Showing 1 words to 3000 words out of 12964 words
Chapter 1 - TSATSUBA BOOK 8&9 By Abdulaziz Sani .pdf
TSATSUBA
Littafi Na Tara (9)
Part A
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Abubakar Saleh AlQuyraemey
.
Lokacin da dakarun sarki shardas suka fice daga cikin falon gasar domin cika umarnin da yayi
musu na zuwa bayan gari su dauko masa matar attajiri amsar bayan sun kashe dakarun dake
tsaron lafiyarta. Kawai sai sarki shardas ya tsugunna a gaban attajiri amsar wanda har a
sannan bai daina kakarin mutuwa ba ya tallafo keyarsa da hannu guda ya dubeshi yace ta yaya
kake tsammanin cewa zan barka ka rayu alhalin kafi ni kudi kuma kana da kyakkyawar matar
da bani da kamarta kuma kana da karfin sihirin tsafi na ban mamaki ta yaya zan barka ka lashe
wannan gagarumar gasa ka barni da abin kunya ?
.
To ka sani cewa komai sammakonka wani a tafe ya kwana, tun daga lokacin da akayi shelar
wannan gasa nasa bokana ya shiga bincike akan sirrinka, don haka da gayya na gayyaceka
izuwa wannan gasa domin naga bayanka sai a jiya ne bokan nawa ya gano cewa gaba daya
tasirin sihirinka na tsafi yana jikin kwagirin da kake rikewa a hannunka in ba don na fisgeshi
daga hannunka ba da ba zan taba iya kashe ka ba kaga kenan yanzu mutuwa zaka yi na gaje
duk dukiyar nan da ka zo da ita kuma na gaji wannan kyakkyawar mata taka, Bani da wani buri
a doron kasa wanda ya fi na ajiye tarihin da babu wani sarki ko wani boka ko jarumin da ya
ajiyeshi, gama fadin hakan keda wuya sai attajiri amsar ya yunkura cikin karfin hali ya cakumi
kwalar rigar sarki shardas ya budi baki da kyar cikin murmushin karfin hali yace tabbas ka sami
nasarar hallakani to amma ka sani matata tana da kariyar dani kaina bani da ita don haka ina
tabbatar maka da cewar har abada bazaka mallaketa ba sannan kuma matata tana dauke da
juna biyu tsawon wata biyar duk abinda ta haifa namiji ko mace sune zasu dauki fansar raina a
hannunka bakin azzalumi.
.
Koda gama fadin hakan sai idanun Attajiri amsar suka kafe gaba dayan jikinsa ya sandare ya
zama gawa koda ganin haka sai sarki shardas ya kurma uban ihu wanda ya razana kowa dake
cikin dakin gasar kawai sai ya zare takobinsa ya dubi wazirinsa ya damka masa kubar gidan
darul daulat yace kowa ya fita ka kullue mini gidana, yanzu zan tafi izuwa can bayan gari na
gani ko dakaruna sun cika aikinsu yana gama fadin hakan ya juya ya cife daga cikin gidan da
gudu ya shiga jirgin ruwa aka ketare kogin dashi yana isa bakin gabar kogin ya fito daga cikin
jirgin ruwan ya sake hawa doki ya zabureshi da gudu ya nufi hanyar bayan gari da karfin sihirin
tsafi sarki shardas ya shafe tafiyar kwana uku a cikin yini guda kacal amma kuma yana isa inda
su matar attajiri amsar suka yada sansani bai iske komai ba sai gawarwakin dakarunsa dana
attajiri amsar gaba dayansu babu wanda ya tsira da rayuwarsa, ga keken dokin da matar attajiri
amsar ke ciki amma babu ita babu alamarta, nan fa sarki shardas ya dimauce kuma ya haukace
yayi ta neman mahaifiyata a cikin daji yana ihu yana kwallah mata kira amma shiru kamar maye
yaci shirwa bisa dole ya hakura ya juya ya koma birninsa cikin tsananin bakin ciki da takaici.
.
Lokacin da yarinya Rulaiya tazo dai dai nan a labarinda take baiwa yarima hulkas sai tayi shiru
ga barin zancenta a lokacin da hawaye ya zubo mata, cikin kaduwa da zumudi yarima hulkas ya
dubeta yace to daga nan kuma menene ya faru ga mahaifiyarki shin guduwa tayi sa adda
dakarun sarki shardas suka kawo musu hari, koda jin wannan tambaya sai yarinya rulaiya tasa
hannu ta share hawayanta sannan tace mahaifiyata
ba gudu tayi ba ta bani labarin cewa agaban idanunka aka fafata KAZAMIN YAKI tsakanin
dakarun sarki shardas dana mijinta masu tsaron lafiyarta kuma gaba dayansu sai suka yi
RAGAS Faruwar hakan keda wuya sai taji jiri ya fara dibarta daga can kuma sai ta yanke jiki ta
fadi kasa sumammiya lokacin da mahaifiyata ta farfado daga suman da tayi ne sai ta tsinci
kanta a cikin wannan gida kwance a kas a gaban wani Aljani ma abocin kwarjini da ko a labari
bata taba jin kamarsa ba.
.
Ba tare da aljanin ya gabatar da kansa a gareta ba ya dubeta a lokacin da gaba dayan jikinta
yake karkarwa saboda firgita da ganinsa yace ki kwantar da hankalinki ya ke matar sarkin
attajiran duniya kiyi sani cewa babu mai cutar dake anan iya tsawon rayuwarki, domin na
daukarwa mijinki wannan alkawari anan ne kadai zaki iya tsira daga sharrin abokan gabar
mijinki irin sarki shardas.
.
Koda jin wannan batu sai zuciyar mahaifiyata ta buga da karfi ta dafe kirjinta da hannayanta
biyu sannan ta dubi aljanin tace ina labarin masoyina amsar shin an gama wannan ga sa ne ta
siyan gidan darul daulat ? Maimakon aljanin ya bata amsar wannan tambaya sai yayi nuni da
hannunsa izuwa ga jikin bango take hoton duk abinda ya faru a dakin gasar ya bayyana tun
daga ranar farko har izuwa zagaye na karshen gasar.
.
Koda mahaifiyata taga sarki shardas ya kashe mijinta sai ta kwalla uban ihu ta sake sulalewa
kasa sumammiya wannan shine asalin sanadin da ya sa mahaifiyata ta kamu da cutar ciwon
zuciya kuma ciwon ne ya zamo.sanadin ajalinta bayan haihuwata da shekara shida. Bayan
mutuwarta ne wannan aljani ya cigaba da kula da ni kuma ya zamana cewa kullum yana koya
mini yaki yana mai cewa nan gaba zan dauki fansa akan makiyina sarki shardas da ya kashe
min mahaifina amma ba ba sai idan lokacin yayi, lokacin da ban sani ba ke nan har kawo i
yanzu gashi gaba dayan rayuwata ta kasance a cikin kadaici in ban da uwata da kuma wannan
aljani da ya cigaba da kula dani
kaine mahaluki na uku da na gani a gaba dayan fadin wannan duniyar, koda yarinya rulaiya
tazo nan a labarinta sai ta fashe da matsanancin kuka,
.
Al amarin da ya sa yarima hulkas yaji ya kamu da tsananin tausayinta kenan gami da matukar
kaunarta fiye da ko yaushe, don haka bai san sa adda shima idanunsa suka kama zubar da
hawaye ba, tsawon yan dakiku dayansu baice uffan ba daga can sai ya dubeta cikin nutsuwa
yace yake rulaiya ai labarina da naki duk kusan iri daya ne kuma abokin gabarmu guda ne, nan
take yarima hulkas ya zaiyane mata tun daga farko har karshe da yadda akayi ma ya tsinci
kansa a wannan gida nata da kuma shirin da suke yi na tafiya neman hular lamsara don daukar
fansa akan sarki shardas.
.
koda rulaiya taji wannan labari sai ta kamu da tsananin Al'ajabi sannan tayi shiru tana tunani da
nazari daga can sai ta dago kai ta dubi yarima hulkas tace duk yadda akayi aljanin da ya ceci
rayuwar mahaifiyata ya kawota nan kuma ya koya mini yaki shine ya daukoka ya kawoka nan
lallai akwai wata manufa a cikin hadamu da yayi tunda duk burinmu iri guda ne, kash ! .
Zanso ace nima zanga yadda karshen gasar fadan yar uwarka jaruma siyama zai kasance da
sadauki Darkus kuma zanso ace tare dani za ayi wannan gagarumar tafiya ta neman HULAR
LAMSARA.
.
Kafin Rulaiya ta gama rufe bakinta sai kawai sukaga aljani Arwasul masadul ya bayyana
tsuluum ! A gabansu yana mai kyalkyala dariyar farin ciki kawai sai ya dubesu duk su biyun
cikin murmushi yace tabbas na gama cika aikina yanzu zan doraku akan tafarki na karshe
wanda zaku dauki fansa kamar yadda na yiwa iyayenku alkawari daga nan zaku tafi izuwa can
birnin sarki hulbasu tare kuma gobene za ayi wannan gasar ta karshe ke rulaiya ki boye fuskarki
ga kowa kuma ki zamo mai taimakon su hulkas bisa duk abinda yazo musu zan baku wani
tsuntsu wanda zai yi muku jagora izuwa inda hular lamsara take
ku sani cewa yanzu haka makiyanku sarki shardas tare da bokansa basu da burin da yafi su
hadu dani domin na sanar dasu inda hular lamsara take amma wannan damar tuni ta wucesu
ina mai gargadinku da ku kula sosai da wannan tsuntsu
da zan hadaku dashi domin ko yaya ku kayi sakaci ya subuce muku to fa zai koma hannun su
sarki shardas ne ya kai su izuwa inda hular Lamsara take idan kuwa sarki shardas ya rigaku
taba hular lamsara to dayanku ba zai tsira da rayuwarsa ba bare ma ya dauki fansa akansa.
.
Koda gama fadin wannan jawabi sai Aljani Arwasul masadul ya bude tafin hannunsa ya lumshe
idanunsa yana mai karanta wadansu dalasiman tsafi faruwar hakan keda wuya ai ga wani farin
tsuntsu dan karami wanda baifi girman kanari ba ya baiyana akan tafin hannun nasa gwanin
ban sha awa, kawai sai ya mikawa yarima hulkas tsuntsun yace kaine ka cancanci rike wannan
tsuntsu saboda kai kadai ne ka haye jarrabawata a duniya kai yakamata ka mallaki hular
lamsara amma zanyi maka gargadi guda daya Gargadin kuwa shine duk abinda zaka so to ka
soshi SAISA SAISA idan kuwa ka zurma a cikin soyayyarsa tabbas wannan abu shine
Ajalinka, da wannan furuci nake yi muku bankwana na karshe har abada ba zamu sake haduwa
daku ba ina mai yi muku fatan samun nasara akan babban makiyinku amma fa ku sani cewa
aikin dake gabanku ya wuce yadda duk kuke zatonsa dole ne ku fuskanci BARAK WUYA da
hadarurrukan da ba lallai ba ku kaiga gaci.
.
Aljani Arwasul Masadul na gama fadin hakan sai ya bace bat ! Tamkar bai taba wanzuwa ba a
wajan, cikin rudewa yarima hulkas ya dubi yarinya Rulaiya yace saboda me wannan aljani zai
tafi ya barmu ba tare da ya gaya mana yadda zamu iya kai kanmu can birnin sarki hulbasu ba
da kuma yadda yakamata mu tafiyar da komai a cikin wannan gagarumar tafiya dake gabanmu. .
Koda jin wannan batu sai rulaiya tayi murmushi sannan tace lallai kai so kake ma ka sami komai
kenan a bati ?
To ka sani cewa ba a zama wane a banza kuma sai ansha bakar
wuya sannan ake shan dadi barina kimtsa sannan mu tafi ka jirani anan kada kayi karambanin
zuwa ko ina ko taba wani abu a cikin dakin nan muddin bana kusa Rulaiya na gama fadin haka
sai ta juya ta nufi cikin wani daki ta shige cikinsa ta rufe kofa.
.
Shi kuwa yarima hulkas sai ya kara kamuwa da tsananin mamaki yace a cikin ransa ' to wai
shin menene a cikin wannan gidan mai hadari wanda har rulaiya zata gargadeni da kada in
Tabashi ?
.
Ai kuwa matsoraci baya zama gwani don haka bari na yawata a cikin gidan nan na morewa
idanuna kallo Gama ayyana hakan keda wuya sai yarima hulkas ya kama yawo a cikin gidan ya
nufi
wani bangare daban yana kalle kalle yana mamakin irin yadda ginin gidan da kuma kayan
alatun da aka zuba acikinsa nan take wani tunani ya fado masa a cikin zuciyarsa yace ni kuwa
bayan mun sami nasarar kashe sarki shardas sai na shiga cikin gidan darul daulat na gani
tsakaninsa da wannan gida nasu rulaiya wanne yafi girma da kawatuwa a cikinsa. .
Koda yarima hulkas yazo nan a zancen zucinsa sai zuciyarsa ta buga da karfi tsoro ya kamashi
ya tambayi kansa yace 'saboda me zan bar wa rulaiya wannan gida da dumbin dukiyar dake
cikinta data kasance dukiya mai tsananin yawa alhalin yane ranar farko dana fara ganinta a
rayuwata shin wannan yana nufin ke nan na kamu da tsananin sonta fiye da yadda ma nake
son iyayena da yar uwata siyama tunda gashi zan mallaka mata abinda su ban mallaka musu
ba ai kuwa idan hakan ne maganar Aljani Arwasul masadul ce zata tabbata gaskiya, wato zan
hallaka a dalilin soyayya kai ! Ba zai yuwu ba dole ne na takawa wannan soyayya birki komai
zai faru gareni sai dai ya faru !!
.
Yarima hulkas na cikin yin wannan tunani ne yaga wata kofar daki ta bakin karfe wacce gaba
dayanta a lullube take da yanah
a kura tamkar ma ba a taba bude ta ba, kawai sai yarima hulkas ya tunkari wannan kofa da
zuwansa daf da ita ya sa hannu ya murda marukinta bisa mamaki sai yaga kofar ta bude ba
tare da shakkar komai ba ya kunna kai cikin dakin koda yayi taku uku a cikin dakin sai yaji kofar
dakin ta kulle kanta cikin sauri ya koma da baya ya kama kofar da nufin ya bude amma sai kofar
taki buduwa sai da yayi iya karfinsa har ya jike sharkaf da gumi amma ya kasa bude kofar.
.
Koda ganin haka sai ya saduda ya juya ya sake nausawa cikin dakin ba komai a cikin dakin
face tarin gumaka na dakarun yaki
fululu babu adadi sai dai kowanne badakare yanayin shigarsa daban da dan uwansa kuma
makamin yakinsa ma daban, gaba dayan wadannan dakarun yaki suna da siffa ta kwarjini da
ban tsoro duk kuwa da cewa gumaka ne komai jarumtakar mutum da dakewar zuciyarsa sai ya
firgita da ganinsu saboda gani zaiyi tamkar masu raine ba gumaka ba nan fa uarima hulkas ya
cigaba da ratsawa ta tsakiyar gumakan dakarun domin ya isa karshensu, sai da ya yi yar
doguwar tafiya sannan ya iso karshen dakim, nan take yayi arba da abinda yai matukar daure
masa kai, ba komai ya gani ba face tarin dukiya mai tsananin yawa tsubi tsubi zube a kasa ta lu
u lu u zinare da yakutu wacce inda za a yi aikin kwasheta da magalar rakuma sai an shafe a
kalla kwanaki dari ana dibarta bata kare ba.
.
Koda yarima hulkas ya dubi jikin bangon dake gaban wannan dukiya sai yaga anyi rubutu
kamar Haka '- WANNAN DUKIYA HARAMTACCIYACE GA KOWANNE MAHALUKI, BABU
WANDA YA ISA YA DAUKO KODA KWAYAR ZARRA A CIKINTA HAR YA FITA DA ITA DAGA
CIKIN WANNAN DAKI !! .
Sa adda yarima hulkas ya gama karanta wannan jawabi sai ya bushe da dariya yace ka ji wani
zancen banza kuma ya ma za ayi ace wai ba zan iya daukar koda kwayar zinare daya ba
alhalin babu mai gadin wannan dukiya a cikin wannan daki face wadannan gumakan banza ??
.
Gama fadin hakan ke da wuya sai yarima hulkas ya luma hannunsa a cikin tarin lu'u lu'un ya
duntso cikin hannunsa ya zuba a cikin Aljihunsa, koda ya juyo da nufin ya koma da baya can
inda kofar dakin take sai kawai yaga gaba dayan wadannan gumaka na dakarun yaki sun yi
girgiza sun zama rayayyu suna karkade kurar jikinsu gami da zare makaman yakinsu kuma
gaba dayansu sai suka durfafo inda yake.
.
Cikin firgita yarima hulkas ya daka tsalle bay a dai dai lokacin da daya daga cikin su ya kawo
masa wawan sara da wani katon barandami, koda yarima hulkas ya goce barandamin ya sari
wata dirkar gini mai kaurin gaske sai dirkar ta rabe gida biyu ta fadi kasa saboda karfin saran
da kuma kaifin barandamin. .
Al amarin da ya kara razana yarima hulkas kenan babu shiri ya zare takobinsa ya tari dakarun
aka ruguntsume da AZABABBEN YAKI......
To nima dai AlQuyraemey ganin wannan azababben yakin da
ake fafatawa yasani dakatawa a wannan waje saboda haka sai kuma Allah ya kaimu wani
lokacin sannan zan cigaba daga inda na tsaya.
TSATSUBA
Littafi Na Tara (9)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Abubakar Saleh AlQuyraemey
.
.
Al amarin Da ya kara razana yarima hulkas kenan babu shiri ya zare takobinsa ya tari dakarun
aka ruguntsume da azababben yaki, hakika masu iya magana sunyi gaskiya da sukace
tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka nan fa dakarun yakin suka kuntata yarima hulkas suka
rinka kai masa SARA DA SUKA ta ko ina ya zamana cewa da kyar yake iya kare kansa idan ba
don ma yana da zafin nama ba da tuni sunyi gunduwa gunduwa da sassan jikinsa, nan take ya
raina kansa nadama tazo masa bisa gangancin da yayi ya taba wannan dukiya alhalin an
gargadeshi, cikin kankanin lokaci dakarun suka yiwa yarima hulkas rauni har guda biyar a
jikinsa ya zamana cewa jini na zubar masa kuma jiri
ya fara dibarsa amma saboda jarumtaka da juriya da mugun naci yaki yarda yaje kasa, a haka
ya cigaba da maida martanin sara da sukan da suke kawo masa yana kare miyagun hare
harensu kokarinsa shine ya kutsa ta tsakiyarsu ya isa can inda kofar dakin take ya sake jarraba
budeta amma sai abun ya gagara, Ana cikin wannan bakin gumurzu ne daya daga cikin
dakarun ya shammaci yarima hulkas ya gabza masa wawan naushi a kasan habarsa saboda
karfin naushin sai da yarima hulkas yayi sama ya gwaru da rufin dakin jini yayi feshi daaga cikin
hancinsa da bakinsa ya fado kasa tIm magashiyan, ai kuwa sai dakarun suka yunkura da nufin
su gididdibashi, kwatsam ! Sai suka ji an doki kofar dakin ta balle daga jikin garu ta fado kansu
sama suna juyowa suka ga ashe Rulaiya ce ta dako tsalle sama izuwa tsakiyarsu tayi wata irin
katantanwa ta tarwatsasu da saran takubban hannayanta biyu kafin su sake taso mata ta dira a
gaban yarima hulkas wanda ke kwance magashiyan kawai sai ta kama kafarsa da hannu daya
ta dagashi sama ta zazzage su, nan take duk lu'u lu un da yarima hulkas ya diba ya zuba a cikin
Aljihunsa ya zubo kasa faruwar hakan keda wuya sai gaba dayan dakarun yakin suka kame
suka koma gumakansu tamkar
basu taba motsawa ba.
.
A sannanne Rulaiya ta sunkuya ta dauki yarima hulkas ta sabashi a kafadarta ta fice daga cikin
dakin ta kaishi can turakarta ta shiga dinke raunikan dake jikinsa cikin gaggawa don ceto
rayuwarsa, jaruma rulaiya na cikin yiwa yarima hulkas dinkine a raunikansa kawai sai