke tayin amsa
kuwa a dajin gaba daya shi kansa jarumi hilairu sai da ya firgita bisa jin wannan kururuwa ya
kura idanu izuwa sashin da kuwar ta fito da yake a sannan ne kurar yakin take lafawa sai da
yan dakiku suka shude sannan ya hango sarki shardas ya tunkaroshi daga can nesa kadan
take zuciyar jarumi hailur ta buga da karfi ya ji tsoro ya darsu a cikin ransa a karon farko a duk
gwagwarmayar da yakeyi da mazaje a rayuwarsa bakomai ne ya haddasa hakan ba face a iya
rayuwar jarumi hailur bai taba ganin mutum mai kirar sadaukai da kwarjininsa ba kamar sarki
Shardas duk da cewar fuskar sarki shardas a rufe take cikin rawani sai da jarumi hailur ya gane
cewa lallai wannan sadaukiba saurayi bane shekarunsa sun kai arba in da 'ya'ya kuma
idanunsa ya kalla kawai ya gane hakan abinka da jarumi mai dakakkiyar zuciya kuma wanda
baya fidda rai ga samun sa a da rabo sai hailur ya gyara tsayuwarsa ya rike takobinsa da
garkuwarsa da kyau koda ganin haka sai sarki shardas yayi murmushin mugunta kawai sai
shima ya zare takobinsa daga cikin kufenta wata irin takobi ce mai tsawo da kaifi kuma anyita
ne da wani irin karfe na musamman wanda sai kwararren makeri ne zai iya gano hakan take
sarki shardas ya falfalo da gudun tsiya izuwa kan jarumi hailu duk sa adda sawun kafafun sa
suka taba kasa sai kaji kamar takun giwa ne saboda nauyinsu.
.
Koda jarumi Hailur ya hango sarki shardas ya rugo izuwa kansa cikin mugun nufi haka sai
shima ya ruga izuwa gareshi duk su biyun suna ihu da karaji yayin da ya rage saura baifi taku
biyar ba su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama yakai wawan hari sarki shardas ya kaiwa
hailur sara a wuya da nufin ya cire masa kai hailur ya kare saran da garkuwarsa take garkuwar
ta rabe gida biyu tamkar an yanka tsakiyar tufa da wuka cikin zafin nama hailur ya kaiwa
shardas suka da takobinsa a ciki shardas yasa garkuwarsa don tare sukan amma duk da haka
sai da takobin ta huda rigarsa ta tsargeta in ba don ma ya kare harin ba cikin zafin nama dasai
takobin ta huda cikinsa koda suka duro kasa sai kowannansu ya cika da mamaki shi dai sarki
shardas bai taba karo da jarumin da ya taba samun nasarar ko da lakutar rigar jikinsa ba amma
yau gashi ya hadu da wanda ma ya tsargeta da takobi shi kuwa jarumi hailur firgita yayi ainun
bisa ganin yadda takobin sarki shardas ta tsarge garkuwarsa gida biyu don haka ya tabbatar da
cewar duk sa adda takobin shardas ta sami jikinsa ba karamar illa zata yi masa ba, nan fa
Hailur ya fara tunanin hanyar da zaibi ya iya kare kansa koda ya dubi garkuwar dake hannun
sarki shardas sai yaga anyi tane da irin karfen da akayi Takobin, cikin sauri hailur ya dubi kaifin
takobinsa sai yaga she har ta dan dakushe a wajen tsininta sakamakon haduwa da tayi da
garkuwar sarki Shardas.
.
Al amarin da ya kara dugunzuma hankalin hailur kenan ya tabbatar da cewar babu wata hanya
da zai iya kare kansa a wajen sarki shardas face ya kwaci garkuwar dake hannunsa yin hakan
kuwa yasan cewa ba karamar sa a bace da nasara.
.
A wannan lokaci gaba dayan dakarun sarki shardas da tsirarun dakarun su hailur da sukayi
saura a wajan sun zuba idanunsu a kansu kawai kowa so yake yaga yadda karshen wannan
gumurzu zai kasance tamkar dacan ba yaki ake ba a wajan su kuwa matan da aka kama
amatsayin bayi aka daddauresu tuni sun fara kuka tare da ya yansu kananan yara wadanda
kusan su duka an kashe iyayansu maza an mai dasu marayu sai da kimanin dakiku dari da arba
in suka shede ana kallon kallo tsakanin sarki shardas da jarumi hailur kowannansu tunanin
dabarar da zaiyi ya cutar da abokin gwaminsa yake sannan suka sake rugawa izuwa kan juna a
karo na biyu suna haduwa asama sai sarki shardas ya kawowa hailur sara a cinya shi kuma
yakai masa sara a ka kowannansu
yayi iya kokarinsa wajan kaucewa harin cikin zafin nama amma sai da takobin sarki shardas ta
yanki hailu ta dara naman cinyar jini yayi tsartuwa hailur ya kwala uban ihu sakamakon tsananin
zafi da zogin da yaji shi kuwa sarki shardas bai ankara ba sai gani yayi hailur ya tuje rawanin
dake kansa ya fado kasa sai ga fuskarsa ta baiyana a fili karara kafin su duro kasa gaba daya
tuni hailur ya doki hannun sarki shardas mai dauke da garkuwa garkuwar ta subuto kasa cikin
bakin zafin nama hailur ya fada kan garkuwar ya sureta kuma yayi 'yardungure sau uku izuwa
can gaba yana mikewa tsaye yayi sauri ya yagi rigar jikinsa ya daure raunin cinyar tasa don
tsaida jini.
.
Shi kuwa sarki shardas ko da yaga tsirarun dakarun su hailur sunyi arba da fuskarshi kuma sun
shaida ko shi wanene sai ya dakawa dakarunsa tsawa yace su karasasu gaba daya take
dakarun suka hau tsirarun dakarun da sara da suka suka karkashesu a cikin 'yan dakiku kadan
koda ganin abinda ya faru sai jarumi hailur ya kurma uban ihu ya ruga izuwa kan sarki shardas
har dakaru sun yunkura zasu tareshi sai sarki shardas ya tsaidasu yace ai wannan nawa ne ba
naku ba kuma abin kunya ne a ce nidaku munyi masa rubdugu ku zuba ido kamar yadda kukayi
da farko kuga yadda zamuyi dashi koda gama fadin hakan sai sarki shardas ya tari jarumi hailur
suka ci gaba da kaiwa juna mugayen hare hare wannan karon dai sarki shardas yana kaiwa
hailur sara da suka ne da dukkan karfinsa cikin azababben zafin nama na gaban kwatance.
.
Kaico mai karfi sai Allah ya isa kuma na gaba yayi gaba na baya sai labari duk da irin tsananin
juriya da jarumtaka irin ta hailur wannan karon sai da ya raina kansa domin bambancin a
baiyane yake kuma sarki shardas ya shammaceshi wajan sauya salon fadan, a lokaci guda ya
hada da kai masa naushi da bugu da hannu da kafa sai gashi nan da nan ya hadawa hailur jini
da majina yana bal dashi kamar tamola...
.
Tab ganin wannan yanayi da hailur ya shiga ya sa ni tsaya wa cak! Da typing ɗin da nake, kuyi
haƙuri bisa jin shiru na wasu kwanaki da kuka jini InSha Allahu zamu ci gaba a gobe idan Allah
ya kafin
TSATSUBA
BOOK 2
PART (E)
Na Abdul'aziz Sani Madakin Gini
Posting By Abubakar Saleh AlQuyraemey
08138873799 For More Littattafan